menene kasuwancin da ba kudin ruwa a · pdf fileba zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi...

20
Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a cikinsa (Banki, Saka jari, da Inshora) Kasuwanci na gari bisa adalci da sanin hakkin zamantakewa. ? www.noninterest.org.ng

Upload: lekhue

Post on 06-Mar-2018

305 views

Category:

Documents


18 download

TRANSCRIPT

Page 1: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a cikinsa

(Banki, Saka jari, da Inshora)

Kasuwanci na gari bisa adalci da sanin hakkin zamantakewa.

?

www.noninterest.org.ng

Page 2: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron
Page 3: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

3

Kasuwancin da ba kudin ruwa ya haramta karba ko biyan kudin ruwa. Dukkanin addinai masu alaqa da Annabi Ibrahim (wato addinin Musulunci, addinin yahudu, da addinin Kirista) sun yi hani ga karba ko biyan kudin ruwa.

Kasuwancin da babu kudin ruwa bai yarda da saka kudi ko yin harka a cikin duk ma’amallar da za ta iya kawo barna ko bata tarbiya a tsakanin al’umma ba.

Kasuwancin da babu kudin ruwa a cikin saWani nau’i ne na kasuwanci dake kunshe da ka’idoji da hani bisa ga karba ko biyan kudin ruwa. Kasuwancin da ba kudin ruwa an fi saninsa da kasuwancin musulunci a kasashe masu yawa.

* Tushe: 1) The Banker Islamic Report, watan nuwamba shekara ta 2013.2) Ernst & Young World islamic Banking competitiveness Report shekarar 2013-14.

ALKALUMMA DAKE NUNA GIRMAN BANGAREN

KASUWANCI DA BA KUDIN RUWA A CIKINSA A DUNIYA*

Mu’amaloli Kasuwanci da babu kudin ruwa a cikinsu ko kuma hada hada ta tsarin musulunci ana samun su a kasashe sama da 37

a kididdiga ta 2013.

Kamfanonin kasuwanci 349 ne suke gudanar da hada hadar kasuwancin su ba tare da kudin ruwa ba a fadin duniya gaba daya. Haka kuma

kamfanonin inshora guda 86 a kididdiga ta 2013.

Cikin shekarar 2013 mizanin hada hadar kasuwanci da babu kudin ruwa a cikinta a duniya ta kai $1.3 triliyan. Kuma kasuwar ta na kara habaka

da bunkasa duk shekara da misalin kashi 16 bisa 100 tun shekarar 2006.

Kasar Ingila ita ce kasar turai da ta fara karbar bashi na hannun jari na Sukuk na pan miliyan 200 (£200m) a shekarar 2014.

Rahotanni sun nuna cewa tsarin kasuwanci na musulunci yana ta bunkasa a Afrika. A halin yanzu a kwai hada hada ta sama da dala

biliyan goma ($10bn) a kididdiga ta 2013.

Jihar Osun a Najeriya ta sami nasarar karbar bashi ta wannan hanya (da ba ruwa a ciki) na kimanin

kudi dalar Amurka miliyan saba’in ($70 million).

Page 4: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

4

Wadannan sune ka’idojin da ke jagora ga kamfanonin da basa ta’ammali da kudin ruwa a Najeriya:

Ka’idojin kasuwancin da babu kudin ruwa

Kyautatawa cikin zamantakewar Jama’a ta hanyar taimakawa marasa karfi

Hani da gujewa harkoki da basu yi daidai da dabi’u masu kyau ba, da harkoki da ke gurbata tarbiyar al’umma, kamar kasuwancin taba sigari, giya da duk abu mai saka maye, naman alade, caca, karuwanci da kuma fina finan batsa.

Yadda da Qaddara (Kasuwanci yana tare da asara hakazali samun riba)

Duk wanda ke bukatar samun riba to dole ne ya dauki qaddara (watau ya san akwai yiwuwar yin asara). Ba zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, don haka duk mai nema sai ya san da yiyuwar aukuwar haka.

Hana ta’ammalli da kudin ruwa

Tara dukiya ta hanyar rashin adalci ko cin kudin ruwa, hanyoyin ne da suke kara wa mai karfi, karfi su kuma kara talauci a cikin jama’a.

Dalilai na tattalin arziki

Hada hadar kasuwanci ya kamata ya kasance yana da alaqa ne na kai tsaye da tattalin arziki na kasa. Duk Naira daya da bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa ya kashe, yana yin hakane kan harka da zata kara habaka arzikin kasa da jama’a baki daya. Misali kamar gina hanyoyi, gidaje, taimakawa kananan sana’o’i, ko taimakon manoma wajen saya masu kayan aiki.

Adalci, daidaito da fayyace komai a fili

Masu kasuwanci ya kamata su sami cikakken bayani game da sharuddan kasuwanci da za su shiga. Rashin cikaken bayani kan iya jawo rashin fahimtar juna da matsaloli don haka ya kamata a guju hakan.

Page 5: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

5

Manyan addinai masu alaqa da Annabi Ibrahim (wato addinin Musulunci, addinin Yahudu da addinin Kirista) duk sun yi tarayya akan kyamar ta’ammalli da kudin ruwa. Za a iya ganin misalan wannan kyama a cikin litittafan wadannan addinai kamar haka;

Abubuwan da addinan dake da alaqa da Annabi Ibrahim sukayi tarayya da juna akai

Zabura Sura 15 aya 1-5: “Wanene zai dawwama a cikin aljannar ka, wato tudun ka tsattsarka? Shine mutumin da yabi hanya madaidaiciya, ya yi aiki na gari sannan ya riki gaskiya a zuciyarsa. Wanda baya bada rance da kudin ruwa, wanda bai zalunci mara karfi ba wanda yayi wannan yana da babban rabo.”

Deuteronomy (Littafin Attaura na 5), Sura 23, aya 19 : “Kada kuba danginku rance da ruwa, ko rancen kudi, kona abinci, ko na wane irin abu da akan badashi da ruwa”

Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron Allah, ku bar abunda yake daga riba idan kun kasance masu imani. Idan baku bari ba, to ku shirya damarar yaki da Allah da ma’aikinsa. Amman idan kuka bari dukiyoyinku na asali halaliyar ku ne kada kuyi zulunci kuma ba za’a zalunce ku ba”

Page 6: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

6

Hukumomin da ke lura da al’amuran hada hadar kasuwancin da ba kudin ruwa a Najeriya

Kamar Yadda Baban Bankin Najeriya (CBN) ke lura da aiyukan bankunan Najeriya, haka bankin na CBN ke lura da duk mu’ammallolin da bankunan da basa ta’ammali da kudin ruwa ke yi. Kamar Kuma yadda Hukumar Inshorar Bankuna ta kasa (NDIC) ke kare kudaden masu ajiya a bankunan Najeriya, haka hukumar ta NDIC ke kare kudaden masu ajiya a bankunan da basa ta’ammali da kudin ruwa.

A bisa ga tsaretsaren da hukumar NDIC ta gabatar:

“Mafi girman ajiyar bankuna da hukumar NDIC ke karewa ga masu

ajiya a bankuna da basa ta’ammali da kudin ruwa daidai yake dana sauran bankunnan ajiya a Najeriya. Akasarin kudin da hukumar ke karewa shine

₦500,000 akan kowane asusun ajiya a manyan bankuna da kuma ₦200,000 akan kowane asusun ajiya a kananan

bankuna (micro finance).”

Bankunan da basu ta’ammali da kudin ruwa na gudanar da hada hadar su ne a kan ka’idojin kasuwanci da musulunci ya kafa. A domin haka suna bukatar karin shugabanci da biyayya fiye da sauran bankuna domin tabbatar da hada hadar su na tafiya dai dai da ko bisa tsarin

shari’ar Musulunci. Ko wane bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa yana da majalinsar malaman musulunci da ke yi masa jagora akan duk harkokinsa. Haka zalika a karshen kowace shekara, majalisar malaman tana b wa bankin takardar shaidar tabbatar da biyayya na wadannan bankunan a bisa tsarin musulunci.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya bukaci dukkanin bankunan da basa ta’ammali da kudin ruwa su saka taswirar wannan hoto dake kasa a duk takardunsu na tallace-tallace.

Hada hadar hannun jari da ba kudin ruwa a ciki wanda kuma ake kira da hada hadar kasuwancin hannun jari na musulunci na samun kulawar hukumar dake kula da hada-hadar hannun jari a Najeriya da ake kira da suna; Securities and Exchange Commission (SEC)

A kasar Ingila da sauran kasashe na duniya, hukumomin kula da harkokin kudade sun kirkiro da tsare tsaren gudanarwa domin tabbatar da kulawa da sa ido ga wannan fanni na kasuwanci da ba babu kudin ruwa a cikinsa. Dadi a kan haka, hukumomi masu kula da hadar-hadar kudade a kasashen duniya dabam-dabam na cigaba da aikin su na tabbatar da daidaito tsakanin bankunan musulunci da sauran bankuna na gama gari.

Page 7: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

7

Bankin da baya hada-hada da kudin ruwa wani nau’i ne na banki da aka kawo domin duk’yan Najeriya ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba. Wato shi wannan banki ko wane irin mutum na iya bude asusu a cikinsa kuma yayi harka dashi. Da yawa daga cikin ka’idojin gudanar da bankin da babu kudin ruwa a ciki, ka’idoji ne da addinai da yawa suka yarda dasu. Kaidoji kamar su adalci tsakanin jama’a, taimakekeniya, gaskiya da rikon amana tsakanin jama’a da suka kulla alakar kasuwanci a tsakaninsu, kore duk wata baraka ta harkokin gudanarwa da bayanai da kuma batanci kamar gurbata farashi, rashawa da zalunci.

Mutane da dama a duniya masu bin tsarin addinai daban daban da ma wadanda basu da addinin na nuna sha’awarsu ga tsarin hada-hadar kasuwanci wanda ba cuta ba cutarwa. Sunyi bayani game da kyamarsu akan illar da kudin ruwa ke haifarwa.

Bankin da ba kudin ruwa na kowa da kowa ne, bana wasu kayyadadun al’uma ba ne

“Kaidojin da aka gina harkar kasuwancin musulunci a kai na iya kara kusanci da dankon zumunci tsakanin bankunan da abokanan huldansu na kuma tabbatar da cikakken yakini na hada hadar ko wane irin kasuwanci” a fadin Mujjalar fadar paparoma ta Vatican (Osservatore Romano 04/03/2009)

Page 8: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

8

Manufofin Bankin da baya ta’ammali da kudin ruwaA kowace al umma babban aikin bankuna shine karbar ajiyar kudi daga bangaren da ke da yalwa (masu ajiya) domin baiwa wadanda ke bukata (masu karbar bashi).

A duk inda bankuna ke gudanar da harkokinsu bisa tsari na karba da biyan kudin ruwa, hakan kan haifar da wariya ga wasu bangare na jama’a da basu yarda da wannan tsari ba a bisa ga dalilai na addini ko tarbiya tunda ba zasu iya mu’amala da bankuna masu ta’ammali da kudin ruwa ba.

Wannan wariya kan haifar da mummunar tasiri ga al umma ta hanyar gurbatar tattalin

arziki da hada hadar kudi a kasa da kuma kawo nakasu ga cigaban arizikin kasa. Bayanai da aka samu daga kamfanin EFInA a Najeriya ta shekarar 2012 ne ya nuna haka.

Kimanin mutune miliyan 39.9 (wato kaso 39.7 cikin dari na al ummar Najeriya) basa samun damar mu’amala da banki. Kafa bankuna da basa hulda da kudin ruwa yana daya daga cikin hanyoyin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da kawo cigaban al umma.

BAYANAI KAN KASUWANCIN BANKIN DA BABU

KUDIN RUWA A NAJERIYA*

A. Mutane a kalla dubu dari uku ne (kashi 0.3 cikin dari) na kididdigar yawan jama’a ke mu’amala da bankin da

babu kudin ruwa a cikin sa a Najeriya.

B. Daga cikin masu mu’amalla da Bankin da babu kudin ruwa a cikinsa, kashi 57.9 cikin dari maza ne, kashi 42.1

cikin dari kuma sun kasance mata ne.

C. Manyan kalu bale guda uku dake hana jama’a hulda da bankunan da babu kudin ruwa a cikinsu a Najeriya sune; karancin ilimin yadda harkar bankin take, rashin ra’ayin

amfani da bankin da kuma rashin fahimtar shi kansa harkar bankin.

* Tushe: Binciken EFInA akan samar da hanyoyin hada hadar kasuwanci na zamani shekarar 2012

Page 9: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

9

Bankin da ba ya ta’ammali da kudin ruwa yana cinikayya ne da kadara, da kuma hidima/aiki na zahiri da akan anfana dashi.

Wanna tebir na kasa yana nuna banbance banbance tsakanin bankunan da ba sa ta’ammali da kudin ruwa da sauran gama garin bankuna.

Manyan banbance banbancen dake tsakanin bankuna na gama gari da kuma bankuna da basa ta’ammali da kudin ruwa

Gama garin Banki Bankin da ba ya ta’ammuli da kudin ruwa

Kudi wani haha ne kuma ana amfani dashi wajen musaya da kuma adana kadara.

Anan Kudi ba kadara bane, kawai dai ya na da amfanine wajen musaya da kuma wajen

ajiye/adana dukiya.

Ana amfani da shudewar lokaci wajen kayyade kudin ruwan da za a kara akan uwar

kudi.

Cin riba ta hanyar ciniki ko bayar da hayar kadara sune manyan hanyoyin samun riba.

Ana karbar kudin ruwa ne akan duk bashin da aka bada, bayan an karbi jinginar kadara. Bankin baya daukar wata asara akan ciniki.

Bankin yana daukar kasada, ya sayi kadara, sannan ya sayar ko ya bada haya. Ribar da

aka samu daga sayarwa ko kudin haya da za’a karba sune ake rabawa tsakanin bankin da

masu ajiya a bankin.

Wajen sayan kadara (kamar mota ko gida), bankin zai bada bashi ne na kudi ya dora kudin ruwa akai. Sai mutum ya je ya sai

kadarar da yake bukata.

Bankin zai sayi kadarar da fari sa’annan ya bayar haya ko ya sayar wa abokan ciniki (ya

dora riba akan farashin da ya saya sannan ayi lamuni abiya a hankali).

Banki na gama gari yakan ninninka kudin ruwa akan duk abin da yake bi bashi.

Riba ko kudin haya da akayi yarjejeniya a kansa ba zai canza ba.

Page 10: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

10

Bankin da ba ya hulda da kudin ruwa ba yana nufin bankin da ba a cin riba a cikinsa ba neRashin biya ko karbar kudin ruwa na bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa ba yana nufin ba ya cin riba bane ko masu ajiya a bankin basa samun wata karuwa daga ajiyarsu. A wannan banki ana raba ribar da aka samu ta hanyar kasuwanci (ta hanyar halaliya) tsakanin masu ajiya da masu hannun jari a bankin.

Bankin na samun riba ta hanyar saye da sayarwa. Yana kuma iya sayan kadara ya bayar da ita haya ga abokan huldar sa. Kudin hayar da bankin zai karba shine ribarsa a irin wannan harkar kasuwancin. Haka kuma yana iya sayen kadara ya saidawa abokan huldar sa ta hanyar dora riba akan farashin kayan da ya saya, wannan shine ribar bankin. Bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa na kuma iya cajar kudi a duk lokacin da yayi wa kostomarsa wata hidima kamar na bankin gama gari. Misali taransfa ta kudi.

Page 11: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

11

Hajojin da bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa ke hulda dasu

Page 12: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

12

Harkar sai da motaAna saye da sayar da mota ko wasu kadarori masu kamar haka ta tsarin da ake kira ijarah. A karkashin tsarin Ijarah banki na sayen motar da abokin cinikinsa (wato kostoma) yake so, kuma ya bai wa kostomar ita motar a matsayin haya zuwa wani kayyadajjen lokaci. Kostoman zai karbi motar da yarjejeniyar cewar, a karshen lokacin hayar zai sayi motar

daga hannun banki. Wannan ya bambamta da bashin mota da bankin gama gari ke bayarwa. Domin a karkashin tsarin ijarah, banki zai sayi motar a matsayin tasa kuma ya dauki duk wata asara daka iya tasowa a lokacin da abokin cinikin yake hayar motar.

1

Banki zai sayi ainihin motar da abokin ciniki yake muradi

2

Banki zai bawa abokin ciniki motar a matsayin haya, shi kuma ya dinga biyan bankin kudin haya a duk karshen wata

3

A karshen lokacin da aka kayyade na biyan kudin hayar, abokin ciniki zai sayi motar daga wajen banki

Page 13: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

13

Bankin da baya ta’ammali da kudin ruwa na huddar cinikayya ta hanyar saye da sayarwa abokan huldarsa kayan masarufi da sauran hajoji ta hanyar amfani da tsarin ciniki da ake kira da suna Murabaha. Kostoma zai zo da bayanin kayanda yake so banki ta saya masa. Bankin zai sayi kayan, ya kuma sayarwa kostoma bayan ya dora ribarsa. Wannan sabon farashi da aka sayar da kayan ba zai canza ba. Bayan bankin ya sayarwa da abokin cinikin zai bashi wani kayyadajjen lokaci da zai biya kudin kayan da aka sayar masa misali kamar watanni 12.

Wannan ya bambanta da cinikayyar bankin gama gari saboda anan bankin yana siyan kayan da farko sa’ilinnan daga baya ya siyar wa da abokin cinikinsa. Bayan haka bankin ba zai iya kara wa abokin cinikinsa wani kudi ba (a matsayin tara) idan har bai sami damar biya akan lokacin da aka yi ka’ida dashi ba. Wani muhimmin abin lura anan shine bankin na iya sanya tara ga abokin cinikin da bai biya akan kari ba, amma banki ba zai iya sa kudin tarar cikin ribarsa ba, sai dai ya bayar dasu sadaka.

Cinikayya ta kayan masarufi da sauran hajoji

1

Banki zai sayi kayan masarufin da aka zayyana

2

Daga baya kostoman zai sayi kayan daga wajen bankin a farashin da ya kumshi ribar bankin tare da yarjejeniyar cewa bankin zai yi lamuni ga kostoman akan ya biya a wani lokaci na gaba.

Page 14: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

14

Hannun jari mara kudin ruwa da inshora (Takaful)

Page 15: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

15

Harkar hannun jari da ba kudin ruwa acikinsa wanda aka fi sani da harkar hanun jari na musulunci na da ka’idoji kamar irin ka’idojin da hannun jari mai kyakykyawar akidoji ke dasu. Wannan na nufin masu kulawa da kudaden da akasa na hannun jari ba za su iya yin wata mu’amala ba mai mummunar akida ko wadda zata jawo cutar al’umma ba (kamar yadda aka yi bayani a shafi na 4 da ya gabata a baya) a bangaren hakkokin zamantakewar jama’a. Bayan haka karba ko biyan kudin ruwa ya haramta a cikin wannan. Sakamakon haka masu kula da kudade na hannun jarin da ba kudin ruwa a cikinsa baza su yi amfani da kudin dake da ruwa a ckinsa ba, haka kuma an iyakance masu irin kamfanoni da zasu saka jari ta wajen kayyade ma’amalar kudin ruwa dake cikin irin wadannan kamfanoni da zasu saka jari a cikinsu.

Alfanun da akan samu ta hanyan sanya jari da kasuwanci ta hanyar halaq (hanyar da ta dace da zamantakewar jama’a) kusan daya ne da abin da ake samu ta hanyar harkar sanya hannun jari da kasuwanci na gama gari. Kamfanoni da dama a duniya masu harkar sanya hannun jari da kasuwanci ta hanyar halaq (hanyar da ta dace da zamantakewar jama’a) kan sami riba da alfanu kwatankwacin wanda sauran kamfanonin masu huldar kasuwanci da sanya hannun jari na gama gari kan samu koma fiye dasu. Kamfanoni marasa hulda da kudin ruwa na harkoki da dama da suka hada da; saka jari a kamfanoni, gine gine

(gidaje, ofisoshi da sauransu), saye ko saida hannun jari na Sukuk da sauransu.

Zuba jari a takardun shaidun jingina da ake kira da suna Sukuk

Sa hannu jari a takardun shaidun jingina da suka dace da tsarin musulunci da ake kira da suna Sukuk shine ke daukar kaso mafi tsoka a bangaren kasuwar hada hadar hannun jari da babu kudin ruwa a cikinsa. Sukuk wata takardar ce da ke nuna shaidar mallakar kadara wanda ke baiwa mai rike da ita damar a bashi ribar da ake samu sakamakon amfani da kadarar. Jihar Osun ta Najeriya ta zamo jiha ta farko a Afrika da ta fara karbar bashin kudi kimanin Naira biliyan 11.4 domin gina makarantu a shekara 2013.

Fitattun ka’idoji na Sukuk

Ayyukan da za’ayi da kudaden Sukuk dole su kasance ayyuka ne da ba zasu zama masu cutar da alumma ba sa’annan su zama ayyuka ne da basu karya dokar muslunci ba.

- Ana amfani da kudin da aka tara ta hanyar sayar da takardun Sukuk ne domin ginawa, ko sana’anta wata kaddara

- Ribar Sukuk ana samunta ne daga yin amfani da kadarar da aka sana’anta da kudin Sukuk da aka tara (misali bada haya)

- Ana iya siyar da ko cinikin takardar shaida ta Sukuk

Hannun jari da ba kudin ruwa a cikinsa

Page 16: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

16

Yadda inshora da ba kudin ruwa a ciki ke aikiInshora ta gama gari wani nau’i ne na kasuwanci inda kamfanin inshora bayan karbar wani kayyadadden kudi daga hannun kostamarsa (mai sayan inshora) kanyi alkawarin daukar duk wata asara da ka iya afkawa wata kadara ta mai sayan inshoran ko kuma shi kansa kostoman ta hanyar biyansa kudi a matsayin diyya na asarar da ta faru dashi (misali; asarar konewar mota, asarar hadari, ko sata) da sauransu.

Gundarin ma’anar Inshorar da ba kudin ruwa a cikin ta (Takaful) shine bada kariya ta hanyar hada hannu da taimakon kai-da-kai. Tana kamanceceniya da inshorar kungiyoyin gama kai

Ka’idojin Takaful

Tarayya - Babban burin adashin Takaful shine biyan diyya na wata asara da ka iya afkawa daya daga cikin masu tara kudi a cikin asusun.

Mallakar Kudin Takaful - Wadanda suka tara kudi domin adashin Takaful suke da mallakar duk kudi da kuma riba da aka samu ta hanyar sarrafa kudin da aka tara. Yadda za’a raba ribar da aka samu ya danganta ne da tsarin Takaful da aka dauka.

Kore Shakka - Kudin da masu adashin

Takaful suka tara ana daukarsa ne a matsayin gudunmuwa ba kamar inshorar gama gari ba da suke karbar kudade domin daukewa mai kadara wata asara wacce ba lallai bane ta auku. Ana amfani da kudaden da aka tara ta hanyar gudumuwar Takaful domin tallafawa duk wani mamba wanda yake cikin adashin idan asara ta same shi.

Kulawa da kudaden gidauniyar Takaful - Ana kulawa da kudaden asusun Takaful ta hanyar tsarin ciniki na Mudarabah ko Wakalah ko kuma hadakar guda biyun.

Ka’idojin cinikin da za’ayi da kudin asusun Takaful - An haramta yin amfani da kudin asusun Takaful a hada hadar da ta kunshi mummunar akida kamar caca da kallon batsa. Ana bukatar a sarrafa kudaden ne ta hanyar saka su a cikin hada hadar kasuwanci da babu kudin ruwa a ciki.

Bambamci tsakanin inshora gama gari da Inshorar Takaful

Tsarin Takaful ya bambamta da inshora gama gari ta hanyoyi guda biyu. Na farko a tsari na Takaful, masu sanya kudi a gidauniyar Takaful kan tara kudadensu waje daya da zimmar ba da kariya tsakaninisu in har wata asara ta fadawa daya daga cikinsu. Idan har a karshen shekara aka sami rarar kudi da ta rage a cikin gidauniyar takaful (bayan an biya kudin kariya game da duk wata asara da ta afku ga daya daga cikin masu sanya kudade a gidauniyar), za a raba

Page 17: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

17

Gidauniyar Takaful

₦Masu sanya kudi a cikin gidauniyar Takaful

1

Hakkokin da aka biya

2 ₦Gidauniyar Takaful

Asusun hannun jari mai tsabta

Riba

3 ₦Asusun

Rarar da aka samu a hada hadar ciniki ta Takaful ana rabata ne tsakanin masu ajiya a gidauniyar Takaful da ma’aikata masu lura da gidauniyar. Kason da kowa zai samu ya danganta ne da tsarin Takaful da akayi anfani da shi

4 ₦Asusu

kudin tsakanin masu kula da gidauniyar takaful da kuma su masu sanya kudi a cikin gidauniyar. Karin bambamci na biyu shine, kamfanonin inshora na gama gari kan iya yin kowane nau’i na kasuwanci da kudaden da suke karba daga hannun masu sayan

inshora domin samin karin riba. A nasu bangaren, kamfanonin Takaful na iya sarrafa kudadensu kadai ne ta hanyoyin kasuwanci da suka dace da ka’idojin kasuwancin da ba kudin ruwa a cikinsa kamar yadda bayanin ya gabata a cikin wannan littafi.

Page 18: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

18

National Pension Commission Nigeria

HUKUMOMI MASU LURA DA KASUWANCI

MASU HARKAR HADA HADAR KASUWANCI

Babban abokan ciniki dake da kwarewaBabban abokin harkar kasuwanci

ABOKAN CINIKI

Page 19: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

19

Ita wannan kungiya mai suna EFInA Non-interest Finance Working Group an kafa ta ne a watan oktoba shekara ta 2009 a matsayin wani dandali da zai kawo hadin kai tsakanin ya’n kasuwa masu gudanar da harkokinsu a tsari da baya ta’ammali da kudin ruwa da kuma hukumomi masu lura da wannan bangare a Najeriya.

Domin neman karin bayani ziyarci shafin internet na:

www.noninterest.org.ng

Bayani kan kungiya da aka kafa domin kawo cigaban harkokin kasuwanci da babu kudin ruwa a cikinsu a Najeriya mai suna - EFInA Non-interest Finance Working Group

Page 20: Menene Kasuwancin da ba kudin ruwa a · PDF fileBa zai yiwu a samu riba ba sai an rungumi kaddarar samun asara, ... Qura’n 2 aya ta 278-279: “Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron

20

www.noninterest.org.ng