matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar hadari ko ...gabatarwa rashin lafiya ta jiki da...

8
This leaflet is based on material produced by the Royal College of Psychiatrists (www.rcpsych.ac.uk/info). © 2014 The Royal College of Psychiatrists. Reproduced by permission. Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko Annoba Murtala Muhammed Foundation Murtala Muhammed Foundation

Upload: others

Post on 05-Mar-2021

5 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

This leaflet is based on material produced by the Royal College of Psychiatrists

(www.rcpsych.ac.uk/info). © 2014 The Royal College of Psychiatrists.

Reproduced by permission.

Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar

Hadari ko Annoba

M u r t a l a M u h a m m e d F o u n d a t i o nM u r t a l a M u h a m m e d F o u n d a t i o n

Page 2: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

GABATARWAGABATARWA

Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin bakin ciki, firgici da alhini. Haka kuma, suna da tasiri mutuka wajen haifar da gagarimar dimuwa mai karfin gaske, wanda yakan raguwa da lokaci ba tare da ziyartar wasu kwararrun taimako ba.

• Ka tsinci kanka cikin halin rudewa, sakamakon wani hadari ko annoba, kuma kana bukatar fahimtar halin da kake?

• Ko ka san wani wanda yake cikin halin dimuwa, sakamakon wani hadarin ko annoba, kuma kana bukatar fahimtar halin da yake?

• Ka na bukartar ka fahimtar yarda mutanen da suka shiga irin wannan hali ke ji.

Ta kuma nuna irin halin da za su iya shiga a gaba, da hanyoyin da mutum zai bi ya dawo hayyacinsa har ma ya iya fahimtar kuma ya yadda da abunda ya faru da shi

WANNAN TAKARDAR NA IYA TAIMAKA MAKA IDAN:WANNAN TAKARDAR NA IYA TAIMAKA MAKA IDAN:

Rudewa wahala ko gushewar hankali na faruwa ne yayin da mutum ya ga ko ya kasance a wani hadari ko tashin hankali na ganganci wanda zai iya haifar da mummunar illa ga mutane ko ma ya yi sanadiyyar rayuka. Ganin irin wannan, kan sa mutum ya tsorata ko ya shiga dimuwa da alhini. A wannan matakin sai mutum ya rasa abin da zai yi.

1

Page 3: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

MISALAN HADURRA KO ANNOBA DA KAN HAIFAR DA BIRKICEWAR AL AMURRA KO GUSHEWAR HANKALI?

MISALAN HADURRA KO ANNOBA DA KAN HAIFAR DA BIRKICEWAR AL AMURRA KO GUSHEWAR HANKALI?

• Kazamin hadurra.

• A sanar da marasa lafiya cewa, cutarsa na da wuyar magani ko tana kisa farat ta daya.

• Rashi saboda rasuwa.

• Tashe-tashen hankula irin na, sare-sare da yanke-yanke ko na 'yan daba, fyade, ko cin zarafin mata da kananan yara, ko fashi da makami da makamantan su.

• Yaki ko wane iri.

• Annoba ko sakacin Al'umma.

• Tarzomar 'yan ta'adda.

• Garkuwa da mutun don wata bukata.

Firsinonin dake kurkuku ko bayi bayan yaki.

ME YAKE FARUWA GA MUTUMIN DA YA GA MUMMUNAN HADARI KO ANNOBA?

Dimuwa:

Rashin yarda:

ME ZAI FARU A GABA?

ME YAKE FARUWA GA MUTUMIN DA YA GA MUMMUNAN HADARI KO ANNOBA?

Dimuwa:

Rashin yarda:

ME ZAI FARU A GABA?

Abu na farko da kan sami mutumin da ya ga mummunan hadari ko annoba, shine, mutum zai zama ya kasa gane komai, ba zai san abinda ya ke ciki sabo da dimuwa, har ma ya dinga ganin kamar abin be faru ba.

Yayin da dimuwa ta faru, mutum zai fara jin:• Mamaki, hajijiya da batan basira.• Mutum sai ya zama baya son shiga

cikin jama’a ko yin abubuwan rayuwar daya saba yi a da.

Mutum yana rasa yarda da abinda ya faru, domin haka sai mutum ya sa aransa cewar wannan abu bai faru ba. Sauran jama'a zasu yi tunanin cewar mutumin mai kwarin zuciya ne ko kuma mutum bai damu ba ne

Bayan wani dan lokaci, sai wadannan tunanin su wuce, sai wasu kuma su shigo marassa kyau.

Kowa da irin yarda ya ke ji, yayin da ya ga mummunan hadari ko annoba, da tsawon lokacin da zai dauka kafin ya yanke hukunci a kan hadarin da ya gani. Yawanci mutanne suna mamaki da irin jurewa zuciyar su. Amma dai ta kowanne hali, mutum zai kasance wa a sahun masu:

• Fargabar: hadarin ko annobar da ya gani, na iya sake faruwa. Wannan fargabar na iya sa zuciyar mutum ta yi rauni, ya kasa jurewa, har ya shiga wani hali na ha'ula'i.

2

Page 4: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

• Rashin iya yin komai: halin iya yin komai a kan abinda ya faru wanda mutum yake saddakarwa don ba abinda zai iya yi.

• Haushi: haushi a kan abin da ya faru da kuma da duk wanda ya yi sanadin afkuwar hadarin.

• Mai laifi: za ka ji kai kanka, ka zama mai laifi a kan afkuwar hadarin. Ka dinga jin kunyar cewar ya ya kai ka tsira, amma ga wasu sun raunana, wasu ma sun mutu.

• Rashin jin dadi: halin rashin jin dadi, ba kamar in akwai dan'uwanka ko wanda kuka shaku a cikin wadanda suka mutu ko suka sami rauni.

• Kunya: za ka koma jin kunyar kanka, ka kasa daurewa, musamman idan kana son wasu su tai make ka.

• Samun sa'ida ko sauki: bayan

duk abin daya faru ya wuce, hankali ya kwanta abin tsoro ya gushe.

• Fata na gari: bayan an sami lafiyar ciwuka da duk wa ta cuta da idanu kan gani, hankali ya kwanta, mutum zai fara tunanin samun ci gaba ta rayuwa.

WADANNE ABUBUWA MUTUM ZAI FUSKANTA?

YA ZAN YI?

SAI KA BAIWA KANKA LOKACI:

KA YARDA ZA KA GANO ME YA FARU:

KA KUSANCI MUTANEN DA SUKA TABA HADARI KUMA SUKA TSIRA:

NEMAN TAIMAKO:

WADANNE ABUBUWA MUTUM ZAI FUSKANTA?

YA ZAN YI?

SAI KA BAIWA KANKA LOKACI:

KA YARDA ZA KA GANO ME YA FARU:

KA KUSANCI MUTANEN DA SUKA TABA HADARI KUMA SUKA TSIRA:

NEMAN TAIMAKO:

Akwai wasu ‘yan matsaloli da mutum zai iya fiskanta bayan halin da ya shiga. Wadannan abubuwan sun hada da:

• Rashin wadataccen bacci• Jin gajiya• Mafarke iri-iri marassa kyau• Rashin nutsuwa• Mantuwa• Tunani zai yi rauni• Ciwon kai• Karancin ko karin cin abinci• Rauni wurin mu'amullar, musamman

bangaren saduwa• Ciwukan jiki iri-iri• Saurin bugawar zuciyar

A zahiri, wanda duk yake a wannan hali, ya kan dauki makwanni ko ma watanni kafin ya dawo hankalinsa har ya yarda cewar abin da ya faru da shi gaske ne.

Zai fi sauki,mutum ya saddakar cewa abinda ya faru ya riga ya faru babu abinda zai canja shi.

In har ka taba zuwa jana'iza ko dubiyar wasu da hadari ya ritsa da su, haka zai saukaka ma ka wajen warware matsalarka. Saboda haka zai yi kyau ka dinga hira da wadanda suka taba samun matsala irin ta ka.

Zai yi kyau ka dinga tattaunawa da mutane a kan a bin da ya faru. Zai kuma yi kyau, ka tambayi 'yan'uwa da abokan arziki lokaci har ka warware ko da kuwa za su kasance cikin halin rashin amsar da za su bayar daga farko.

3

Page 5: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

MUTUM YA SAMU LOKACIN KAN SA:

TATTAUNAWA A KAN ABIN DA YA FARU:

ZAMAN YAU DA KULLUM:

SHIGA CIKIN JAMA’A:

KIYAYEWA

ME DA ME ZAN KIYAYE?

RIKON ABU A ZUCIYA:

KADA MUTUM YA DAUKI KOMAI DA ZAFI:

MUTUM YA SAMU LOKACIN KAN SA:

TATTAUNAWA A KAN ABIN DA YA FARU:

ZAMAN YAU DA KULLUM:

SHIGA CIKIN JAMA’A:

KIYAYEWA

ME DA ME ZAN KIYAYE?

RIKON ABU A ZUCIYA:

KADA MUTUM YA DAUKI KOMAI DA ZAFI:

Zai yi kyau, ka ware wasu lokuta da za ka kasance kai kadai ko da iyali ko wanda ranka ya kwanta da.

A hankali ka dinga tunawa da tattaunawa da mutane a kan abin da ya faru.. Ka da ka damu ko haka zai sa ka kuka. Yin hakan zai rage maka radadin da kake fama da shi.

Hakika wanda yake cikin wanna hali, zai dinga fama da rashin dandano, ya din ga jin baya bukatar cin abinci bisa ka’ida. Ma’ana, ya tabbatar da ya ci abinci sau uku a rana, kamar yadda yake a tsarin cin abinci. Ba wai sai ya take cikinsa ba, ya ci ko ya ya yake. Ya kuma dinga motsa jikinsa da kadan-kadan har ya saba.

A wasu lokuta mutum kan yi sha'awar shiga jama'a amma bada niyar tattauna abinda ke damunsa ba. Hakan ba laifi ba ne, wata hanyar ce ta samun sauki.

Bayan alhini, mutum ya rinka kula saboda tsautsayi na haddura da sauransu a cikin gida ko a kan titi. Hadari ba shi da tsayayyen lokaci.

Barin abu a zuciya hadari ne, musamman ga wanda ya tsallake siradi irin wannan. Karo da abubuwan marassa dadi, abu ne da ya shafi kowa, saboda haka ba abin kunya ba ne, ka bayyana abin da ke damunka don neman mafita. Kunshe su a zuciya na iya yi ma illa a lafiyarka. Fito da abin da yake damun ka fili, ko da kuwa za ka yi kuka.

Ba shakka kazar-kazar na iya sa mutum ya manta da abin da ya faru da shi, to, amma kuma hadari ne mutum ya dauki komai da zafi, saisa-saisa, a sannu sai mutum ya

koma kamar yadda ya saba.

Ya zama dole mutum ya guji shaye-shayen kwayoyi da giya wai don mutum ya manta da abubuwan da ke damunsa. Shan su na iya zama illa ga lafiyarka. In ka bi abin a sannu, komai zai wuce.

Kiyayi garajen yanke hukunci ga duk wani babban al'amari da kake son yi. Zabinka a wannan hali, ba lallai ne ya zama ingantacce ba. Nemi shawarar wadanda ka yarda dasu, don kaucewa halin, 'da na sani’.

• Baka da wanda za ka yi shawara dashi.

• Abubuwa sun cakude ma ka, kuma ka kasa warware su, jin bakin ciki haka siddan, jin kasala akai-akai ko damuwa ba tare da wani cikakken dalili ba.

• Ka dinga jin kamar ba ka dawo yadda kake ba, bayan mako shida.

• Rashin samun wadataccen bacci gami da mafarkai masu ban tsoro.

• Ka fara tsanar mutanen da ke kusa da kai.

• Kana nisantar mutane.• Ka fara sakaci da aikinka. • Idan ka ji makusantanka na ba ka

shawarar ka nemi taimakon Likita• Ka na samun hatsari• In ka ga shan sigarinka ko barasa ya

karu, ko ka tsiri dayan biyun, ko shan kwaya don ka manta da abinda

KA KIYAYI SHAN GIYA KO KWAYOYI MASU SAKA MAYE:

KIYAYI GARAJEN YANKE HUKUNCI GA MANYAN AL'AMURRANKA:

YAUSHE YA KAMATA KA NEMI SHAWARAR KWARARRU?

KA KIYAYI SHAN GIYA KO KWAYOYI MASU SAKA MAYE:

KIYAYI GARAJEN YANKE HUKUNCI GA MANYAN AL'AMURRANKA:

YAUSHE YA KAMATA KA NEMI SHAWARAR KWARARRU?

4

Page 6: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

MENENE ABIN DA ZAI FARU LOKACIN ALHINI?

MENENE MATSALA GABANIN ALHINI:

WANE IRIN TAIMAKON LIKITAN YA KE DA SHI?

MENENE ABIN DA ZAI FARU LOKACIN ALHINI?

MENENE MATSALA GABANIN ALHINI:

WANE IRIN TAIMAKON LIKITAN YA KE DA SHI?

Yayin da mutane su ka shiga halin ]imuwa ko birkicewar kwakwalwa, sakammakon wani hadari ko afkuwar annoba wasu mutane suna zarcewa su samu wannan matsalar da ake kira (1) Post-Traumatic Stress Disorder (PTSD). Alamun da kan nuna mutum ya shiga wannan matsalar, sun hada da:

• Kara shiga cikin wani yanayi na matsanancin tunani ko mafarkai game da hadarin da mutum ya hadu da shi.

• Kaucewa abubuwa da ke iya sa mutum ya tuno hadarin da ya faru da shi a baya.

• Mutuwan zuciya, mutum ya dinga ganin ya fita daga sahun masu hankali ko lafiyayyu.

• A ko yaushe mutum ya na tunanin wata masifa zata same shi.

In har ka fahimci kana fuskantar matsalar (PTSD), ka sauri ka ziyarci Likita.

Likita zai iya ba ka shawara ka je ka ga kwararre a bangaren warkar da masu matsalar rudewa. Irin wadannan Likitocin na warkar da mutane ta hanyar hira da shawara, da haka suke gane matsalar mutum kuma su yi masa maganinta. Irin wadannan Likitocin na samun agaji daga iri-irin mutanen da suka sami matsala makamanciyar ta ka, amma sun warke. Kai kanka za ka saki jikinka, jin cewar ga wani da ya taba samun irin matsalar da kake fama da ita, kuma ya warke ras.

KO LIKITANA ZAI IYA RUBUTA MIN MAGUNGUNAN DA ZAN SHA DON SAMUN LAFIYA?

MAGUNGUNA:

MAGUNGUNAN RAGE BACIN RAI (ANTIDEPRESSANTS)

KO LIKITANA ZAI IYA RUBUTA MIN MAGUNGUNAN DA ZAN SHA DON SAMUN LAFIYA?

MAGUNGUNA:

MAGUNGUNAN RAGE BACIN RAI (ANTIDEPRESSANTS)

Wasu lokutan shan magunguna na taimakawa wajen samun sauki, amma kuma yana da muhimmanci ka dinga ziyartar Likitanka, akai-akai don tabbatar da ci gaban lafiya.

Magungunan da kan bai wa masu irin wannan matsala su ake kira, tranqullizers. Suna taimakawa matuka ga wajen saukaka damuwa su kuma sa mutum ya sami wadataccen bacci. Su kuma suna da tasu matsalar. Idan aka wuce mako uku zuwa hudu ana shan su, abubuwa kamar haka na iya faruwa: • Za su iya daina aiki in jikin mutum

ya saba da su.

• Zai sa ka sha fiye da kima, ma'ana, maimakon sau daya, sai ka sha sau biyu kafin ya yi ma magani.

• Za su iya zamar ma jiki, ka dinga jin in har ba ka sha ba za ka ji kamar ba ka da lafiya.

Mutum kan kasance cikin rashin laka, jikinsa ya yi rauni ba kwari yayin da yake halin damuwa a hadarin da ya hadu da shi. Wannan ya sha banban da bacin rai kawai don ya kan shafi lafiyar mutum kuma yana dadewa a jikin mutum. Ana iya maganin wannan matsalar ta shan magani ko ta hira da kwararru a kan matsalar.

5

Page 7: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

This leaflet is based on material produced by the Royal College of Psychiatrists (www.rcpsych.ac.uk/info). © 2014 The Royal College of Psychiatrists. Reproduced by permission.

Matakan jurewa bayan jirkitar hankali

Matakan jurewa bayan jirkitar hankali

Page 8: Matakan juriya bayan jirkitar hankali sanadiyyar Hadari ko ...GABATARWA Rashin lafiya ta jiki da cuta farat daya, afkuwar hadari ko saukar annoba, wasu abubuwa ne da kan jefa mu cikin

HEAD OFFICE:6th Floor Foreshore Towers

2A Osborne Road, Ikoyi Lagos.Tel: +234 (0)812 957 5052

+234 (0)807 717 7335+234 (0)816 354 6061

Email: [email protected]

KANO OFFICE:15 Usman Baraya Streetoff Yahaya Gusau Road,

Sharada (Rinji), KanoKano State.

Tel: +234 803 334 0089

ABUJA OFFICE:Asokoro Lifestyle & Business Centre

84 Kwame Nkrumah Crescent Asokoro, FCT - Abuja.

Tel: +234 (0)812 957 5052+234 (0)807 717 7335+234 (0)816 354 6061

For more information please contact:[email protected]

or +234 (0)807 717 7335

You can also visit www.mmfng.org

to view the activities of the Foundation