jikin mai shan taba · wadanda suke shan taba kara daya a kowace rana sunadada kimanin rabin...

1
BUGAWAR ZUCIYA, SHANYEWAR SASSAN JIKI DA KUMA SAURAN NAU’IKAN CUTUTTUKAN ZUCIYA Kusan duk ɗaya daga cikin mutawar mutane uku a duniya ana danganta ta ne dacutar cututtukan zuciya. Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa sune ke bayar da gudummawa wajen haifar da larurar ciwon zuciya ga kimanin mutane miliyan uku a duniya a kowace shekara. Masu shan taba na da ninki biyu na hadarin bugun zuciya da kuma ninki hudu na karuwar hadarin kamuwa da cututtukan zuciya. Shakar hayakin taba na lalata manyan hanyoyin jini na zuciya, wanda kan zaunar da datti a hanyoyin jini, hakan ya kan sa jini ya daskare, daga nan kuma ya hana gudanar jinin (1) daga nan kuma ya sa zuciya ta buga (2) . Rashin samun gudanar jini, idan ba a yi maganin ta ba, kan haifar da mutuwar wasu sassan jikin dan adam, wato bushewa kamar konewa – gangrene (3) wanda kuma ya kan sa lallai sai an yanke wuraren da abin ya shafa (4) . Bugawar zuciya, kamar sauran cututtukan zuciya na da mummunanhadarin wanda kan kai ga mutuwa, kuma waɗanda suka sami warka daga bugun jinin na iya fuskantar matsalolin da za su lalata jiki, irin su shanyewar jiki ko rashin iya hangen nesa ko magana. Shan taba yana da illa, ko yaya yawan shan tabar yake. Wadanda suke shan taba kara daya a kowace rana sunadada kimanin rabin hadarin da masu shan taba kara ashirin kowace rana keda shi wajen kamuwa da cututtukan zuciya da kuma bugun jini. Duk da haka, ba wai shan taba ko shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa ba ne ke kara yawan hadarin kamuwa da cututtukan zuciya ba. Yin amfani da kayan da a ka yi da taba ba ba na konawa baa yana kara haɗarin mutuwa saboda ciwon zuciya ko bugun jini. CUTUTTUKAN DA DUKKANIN KAYAYYAKIN TABA KE JAWOWA CIWON DAJI NA HUHU Masu shan taba na iya kamuwa da ciwon daji na huhu (9) har sau ashirin da biyu fiye da wadanda basu taba shan taba ba. Shan taba shine babban dalilin kamuwa da ciwon daji na huhu, wanda ya kan haddasa kashi biyu bisa uku na mutuwa sakamakon ciwon huhu a duniya, wannan kuma yana shafar kimanin mutane miliyan daya da dari biyu a kowace shekara. Wadanda ba su taba shan taba ba, amma kuma suna shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a gida ko a wurin aiki suna cikin hadarin samun ciwon daji na huhu. TOSHEWAR MANYAN HANYOYIN JINI MASU KAIWA GA HUHU A duk mutum biyar da ke shan taba mutum ɗaya na iya samun matsananciyar cutar toshewar manyan hanyoyin jini masu kaiwa ga huhu (COPD) (10) a rayuwar sa, musamman ma mutanen da suka fara shan taba a lokacin yarinta da shekarunsu basu wuce ashirin ba, tun da yake hayakin na taba na jinkirta girma da ci gaban lafiyar jiki. Masu shan taba sun fi sauƙin kamuwa da cutar toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya har sau uku zuwa hudu. Shan taba yana haifar da kumburi da fashewar jakar iska a cikin huhu wanda ya kan rage karfin shakar iskar ‘oxygen’ da kuma damar fitar da iskar ‘carbon dioxide’. Har ila yau, yana haifar da zaunewar majina wadda kuma kan sa tari mai zafi da kuma wahalar numfashi. Mutanen da su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa tun suna yara har suka girma suna da yawan kamuwa da cututtuka a hanyoyin numfashin su,a sakamakon haka kuma suna cikin hadarin samun toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya (COPD). CUTAR ‘ASTHMA’ An san cewa shan taba na tayar da ciwon asthma ga mutanen da suka manyanta, wanda yakan ƙuntata musu, da kuma karawa rashin lafiya tsanani da kuma kara haɗarin cutar wanda yake buƙatar kulawa ta gaggawa. Yara‘yan makaranta da iyayen su ke shan taba suna da haɗarin shakar hayakin tabawanda ke zama musabbabin faruwar cutar asthma da kuma tsananin ciwon kumburi a hanyoyi da ke isar da iska zuwa ga huhu. CUTUTTUKAN DA A KE SAMU DAGA HAYAKIN TABA Dukkan kayayyakin taba suna da illa, kuma babu wani matakin da zai iya nunawa rashin lahanin taba. Shan hayakin taba shi ne mafi yawadaga cikin hanyoyinamfani da taba a duniya baki daya. Sauran kayayyakin cin taba sun hada da taba gari, da ganyes, da anguru, da sauransu wadanda a ke sanyawa a lofe da shishaa shata bututun ruwa, da sauran kayayyakin taba na zamani. CIWON DAJI NA BAKI DA KUMA SAURAN CUTUTTUKAN BAKI Yin amfani da taba (ta hanyar shan hayakin ta ko wani nau’i na tabar) yana zama dalilin kamuwa da cututtukan baki da yawa. Dukkanin nau’ikan tabar su kan zama sanadin samun ciwon daji na baki (5) . A kasashe da yawa, da wuya a rayu sama da shekaru biyar bayan gano cutar daji a baki. Wadanda ke warkewa daga ciwon daji na baki sukan sami lahani a fuska da kasa yin magana, ko haɗiya ko tauna wani abu. Yin amfani da taba yana kara haɗarin cutar dasashi, waccedasashi ke kumburasannan ya dauke ya kai ga kashin mukamuki har ya haifar da asarar hakori (6) . SShan taba da kuma amfani da kayan taba ba yana jirkita yanayin sinadaran da baki ke dauke da su, wanda ke sa makalewar bakin datti da sa hakora rawaya da kuma haddasa mummunan numfashi. CIWON DAJIN MAƘOGARO Amfani da kayan taba tare da shan hayakin taba bayana kara haɗarin Ciwon daji na ka da wuya, wannan ya hada da lebe da kuma cikin baki. Cire ciwon na buƙatar aiki na musamman (7) , yadda za a huda rami a wuya yadda za a sami damar yin numfashi.Yin amfani da hasken na’ura wajen kawar da ciwon yana da illa kwarai wajen lalata harshe har ya kasha dandano, da rage yawan gudanar yawun baki da kuma kara samar da majina a makogoro, wanda zai sa ciwo da kuma wahala wajen cin abinci. SAURAN CUTUTTUKAN DAJI Yin amfani da taba ya kan haifar da cututtukan daji fiye da nau’iuka goma. A duk lokacin da a ka shaki hayakin taba, akwai sinadarai masu guba da a ke kaiwa ga jiki. Daga yawancin sinadaranna taba, akalla nau’ika saba’in an gano sunahaddasa cutar daji. Masu shan taba suna cikin haɗari mafi girma na samun cutar sankarar bargon kashi; da ciwon daji na hanci da kuma na sauran sassan cikin hanci (8a); da hanji (8b), da koda (8c), da hanta, da matsarmama (8d), da ciki (8e) ko kuma ciwon daji na halittar da ke fitar da kwayayen haihuwa na mata; da kuma ciwon daji na hanyoyin fitsari (ciki har da mafitsara, da kuma sauran jijiyoyin bangaren). Binciken da aka yi kwanan nan sun nuna alakar shan taba da kuma karuwar hadarin samun ciwon daji na nono (8f), musamman ma mata masu shan taba da suka fara shan taba kafin su fara daukar ciki. Haka kuma shan taba na kara hadarin samun ciwon daji na mahaifaga matan (8g) da ke fama da cutar da kananan kwayoyin cututtuka ke haifarwa. Haɗarin waɗannan cututtuka na yawan ƙaruwa ne tare da yawan tabar da kuma tsawon lokacin da a ka yi a na sha, saboda tsawon lokaci a na shan taba na sa jiki kamuwa da sinadarai masu guba. Shan taba mara hayaki na dauke da kwayoyin cuta har 28 wanda ke haifar da ciwon daji na cikin baki da makogoro da kuma matsarmama. Ci gaba da yin amfani da taba bayan an ganociwon daji yana kara tsananta cutar, saboda da hayakintaba na iya canza kwayar halitta, wanda zai iya kara girman ciwon dajin; da kawo tangarda ga maganin ciwon daji; da kuma ƙara yawan matsalolin maganin. MUTUWAR DAN TAYIN CIKI Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin taba a lokacin daukar ciki na ƙara haɗarin mutuwar dan tayin ciki. Mata da suke shan taba ko kuma ke shakar hayaƙin taba lokacin da suke renon ciki suna cikin haɗarin zubewar cikin. Zubewar ciki (haihuwar tayin da ya mutu a cikin mahaifa) na faruwa a lokuta da yawa a sakamakon rashin isasshiyar ‘oxygen’ da rashin dai-daiton mahaifa wanda iskar ‘carbon monoxide’ke haifarwa daga hayakin taba da sinadarin ‘nicotine’dake cikin taba. Masu shan taba suna cikin haɗarinsamun ciki a wajen mahaifa, mai mummunan haɗari ga mahaifiya, a nan yayin da ta ke reon cikin ya kan makale a wajen mahaifa. Saboda da haka, daina shan taba da kuma samun kariya daga shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa yana da mahimmanci ga mata masu haifuwa, ko kuma masu shirin daukai ciki da kuma yayin renon cikin. HANA GIRMAN DAN TAYIN DA KE CIKI. DA HAIHUWAR DA MARA CIKAKKEN NAUYI DA HAIHUWAR DAN DA BAI CIKA WATA TARA BA Duk wani nau’i na amfani da taba ko kuma shiga cikin hayakin taba yayinrenon ciki zai iya zama abu mai illa ga lafiya da kuma girman dan tayin yaron da ke ciki. Yaran da aka haifa ga matan da suke shan taba, ko yin amfani da taba gari, ko kuma su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a lokacin da suke renon ciki suna da haɗarin haihuwar bakwaini da kuma haihuwar yaron da nauyin sa bai cika ba. Yaran da aka haife su a bakwaini da kuma wadanda nauyin su bai cika ba na iya samun matsalolin rashi lafiyana tsawon rayuwar su, ciki har da samun cututtuka masu tsanani bayan sun girma. KARANCIN TUNANI/MANTUWA Shan taba abu ne mai haɗarin lalata kwakwalwa, wanda wani rukuni na cututtuka ne wanda kan haifar da karancin tunanin mutum wanda kuma bashi da magani tabbatacce a halin yanzu. Karancin tunanin abu ne da ya ke habaka, ya kan shafi ƙwaƙwalwar mutum, da halayyar mutum da kuma ƙwarewa da tsayawa ga ayyukan yau da kullum. Baya ga abin da wannan ciwo ke haifarwa wajen hana mutum zarafin aiyuka, cutar zata iya zama mai nauyi kwarai ga iyali ko masu kulawa da mai cutar. Cutar ‘Alzheimer’mafi yawa a cikin irin wannan cututtuka, kuma an kiyasta kimanin kashi goma sha huhu (14) cikin dari (100) na cutar a duniya na da alaka da shan taba. RAUNIN MAZAKUTA Shan taba yana hanaisasshen jini zuwa azzakari, wanda zai iya haifar da rashin ƙarfin mazakuta (rashin yiwuwar mikewar azzakari). Raunin mazakutayafi yawa a cikin mashaya taba kuma mai yiwuwa ya ci gaba ko zama dindindin sai dai idan mutumin ya daina shan taba a farkon rayuwarsa. MUTUWAR JARIRAI FARAT-DAYA Mutuwar jarirai farat-daya (SIDS) ita ce mai faruwa kwatsam, ba tare da wani dalili da a ke iya gani baga yara‘yan kasa da shekara 1. An san cewa shan taba yayin goyon ciki naƙara haɗarin mutuwar farat-daya ga yara, kuma haɗarin ya kan ƙara karuwa tare da bin ‘ya’yan da suka Haifa,kuma suka ci gaba da shan taba bayan haihuwar. JININ HAILA/WATA DA YANKEWAR HAIHUWA Mata masu shan taba zasu iya jinin haila/wata mai ciwo da zafi da kuma samunalamomin yankewar haihuwa. Yankewar haihuwa kan faru cikin shekara daya (1) zuwa hudu (4) ga mata masu shan taba, kasa da lokacin da a ka sani saboda shan taba yana rage damar samar da kwan haihuwana mace, wanda ya kan haifar da rashin samun damar haihuwa da kuma karancin rowan halittar ‘estrogen’. HAIHUWAR YARA MASU LAHANIN HALITTA Shan taba na iya lalata kwayar halittatare da lalata kwayar halitta ta gado (DNA), wanda kan haifar da lahani ga halit- tar jariri. A wasu binciken ilimi angano cewa mutanen da suke shan taba suna da haɗarin haihuwar yaron\ wanda ke iya kamuwa da ciwon daji. Shan taba ga mace a farkon lokacin da ta ke renon ciki na ƙara da hadarin haihuwar jariri mai yankakken lebe ko baki. An kuma lura cewa mutanen da iyayensu suka sha taba a lokacin renonciki suna da ƙarancin yawan kwayar halitta fiye da maza waɗanda iyayensu ba su taba shan taba ba. RASHIN GANI Shan taba yana haifar da cututtukan ido da yawa, waɗanda idan ba a yi maganin su ba, za su iya haifar da rashin iya hangen nesa. Masu shan taba suna da alaƙa da lalacewar ‘macular’ fiye da wadanda ba su taba shan taba ba, wanda yanayine da zai haifar da rashin hangen nesa. Lalacewar ‘macular’ ya kan shafi yawancin mutane,ya hana karatu, ko tukin mota, da gane fuskoki da launuka da kuma ganin abubuwa yadda su ke. Har ila yau masu shan taba suna da haɗarin samun cutar yanar ido wanda ke kare haske ko gani. Yanar ido (11) na iya haifar da rashin hangen nesa, kuma yin tiyata ne kawai zaɓi don mayar da gani yadda yake. Sababbin hujjoji sun nuna cewa shan taba yana haifar da hawan jinin ido, yanayin da zai kara yawan matsina lamba a idanu kuma zai iya lalata gani. Shan taba na sa radadi a idanu da kuma kara zafin cututtukan idanuga masu shan taba da masu shakar hayaƙinda masu shan tabe ke fitarwa, musamman ma a tsakanin waɗanda suke ɗauketubaran gani na cikin ido. RASHIN JI/KURUMCEWA Iyayen da su ke shan taba kan samu yara ‘yan kasa da shekaru biyu masu fama da ciwon kunne wanda ruwa ke zuba daga cikin kunne, Sakamakon shakar hayakin tabar da iyayen su ke sha a gida. Matsanancin ciwon kunne (tsakiyar kunne) ga yara shine dalilin da ya kan sa a sami bebantaka (12) da kurumta. Manyan mutane masu shan taba sun fi fama da rashin ji saboda tsawon lokacin da su ka yi suna shan taba na hana zagayawar jini cikin kunne. Rashin magance ciwon rashin ji ko kurumtana iya tasiri a zamantakewar jama’a, da tunani da kuma tattalin arziki. RAUNIN KASHI Iskar ‘Carbon monoxide’ da ke cikin hayakin taba, babbar guba ce irin wacce a ke samu a hayakin mota, ta kan danfarazuwa ga ‘hemoglobin’na cikin jini cikin sauƙi fiye da iskar ‘oxygen’ da jiki ke bukata, don haka sai ta rage zuwan iskar oxygen zuwa jikin mutum. Masu shan taba sun fi saukin samun raunin kashi, yadda karfin kashin ke raguwa da sauƙin karyewa.Idankuma suka fuskanci matsalolin a kashi,akwai jinjiri ko rashinsamun nasarar warkewa. LALACEWAR FATAR JIKI Shan taba na kara yawan hadarin samun cututtukan fata na‘psoriasis’ (13), wanda wani mummunan yanayine da ke sa kumburi da dashewar fatata dashe ya bar wani ja a dukkanin jiki. Shan taba yana sa fata ta tsufa da wuri wajen sa sinadarai wanda su ke ba fata da laushi suragutare da daukewar ‘vitamin A’ da kuma hana zagayawar jini. Don haka masu shan taba suna iya samun bushewar fata (14), bayan nan kuma ta yankwane, musamman a kusa da lebe da idanu. RAUNANA GARKUWA JIKI Sinadaran da suke cikin hayakin taba na raunana tsarin garkuwar jiki, su sa masu shan taba cikin hadarin kamuwa da cutar huhu. Bugu da ƙari, masu shan taba suna tattare da yiwuwar cewa kwayoyin halittar suna iya samun cututtuka dare da haɗarin samun ƙwayar cututtuka da dama, ciki har da cututtukan zuciya, cututtukan kurga, da kwayoyin cuta, da cututtukan daji. Shan taba yana sanya garkuwar jikin mutum ta raunana, kamar irin wadanda ke da ciwon kwan- tacce’, ko wani nau’i na ciwon daji, da kuma mafi girman hadarin cututtuka daban-daban. Illar shan taba ga garkuwar jiki na sanya mutanen da ke da kwayar cutar HIV su kara yawan haɗarin fadawa matakin cutar AIDS. Haka kuma masu shan taba kuma suna dauke da kwayar cutar HIV, yawancitsawon rayuwasu da cutar baya wuce shekaru goma sha biyu da digo uku (12.3), kusan yana jawo rasa rai daga cutar HIV har rubi fiye da biyu na kasa da yawan shekarun da kwayoyin cutar ta HIV kan zauna a jikin mutum kafin mutuwa. CIWON SUKARI NA BIYU (2) Hadarin kamuwa da ciwon sukari ya fi yawa a tsakanin masu shan taba, kuma wannan hadarin ya kan karu da yawan shan taba sigarin da akesha a kowacce rana. Shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa ma yana tattare dasamun ciwon sukari na biyu (2). SAURAN CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI NUMFASHI DA KUMA GAZAWAR AIKIN HUHU An sancewa shan taba na haifar da ciwon lala da dukkanin cututtukan numfashi, ciki har da tari, da numfashi da kyar da kuma yawan majina mai kauri a makogoro. Girma da aikin huhu kuma kan sami gazawa a jikin masu shan taba. Kananan yaran da iyayensuke shan taba suma su kan yi fama da irin wadannan cututtuka na numfashi da kuma gazawar aikin huhu a lokacin yarinta. Yaran da iyayen su ka haife su suna shan taba a lokacin da suke da ciki suna da saukin kamuwa da cututtukan, tun da an riga an shigar musu da sinadaran da ake samu a taba a lokacin da a ke renon su a ciki. TARIN FUKA Kimanin kashi daya a cikin mutane hudu na mutanen duniya gaba daya ne ke dauke da kwayar cutar tarin fuka wacce bata bayyana ba, hakan kuma na sanya su cikin hadarin habakar cutar har ta bayyana. Shan taba yana kara hadarin bayyanar cutar tarin fuka har sau biyu, kuma an san cewa shan taba yana kara tsananta cigaban cutar. Bugu da ƙari, shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa na iya kara haɗarin bayyanar cutar tarin fuka a cikin jikin dan adam. Tarin fuka yana lalata huhu, hakan kuma yana rage karfin aikin huhu, kuma yana kara yawan haɗarin samun rashin lafiya da mutuwa sakamakon gazawar numfashi. 14 12 11 8a 6 5 7 8f 1 10 9 8e 8d 8c 8b 8g 13 3 13 3 4 4 Kayayyakin hayakin taba: Sune duk wani nau’i da aka yi ko aka samo shi daga taba ta hanyar konawa. Misalai sun hada da taba cigari, da kulli, da babbar taba, da lofe, da shisha (wanda a ke sha ta bututun ruwa), da sauransu. Kayan taba bana hayakin ba: Kowane samfurin taba da ya kunshi yankakke ko dakakken ganye, ko garin taba, da nufin sa shi baki ko hanci. Misalai sun hada da snuff, shan taba fure, gutka, mishri da snus. Shakar hayakin da mai shan tabe ke fitarwa: haɗuwa da hayakin taba wanda ya fito daga baki ko hancin mai shan taba da kuma hayakin»gefe» wadansa suka shiga cikin yanayin muhalli daga ci masushan taba da sauran kayayyakin taba. Hakanan ana amfani da kalmomin “shan tabar daga bayan fage» ko «shan taba ba niyya» duk a na amfani da wadannan domin yin bayanin shan ‘SHS’. Taba sigari tana da illa ga rayuwar dan adam ta kowanne fanni. Kayayyakin da suke da nasaba da hayakin taba, har da bututun ruwa na shan shisha, sun ƙunshi fiye da sinadarai dubu dari bakwai,wadanda a kalla dari biyu da hamsin da ciki suna da guba ko kuma kan haifar da ciwon daji. Yin amfani da sauran nau’in taba, ba lallai na hayaki ba, na iya haifar da larura mai tsanani - wani lokacin ma a kan sami rashin lafiya wadda kan kai ga halaka. Shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa na zama musabbabin rashin lafiya ga mutane, wanda kuma ya kan kai ga hallaka. Sabbin kayayyakin taba suna dauke da sinadarai masu kama da sauran nau’ikan taba na asali kuma suna da illa ga lafiyar jiki. Masu shan taba a kowanne lokaci suna rasa akalla shekaru goma na tsawon rayuwar su a matsakaicin zango. A duk fadin duniya, fiye da mutane dubu ashirin da biyu suke mutuwasakamakon amfani da taba ko kuma shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa,a kowacce rana – wannan ya nuna ke nana duk tsawon dakika hudu mutum daya kan rasa ransa.Yin amfani da taba yana cutar da kusan dukkannin sassan jikin mutum. Wasu daga cikin wadannan cututtuka an nuna sua kasa –sun kama tun daga kahar zuwa dan yatsan kafa. 2 AMFANIN DAINA SHAN TABA Ba a makara ba wajen barin amfani da taba. Daina shan taba yana da amfani da yiwuwar rage hadurra da yawa daga cikin wadannan cututtuka, a wasu lokuta, daina shan taba kan rage haduran ya zama cewa kamar mutum mabai taba shan taba ba. Domin Karin bayani da kuma abubuwan da aka duba, sai a shiga shafin: http://www.who.int/tobacco/ Hotuna da zane-zane: © Australian Government Department of Health; © Convention Secretariat WHO Framework Convention on Tobacco Control; © Georgios Kekos; © Ministry of Public Health, Thailand; © Richard Schneider/lndiana University; © Shutterstock.com Haussa translation by WHO Country Office of Nigeria. WHO/NMH/PND/19.1 © World Health Organization 2019. Some rights reserved. This work is available under the CC BY-NC-5A 3.0 IGO licence. Bayan awanni goma sha biyu Bayan Shekaru goma Bayan shekara daya Bayan makonni biyu zuwa watanni uku Bayan minti ashirin Bayan wata daya zuwa watanni tara Bayan shekaru biyar Bayan Shekaru goma sha biyar Haduran da zuciya ke fadawa zaifara raguwa. Yanayin aikin huhu zai fara inganta. Hadurancututtukan zuciya na yankewa zuwa rabin na masu shan taba. Haɗarin bugun zuciya ya kan ragu zuwa ga matakin wadanda ba su sha taba ba a cikin shekaru biyar zuwa goma sha biyar bayan sun bari. Mizanin mutuwa daga ciwon dajin huhu kan zama rabin abin da ya ke ga ma su shan taba. Rashin haɗarin ciwon daji na baki, da makogwaro, da mafitsara, da koda da kuma matsarmama na raguwa. Tari da shakewar numfashin za su ragu. Mizanin‘carbonmonoxide’ a cikin jini zai ragu. Haɗarin cututtukan jijiyoyin zuciya yana komawa tamkar wanda bai taba shan taba ba. Bugun zuciya zai sauka. In da a ka Sami bayanin: Hukumar Lafiya ta Duniya, Yankin Yammacin Tekun Pacific. RASHIN SAMUN HAIHUWA GA MAZA DA MATA Masu shan taba suna iya samun larurar rashin iya haihuwa. Mata masu shan taba sun fi wadanda basu taba shan taba ba fuskantar kalubale wajen samun ciki, da kuma karin yawan lokacindaukar ciki da kuma haɗarin barin ciki. Shan taba yana rage yawan ƙwayoyin halitta na maza, da damar motsin kwayar da kumajirkita siffar halittar kwayar. Masu shan taba wadanda suke kokarin samun juna biyu ta hanyar amfani da fasahar zamani ba kowanne lokaci suke samun nasara ba, wasu lokuta suna buƙatar yin baye ta wannan hanya har kusan sau biyu kafin a cimma burin samun juna biyun. CUTUTTUKAN HANJI/CIKI Masu shan taba na iya samun cututtukanhanji, irin su ciwon ciki, cututtukan ulsa, da kumburin ciki irin su cutar kurga, da kuma sauran cututtuka ciki.Kuma cutar kumburin cikin na da alaka da ƙullewar ciki, da gudawa,da zazzaɓi, da zubar da jini ta dubura. JIKIN MAI SHAN TABA

Upload: others

Post on 18-Jan-2020

17 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

BUGAWAR ZUCIYA, SHANYEWAR SASSAN JIKI DA KUMA SAURAN NAU’IKAN CUTUTTUKAN ZUCIYAKusan duk ɗaya daga cikin mutawar mutane uku a duniya ana danganta ta ne dacutar cututtukan zuciya. Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa sune ke bayar da gudummawa wajen haifar da larurar ciwon zuciya ga kimanin mutane miliyan uku a duniya a kowace shekara. Masu shan taba na da ninki biyu na hadarin bugun zuciya da kuma ninki hudu na karuwar hadarin kamuwa da cututtukan zuciya.Shakar hayakin taba na lalata manyan hanyoyin jini na zuciya, wanda kan zaunar da datti a hanyoyin jini, hakan ya kan sa jini ya daskare, daga nan kuma ya hana gudanar jinin (1) daga nan kuma ya sa zuciya ta buga (2). Rashin samun gudanar jini, idan ba a yi maganin ta ba, kan haifar da mutuwar wasu sassan jikin dan adam, wato bushewa kamar konewa – gangrene (3) wanda kuma ya kan sa lallai sai an yanke wuraren da abin ya shafa (4). Bugawar zuciya, kamar sauran cututtukan zuciya na da mummunanhadarin wanda kan kai ga mutuwa, kuma waɗanda suka sami warka daga bugun jinin na iya fuskantar matsalolin da za su lalata jiki, irin su shanyewar jiki ko rashin iya hangen nesa ko magana.Shan taba yana da illa, ko yaya yawan shan tabar yake. Wadanda suke shan taba kara daya a kowace rana sunadada kimanin rabin hadarin da masu shan taba kara ashirin kowace rana keda shi wajen kamuwa da cututtukan zuciya da kuma bugun jini.Duk da haka, ba wai shan taba ko shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa ba ne ke kara yawan hadarin kamuwa da cututtukan zuciya ba. Yin amfani da kayan da a ka yi da taba ba ba na konawa baa yana kara haɗarin mutuwa saboda ciwon zuciya ko bugun jini.

CUTUTTUKAN DA DUKKANIN KAYAYYAKIN TABA KE JAWOWA

CIWON DAJI NA HUHUMasu shan taba na iya kamuwa da ciwon daji na huhu (9) har sau ashirin da biyu fiye da wadanda basu taba shan taba ba. Shan

taba shine babban dalilin kamuwa da ciwon daji na huhu, wanda ya kan haddasa kashi biyu bisa uku na mutuwa sakamakon ciwon huhu a duniya, wannan kuma yana shafar kimanin mutane miliyan daya da dari biyu a kowace shekara. Wadanda ba

su taba shan taba ba, amma kuma suna shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a gida ko a wurin aiki suna cikin hadarin samun ciwon daji na huhu.

TOSHEWAR MANYAN HANYOYIN JINI MASU KAIWA GA HUHU

A duk mutum biyar da ke shan taba mutum ɗaya na iya samun matsananciyar cutar toshewar manyan hanyoyin jini masu kaiwa ga huhu (COPD) (10) a rayuwar sa, musamman ma mutanen da suka fara shan taba a lokacin

yarinta da shekarunsu basu wuce ashirin ba, tun da yake hayakin na taba na jinkirta girma da ci gaban lafiyar jiki. Masu shan taba sun fi sauƙin kamuwa da cutar toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya har sau uku

zuwa hudu. Shan taba yana haifar da kumburi da fashewar jakar iska a cikin huhu wanda ya kan rage karfin shakar iskar ‘oxygen’ da kuma damar fitar da iskar ‘carbon dioxide’. Har ila yau, yana haifar da zaunewar majina

wadda kuma kan sa tari mai zafi da kuma wahalar numfashi. Mutanen da su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa tun suna yara har suka girma suna da yawan kamuwa da cututtuka a hanyoyin numfashin su,a

sakamakon haka kuma suna cikin hadarin samun toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya (COPD).

CUTAR ‘ASTHMA’An san cewa shan taba na tayar da ciwon asthma ga mutanen da suka manyanta, wanda yakan ƙuntata musu, da kuma

karawa rashin lafiya tsanani da kuma kara haɗarin cutar wanda yake buƙatar kulawa ta gaggawa. Yara‘yan makaranta da iyayen su ke shan taba suna da haɗarin shakar hayakin tabawanda ke zama musabbabin faruwar cutar asthma da kuma

tsananin ciwon kumburi a hanyoyi da ke isar da iska zuwa ga huhu.

CUTUTTUKAN DA A KE SAMU DAGA HAYAKIN TABA

Dukkan kayayyakin taba suna da illa, kuma babu wani matakin da zai iya nunawa rashin lahanin taba. Shan hayakin taba shi ne mafi yawadaga cikin hanyoyinamfani da taba a duniya baki daya. Sauran kayayyakin cin taba sun hada da taba gari, da ganyes, da anguru, da sauransu wadanda a ke sanyawa a lofe da shishaa shata bututun ruwa, da sauran kayayyakin taba na zamani.

CIWON DAJI NA BAKI DA KUMA SAURAN CUTUTTUKAN BAKIYin amfani da taba (ta hanyar shan hayakin ta ko wani nau’i na tabar) yana zama dalilin kamuwa da cututtukan baki da yawa. Dukkanin nau’ikan tabar su kan zama sanadin samun ciwon daji na baki (5). A kasashe da yawa, da wuya a rayu sama da shekaru biyar bayan gano cutar daji a baki. Wadanda ke warkewa daga ciwon daji na baki sukan sami lahani a fuska da kasa yin magana, ko haɗiya ko tauna wani abu. Yin amfani da taba yana kara haɗarin cutar dasashi, waccedasashi ke kumburasannan ya dauke ya kai ga kashin mukamuki har ya haifar da asarar hakori (6). SShan taba da kuma amfani da kayan taba ba yana jirkita yanayin sinadaran da baki ke dauke da su, wanda ke sa makalewar bakin datti da sa hakora rawaya da kuma haddasa mummunan numfashi.

CIWON DAJIN MAƘOGAROAmfani da kayan taba tare da shan hayakin taba bayana kara haɗarin Ciwon daji na ka da wuya, wannan ya hada da lebe da kuma cikin baki. Cire ciwon na buƙatar aiki na musamman (7), yadda za a huda rami a wuya yadda za a sami damar yin numfashi.Yin amfani da hasken na’ura wajen kawar da ciwon yana da illa kwarai wajen lalata harshe har ya kasha dandano, da rage yawan gudanar yawun baki da kuma kara samar da majina a makogoro, wanda zai sa ciwo da kuma wahala wajen cin abinci.

SAURAN CUTUTTUKAN DAJIYin amfani da taba ya kan haifar da cututtukan daji fiye da nau’iuka goma. A duk lokacin da a ka shaki hayakin taba, akwai sinadarai masu guba da a ke kaiwa ga jiki. Daga yawancin sinadaranna taba, akalla nau’ika saba’in an gano sunahaddasa cutar daji. Masu shan taba suna cikin haɗari mafi girma na samun cutar sankarar bargon kashi; da ciwon daji na hanci da kuma na sauran sassan cikin hanci (8a); da hanji (8b), da koda (8c), da hanta, da matsarmama (8d), da ciki (8e) ko kuma ciwon daji na halittar da ke fitar da kwayayen haihuwa na mata; da kuma ciwon daji na hanyoyin fitsari (ciki har da mafitsara, da kuma sauran jijiyoyin bangaren). Binciken da aka yi kwanan nan sun nuna alakar shan taba da kuma karuwar hadarin samun ciwon daji na nono (8f), musamman ma mata masu shan taba da suka fara shan taba kafin su fara daukar ciki. Haka kuma shan taba na kara hadarin samun ciwon daji na mahaifaga matan (8g) da ke fama da cutar da kananan kwayoyin cututtuka ke haifarwa. Haɗarin waɗannan cututtuka na yawan ƙaruwa ne tare da yawan tabar da kuma tsawon lokacin da a ka yi a na sha, saboda tsawon lokaci a na shan taba na sa jiki kamuwa da sinadarai masu guba. Shan taba mara hayaki na dauke da kwayoyin cuta har 28 wanda ke haifar da ciwon daji na cikin baki da makogoro da kuma matsarmama.Ci gaba da yin amfani da taba bayan an ganociwon daji yana kara tsananta cutar, saboda da hayakintaba na iya canza kwayar halitta, wanda zai iya kara girman ciwon dajin; da kawo tangarda ga maganin ciwon daji; da kuma ƙara yawan matsalolin maganin.

MUTUWAR DAN TAYIN CIKIYin amfani da taba da kuma shakar hayakin taba a lokacin daukar ciki na ƙara haɗarin mutuwar dan tayin ciki. Mata da suke shan taba ko kuma ke shakar hayaƙin taba lokacin da suke renon ciki suna cikin haɗarin zubewar cikin. Zubewar ciki (haihuwar tayin da ya mutu a cikin mahaifa) na faruwa a lokuta da yawa a sakamakon rashin isasshiyar ‘oxygen’ da rashin dai-daiton mahaifa wanda iskar ‘carbon monoxide’ke haifarwa daga hayakin taba da sinadarin ‘nicotine’dake cikin taba. Masu shan taba suna cikin haɗarinsamun ciki a wajen mahaifa, mai mummunan haɗari ga mahaifiya, a nan yayin da ta ke reon cikin ya kan makale a wajen mahaifa. Saboda da haka, daina shan taba da kuma samun kariya daga shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa yana da mahimmanci ga mata masu haifuwa, ko kuma masu shirin daukai ciki da kuma yayin renon cikin.

HANA GIRMAN DAN TAYIN DA KE CIKI. DA HAIHUWAR DA MARA CIKAKKEN NAUYI DA HAIHUWAR DAN DA BAI CIKA WATA TARA BADuk wani nau’i na amfani da taba ko kuma shiga cikin hayakin taba yayinrenon ciki zai iya zama abu mai illa ga lafiya da kuma girman dan tayin yaron da ke ciki. Yaran da aka haifa ga matan da suke shan taba, ko yin amfani da taba gari, ko kuma su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a lokacin da suke renon ciki suna da haɗarin haihuwar bakwaini da kuma haihuwar yaron da nauyin sa bai cika ba. Yaran da aka haife su a bakwaini da kuma wadanda nauyin su bai cika ba na iya samun matsalolin rashi lafiyana tsawon rayuwar su, ciki har da samun cututtuka masu tsanani bayan sun girma.

KARANCIN TUNANI/MANTUWAShan taba abu ne mai haɗarin lalata kwakwalwa, wanda wani rukuni na cututtuka ne

wanda kan haifar da karancin tunanin mutum wanda kuma bashi da magani tabbatacce a halin yanzu. Karancin tunanin abu ne da ya ke habaka, ya kan shafi ƙwaƙwalwar

mutum, da halayyar mutum da kuma ƙwarewa da tsayawa ga ayyukan yau da kullum. Baya ga abin da wannan ciwo ke haifarwa wajen hana mutum zarafin aiyuka, cutar zata iya zama mai nauyi kwarai ga iyali ko masu kulawa da mai cutar. Cutar ‘Alzheimer’mafi yawa a cikin irin wannan cututtuka, kuma an kiyasta kimanin kashi goma sha huhu (14)

cikin dari (100) na cutar a duniya na da alaka da shan taba.

RAUNIN MAZAKUTAShan taba yana hanaisasshen jini zuwa azzakari, wanda zai iya haifar da rashin

ƙarfin mazakuta (rashin yiwuwar mikewar azzakari). Raunin mazakutayafi yawa a cikin mashaya taba kuma mai yiwuwa ya ci gaba ko zama dindindin sai dai idan

mutumin ya daina shan taba a farkon rayuwarsa.

MUTUWAR JARIRAI FARAT-DAYAMutuwar jarirai farat-daya (SIDS) ita ce mai faruwa kwatsam, ba tare da wani dalili da a ke iya gani baga yara‘yan kasa da shekara 1. An san cewa shan taba yayin goyon ciki naƙara

haɗarin mutuwar farat-daya ga yara, kuma haɗarin ya kan ƙara karuwa tare da bin ‘ya’yan da suka Haifa,kuma suka ci gaba da shan taba bayan haihuwar.

JININ HAILA/WATA DA YANKEWAR HAIHUWAMata masu shan taba zasu iya jinin haila/wata mai ciwo da zafi da kuma samunalamomin yankewar

haihuwa. Yankewar haihuwa kan faru cikin shekara daya (1) zuwa hudu (4) ga mata masu shan taba, kasa da lokacin da a ka sani saboda shan taba yana rage damar samar da kwan haihuwana mace,

wanda ya kan haifar da rashin samun damar haihuwa da kuma karancin rowan halittar ‘estrogen’.

HAIHUWAR YARA MASU LAHANIN HALITTA Shan taba na iya lalata kwayar halittatare da lalata kwayar halitta ta gado (DNA), wanda kan haifar da lahani ga halit-tar jariri. A wasu binciken ilimi angano cewa mutanen da suke shan taba suna da haɗarin haihuwar yaron\ wanda ke iya kamuwa da ciwon daji. Shan taba ga mace a farkon lokacin da ta ke renon ciki na ƙara da hadarin haihuwar jariri

mai yankakken lebe ko baki. An kuma lura cewa mutanen da iyayensu suka sha taba a lokacin renonciki suna da ƙarancin yawan kwayar halitta fiye da maza waɗanda iyayensu ba su taba shan taba ba.

RASHIN GANIShan taba yana haifar da cututtukan ido da yawa, waɗanda idan ba a yi maganin su ba, za su iya haifar da rashin

iya hangen nesa. Masu shan taba suna da alaƙa da lalacewar ‘macular’ fiye da wadanda ba su taba shan taba ba, wanda yanayine da zai haifar da rashin hangen nesa. Lalacewar ‘macular’ ya kan shafi yawancin mutane,ya hana

karatu, ko tukin mota, da gane fuskoki da launuka da kuma ganin abubuwa yadda su ke. Har ila yau masu shan taba suna da haɗarin samun cutar yanar ido wanda ke kare haske ko gani. Yanar ido (11) na iya haifar da rashin

hangen nesa, kuma yin tiyata ne kawai zaɓi don mayar da gani yadda yake. Sababbin hujjoji sun nuna cewa shan taba yana haifar da hawan jinin ido, yanayin da zai kara yawan matsina lamba a idanu kuma zai iya lalata gani. Shan taba na sa radadi a idanu da kuma kara zafin cututtukan idanuga masu shan taba da masu shakar

hayaƙinda masu shan tabe ke fitarwa, musamman ma a tsakanin waɗanda suke ɗauketubaran gani na cikin ido.

RASHIN JI/KURUMCEWAIyayen da su ke shan taba kan samu yara ‘yan kasa da shekaru biyu masu fama da ciwon kunne wanda ruwa ke zuba daga cikin kunne, Sakamakon shakar hayakin tabar da iyayen su ke sha a gida. Matsanancin ciwon kunne

(tsakiyar kunne) ga yara shine dalilin da ya kan sa a sami bebantaka (12) da kurumta. Manyan mutane masu shan taba sun fi fama da rashin ji saboda tsawon lokacin da su ka yi suna shan taba na hana zagayawar jini cikin kunne.

Rashin magance ciwon rashin ji ko kurumtana iya tasiri a zamantakewar jama’a, da tunani da kuma tattalin arziki.

RAUNIN KASHI Iskar ‘Carbon monoxide’ da ke cikin hayakin taba, babbar guba ce irin wacce a ke samu a hayakin mota, ta kan danfarazuwa ga ‘hemoglobin’na cikin jini cikin sauƙi fiye da iskar ‘oxygen’ da jiki ke bukata, don haka sai ta rage zuwan iskar oxygen zuwa jikin mutum. Masu shan taba sun fi saukin samun raunin kashi, yadda karfin kashin ke raguwa da sauƙin karyewa.Idankuma

suka fuskanci matsalolin a kashi,akwai jinjiri ko rashinsamun nasarar warkewa.

LALACEWAR FATAR JIKIShan taba na kara yawan hadarin samun cututtukan fata na‘psoriasis’ (13), wanda wani mummunan yanayine da ke

sa kumburi da dashewar fatata dashe ya bar wani ja a dukkanin jiki. Shan taba yana sa fata ta tsufa da wuri wajen sa sinadarai wanda su ke ba fata da laushi suragutare da daukewar ‘vitamin A’ da kuma hana zagayawar jini. Don haka

masu shan taba suna iya samun bushewar fata (14), bayan nan kuma ta yankwane, musamman a kusa da lebe da idanu.

RAUNANA GARKUWA JIKI Sinadaran da suke cikin hayakin taba na raunana tsarin garkuwar jiki, su sa masu shan taba cikin hadarin kamuwa da

cutar huhu. Bugu da ƙari, masu shan taba suna tattare da yiwuwar cewa kwayoyin halittar suna iya samun cututtuka dare da haɗarin samun ƙwayar cututtuka da dama, ciki har da cututtukan zuciya, cututtukan kurga, da kwayoyin cuta,

da cututtukan daji. Shan taba yana sanya garkuwar jikin mutum ta raunana, kamar irin wadanda ke da ciwon kwan-tacce’, ko wani nau’i na ciwon daji, da kuma mafi girman hadarin cututtuka daban-daban. Illar shan taba ga garkuwar

jiki na sanya mutanen da ke da kwayar cutar HIV su kara yawan haɗarin fadawa matakin cutar AIDS. Haka kuma masu shan taba kuma suna dauke da kwayar cutar HIV, yawancitsawon rayuwasu da cutar baya wuce shekaru goma sha

biyu da digo uku (12.3), kusan yana jawo rasa rai daga cutar HIV har rubi fiye da biyu na kasa da yawan shekarun da kwayoyin cutar ta HIV kan zauna a jikin mutum kafin mutuwa.

CIWON SUKARI NA BIYU (2)Hadarin kamuwa da ciwon sukari ya fi yawa a tsakanin masu shan taba, kuma wannan

hadarin ya kan karu da yawan shan taba sigarin da akesha a kowacce rana. Shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa ma yana tattare dasamun ciwon sukari na biyu (2).

SAURAN CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI NUMFASHI DA KUMA GAZAWAR AIKIN HUHUAn sancewa shan taba na haifar da ciwon lala da dukkanin cututtukan numfashi, ciki har

da tari, da numfashi da kyar da kuma yawan majina mai kauri a makogoro. Girma da aikin huhu kuma kan sami gazawa a jikin masu shan taba. Kananan yaran da iyayensuke shan taba suma su kan yi fama da irin wadannan cututtuka na numfashi da kuma gazawar aikin

huhu a lokacin yarinta. Yaran da iyayen su ka haife su suna shan taba a lokacin da suke da ciki suna da saukin kamuwa da cututtukan, tun da an riga an shigar musu da sinadaran da

ake samu a taba a lokacin da a ke renon su a ciki.

TARIN FUKAKimanin kashi daya a cikin mutane hudu na mutanen duniya gaba daya ne ke dauke da kwayar

cutar tarin fuka wacce bata bayyana ba, hakan kuma na sanya su cikin hadarin habakar cutar har ta bayyana. Shan taba yana kara hadarin bayyanar cutar tarin fuka har sau biyu, kuma an san cewa shan

taba yana kara tsananta cigaban cutar. Bugu da ƙari, shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa na iya kara haɗarin bayyanar cutar tarin fuka a cikin jikin dan adam. Tarin fuka yana lalata huhu, hakan kuma yana rage karfin aikin huhu, kuma yana kara yawan haɗarin samun rashin lafiya da mutuwa

sakamakon gazawar numfashi.

14

12

118a

65

7

8f

1

10

9

8e

8d8c

8b

8g

13

3

13

3

4

4

Kayayyakin hayakin taba: Sune duk wani nau’i da aka yi ko aka samo shi daga taba ta hanyar konawa. Misalai sun hada da taba cigari, da kulli, da babbar taba, da lofe, da shisha (wanda a ke sha ta bututun ruwa), da sauransu.

Kayan taba bana hayakin ba: Kowane samfurin taba da ya kunshi yankakke ko dakakken ganye, ko garin taba, da nufin sa shi baki ko hanci. Misalai sun hada da snuff, shan taba fure, gutka, mishri da snus.

Shakar hayakin da mai shan tabe ke fitarwa: haɗuwa da hayakin taba wanda ya fito daga baki ko hancin mai shan taba da kuma hayakin»gefe» wadansa suka shiga cikin yanayin muhalli daga ci masushan taba da sauran kayayyakin taba. Hakanan ana amfani da kalmomin “shan tabar daga bayan fage» ko «shan taba ba niyya» duk a na amfani da wadannan domin yin bayanin shan ‘SHS’.

Taba sigari tana da illa ga rayuwar dan adam ta kowanne fanni. Kayayyakin da suke da nasaba da hayakin taba, har da bututun ruwa na shan shisha, sun ƙunshi fiye da sinadarai dubu dari bakwai,wadanda a kalla dari biyu da hamsin da ciki suna da guba ko kuma kan haifar da ciwon daji. Yin amfani da sauran nau’in taba, ba lallai na hayaki ba, na iya haifar da larura mai tsanani - wani lokacin ma a kan sami rashin lafiya wadda kan kai ga halaka. Shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa na zama musabbabin rashin lafiya ga mutane, wanda kuma ya kan kai ga hallaka. Sabbin kayayyakin taba suna dauke da sinadarai masu kama da sauran nau’ikan taba na asali kuma suna da illa ga lafiyar jiki. Masu shan taba a kowanne lokaci suna rasa akalla shekaru goma na tsawon rayuwar su a matsakaicin zango. A duk fadin duniya, fiye da mutane dubu ashirin da biyu suke mutuwasakamakon amfani da taba ko kuma shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa,a kowacce rana – wannan ya nuna ke nana duk tsawon dakika hudu mutum daya kan rasa ransa.Yin amfani da taba yana cutar da kusan dukkannin sassan jikin mutum. Wasu daga cikin wadannan cututtuka an nuna sua kasa –sun kama tun daga kahar zuwa dan yatsan kafa.

2

AMFANIN DAINA SHAN TABABa a makara ba wajen barin amfani da taba. Daina shan taba yana da amfani da yiwuwar rage hadurra da yawa daga cikin wadannan cututtuka, a wasu lokuta, daina shan taba kan rage haduran ya zama cewa kamar mutum mabai taba shan taba ba. Domin Karin bayani da kuma abubuwan da aka duba, sai a shiga shafin: http://www.who.int/tobacco/

Hotuna da zane-zane: © Australian Government Department of Health; © Convention Secretariat WHO Framework Convention on Tobacco Control; © Georgios Kekos; © Ministry of Public Health, Thailand; © Richard Schneider/lndiana University; © Shutterstock.comHaussa translation by WHO Country Office of Nigeria. WHO/NMH/PND/19.1© World Health Organization 2019. Some rights reserved. This work is available under the CC BY-NC-5A 3.0 IGO licence.

Bayan awanni goma sha biyu

Bayan Shekaru gomaBayan shekara dayaBayan makonni biyu zuwa watanni ukuBayan minti ashirin

Bayan wata daya zuwa watanni tara Bayan shekaru biyar

Bayan Shekaru goma sha biyar

Haduran da zuciya ke fadawa zaifara raguwa. Yanayin aikin huhu zai fara inganta.

Hadurancututtukan zuciya na yankewa zuwa rabin na masu shan taba.

Haɗarin bugun zuciya ya kan ragu zuwa ga matakin wadanda ba su sha taba ba a cikin shekaru biyar zuwa goma sha biyar bayan sun bari.

Mizanin mutuwa daga ciwon dajin huhu kan zama rabin abin da ya ke ga ma su shan taba. Rashin haɗarin ciwon daji na baki, da makogwaro, da mafitsara, da koda da kuma matsarmama na raguwa.

Tari da shakewar numfashin za su ragu.Mizanin‘carbonmonoxide’ a cikin jini zai ragu.

Haɗarin cututtukan jijiyoyin zuciya yana komawa tamkar wanda bai taba shan taba ba.

Bugun zuciya zai sauka.

In da a ka Sami bayanin: Hukumar Lafiya ta Duniya, Yankin Yammacin Tekun Pacific.

RASHIN SAMUN HAIHUWA GA MAZA DA MATAMasu shan taba suna iya samun larurar rashin iya haihuwa. Mata masu shan taba sun

fi wadanda basu taba shan taba ba fuskantar kalubale wajen samun ciki, da kuma karin yawan lokacindaukar ciki da kuma haɗarin barin ciki. Shan taba yana rage yawan ƙwayoyin

halitta na maza, da damar motsin kwayar da kumajirkita siffar halittar kwayar. Masu shan taba wadanda suke kokarin samun juna biyu ta hanyar amfani da fasahar zamani ba

kowanne lokaci suke samun nasara ba, wasu lokuta suna buƙatar yin baye ta wannan hanya har kusan sau biyu kafin a cimma burin samun juna biyun.

CUTUTTUKAN HANJI/CIKIMasu shan taba na iya samun cututtukanhanji, irin su ciwon ciki, cututtukan ulsa, da kumburin ciki irin su cutar kurga,

da kuma sauran cututtuka ciki.Kuma cutar kumburin cikin na da alaka da ƙullewar ciki, da gudawa,da zazzaɓi, da zubar da jini ta dubura.

JIKIN MAI SHAN TABA