matsayin aure a musulunci - nazari a kan al'adun da aka kago a aure

14
MATSAYIN AURE A MUSULUNCI: NAZARI A KAN MUNANAN XABI’UN DA AKA QAGO A BIKIN AURE Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmān Sashen Koyar da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria +2348026499981 ([email protected])

Upload: tarbiyyarmusulunci

Post on 26-Jun-2015

260 views

Category:

Documents


34 download

TRANSCRIPT

Page 1: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

MATSAYIN AURE A MUSULUNCI:

NAZARI A KAN MUNANAN XABI’UN

DA AKA QAGO A BIKIN AURE

Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmān

Sashen Koyar da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria

+2348026499981 ([email protected])

Page 2: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

GABATARWA

Aure aya ce daga cikin ayoyin Allah kuma ni’ima ce daga cikin

ni’imominSa da Ya yi a kan Manzanni

إليها لتسكنوا أزواجا أنفسكم من لكم خلق أن آياته ومن ... [Ruum, 30:21]وذرية أزواجا لهم وجعلنا قبلك من رسال أرسلنا ولقد[Ra’aad, 13:38]

An shar’anta aure, aka qarfafe shi, kuma aka kwaxaitar da shi

ورباعا وثالثا مثنى النساء من لكم طاب ما فانكوا ... [Nisaa, 4:3]وجاء له فإنه بالصوم فعليه يستطع لم ومن فليتزوج، الباءة منكم استطاع من الشباب معشر يا

[Bukhari da Muslim]

بكم مكاثر فإني الولود؛ الودود تزوجوا [Abu Daawud; Nasaa’i]

النصارى كَرهبانية تكونوا وال األمم، بكم مكاثر فإني تزوجوا [Baihaqi] An hana tabattul; kuma barin aure don yi ibada, ya sava wa Sunnah

التخصر فى هريرة وأبى التبتل فى مظعون بن عثمان حديث[Bukhari]

منى فليس سنتى عن رغب فمن سنتى النكاح[Bukhari]

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 2

Page 3: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

HUKUNCIN AUREMusulunci ya kwaxaitar da yin aure a matsayin aikin ibada da a

ke so; kuma hanyar Annabawa.

Da yawa daga Malamai na ganin cewa aure a haqqin xaixaikun

mutane yana xaukar xayan hukunce-hukuncen Shari’a guda biyar( التكليفية األحكام ): waajib; istihbaab; jaa’iz; makruh; haraam

Maganar da ta fi qarfi ita ce, aure mustahabbi ne ko da ya ke yana

kai wa matsayin wajibi a kan wanda ke da ikon yin aure, da

xaukar xawainiyar iyali, kuma ya ke tsoron aukawa cikin zina

idan bai yi ba, saboda Hadisin Manzon Allah (SAW):

فاليتزوج البائة منكم استطاع من الشباب معشر يا... [Bukhari]Wajibi ne a kan al’umma gaba xayanta ( الكفاية فرض ) ta qarfafi

al’amarin aure; ta kare martabarsa; kuma ta sauqaqe hanyoyin

yinsa.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 3

Page 4: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

MATSAYI/MUHIMMANCIN AURE A MUSULUNCI

Aure ya qunshi qulla qwaqqwarar alaqa a tsakanin namiji da mace,

wadda za ta halatta masu zaman tare a matsayin ma’aura, da kuma

jin daxin juna, bisa niyyar bauta wa Allah (TWT).

Allah (TWT) Ya shar’anta aure a matsayin halattaciyar hanya guda

xaya tilo ta samar da ‘ya’ya da kuma yawaita jama’a a doron qasa,

in ban da hanyar kuyangi/sa xaka.

Ta hanyar aure ne a ke samar da iyali a matsayin babban rukunin

al’ummar Musulmi.

Aure na daga matakan da Shari’ar Musulunci ta bi wajen ba da

kariya ga nasaba da mutuncin al’umma.

Aure na da matuqar muhimmanci a cikin tsarin zamantakewar

al’umma, kasancewar yana kare haqqoqin maza da mata da `ya`ya,

xoriya a kan biyan buqatar xabi’a da sha’awa, da kuma gyara

tunanin mutane da kyautata addinin jama’a.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 4

Page 5: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

MATSAYI/MUHIMMANCIN AURE A MUSULUNCI

Auren da aka gina shi a kan soyayya da qauna, da girmamawa da

mutunta juna, da kyautatawa na ba da gagarumar gudummuwa wajen

tabbatuwar al’umma da inganta al’amuranta.

Wannan ya sa Musulunci ya qarfafi aure kuma ya xauki matakan

dawwamar da shi ta hanyoyin: fifita addini da kyakkyawar xabi’a a

wajen zaven miji/mata; halatta kallon wadda a ke son a aura domin

kada a yi kitso da qwarqwata; sharxanta yardar wadda za a aura,

matuqar ta balaga; hana wa miji neman kamala daga wajen matarsa,

da bayyanar da muhimmancin yin haquri da juna; halatta wa mutane

shiga cikin al’amarin ma’aura domin yin gyara da sulhu a

tsakaninsu, idan akwai buqatar haka; halatta qarya (ba yaudara ba) a

tsakanin ma’aura domin zamantakewa ta qara danqo; da wajabta wa

ma’aurata zamantakewa kyakkyawa a tsakaninsu, ta hanyar bayyana

wa kowannensu haqqoqinsa, da kuma haqqoqin da ke kansa.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 5

Page 6: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

8/15/2010 A.B. Dogarawa, A.B.U., Zaria 6

ME YA SA A KE YIN AURE?

Manufofi da Fa’idodin Aure

Manufofi Fa’idodi

Xorewar jinsin xan Adam

Biyan buqatar sha’awa ta xabi’a

Samun natsuwa da sukuni

Samar da iyali da yawaita al’umma

Samun kamala a cikin al’umma

Xa’a ga Allah (TWT) da Manzon Allah (SAW)

Samun ladan ciyarwa

Kamewa daga zina da tsare mutunci

Amfana daga addu’ar xa na qwarai bayan mutuwa

Samun ladan tarbiyya da xaukar xawainiyar `ya`ya

Dacewa da abin da Manzon Allah (SAW) ke so

Raya Sunnar Annabawa

Dacewa da taimakon Allah saboda kange kai

Page 7: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

ABUBUWAN HANI WAJEN NEMAN AURE

Rashin kiyaye sharuxxa da rukunan da Shari’a ta tanada

game da aure

Kaxaituwa tsakanin saurayi da budurwa wajen

zance/hira ko zuwa unguwa ba tare da muharrami ba

Tava wadda a ke nema ko rungumemeniya ko sumbantar

juna

Maganganun da ba su dace ba a kan waya ko yanar gizo

Aikawa da saqonnin batsa ko hotunan tsiraici

Mu’amalar ma’aura don kawai an sanya rana/baiko tun

kafin xaura aure

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 7

Page 8: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 8

AL’ADUN DA AKA SHIGAR CIKIN AURE

Credit

Qin neman iznin waliyyai kafin a fara magana

Gaisuwar uwa da uba da kayan baiko/sanya rana

Kallafawa mai neman aure zuwa gaishe da dangi

Amfani da zoben sanya rana

Kallafa wa kai buga katin gayyata

Ashobe/kayan anko

Sanya kayan coci da yanka cake a lokacin biki

Al’adu

Page 9: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 9

AL’ADUN DA AKA SHIGAR CIKIN AURE

Credit

Yi wa motar Ango/Amarya adon flower

Abincin bikon Amarya

Kayan qawayen Amarya

Tsanantawa wajen motocin xaukar Amarya

Tilasta kwana a gidan Amarya bayan an kai ta

Buxen kai

Kayan sayen baki

Al’adu

Page 10: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

ILLOLIN QAGO AL’ADU A CIKIN AURE

Yawan `yan mata da zawarawa a cikin al’umma saboda rashin

waxanda za su iya yin abubuwan da a ka tsawwala a cikin aure.

Xaukar aure a matsayin wata al’ada da ta shafi haxuwar mace

da namiji don kawai biyan buqatar sha’awar rai.

Rashin qimanta aure a matsayin ibada, da kuma qin la’akari da

manufar Shari’a game da aure.

Jawo wa addini raini da gori a idon waxanda ba Musulmi ba, da

kuma dakushe hasken kevantacciyar karantarwar Musulunci da

tsarinsa na rayuwa.

Kamanceceniya da waxanda ba Musulmi ba a cikin waxansu

al’adun.

Yawan matuwar aure.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 10

Page 11: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

MUTUWAR AURE A CIKIN AL’UMMA

Rashin fahimtar manufar aure a Musulunci

Auren dole

Rashin tattaunawa a tsakanin ma’aura

Talauci da sauran matsalolin rayuwa

Rashin ba da muhimmanci ga rayuwar aure

Canjin tunani game da abokin zama

Rashin samun yadda a ke zato daga abokin zama

Rashin kula da haqqoqin aure

Ha’intar abokin zama, da rashin kamun kai

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 11

Page 12: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

MUTUWAR AURE A CIKIN AL’UMMA

Shaye-shayen barasa ko abubuwan da ke gusar da hankali.

Cin mutuncin abokin zama, ko wulaqanta surukai.

Yawan duka ko zagi.

Rashin sanya ido daga iyaye ko kuma rashin tarbiyya tun

daga gida, kafin aure.

Rashin sanin hanyoyin warware matsala idan ta auku.

Rashin agaji daga al’umma.

Son kai, ko bin son zuciya a tsakanin ma’aura.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 12

Page 13: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 13

Ikhlaas

Fahimtar manufa

Kiyaye Shari’a

Haquri

Koyi da Magabata

Qoqarin faranta wa abokin zama rai

Neman yardar Allah

Qoqarin sauke nauyiGudanar da rayuwa yadda ta ke

MAGANCE MATSALAR MUTUWAR AURE

Page 14: Matsayin Aure a Musulunci - Nazari a Kan Al'adun Da Aka Kago a Aure

KAMMALAWA

A yau, rayuwar aure na cikin matsanancin hali, kuma tana

fuskantar qalu-bale daga cikin gida da waje. Hakan ya sa

al ’amarin aure ya ke tangal-tangal, kuma da yawa mutane ba su

kai wa ga cinma manufar da ta sa Musulunci ya Shar’anta aure.

Akwai buqatar Musulmi su dawo cikin hayyacinsu; su sake

nazari cikin al ’amuransu; su qara fahimtar matsalolin da harkar

iyali ke fuskanta a cikin al ’umma; sannan su ba juna shawarwari

game da hanyoyin magance su.

Sunday, August 15, 2010 Ahmad Bello Dogarawa, A.BU., Zaria 14