mujallar fim - july 2001

61
FIM, YULI 2001 2

Upload: trinhbao

Post on 01-Jan-2017

2.046 views

Category:

Documents


4 download

TRANSCRIPT

Page 1: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 20012

Page 2: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Ashiru Sani Bazanga

INA karanta mujallar Fim }warai da gaske. Duk wata ba ta wuce ni, saboda ina samun wasulabarai da suka shafi wannan harka da nake ciki. Domin ba komai ba ne zan sani ba, wani abin saina duba mujallar, musamman sharhin da ake kan finafinai. To, idan na karanta kuma na zauna nakalli fim ]in, sharhin na taimaka mani a matsayina na furodusa.

Shawarar da zan ba Fim ita ce, na riga na san duk inda jarida take ba a raba ta da maganganuwa]anda wani lokaci sukan iya haddasa fitina. Koda yake dai ita mujallar Fim tana }o}arin ganinta kauce wa irin wa]annan, duk da haka dai a yi }o}arin kauce wa abin da zai haddasa husumatsakanin wani da wata ko wani da wani, ko wata da wata.

SANI IDRIS KAURU (MODA), fitaccen dan wasa:

3

Abin da ya sa muke karanta mujallar

Tijjani Ibrahim

TIJJANI IBRAHIM BALA, shaharren daraktaNI dai ina karanta mujallar Fim saboda ta tsaya tsayin

daka wajen tace labarai ta yadda take buga su a sahihance.Ma�aikatanta kuma, gaskiya sun }warance da iya aiki.Ka san aiki, musamman na jarida, idan ba saninsa ka yiba ka ce za ka shiga, to akwai ha]ari, za ka yi ta tuntu~eda kurakurai, koda yake dai wasu }alilan kan shiga darana tsaka kuma sukan dace.

Shawarata ita ce, ku daure kan ri}e wannan }a�idaraikin jarida da mujallar Fim take bi a koyaushe. Inakuma so mujallar Fim ta ci gaba da zama garkuwarharkar fim da kuma }ara ya]a mutuncin �yan wasa daharkar fim gaba ]aya. Duk abin da zai tozarta harkar, aguje shi. Mujallar ta sani cewa har yanzu harkar fim nacikin sira]i, musamman nan Kano.

ALI NUHU, fitaccen dan wasa/furodusa

Sani Moda

MUJALLAR Fim, a wajena, ba wai na ]auke ta amatsayin takarda ce kawai ta karantawa a manta da ita ba.Abin da na ]auke ta shi ne, mujalla ce mai ilimantarwa dafa]akarwa, kuma mai wa�azi da nasha]antarwa. Tanasanar da ni abin da ban sani ba, kuma tana ba ni sha�awawajen nisha]antar da ni. Domin da zarar ina karantamujallar Fim sai in ji hankalina ya }ara kwanciya, sannankuma takan kare mani ba}in cikin da ke tare da ni.

ASHIRU SANI BAZANGA (SAWUN KEKE),fitaccen dan wasa/furodusa:

BA don komai nake karanta mujallar Fim ba, sai donyadda na fahimci cewa ita ka]ai ce mujallar da take bugasahihin labarin masu wayar wa jama�ar arewacin }asarnan da kawunansu a kan harkar shirin fim. Kai, ba maarewacin }asar nan ba, Nijeriya gaba ]aya babu lungunda ba a neman mujallar Fim.

Fati Suleiman

Ali Nuhu

Allah Ya }ara taimaka wa Ibrahim Sheme da ma�aikatansa saboda }o}arin da suke yi wajenha~aka al�ada da kuma harshen Hausa a duniya, ta hanyar buga ingantattun labarai a cikin mujallarFim. Allah Ya }ara ]aukaka ku!

FATI SULEIMAN, fitacciyar ’yar wasa:INA karanta mujallar Fim don in samu cikakken bayani a kan abin da yake faruwa a fa]a, idan

bai faru ba kuma babu }age; idan kuma an yi }aryar ya faru ne za su fa]a. Gaskiya shawarar da zanbai wa mujallar Fim shi ne yadda suke fa]in gaskiya suke rubuta gaskiya su ci gaba da yin hakan.Allah zai taimake su.

Page 3: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 20014

Tsokaci A Kan Auren �YanWasa Mata

amma har yanzu bayan watanni shiru kake ji.To anya ita ma ba ta bi sahu ba kuwa? Kodayake an ce ]an gida ne. Ita kuwa ]ayar daman ba ta ambata ba. To wallahi inashawartarsu da su yi aure, kar su bari suzama kamar su wance da suka fara fitowa afim a matsayin tsofaffi bayan tsoffin namuna fim, wa]anda ba su wuce yawan yatsunhannu ba, suna nan. Amma su ma tsofaffinakwai bayani a kansu, amma sai nan gaba inna gama bincike kansu a }o}arin da nake naba da shawarwari don a gyara wannan sana�a.Akwai wacce ta ce gwanin nata yana wanibabban birni daga cikin biranen }asar nan,amma sai yanzu muka ji abin ya koma wanibirnin da ke da take da ke cewa �... ko da me

BATUN aure da �yan wasa mata kullumsuke cewa za su yi yana bu}atardogon tunani da natsuwa. Daga

cikinsu dai akwai wacce ta yi aure na burgewawanda aka yi ta yayata shi a mujallar Fim dabakunan mutanen gari, amma kash! sai aurenya zo }arshe bayan �yan watanni. Abin murnaya koma abin haushi. Sakin ya faru a lokacinda ita jarumar take da ciki na wasu �yanwatanni; ga cin mutunci da zarge-zarge. Itadai wannan yarinya tana da hankali, ganatsuwa da kamun kai. Don idan ka ce acikin �yan fim babu yarinyar da ta kai tahankali, zan iya cewa ba ka yi }arya ba. Tosai ga shi hakan ta faru a kan ta.Me za ka ce a kan sauran marasa kunya da

rashin kamun kai wa]anda idonsu ya bu]eda samu ku]i? In ka ce kana tsoron aurensuai kana da gaskiya. Ko wacce aka tambayasai ta ce ai babban burinta shi ne aure. Anyaba fakewa suke da guzuma ba suna harbinharsana? To malam, yarinya ce take samuna}alla N5,000 a wata, to ko ma�aikatangwamnati ai sai wane-da-wane za su samihaka. Anya za ta yi ha}uri ta zauna da talakamai-hannu-baka-hannu-}warya in ba tanatsananin son mijin ba kuma tana da tsoronAllah? Anya a cikin �yan fim mata akwai maialamun wa]annan halaye bayan ita waccanda }addara ta fa]a a kanta? Babu ma kamarwa]anda suke ganin sun shahara. Har fa damasu kasuwanci a cikinsu. To in ka aure takai za ta dan}a wa harkokin ko ko yaya za ayi? Ko �mijin Hajiya� za ka zama? Allah yasauwa}e!Akwai wasu kyawawa guda biyu a yanzu;]aya ta ce bayan Sallah za ta yi auren, to

Wasu wadanda suke zaune a gidajen mazansu: Fati Mohammed 1, Halisa Mohammed, Dayyaba Isyaku

DAGA

SHU’AIBU A. UMARRA’AYI BA GABA BA NE

Fa]i Son Ka

ka zo...� Ita kam watakila abokin sana�arta]in ne zai kwashe ta, bayan wancan an cemana ma�aikacin gwamnati ne. To ba mu saniba ko shi ne ya dawo suna sana�a ana samu.In ko haka ne, ni ma ba za a bar ni a baya ba,don ni ma ina da masoyiya cikin kyawawanguda biyu masu tashe.

An sha yin soyayya a tsakanin �yan wasamaza da takwarorinsu mata. Sai dai ba musan matsayin wannan soyayya a addinanceba ko al�ada. Kuma ba mu san nau�in da za tafa]o daga cikin nau�ukan soyayya ba. Anyata gaskiya ce? In ko ba ita ba ce, Allah yatsare mu da ita!

Na gode wa wata mujalla da ta ta~a yinsharhi a kan irin wannan soyayya.

Wasu da aka sako: Halima Adamu Yahaya da Jamila Haruna Yakasai

Page 4: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

5

Muna maraba da wasi}un masukaratu. A tabbatar an sa cikakkensuna da adireshi, kuma a yirubutu mai kyau. A ta}aitabayani. A aiko da sauri zuwa gaEdita, FIM, P.O. Box 10784,Kano. Tel.: 062-417347;243112E-mail: [email protected]

Wasi}u

MAWALLAFIIbrahim Sheme

*DARAKTA

Alh. Garba Dangida*

MATAIMAKIN EDITAAshafa Murnai Barkiya

*WAKILAI

Kano: Kallamu Shu’aibu, Yakubu IbrahimYakasai; Kaduna: Iro Mamman, Aliyu

Abdullahi Gora; Jos: Sani MuhammedSani; Katsina: Bashir Yahuza;

Sokoto: Bashir Abusabe*

MARUBUTA NA MUSAMMANDanjuma Katsina

Halima Adamu Yahaya*

KASUWANCIMukhtar Musa DikwaSadiya Abdu Rano

Jamila Yakubu*

HOTOBala Mohammed

*KOMFUTA

Mary Isa Chonoko,Mohammed K. Ibrahim

*MASHAWARTA

Alh. Kasimu Yero, Dr. Abubakar A.Rasheed, Alh. Yusuf Barau, Haj.

Balaraba Ramat Yakubu, Alh. Sa’idu M.Sanusi, Alh. A. Maikano Usman,

Alh. Habibu Sani Kofar-Soro*

LAUYOYIMamman Nasir & Co., Kaduna, Sadau

Garba & Co., Kaduna

Mujallar FIM (ISSN 1595-7780) tana fitowane a kowane wata daga kamfanin Fim Publi-cations , No. 22, Zaria Road, Gya]i-Gya]i,by Fly-over, Kano, Nijeriya. Ofishinmu aKaduna: S. 11, Ibrahim Taiwo Road, samanasibitin �Ya�u Memorial,� gefen Kasuwar Barci,Tudun Wada, Kaduna. A aiko da dukkanwasi}u zuwa ga Mujallar FIM, P.O. Box 10784,Kano. Tel.: 062-417347, 243112.Adireshinmu na E-mail: [email protected] a yarda a sarrafa kowane ~angare na wannanmujalla ba tare da izini a rubuce dagamawallafanta ba. Mai sha�awa zai iya karantaFim kyauta a ko�ina a duniya ta hanyar Internetta wannan adireshin: www.kanoonline.comHa}}in mallaka (m) Fim Publications

DALILIN da ya sa na yo mukuwannan wasi}ar shi ne shin yaya

maganar auren jaruma Fati Mohammed?Mun ji ta ce za ta yi aure amma har yanzushiru kamar an jefa dutse a ruwa. Ko anyi ne cikin sirri mujallar Fim ba ta gayamana ba? Domin ba mu da wata mujallada muke karatu da ta wuce ta. Ko maganarauren ta rushe? Ko ta ga sana�ar fim ta fimata auren? To gaskiya idan haka ne donAllah ta yi aure tun darajarta ba ta fa]i gamutane ba. Domin darajar mace ]akinmijinta.

A }arshe don Allah ku isar min dagaisuwata zuwa ga Mandawari, Zilkifilu,Galin Money, da Sanusi Burhan.

Abdullahi Bello Ubandawaki,Sultan Atiku Secondary School

Sokoto, PMB 2277, Sokoto.

FATI, KI MANTA DA BAYAZUWA GA FATI MOHAMMED,

A GASKIYA ni dai na ji da]in wannan aure da Fati za ki yi. Ga garga]i koin ce jan kunne zuwa gare ki. Fati duk wani wasa da kika yi a baya kada

ki yi lissafi da shi. Ki tsaya ki yi zaman aure saboda darajar ]diya mace tana]akin mijinta. Hakika kin nuna bajinta tare da taka rawar gani a filin fa]akar damutane. Wannan kuma aure da za ki yi ki ha}ura ki zauna gidan mijinki ki rufama kanki asiri; ba ke kanki ba hatta sauran �yan wasa ma za ki rufa masu asiri.Ki yi lissafi da abin da ya samu �yan�uwanki kamar su Halima Adamu Yahayada Jamila Haruna, koda yake su ma ba da son su ba haka ta faru gare su, sabodaabin da Allah Ya }addara Annabi sai ceto. Kuma na ji an ce kina da kishiya. Toki tsaya ki yi biyayya ga mijinki kuma da kishiyarki. Allah Ya ba ku �ya�yanagari masu albarka da son addini.

Umaru Abarchi (Dits) Sanda,Unguwan Buzu Dan Zambadi Commercent, Maradi, Nijer.

KI AIKO MANI DA TAKARDAR GAYYATAZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto muku wannan wasi}a tawa shi ne don in bayyana farincikina kan labarin auren fitacciyar �yar wasa Fati Mohammed da Sani

Musa Mai Iska wanda kuka buga. Ina fatan alheri da addu�ar Allah Ya ba daalbarka, amin! A }arshe ina fatan Fati za ta aiko min da takardar gayyata. Allah

immediatepast

edition

AUREN FATI: ME YA HANA?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

(ISSN 1595-7780)Jagorar Mujallun Hausa

Mujallar FIM a ‘Internet’Za ka iya karanta mujallar Fim kyauta a ko�ina kake a duniya tahanyar zamani ta �Internet.� Kawai ka duba wannan adireshin ana�urar komfuta ]in ka, za ka ga fili mai suna �Publications.�Acikinsa za ka ga mujallar baki ]ayanta, watowww.kanoonline.com/Publications

WWW.KANOONLINE.COM

Page 5: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 20016

Wasi}u

Duk wani wanda yake so yafa]i wani abu muhimmi a kanharkar finafinan Hausa,to a Mujallar FIM zai so ya fa]imaganarsa...

* an fi karanta ta* ga kyan tsari da yawan shafuka* ga hikimar lafazi* ga kamanta gaskiya* ga isa kowace jiha* ga fitowa a kowane wataShirya fim ba tare da tallata shi ba kamar harara a duhu ne. Me zai hana ka sa tallarka a cikin FIM?

Jagorar Mujallun Hausa

Ya sa haka, amin.Hama Qumaku Attahir,c/o Murou Zakari, SNC Malhaza, Box 03 Malbaza,

Jamhuriyar Niger

FATI BA KI KYAUTA MANA BAZUWA GA MUJALLAR FIM,

MUNA son mu nuna ba}in cikinmu game da wula}ancin da FatiMohammed ta yi mana. Mun je Kurna a Kano (biki), to gidan

da muka je ya kasance kusa da gidan su Fati ne. Mu a yadda muka]auka ita �yar mutunci ce mai son jama�a. Sai muka ce bari mu shigamu gaisa da ita. Mun shiga har tsakar gidan bayan mun yi sallama,wani yaro ya le}o daga da}inta. Muka ce mun zo wurin Fati ne. Yashiga ya ce mata ta yi ba}i. Maimakon ta le}o ta gan mu ko ta ce mushiga, sai kawai muka ji ta fara magana cikin sauti mai }arfi cewa itaba za ta fito ba a gaya mana ta gaji. Sai muka ce daga Kaduna fa muke.Ba tare da ta le}o ta ga ko mu su waye ba, daga cikin ]aki ta ce ita fawallahi ba za ta zo ba, mu tafi mu ba ta wuri. Abin dai kamar a fim!Sai muka ka]a kai muka tafi, muka ce sai anjima ba tare da munmaida mata martani ba, domin mu muka je; in da ba mu je ba da ba tayi mana haka ba.

A gaskiya iyakar wula}anci kenan ko da wajen gwamna ka je. Toamma ta tuna ita wace ce? Kuma ta san cewa shi mutum rahama cekuma ]an�adam daraja gare shi. Annabi (SWA) ya ce ba abin da yakai ]an�adam daraja. Sai ga shi kin shure damarki.

Gaskiya idan haka �yan wasa suke ba za ka ta~a marmarin ka ha]uda su ba ko a hanya balle ka je inda suke. Fati da kin san darajar kankida kin mutunta ]an�adam. Mutum ya zo har kofar ]aki, a}alla ai kole}owa kya yi a gaisa. Kuma ba ki san irin alherin da muka zo mikida shi ba kuma ba ki zo kin ga ko mu su waye ba.

Amina da Hadiza Abubakar,No. 2, Benin Crescent, Malali, Kaduna.

YAUSHE FATI TA FARA YIN FIM?ZUWA GA MUJALLAR FIM,INA jinjina muku bisa wannan namijin }o}arin da kuke na fannin

sadarwa a duk inda ]an�adam yake a fa]in duniya.Ina so mujallar Fim ta tantance mani lokacin da Fati Moh�d ta fara

shirin fim. Sannan kuma finafinai nawa ta yi a duniya? Bayan hakakuma a cikin wa}o}inta wacce wa}a ce mutane suka fi so har yazuwa yanzu? Kuma a cikin fim wanne ne ta fi yin action?

Baba Idrith Moh’d,No. 80 K/Mazugal, P.O.Box 965 Dala L.G.A., Kano.

AMSA: Mun ba da cikakken tarihin Fati a Fim ta watan Mayu.Sauraran tambayoyinka kuma suna bu}atar dogon bincike kafin agano amsoshinsu.

FATI TA TABA YIN AURE?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai jin da]in fitowarku a kowane wata. Allah Ya albarkacimujallar Fim. Ina kuma taya ku farin cikin cika shekara biyu. Wai

shin da gaske ne Fati Moh�d ta ta~a yin aure har da �ya�ya biyu (maceda namiji)? In gaskiya ne, to don Allah a buga mana hoton yaran natabu gani, in da hali a fitowa ta gaba.

Ismaila A. Ahmed,c/o Alh. Ahmadu Fatika, Sarkin Fadan Zazzau.

AMSA: Fati ta ta~a yin aure, sai dai ta ta~a haihuwar ]a guda ]ayaya rasu bayan kwanaki ka]an.

TAMBAYA GA SAIMA DA ZAINABZUWA GA MUJALLAR FIM,

YA zama dole a jinjina ma mujallar Fim domin suna taimaka waharshen Hausa wurin bun}asa shi; su ma sai mu ce Allah Ya

taimake su ya sa mu dace, amin. Duk a cikin �yan wasa mata babuwadda ta kai min ko kwata-kwatan Fati Mohammed. Ni dai son ta danike ma ban ta~a zaton zan yi ma wani ko wata shi ba in ban da�ya�yana da �yan�uwana.

Na san kyau na gushewa, ku]i yana }arewa, amma }auna harabada ce. Ina son Fati ina }aunarta, har nike ro}on Allah Ya sa ta auri]an�uwana domin dai mu ha]a jini.

Wai shin da gaske ne Saima Muhammad za ta auri �Ba}in Wake�(alasan Kwalle)? In da gaske ne ina taya ta murna domin ita ma inamatu}ar son ta. Ina son Hindatu Bashir, A�isha Ibrahim, Halima

Page 6: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 7

Wasi}uAdamu, Wasila, Abida, Maijida , ina son don Allah edita ya tambayomin �yar wasa Zainab Abubakar ta Dare [aya: wai shin me ya sa�yan wasa mata idan masu kallonsu �yan�uwansu mata suka je dominsu gan su sai su wula}anta su? Amma idan maza ne suka je wurinsusai ka ga suna haba-haba da su?

Ruqayyat Lawal Usman,No. 251, Lemu, Zariya City, Jihar Kaduna.

WA YA FI WANI A FIM?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto maku wannan wasi}a shi ne don in yi tambayoyiguda uku. Ta farko ita ce: idan mutum yana da ra�ayin shiga fim

ta wace hanya zai bi ya samu shiga don ya samu ya yi suna tamkarAli Nuhu? Tambaya ta biyu ita ce: menene bambancin furodusa dadarakta a fim, kuma wanne ya fi }arfi a fim? Tambaya ta ta }arshe itace: ku ma�aikatan mujallar Fim, kuna kar~ar wani haraji ga masurubuto muku adireshinsu da hotonsu a filin �Abokanmu�? Sai maganta }arshe, ina son kalandar ma�aikatan mujallar Fim. Ku za ma lafiya.

Malam Bello Abdulc/o Al-Musa Wurno, Bakin Kasuwa, P.O. Box 18 Gusau,

Jihar Zamfara.

AMSA: 1. Idan ka san za ka iya yin wasan kwaikwayo, sai katuntu~i wani daraktan fim ya gwada ka ya gani. Shi zai gane inda kadace a wasan, kuma ya saka ka. 2. Furodusa shi ne wanda ke ba daku]i a shirya fim. Wato shi ]an kasuwa ne wanda burinsa aiki ya yikyau ya sami riba. Yana iya na]a wani a matsayin furodusan amadadinsa. Wato dai kamar shi ne shugaba a kamfanin da ake }erawani abu don a sayar. Shi ko darakta, shi ne ke ba �yan wasa umurninabin da za su ce ko za su yi a cikin fim. Kamar shi manaja a kamfani,wanda zai ce a yi kaza ko a bar kaza. Da wuya a ce ga wanda ya fiwani, domin idan babu ]ayan da wuya ne ]ayan ya yi aiki. Wata sa�afurodusa yana iya zama daraktan fim ]insa idan har ya san iliminaikin. 3. Mu a mujallar Fim ba mu kar~ar ku]i don buga hotonmutum a filin abokai ko wasi}u, da sauransu. Sai dai kurum inmutum zai tallata wata hajarsa ko in zai yi wata sanarwa ta musamman.Mun gode.

MUJADALA YA CIRI TUTAZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN }aunarmu a gare ku ya sa muka yanke shawarar rubutomuku wasi}a da kuma tambayarku a kan abubuwan da suka

shigar mana duhu a kan wasu �yan wasa. Shin wai ina tauraron nanAminu Acid Dambazau? Ya koma makaranta ne ko ko dai ya dainafim ne? Kuma wai da gaske ne Zik yana da masters degree?

Kuma fim ]in nan na Mujadala 1&2 ya burge mu kuma ya }ayatarda mu. A gaishe da Ali Nuhu. Ya sani cewa fim ]in ya ciri tuta. Kumaya ci kyauta a gare mu. Sai mun zo Kano zai sha mamaki. Gaisuwa gatauraruwa kuna masoyiya abar bege, wato Fati Moh�d.

Sa’adatu da Maryam Ibrahim,No. B 24 Jajere Road Baddiko, Kaduna. Tel: 062:411758

AMSA: Aminu Dambazau yana nan yana wasa. Kuma Zik yanada digiri guda ]aya, ya soma karatun na biyun amma bai kammala ba.

MUJADALA YA SABA WA HAUSAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto muku wannan wasi}a ne domin in ]an yi wani bayania kan fim ]in nan mai suna Mujadala, wanda kamfanin �FKD

Productions� suka yi, Kuma fim ]in Ali Nuhu.Kowane ]an wasan fim in aka yi hira dashi sai ya ce yana yin fim

ne don fa]akarwa, tunatarwa ilimintarwa, da kuma garga]i kanjama�a. A gaskiya duk irin kayan da su Fati Moh�d, Abida Moh�d,Maijidda Abdul}adir suka sanya a fim ]in Mujadala ba su kamata badomin ba kayin al�adar Hausawa ba ne.

Tunda dai mu Hausawa a al�adarmu ko a Musulinci bai dace mace

ta sa kayan maza ba, sai ga shi a fim ]in an mai da kayan maza namata, ko kuma mace ka ga ta sa kaya wanda ya mammatse mata jiki.To a gaskiya wannan babban kuskure ne. Allah Ya sa mu gane amin!

Hassan M. Abdullahi,c/o Lawal Ali Garba, Radio Nigeria, P.O. Box 250, Kaduna.

INA AKA FI SAYEN MUJALLAR FIM?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN da rubuto wannan wasi}a tawa shi ne ina son in sanmujallar Fim ta wane wata aka fi saye? Sannan kuma a wace jiha

aka fi sayen mujallar Fim? A }arshe ina so a mi}a mani gaisuwata gaIshaq S. Ishaq, Ibrahim Mandawari, Ahmed S. Nuhu, Abida Moh�d,Fati Moh�d, Wasila Isma�il, Zulkifilu Muh�d, Tahir Fagge, GalinMoney, da sauransu.

Jamilu Bello Dogarawa,P.O. Box 1036 Sabon Garin Zariya, Jihar Kaduna.

AMSA: Mujallar da muka fara buga hoton Ali Nuhu da taken�Yaro Mai Tashe� ce ta farko da aka fi saye lokacin muna ]anyu. Toamma akwai na wasu watanni wa]anda muka sayar fiye da waccan]in. Dalili shi ne ka san da kwafe 1,000 muka fara, muka ri}a ci gabahar muka ninninka. Haka kuma mun fi sayar da mujallar a Kano,domin ita cibiya ce inda dillalai daga wasu jihohi da ba mu fara kaiwaba sukan zo su sara su tafi. Mun gode.

ISMA’IL YUSUF, GYARA NASIHARKAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA matu}ar yaba muku a bisa }o}arin da mujallar Fim take yiwajen ya]a sa}onnin mutane a Nijeriya da kuma sauran }asashen

duniya baki ]aya. Ina so in yi gyara tare da bayyana hanyar da yakamata a yi wa mutum raddi. A Fim ta 17 (Mayu 2001, a shafi na 9)wani ya rubuto ya ce wai darakta Ishaq S. Ishaq yana kakkama �yanmata. To Ismail Yusif a gaskiya bai kamata lokaci ]aya ka fito ka tonawa mutum asiri kai tsaye a duniya ba. Abin da ya kamata ka yi shi neya kamata ka rubuta masa takarda don yin nasiha tare da yin garga]ia gare shi. Idan har ka yi hakan bai canza ba, to sai ka ]auki matakinda ya dace.

Ka sani cewa duk ]an�adam yana aikata ba-daidai ba, sai dai a ceta wani ce ta fito fili. Domin idan Yusuf Isma�il Bahaushe ne, toHausawa sun ce laifi tudu ne..., sannan kuma suka }ara da cewa dukwanda ya rufa asirin wani�

Anas Danmaliki Yunusa,No. 91C K/Mazugal, P.O. Box 695, Dala L.G.A., Kano.

RAWAR DOLE ALI NUHU KE YI?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA da tambayoyi guda biyu da fatan za ku samo mani amsoshinsu.1. Shin wai sarkin rawa Ali Nuhu ra�ayinsa ne a ri}a sa shi raye-

raye ko da yaushe ko ko dai ana ba shi ba da son ransa ba?2. Wai ina wa]annan taurari: Maryam Mashahama, A�isha Bashir,

Jamila Haruna, Sanusi Burhan (Elbis), Aminu Sharif (Momo) dakuma Ciroki? Sabbabin finafinai da dama sun fito amma na da]e banga fuskarsu ba.

To ita Jamila ina da labarin abin da ya faru da ita, to amma ai yakamata ta dawo wanda shi ke zai rage mata damuwa ya ]auke matahankali daga sharrin maza. Ita kuma Maryam na gan ta cikin fim ]inta Ajali. To tana nufin ba za ta sake shiga fim ]in kowa ba ne? DonAllah ta yi ha}uri!

Daga }arshe don Allah ina son ku bugo mana tarihin sabuwartauraruwar nan ta cikin Furuci wadda ta yi rawa da Ali Nuhu cikinWasila 3.

Dubu A. Ladan,P.O. Box 2268 Sokoto.

Page 7: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 20018

Wasi}uAMSA: Dukkan wa]annan �yan wasa da kika zana suna nan,

kuma suna fitowa a fim idan dama ta samu. Shi kuma Ali ko wani]an wasan, duk rawar da kika ga yana yi, sa shi aka yi, kuma wasane, ana biyansa, ba tilasta masa ake yi ba.

WASILA, BAN GAMSU BAZUWA GA MUJALLAR FIM,

LABARIN da kuka bayar a Fim ta 16 game da shirin fim ]inWasila 3 ya nuna cewa Wasila Isma�il ta fara shiga shirme ta

kama tashar daji. Me take nufi da mutunci? Mai mutunci yana da]a�a, yana kuma sauraron jama�a, musamman magabata, ko da anzalunce shi. In tana da mutunci da ]a�a me ya hana ta sauraron suIshaq, Ali Nuhu, Saliha da Zik? Ai ko ba komai yayyenta ne a wannanharka. Tunda ta ce Lere ta ]auke shi a matsayin ]an�uwa, ai ko bamutunci ba ne bijire ma ]an�uwa.

Don haka bayaninta na rashin fitowa bai gamsar da ni ba kuma tatona wa kanta asiri. Cewa da ta yi wai ko da miliyan aka ba ta ba za tafito a Wasila 3 ba }arya ce. Bisa bin diddigin da mujallarku ta yi a kanwannan lamarin, mai karatu zai fahimci gaskiya ba tare da wanikokwanto ba. Wasila ki tambayi su Amina Garba, Hajara Usman,Hauwa Ali Dodo, Hafsatu Shara]a, da sauran gaggan �yan wasamata, yaya aka yi suka cimma matsayinsu a harkar fim a yau? Komaina duniya ]an ha}uri ne.

Bako Abdul-Rahman,Ministry of Agriculture and Natural Resources, Planing

Research & Statistics Department, P.M.B. 74, Minna, JiharNeja.

LERE, ALLAH FA KE AZURTAWA!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

A MUJALLA ta 17 Yakubu Lere ya yi magana a kan Galin Moneywanda bai cancanta ba, domin duk mai hankali in har ya karanta

abin da ya ce zai ga akwai rashin tunani, inda ya kira kansa wai shifurodusa ne Gali kuma mawa}i ne, ko kuma Gali ]an wasa ne.Amma ai ya kamata Lere ya yi tunanin cewa idan babu irin su Gali daWasila, shi furodusa ba zai yi tasiri ba komi ku]insu. Ba wai inanufin sai kawai Gali da Wasila ba. Yaya za a yi furodusa ya ci gabaidan babu wa]annan mutane biyu, ]an wasa da mai rera wa}a? AiShata ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba, ashe kuwa�yan wasa su ne fim ba wai shugaban shiri ba. Kamar shi ne yadda yabu]e wurin sai da kaset, idan ba masu saye ai da tuni ya rufe shagon.

Har yana cewa Gali ko ilimin firamare bai yi ba, shi ko ya gamajami�a. To idan bai sani ba bari ni in sanar da shi. Lokacin da Allah Yaba shi wannan abin da yake fahari da shi ba wai cewa aka yi Yakubutashi in ba ka ba, kuma na san bai yi wata rawa da ta burge Ubangijiba balle ya ce ai rawa ya taka, sannan kuma ai Allahu shi mai azurtabawa ne a duk lokacin da ya so, ya kuma talauta bawa duk lokacin daya so. Don haka kar ka yi mamaki ]an lokacin }an}ani Allah Yaazurta Gali fiye da yadda kake tsammani.

Sanin kowa ne akwai wa]anda ba su da ilimin bokon kuma sun yiarziki wanda ba mu Nijeriya ba duk duniya sun san su.

’Yar wasa Binta Lungun Liman,Kabala Costain, Kaduna.

HAMISU IYAN-TAMA YA KYAUTAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA son gimbiyar �yan mata Hindatu Bashir ta ba ni hotunta, domintana matu}ar burge ni. Wallahi ina mi}a godiyata ta musamman

zuwa ga Hamisu Iyan-Tama, don ya ba da ha]in kai wajen zuwabikin da aka yi a Dutsin-ma }warai da gaske.

Hajiya Suwaibatu A. Abdullahi Usman Runka,Katsina Steel Rolling Ltd., Katsina.

GYARA A LINZAMI DA WUTAZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto wannan wasi}a shi ne a kan kamfaninSarauniyya ta Kano, ban ji da]in yadda Sahabi mai halin kirki

ya }are a cikin fim ]in Linzami Da Wuta ba. Bai kamata a ce ya mutuba, kuma aka wula}anta gawarsa. Da }yar aka samu likkafini. Turarekuwa ba a samu ba.

Ya kamata a ce da aka yi masa addu�a ya samu sau}i, ya farfa]o,saboda ku aukaka addininmu ga wa]anda ba Musulmi ba. Alhaji da]ansa Nura su ya kamata su wula}anta, Ldon ba su da halin kirki.

Zarah Abubakar,No. 4, Rafin Guza Road, U/Dosa, Kaduna.

KU BA NI ADIRESHINSUZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mi}a gaisuwa ta zuwa gare ku saboda namijin }o}arin dakuke yi wajen wayar da kan jama�armu ta hanyar mujalla. Saura da

me, Allah ya saka da alheri. Bayan haka ina so don Allah idan da hali ku aiko mani da cikakken

adireshin Bashir Bala Ciroki, Rabilu Musa Ibro, da kuma UsainaTsigai, saboda ni �yar kallon finafinai ce kuma suna burge ni. Dafatan haka zai kasance.

Nafisatu Sani Mohammed,Kanoma, Jihar Zamfara.

AMSA: Idan kika aiko wa da kowane ]an wasa wasi}a tahanyarmu, za mu ba su.

BIBA INA KAUNARKIZUWA GA HAUWA ALI DODO,

DALILIN rubuto maki wannan wasi}ar shi ne don na yabe kikuma in gaya maki irin }aunar da nake maki a zuciyata. Domin

in aka ce fim ba ke ba na jin da]i. Bayan haka Hauwa kina burge ni,domin kina fitowa wuri uku, kuma duk suna dacewa da ke. Na farkokina fitowa a yarinya, ko babbar mace, kuma kina fitowa a tsaka-tsaki. Biba don Allah ki aiko mini da hotonki. Shawarata a gare ki itace, don Allah ki yi aure domin darajar mace ]akin mijinta kuma shi nejin da]inta duniya da lahira. Ki huta lafiya.

Sa’idu Mohammed Tasi’u,Bedde Road, Tudun Wada, Kaduna.

TUBARKALLA FATI DA MAIJIDDAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto ne don in gode muku saboda wayar da kanmu da kukeyi. Ku malamai ne da karantar da mu. allah ya saka da alheri,

amin!Na biyu, ina mi}a gaisuwar taya murna da fatan alheri ga Fati

Moh�d da Maijidda Abdul}adir a kan aurensu. Muna musu addu�arAllah ya ba da zaman lafiya, Allah ya ba da zuriya ]ayyiba. Sauran daba su yi ba Allah ya ba su.

A }arshe, ina gai da Balaraba Mohammed, Tahir Moh�d, AbidaMoh�d, Ibrahim Mandawari, Saima Moh�d da Galin Money.

Mohammed Auwal Ibrahim,Magaji Jingir,P.O. Box 1780, Jos, Jihar Filato.

FATI: BAYAN AUREN SAI ME?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

AURE ya}in �yan mata! Na sami labarin Fati Moh�d za ta auriSani Mai Iska. To Allah ya sa alheri, amin.

Abin tambaya shi ne: kasancewar Fati ga shi za ki yi aure kumawanda za ki aura shi ma ]an wasa ne, to don Allah bayan an ]auraauren ko za ki ci gaba da yin fim? Mijinki ne zai hana ki yin sana�arko kuwa ke da kanki kika yanke shawara?

Page 8: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Bello Ologe Daudawa,c/o Garba Yaro Mohammed,Rijiyar Lemo, P.o. box 13387, Kano.

DON ALLAH MASU AURE SU ZAUNAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA lura wasu daga cikin �yan wasa mata kamar ba su da uwa dauba sai furodusoshi. Ba sa jin maganar gidansu sai ta furodusa,

su kuma furodusoshin gani suke idan ba wa]annan mata a fim, tofim ba zai yi kasuwa ba.

Balle a yi maganar aure.Ina ro}on Abida Mohammed ta yi koyi da Maijidda ta yi aure tun

lokaci bai wuce ba. Ina ro}on wa]anda suka yi aure su yi ha}uri suzauna a gidajen mazansu. Kada su yi amfani da zugar wata. A harkarfim, abin da suka yi Allah ya amfana.

Shafi’u Alh. Musa Aliyu Mai ShagoBakin Kasuwa, Tafida Street, P.O. Box 5, Ibi, Jihar Taraba.

KADA SU FATI SU BA MU KUNYAZUWA GA MUJALLAR FIM,

A MUJALLAR Fim mun sami labarin Fati Moh�d za ta yi aure,kuma Maijidda ta yi nata. Gaskiya ina taya su murna. Don Allah

kada su ba masoyansu kunya. Su ba mara]a kunya. Su jure zamanaure, don an ce aljannar mace tana }ar}ashin }afar mijinta.

Abdurrahman B.H.Block 8 No. 6, Water Board Quarters, Bauchi.

INA JIRAN HOTON ALI DA NA FATIZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN rubuto muku wannan wasi}a shi ne: ina son wannanmujalla ta isar mani da sa}ona ga �yan wasa, kamar su Ali

Nuhu, Abida, Fati, da kuma Ahmad S. Nuhu./Don Allah don Annabisu aiko mani da hotunansu, don in suka aiko min, to zai tabbatar suna}aunata kamar yadda nake }aunarsu. A mujallar Fim ta Disamba,shafi na biyar, na rubuto wasi}a inda na bu}aci Ali da Fati su aikomani da hotunansu amma na yi ta sa ido ban ga amsa ba. Shi ya sa na}ara rubutowa, kuma ina san rai ba za su ba ni kunya irin ta wancankaron ba.

A }arshe ina so don Allah a fa]a mani lambar tarho ]in Ali Nuhuda Fati.

Miss Zainab Isiyaku,G.G.S.S. Tafawa Balewa Way, Kaduna.

KUMURCI DA ABIDA, GWANAYENAZUWA GA MUJALLAR FIM,

NI }aramin yaro ne ]an shekara tara. Ina aji hu]u a makarantarfiramare. A gaskiya ina matu}ar jin da]in kallon wasan

gwanayena Shu�aibu Lawan (Kumurci) da Abida Mohammed. Niduk a cikin �yan wasa ba ni da kamarsu. Don kusan ma in ce wallahisaboda son da nake yi wa Kumurci, yanzu har na iya irin maganarshi.

Don Allah idan Abida da Kumurci sun ga sa}ona su aiko mani dawasi}a da kuma hoto. Su yi amfani da adireshin Jamila, za ta kawomin har Dutsin-ma. Kuma su sa mani adireshinsu yadda ni ma zandinga aiko masu da wasi}una.

Isa Ibrahim Najikamshi,c/o Jameela Suleiman, Abubukar Gumi College, P.O. Box

679, Zango, T/Wada , Kaduna.

HALIMA, ALLAH YA RAYAZUWA GA MUJALLAR FIM,

GODIYA ta tabbata ga Allah da ya ba ni damar rubuto mukuwannan wasi}a a matsayina na mai kallon finafinan Hausa da

karatun mujallar Fim. Ina so in yi amfani da wannan dama domin inisar da sa}on farin cikina game da auren Maijidda Abdul}adir dakuma samun haihuwar da Halima Adamu Yahaya ta yi. Allah Ya rayashi amin.

Kuma ina so in mi}a gaisuwata ga A�isha Ibrahim (Saliha), FatimaMoh�d, Ali Nuhu, Abida Moh�d, Ahmad S. Nuhu, Hajara Usman dakuma furodusa mai tashe, Yakubu Lere.

Usman Musa

Malam Usman a ri}a sanya adireshi - Edita.

WANI GYARAN A LINZAMI DA WUTAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA mai ba da shawara ga wa]anda suka shirya Linzami Da Wutacewa a inda aka kashe Sahabi, ba shi ya kamata a ce ya mutu ba.

Nura ya kamata a ce ya mutu, kuma baban shi ya tsiyace, Sahabikuma ya yi ku]i ya auri yarinyar nan tashi da kuma Tasalla.

Ku mi}a min godiyata ga Ali Nuhu, Tahir M. Fagge, Bashir Bala(BBC), Rabilu Musa ([an Ibro), Sani Musa, Fati Mohammed,Hauwa Ali Dodo, Ibrahim Mandawari, Saima Mohammed, Alh.Hamisu Iyan-Tama da kasaitaccen darektan nan Ishaq Sidi Ishaq.

Aminu Abdulrahman (Mai Chemist)Kore Quaters, Sandamu, Sandamu L.G.A., Jihar Katsina.

YA SUNAN GALI NA MUSULUNCI?ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DON Allah wai yaya sunan shahararren ]an wasan nan kumamawa}i wato Galin Money? Ina so ku gaya mani cikakken

sunansa na Musulunci. Don ban ta~a jin Musulmi da suna GalinMoney ba. Kuhuta lafiya ina nan ina sauraronku da tafatan zakusharemani hawayena, ni da masu karatun Mujallar Fim.

Abdullahi Hassan,A.G.H., Bima Road, Tudun Nupawa, Kaduna.

RIGAR ’YANCI, A TUNA DA GIDA!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

HABA furodusan fim ]in Rigar �Yanci! A gaskiya mu �yan Gombeka ba mu kunya kuma ka ba mu kunya. Don Allah yanzu a ce ka

kashe wa fim ku]i sama da naira miliyan amma ba ka saka �yanGombe su ci arziki ba. Kana ganin kamar babu wasu }wararru acikin }waryar Gombe? To ai a Kano muna da �yan wasa wa]andaasalinsu �yan Gombe ne. A maza akwai irin su Katakore da MalamDare, a mata kuma akwai irin su Husaina Tsigai, Hajara Usman,Maryam Mashahama, da sauransu.

Amma kai ba ka ]auko ko ]aya daga cikinsu ba. Don Allah a ri}atunawa da �yan gida! Ba kuma an ce kada a ]auko �yan waje ba ne.

Alh. Da’u Usman,Bagaja Film Production, Gombe.

E, DA DAN GARI KAN CI GARI!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA karanta sharhinku a kan fim ]in �Holy Law.� A zahiri fim ]inan yi kuskure, ko kuma in ce an ci zarafin Musulunci da

Musulmai. Bai dace a ce su Ali Nuhu da Ibrahim Mandawari sun fitoa fim ]in ba saboda su ne ka]ai Musulmai a cikinsa. Gaskiyarku dakuka ce da ]an gari kan ci gari. Ya kamata su tuba, Allah zai yafemusu. Kuma ina son don Allah furodusoshinmu Musulmai su yimartani ga wannan fim ]in.

Abubakar Muhammad,No. 9, Block 11, Central Market, Bauchi.Tel.: 077-540450

9

Wasi}u

Page 9: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Wasi}u

10

INA TAYA WASILA MURNAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so in yi tsokaci dangane da hukuncin da ita gwanar tawa,Wasila, ta yanke kan furodusa Yakubu Lere na }in fitowa a shirin

Wasila 3. Ba ina nufin ci masa mutunci ba ne, sai dai in yi masa nasihada cewar batun da ya yi game da Galin Money (a mujalla ta 17, cewawai Gali maro}i ne, anya ba ya tunanin batun zai iya kasancewabarazana gare shi daga sauran masu wa}o}in finafinai? Domin, afahimtata, shi Lere mutum ne mai yawan ~atawa da jama�a. Ta iyayiwuwa nan gaba dukkan fim ]in da ya shirya, mawa}an su }i yimasa wa}a domin gudun kada abin da ya yi wa Gali ta same su.Kasancewar Lere mai ilimi, bai kamata ya ri}a fa]in irin wannanmagana ba.

Dangane da shirin Wasila 3 (maras ma�ana gare ni), yaushe: 1. FatiMoh�d ta fito har aka aure ta? 2. Ina }arshen Mo]a? 3. Wane sa}o koilimantarwa ke tare da Wasila 3?

Daga }arshe, ina taya Wasila Isma�il murna na rashin fitowa a fim]in domin kare mutuncinta.Abubakar Bello Yayaji,Ni’ima Shopping Centre, along Maiduguri Rd., Darazo,Darazo LGA, Jihar Bauchi.

ALLAH NE YA DAUKAKA GALIZUWA GA YAKUBU LERE,

A GASKIYA Lere ka ban mamaki. Idan ba ka manta ba a cikinFim ta 12 ka gaya wa duniya cewa kai ]an jarida ne, ni kuma sai

na ]auka duk ]an jarida mutum ne mai hankali da tunani. Sai kumaka yi amai ka lashe a Fim ta 15, na ga sam ba ka dace da zama ]anjarida ba. Ban yarda kai wayayye ba ne; idan aka dubi garinku akadubi garin su Galin Money, za a ga ya fi ka.

Ka ce Gali ba komai ba ne illa maro}i. Ka ce jahili ne shi. Na ukuka ce ba ya da mutunci. To wannan ba }aramin kuskure ba ne. An ce}aryar }iri ta mai ce. Kuma ai idan ka sa mutum abu ya yi, to kai neka aikata abin. To, kai ne ka sa Gali wa}a, ka ga kenan abincinkaro}o ne, abin shan ka ro}o, abin hawanka ro}o. To ka ga kenan kaine babban maro}i. Lere, ka ha}ura da Gali, don Allah ya ba shi]aukaka a idon duniya.Moh’d Zahradeen,Photos ‘2002, Kofar Kaura, Katsina.

LERE, KA IYA BAKINKA NAN GABAZUWA GA YAKUBU LERE,

A GASKIYA Yakubu Lere karatun da ka ce ka yi, bai yi amfaniba, saboda amsar da ka bayar game da maganar Wasila da Galin

Money. Da iliminka na da amfani a gare ka da ba ka mayar da irinwannan maganar ba.

Shi arziki ai nufin Allah ne; ]an-dako ma Allah yana iya ba shi basai wanda ya yi karatu ba. Da fatan za ka iya bakinka idan watamagana irin wannan ta taso.

Bello Amadu Abukur,Federal Inland Revenue Service, P.M.B. 2175, Katsina.

A SASANTA LERE DA SU WASILAZUWA GA MUJALLAR FIM,

RIKICIN da ya taso tsakanin Galin Money da Wasila Isma�il daYakubu Lere, na gamsu da dukkan bayananku tare da nasu.

Amma shawara ita ce, na ga mutane suna neman wuce gona da iriwajen rubuto muku son kansu na zage-zage; wasu na zagin Lere,wasu Wasila, wasu Gali.

To don Allah kada ku sake buga wasi}a mai ]auke da zagin ]ayadaga cikin wa]annan mutane. Sa~ani ya riga ya faru. Fatanmu shi nemutane su mai da hankalinsu ga sasantawarsu ba shiga tsakani ba.

Danladi Mop Mai Fenti,Kasuwar Muda Lawal, Unguwar Makafi, Bauchi.

MUNA MURNA, TAHIR DA FATIZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto ne domin in nuna farin cikina dangane da auren TahirMohammed Fagge da amaryarsa Hajiya Halima Sokoto wanda

kuka ba mu labarinsa a Fim, da kuma auren yarinya kamila FatiMohammed da angonta Sani Musa. Na yi murna matu}a. Allah yatabbatar da alheri, ya ba da zaman lafiya. Kuma ina kira gare su da suri}e mazajensu tsakani da Allah domin ba mara]a kunya. Su kumadubi Allah su ri}e wannan babbar amana da aka dan}a musu.Alh. Abdullahi Ahmed Karaye,Materials Testing Laboratory, China Deo Engineering Corp.,Kaduna Road Project, P.O. Box 7245, Kaduna.

NA YABA DA FILAYEN MUJALLARKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasi}a ne don in yaba ayyukan da wannanmujalla ke yi, bisa ga hasken da take ba mu a kan fim ]in Hausa.

Ina yaba filayen da ke cikin mujallar kamar su Babban Labari, MalamZur}e, Wasi}u, Kacici-kacici, Labarai da labarai muhimmai kamarna auren Fati, Manyan Gobe, �Zan Koma Nigerian Films - SaniDanja.�

Sannan na yaba da sanya fosta da kuka yi na Fati Moh�d daMaijidda, da fatan za ku ci gaba da saka fostar sauran �yan wasa. Inda hali, ku aiko mani da hoton Sani Musa Danja ko na YakubuMuhammad.Idris Tela Gilima,Taura LGA., Jihar Jigawa.

ZAN SAYAR DA MUJALLARKUZUWA GA MUJALLAR FIM,

NA rubuto wannan wasi}a ne domin in bayyana gamsuwata gawannan mujalla. Allah ya }ara muku }warin gwiwar gudanar

da ayyukanku.Bayan haka kuma, ina son ku ]auke ni don in ri}a sayar muku da

mujallar Fim a nan Daura. Ni mai saida jaridu ne a Bakin Tasha,Daura. Har daga Jamhuriyar Nijar ana zuwa don sayen jarida damujallu a wurina. Da fatan zan sami biyan bu}ata.

Lawal Nata’ala Mai Saida Jarida,Bakin Tasha Daura,P.O. Box 299, Daura, Jihar Katsina.

AMSA: Malam Lawal mun yi murna da samun wasi}arka. Za muso mu }ulla hul]a da kai. Don haka sai ka zo ofishinmnu da ke Kanodon mu tattauna da kai, mu gaya maka }a�idojinmu, kai kuma kagaya mana naka. Mun gode sai ka zo.

Muna neman marubuta/�yan rahoto a wa]annangaruruwan:* Kano* Zariya

* Gombe* Sokoto

* Jos* Wudil

Za mu ]auki namiji ko mace. Tilas a nuna shaidar iyarubutu mai kyau a cikin lafazi mai da]i. Kar ka damu dasatifiket in dai ka iya rubutun boko! Za mu biya da tsoka.A aiko da sauri zuwa ga:Mawallafi, Mujallar Fim, P.O. Box 10784, Kano.

* Abuja* Gusau

Ka Iya Rubutu?

GA AIKI YA SAMU!

Page 10: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

TAMBAYA GA ‘SARAUNIYA’ZUWA GA �SARAUNIYA FILMS�,

ALLAH ya }ara muku basira, amin. Dalilin rubuto muku wannanwasi}a shi ne,don Allah ina son in tambaye ku: wai shin wannan

yaron wan Fati Moh�d a cikin Sartse 1&2, Abubakar B. Zakari (wato�Abbas�), wai ]an daudu ne wanda bai gama warkewa ba ko ko hakayake? Don ni ya ba ni mamaki sosai yadda na ga yana ta famankwarkwasa,musamman ma inda suke rawa da Abida Moh�d,yana tawata girgiza irin ta mata. Don Allah ya gyaru. Na gode.

Maryam [email protected]

AMSAR SARAUNIYA: Haba Maryam! Ki ga yaro kamarwannan ki ce masa haka? To, gaskiyar magana dai ita ce: Abubakarba ]an daudu ba ne, a da ko a yanzu. Yanayinsa ne haka. Mun gode.� Auwalu Moh�d Sabo

YAKUBU LERE DATTIJO NEZUWA GA MUJALLAR FIM,

YA YI! El-Saeed Yakubu Lere, a gaskiya bayanin da ka yi yadace. Domin kuwa ko ba a gwada ba komfuta ta fi }arfin

kalkuleto.Ina so masu sukar Lere (a kan batun Wasila 3) su fahimci cewa

bayanin da ya yi wanda Fim ta buga a }ar}ashin taken "Galin Moneyda Wasila Ba Sa'o'ina Ba Ne ta Ko�ina� (Fim ta 17) ba ya yi ba ne donnuna isa ko ta}ama, illa dai kawai ya tauna tsakuwa ne don aya ta jitsoro, duk da yake abin da ya fa]a haka ne. Dalili a nan shi ne dukwanda ya san Lere ya san cewa yana da dattako da sanin ya kamata.{ananan misalai su ne a lokacin da ya yi fim ]in Saliha? an samumutanen da ba su fahimci manufarsa ba. Har wasu suka ce jininsa yahalatta. Lokacin da aka tambaye shi game da su, sai ya nuna ai dukMusulmi ba zai ji tsoron mutuwa ba, sai dai abin da zai tarar. Kumaya ce idan ma sun kashe shi to wata rahama ce tunda yana da gaskiya.Haka ma lokacin da wasu suke ta yi masa bi-ta-da-}ulli a kan wasarda yayi wa Kanawa a wa}ar �Mu Yi Soyayya� ta fim ]in Wasila yanuna cewa �Bakanon asali dai ba zai zage shi ba, kuma su bi ahankali. Wannan ma sanin ya kamata ne. Sannan sai sa~a al}awari dawasu �yan wasan Kano suka yi masa a lokacin ]aukar fim ]in Adalida aka nemi jin irin matakin da zai dauka akan su,Lere ba tare dala'akari da ]imbin asarar da suka janyo masa ba, sai kawai ya nuna aiba komai tun da manyansu sun zo, wannan ma dattako ne. Dominidan da su o�o ne, to da ba haka ba! Kai hatta ta wajen shirya finafinaibarkatai kamar wasan yara,suna shiga kasuwa a kowane wata ko satida wa]ansu furodusoshi ke yi Lere ya bambanta da su, shi yakantsaya ne ya tsara abin da zai fa]akar, ya nisha]antar, ya kuma ilimantarda jama'a. Game da haka an ruwaito gawurtaccen furodusan yanamai cewa: �Ai da haihuwar yuyuyu gwamma ]a ]aya }wa}}wara.�

Don haka ala kulli halin Lere dattijo ne.Alh. Laminou Gonda,Ibn Ai Arzey St., Al Hendaweeya, Jeddah, Saudi [email protected]

KU DAINA WANKE LERE!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

DALILIN wannan i-mel shi ne a kan labarin da kuka buga a kan�Wanene Yakubu Lere?� (Fim ta watan Yuni), kun ban kunya.

Kawai sai kuka yi ta yabonshi, wato shi ba shi da laifi. Kuma dukwa]anda suka yi fa]a laifinsu ne kenan ba nasa ba. Ai da kuma sai kutambayi ]aya ~angaren wa]anda su kuma ya ~ata musu. Kenan kunyi ne don ku gyara shi, shi ne kuka yi sharhin.To don Allah ku daina haka, domin a fahimtata shi mutum ne mai

girman kai da ]aukar kansa shi wani ne, yana zagin �yan wasa damawa}a bayan ba su ne suke rawa da bazarsa ba shi ne yake yi datasu. Sai an jima!Maimuna Adnan Gwammaja Qtrs., [email protected]

KU SADA NI DA ALI NUHUZUWA GA MUJALLAR FIM,

GAISUWA da fatan alheri. Sunana Sa�ad. Na ga adireshinku na i-mel a cikin mujallar Fim. Ina so ku sada ni da Ali Nuhu. Ni

masoyinsa ne matu}a kuma ina so in bu]e kulob na masu }aunarsa(wato fan club) shi da sauran �yan wasa maza da mata wanda zansaka a cikin Intanet. Ban sani ba ko za ku iya ba ni adireshinsa na i-mel idan yana da shi, domin gidajen waya na Nijeriya ba su abindogara a kai ba ne. Idan bai da adireshin i-mel, to ku taimaka ku isarda wannan sa}on nawa a gare shi, kuma ku aiko mani da amsarsa.Na gode.Sa’ad Bashir, daga [email protected]

Sa�ad, ka yi ha}uri mun fassara wannan wasi}ar taka daga Turancidon masu karatunmu su gane abin da ka ce. To, mun tabbatar Ali zaiga wasi}ar, kuma idan ya ba mu amsar za mu aiko maka, ko kuma shiya aiko maka tunda ga adireshinka na i-mel nan. Mun gode.

KU JA KUNNEN ALI NUHUZUWA GA MUJALLAR FIM,

BABBAR gaisuwa ga Ibrahim Sheme. Ga sa}ona, a taimaka yazuwa gun su manyanmu, mazan }warai, masu mutunci, kuma

masu mutunta duk wanda ya kai masu ziyara, walau talaka ne ko maiarziki ne, tare da babbar girmama duk wanda ya kai musu ziyara. Kaidole a jinjina musu tare da yi musu addu�ar su gama lafiya kanwannan harka ta finafinai.To fa ba wasu ba ne wa]annan mutanen illa Ibrahim Mandawari daHamisu Iyan-Tama.Sannan ga wani aiki zan ba ku , domin duk fa]in garin na dosa bawanda na ga ya cancanci bai wa sai ku mazajen }warai.Wato a kan }aninku ne, kuma abokin harkarku ta wannan sana�a,wato Ali Nuhu. Don Allah ku yi mai nasiha ya daina hawan wandasuke }ar}ashinsa da fa]a. Ya dinga girmama ba}o, ko talaka ne komai arziki ne. To, Iyan-Tama da Mandawari, ga wa]annan aiki gudabiyun, ku kun san yadda za ku mi}a su ga Ali, kuma ya ji ya ]auka.Idan ko har ya ]au abin da za ku gaya masa, tare da aiki da shi, to natabbatar yadda ake yabonku a yanzu Mandawari da Iyan-Tama, to shima Ali Nuhu za a yabe shi kamar ku ]in.Mrs Jamila Deenic/o Deeni Sulaiman Adamu, Bauchi Emirate Council,Bauchic/o Aminu Umar, P.O. Box 1122, BauchiE-mail: [email protected]

ABIDA CE TAURARUWATAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA matu}ar murna da na ga an fara aika wasi}u zuwa mujallarFim ta hanyar i-mel, kuma ana samun mujallar ta hayar Intanet.

Allah ya }ara nasara!Ina mi}a gaisuwata zuwa ga Abida. Ita ce tauraruwata, kuma tana

burge ni sosai yadda take wasa a fim.Don Allah Abida in kin karanta wannan wasi}a ki rubuto mun

Wasi}u ta hanyar �E-mail�Muna so masu aiko da wasi}a ta hanyar Intanet su ri}a sa cikakken sunansu da adireshinsu, ba adireshinsu na Intanet kurum ba. Muna

da damar mu }i buga duk wasi}ar da ba mu yarda da ita ba ko don ba ta ]auke da cikakken suna da adireshi

12

Page 11: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

da kan zomusu yau dakullum.

Don hakadaga FIM tawatan gobe,HajiyaBalaraba zata faragabatar dawani fili indaza ta ri}a bamata

amsa ta hanyar adireshina na i-mel ko kuwa na gida tare da hoton ki. Mu hutalafiya.Suleiman Ibrahim,10, Mali Crescent, Bekaji, Yola, Jihar [email protected]

ABIDA NUFSI-NAFSI!ZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA matu}ar farin cikin sanar da jarumata, gwanata, nufsi-nafsi(rabin raina), Abida Mohammed, cewa ya zuwa yanzu fa son ki ya yi nisa a

cikin zuciyata. A nan ina so ki sani cewa in ma da wasu masoyanki, to hakika nine shugabansu!Alhaji Salisu Malan-Malan,Buzzaqat Al Qamar Street, Al Hendaweyyah, Jeddah, Saudi [email protected]

NASIHA GA ABIDAZUWA GA MUJALLAR FIM,

INA so ku ba ni fili a mujallarku mai farin jini don na yi wa Abida Mohammednasiha a kan rashin wayonta na wula}anta mutane da

take yi,wanda irin haka shi ya jawo wa su Hauwa Ali Dodo suka zama kamar baa yi su ba.Jamilu [email protected]

KU DINGA BA ’YAN FIM SHAWARAZUWA GA MUJALLAR FIM,

SANNUNKU da aiki! Yaya yau, da sauran yan�uwa da abokan arziki? Akwanaki na ga mujallarku, kuma na ji da]in ganinta. Sai dai abin da nake

shawartarku shi ne ba wai kawai ku yi ta ba da labarai a kan �yan wasa ba. Ammaku dinga ba su shawarwari dangane da wa]ansu abubuwa da suka shafiwasanninsu.Don a gaskiya suna }o}ari sosai wajen finafinansu. Sai dai wa]ansu matsalolida ba za a rasa ba.Wannan ne karo na farko da na fara rubuto muku wasi}a ta akwatinna'ura mai }wa}walwa. Insha Allahu za ku ji daga gare ni nan ba da da]ewa ba.Na gode. Mukhtar [email protected]

Wasi}u Ta Hanyar Intanet

A FIM ta gaba

Mata kun yi anti!

Hajiya Balaraba Ramat Yakubusananniyar marubuciya ce wadda akegirmamawa. Tana da tsananin masaniyaa kan harkokin mata, musammanrayuwarsu ta aure.

Mun ga zai kyautu mata (musammanmatasa) su amfana da abin da ta sani narayuwar yau, don fuskantar al�amurran

shawarwari tare danuni cikin nisha]i kanrayuwarsu. Haka kumaduk wadda ke so ta yiwata tambaya gaHajiyar a kan wani abuda ya shige mata duhua kan auratayya kowani abu, sai ta aiko tahannun mujallar Fim.In ma ba ki son a sansunanki, sai ki ce musakaya.Hajiya Balaraba Ramat

13

RAHOTON MUSAMMAN A KAN TARON {ASABAKI [AYA DA AKA YI A LEGAS DON INGANTA

HARKAR SHIRYA FINAFINAI A NIJERIYA

NEMI MUJALLAR FIM TA WATAN GOBE!

Page 12: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200114

AL-YUSUFFA�S FILMS, KADUNAke gabatar da SUNAN FIM: JINI [AYA

KAMFANI : AL-YUSUFFA�S FILMS KADUNAFURODUSA: YUSUF MUHAMMEDDARAKTA: IBRAHIM MANDAWARI�YAN WASA: SHEHU HASSAN KANO, IBRAHIM MANDAWARI, SANI MUSA DANJA , MUSBAHU M. AHMED , ASIYA

AYAAH, A�ISHA IBRAHIM (SALIHA), SANIMO[A,WASILA ISMA�IL, da dai sauransu

Shirin JINI [AYA, fim neda aka shirya cikin hikimarda masu kallo suka fi so

da gani. Malam Yusuf Muham-mad, ]aya daga cikin shahararrunsababbin furodusoshin Kaduna,kuma shugaban kamfanin �Al-Yusuffa�s Films,� Kaduna, shi neya ]auki nauyin shirya fim ]in.

A fim ]in JINI [AYA, za aga irin mugun halin da Alh.Bashir (Shehu Hassan Kano) yashiga sakamakon saki uku da yayi wa matarsa Hauwa (A�ishaMusa) ba tare da ha}}inta ba.Wani rashin tunani kuma, sai ya}wace ]ansa namiji Ahmed(Musbahu M. Ahmad) ya bar tada macen Nafisa (Fati Ibrahim).

Ahmed da Nafisa sun ha]u aMaiduguri bayan sun girma, sunkuma tsunduma cikin makauniyarsoyayya ba tare da sanin cewauwarsu ]aya ubansu ]aya ba.Ibrahim Mandawari, wanda ahannansa Nafisa ta girma, ya

yanka wa Ahmed sadaki kumaya biya lakadan. A�isha Musa(Shamsiyya) ita ma ta dage a kancewa ba wanda zai auri Nafisasai Ahmed. Allahu Akbar! Ba tasan cewa Ahmed ]anta ba ne,wanda ta haifa da cikinta.

To mai karatu, Ahmed dai ya

JINI [AYA � COMING SOON !!

A’isha Ibrahim da Shehu Hassan Kano Wa da kanwa suna soyayya: FatiIbrahim da Musbahu M. Ahmed

Babban Furodusa da Sani Danja da Musbahu M. Ahmad

biya sadakin }anwarsa, kuma ansa ranar ]aurin aure. Shin kanaganin za a kwashe lafiya kuwa?Ka nemi fim ]in JINI [AYA,wanda zai fito kwanan nan, donka gane wa kanka rikicin da yaranza su shiga. Iyayen kuma fa? Abinsai wanda ya gari!!

Bayan wannan kuma, akwaida]a]an wa}o}i masu sanyayazuciya guda hu]u, duk a cikinfim ]in JINI [AYA.

*An shirya JINI [AYA nemusamman don nisha]antar damai kallo.

Yusuf Muhammad, BabbanFurodusan Jini Daya

Page 13: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

ABOKANMU

Mohammed Nazif A. Imam,No. 9, Imam House, KwarauBirnin Yero-Kwarau, IgabiLGA, Jihar Kaduna

Hamza Baba MuriT.V. Taraba,P.M.B. 1078 Jalingo,Jihar Taraba

Oga Kabir Hamisu S. Yaro,S.M.C.O. 2 Flat 18, YakubuGowon Barrack, Abuja

Nuhu Yahaya,Mashasha Photo Studio,Albarkawa, P.O. Box 225Gusau, Jihar Zamfara

Abu Sufyan (A.S.B.),Director, A.S.B. Balwan Vid-eos, P.O. Box 547, Bukuru,Jos, Jihar Filato

Muhammadu Auwal Umar,Mataimakin shugaban‘Gamji Memorial Club,’ F.C.E.Kontagora, Jihar Neja

Bello Haske,AwulkitiGadu L.G.A.,Jihar Sokoto

Hamzard Abubakar,Bakin Kofar Kasuwa,Karamar Hukumar Rijau,Jihar Neja

Wasu masu karatu suna aiko da hotuna marasa kyau: ko sun yi duhu,ko wanda ke ciki ya yi nisa. Ba za a iya amfani da irin wa]annan ba!A tabbatar hoto ya fito ra]au, kuma a sa cikakken adireshi.

Rahama Mustapha Sharu,No. 249, Faji Avenue,Fagge ‘A’, Kano

Furodusoshi da darektoci da ’yan kasuwa masu dabara dahangen nesa ne suke saka tallarsu a cikin mujallar Fim

17

Farouk MohammedBachirawa, Kano State Pri-mary Education Board,P.M.B., 3449, Ungogo, Kano

Umar D. Garba (MOP),Sakataren masu kayanFulani, Muda Lawal Market,Bauchi

Sani Jaja,Ruwan Dare Video Club, P.O.Box 255, Gusau, JiharZamfara

Page 14: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200118

SUNA: Tijjani Usman AbubakarMAHAIFA: JosSHEKARU: 35MATSAYIN KARATU: Difloma a �Mass Comm.�WASU FINAFINAI DA KA FITO CIKINSU: Rigar

{aya, Gobara Daga Kogi, Rikicin Amana,Mutuwar Masoyi, �Showdown,� EleventhHour, Girgizar {asa

KAYAN DA KA FI SON SAWA: Doguwar riga dawando

MUTANEN DA KA FI SO: Masu gaskiya da ri}onABIN DA KA FI SO A YI MAKA KYAUTA DASHI: LittafiHALAYEN DA KA FI SO KA GA MACE:

Kamun kaiHALAYEN DA BA KA SO KA GA MACE:

Rashin kunya da tsiwaKA TA~A HA]UWA DA MAI IRIN WA]ANNANHALYEN?: A�aABIN DA KA FI SON KARANTAWA:

Hadisan Annabi (S.A.W).ABIN DA BA KA SO A YI MAKA: {arya da

yaudaraABIN DA BA KA SO A YI MAKA CKINJAMA�A: Wula}anciKA IYA MOTA: EKAYAN LAMBUN DA KA FI SO: KabejiABIN DA KA KE SO KA ZAMA: Mai koyar da

addini

MU SAN �YAN WASA

Tijjani Usman Abubakar

TijjaniGASA TA 9

Wacece wannan?

’Yar wasan a wajen 1981

Wannan �yar yarinyar da kuke gani, ba yarinyaba ce a yau. Uwar mata ce. Domin kuwa an]auki wannan hoto nata ne kimanin shekaru20 da suka wuce, lokacin tana �yar kimaninshekaru biyar da haihuwa.

Jarumar finafinai ce da dama a yau. Sunanta na}arshe yana da nasaba da wata bishiya mai�ya�ya.

Bugu da }ari, ban da fitowa a wasanni wajenhamsin, ba ta da]e da riki]ewa ta zama furodusaba; fim ]in ta na farko zai fito kwanan nan.Af, kada mu manta: a Kano take!

Wacece ita? Sai a rubuto da sauri a gaya mana.{a}a tsara }a}a!

Page 15: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 19

JUNGUDO A. BUBA KEMBU,Babbar Kasuwar Jimeta, JiharAdamawa: Jungu]o matashi ne]an }walisa. Ga shi kuma ]ankasuwa. Ya sha yin tattaki tundaga Jimeta ta yana kai wa FatiMohammed ziyara a Kano.

Fim: Idan Fati ta yi aure ya zaka ji?

Jungu]o: Ni dai ina taya tafarin ciki idan har ta samu ta yiaure. In AllahYa yarda idan ta yiaure zan rage kallon finafinaikenan.

Fim: Kai da ma don Fati kakekallon wasan Hausa?

Jungu]o: Na ]aya dai ita ]ince na fi son kallon wasannintasaboda tana burge ni don ta iyaacting. Amma in ta yi aure nangaba, Allah zai ha]a jinina dawata �yar wasa in dawo in ci gabada kallon finafinai.

Fim: Idan ta yi aure harkar fimza ta girgiza?

Jungu]o: Gaskiya ba zai raguba saboda an riga an ci gaba.Kuma ai akwai wasu �yan wasairin su Abida.

Fim: Ka ta~a ziyartar Fati dagaAdamawa.

Jungudo: {warai! Akwaiwani lokaci da na je na sami AdoGidan Dabino ya ha]a ni dayaronsa ya raka ni wurin Fati, tafito muka gaisa. Daga nan sai naci gaba da zuwa wurinta duklokacin da na zo Kano.

Fim: Ko ka ta~a nemanta daaure?

Jungu]o: A�a, saboda akwaiwa]anda suka fi ni a wurinta,kuma tana ganin na yi nisa daKano.

Fim: Wace nasiha za ka yi matagame da zaman aure?

Jungu]o: Kada ta ji zugarmutane. Ta zauna ta yi biyayyaga mijinta shi ne zai fi yi mata

KAMAR yadda muka ba ku labari a shafi na 41 na wannanfitowar, za a ]aura auren fitacciyar �yar wasan nan FatiMohammed a ran 15 ga wannan watan na Yuni a gidansu dake Kurnar Asabe, Kano. Sai dai bayani ya }ara zuwa cewaabokan ango Sani Musa (Mai Iska) irin su Shu�aibu Liliscoda Umar Bawa Dukku, wa]anda suke ta ha}ilon ganin komaiya tafi daidai, sun shirya gabatar da wani babban bikin ajona �Gala� don wannan aure, a ranar da aka ]aura auren, ba ranjajibiri ba kamar yadda za ku gani a shafi na 41. Za a yi bikina zauren wasanni (�Indoor Hall) na dandalin wasannin matasa

Auren Fati: Ra�ayoyin masoyanta ukuna �Sani Abacha� da ke {ofar Mata, Kano. Za a sayar da tikitiga dubban �yan kallo wa]anda suka zo da wuri don taya Fatida Sani murna. Za a yi abubuwan ban mamaki da }ayatarwaa wurin, kuma jami�an tsaro za su hallara don tabbatar dacewa tsageru sun yi ladab.

A }asa, ga ra�ayoyin mutum uku wa]anda suka san Fati:]aya masoyinta ne mai kallon finafinanta, ]aya �yar wasace, ]ayan kuma darakta/furodusa ne na finafinai.

Allah ya kai mu ranar biki lafiya mu kashe }war}watarido!

alheri.

Rukayya Umar Santa,�yar wasa:Fim: Kun ta~a fitowa a cikin

fim tare da Fati?Ru}ayya: Ba mu ta~a fitowa

fim ]aya da ita ba. Amma daimuna ha]uwa da ita munazaunawa muna hira munagaisawa da ita cikin mutunci.

Fim: Me za ki ce game da aurenda za ta yi?

Ru}ayya: A matsayina na}awarta, budurwa �yar�uwarta,ina ro}on Allah Ya ba ta zamanlafiya. Kuma mu kanmu munafarin ciki kuma abin fariya ne agare mu a ce babbar artist irinFati, superstar cikinmu, za ta yiaure. To za ta }ara mana farin jiniyadda kowa zai fito ya ce yanason mu in an ga Fati ta yi aure.

Fim: Wa kike ganin za ta iyacike gurbin da za ta bari?

Ru}ayya: A gaskiya tun yanzumutane �yan kallo sun fara kawokukan cewa in Fati ta yi aure sunyi asarar �yar fim jaruma. Mu dai

muna sa ran in har ba mu yi aureba, muna ganin za mu yi }o}arinmu ]an ]ebe wa �yan kallo kewasaboda su daina kewarta. Za muyi }o}arin mu ri}a yin ]an waniabu daga cikin abubuwan da Fatitake na burge �yan kallo.

Fim: Sai ki yi wa Fati nasihagame da zaman aure.

Ru}ayya: Don Allah ni daigurina shi ne in ga sun yi aurennan sun zauna lafiya ba tare daan ji wata matsala ta taso ba. Yakamata ta daure, ta cije ta maidakomai ba komai ba ne. Sabodamu �yan wasa ta kar~ar mana�yancinmu a wurin �yan kallo.Domin idan ba ta daure ba, to muta kashe wa kasuwa don tasiri gamaza masu neman aure.

Don Allah Fati ki zauna lafiyada kishiyarki, ki bi mai gidanki.Ki kuma ci gaba da mutunci dakishiyar kamar yadda kike yi tunyanzu kafin ku yi aure.

SIR HAFIZ BELLO,DARAKTAFim: Ka ta~a yin fim da Fati?

Hafizu: Na yi guda ]aya, shine Jumur]a.

Fim: Me ka sani dangane dahalayyarta?

Hafizu: Ni dai ban ta~a jinwani darakta ko furodusa yana}orafi a kan halayen Fati ba, dukda cewa ana samun sa~anitsakanin harshe da ha}ori.

Fim: Za a cike gi~in da za tabari?

Hafizu: Gaskiya za ta bar gi~i.Kuma mai cike wannan gi~i, tosai an sami yarinya mai }wazoda haza}a. Ni a nawa hasashen,kafin a samu za a ]an jima.

Fim: Wace nasiha za ka yimata?

Hafizu: Nasiha ce guda ]aya.Sani shi ma abokinmu ne. Dukabin da ya umarce ta, wanda baisa~a wa shari�a ba, to ta yi shi.Shi ma Sani ya ri}a yin ha}uri,Fati kuma ta daure.

Fim: Aurenta zai iya girgizaKallywood?

Hafizu: Gaskiya ni murna nayi. Abin farin ciki shi ne wandaza ta aura ]in a cikinmu yake.

Rukayya Umar Santa:�Fati ta }watar mana �yanci�

Hafizu Bello:�Fati Yar Halak ce�

Jungudo A. Buba Kembu:�Zan rage kallon fim�

Page 16: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

HA[ARI

�Yan fim su biyu � ]aya fitaccen darakta, ]aya �yar wasa � sun riga mu gidan gaskiyasana diyyar mugun ha]arin mota a hanyar zuwa Katsina. ASHAFA MURNAIBARKIYA ya ruwaito labarin wannan babban abin ba}in ciki

�Ni ba mai raba ni da kaisai mutuwa!�

WANNAN kalami ne aka ceMaijidda Mustapha ta furtawa fitaccen daraktanfinafinan Hausa ]in nanAminu Hassan Yakasai aranar Jumma�a, 15 ga Yuni,2001 a cikin harabardandalin matasa na �FaggeYouth Centre� da ke Kano,sa�ilin da wata tawagar �yanwasa take haramar tafiyabirnin Katsina domin shiryawani fim mai suna Arziki DaTashin Hankali. Fim ]in,mallakar Abdullahi AlhassanJalla ne, wato shugaban}ungiyar wasan kwaikwayota �Tauraruwa,� Kano.Maijidda tana daga cikin�yan wasan da aka shirya zasu fito a wasan wanda Aminuzai yi wa darakta.

Abin ba}in ciki, sai ga shiwashegari, tun kafin a kaiKatsina, motar da ke ]aukeda su Aminu da Maijidda,tare da wasu �yan wasan, tafa]i a }auyen �Yan Kamaye,wanda ke gaban Bichi a kanhanyar zuwa Katsina. A nantake Maijidda ta rasu, bayanta fa]o daga cikin motar alokacin da motar ta }wace tanufi daji. Aminu ya karye acinya. An yi ha]arin damisalin }arfe 3 na yamma.

Labarin ha]arin ya riski�yan fim a Kano dab dagoshin magariba. Nan danan, ba tare da wata-wata bafurodusoshi uku, Mansir A.Shariff da }anensa Aminu A.Shariff (Momo) na kamfamin�Ibrahimawa Film Produc-tion,� da kuma darakta IshaqSidi Ishaq, suka garzayazuwa asibitin da aka faragaggauta kai su a Bichi.Asibitin ya koma tamkarwani dandalin �yan wasanHausa a wannan daren,

Subhannal Lahi! Motar da aka yi hadarin a cikinta ... jim kadan bayan hadarin a kanhanyar Kano zuwa katsina. H OTUNA DAGA BALA MOHAMMED

Marigayi Aminu Hassan Yakasai

domin manyanf u r o d u s o s h i ,daraktoci da kuma�yan wasa duk sunhallara a wurin. Baa da]e ba aka mayarda su Aminu asibitin�Khadija MemorialHospital� da ke kusada masaukinalhazai, watau�Pilgrims�s Camp.�

Sai dai kash! acikin wannan daren,Allah ya kar~i ranAminu da misalin}arfe 12. AllahuAkbar!

Sauran mutumuku wa]anda abinya rutsa da su su ne:fitaccen ]an wasaAbdullahi Zakari(Ligidi na cikinshirin Wasiyya), daBala MohammedYakasai da kumawani yaro }arami

wanda ]a ne a wurin BalaYakasai. Har lokacin darubuta wannan labari, Ligidi,wanda shi ne yake tu}amotar }irar �Toyoto Carina�a lokacin da aka yi ha]arin,yana kwance a asibitin na�Khadija Memorial Hospital.�Ya da]e bai ma san inda yakeba, sai bayan kamar kwanabiyu sannan ya soma samunsau}i.

Mujallar Fim ta fahimcicewa a da can �yan fim ]inna Arziki Da Tashin Hankalisun shirya tafiya Abuja ne,amma daga baya sai sukasake shawara. Kafin tafiyartasu, tuni a wannan ranarwasu motoci biyu ]auke da�yan wasa sun yi gaba sunajiran isarsu a Katsina.

Wannan abin ba}in ciki yaru]a �yan fim a Kano matu}a.Kowa ya yi la�asar jin cewasu Aminu sun rasu. Kowayana tuna irin halayyarlumana da son zumunci na

20

Page 17: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Aminu, wanda shi ne aka fi sani a cikinmamatan. Babu mamaki ganin a ranarAsabar, wato washegarin ranar da aka yiha]arin, tun da misalin }arfe 6 na safiyamanyan �yan wasa da }anana da damasuka dinga zuwa gidan su Aminu daMaijidda. Har zuwa }arfe 11 na ranakimamin �yan wasa ]ari uku sun je sunyi ta�aziyya ga iyalan mamatan. Kumamutane sun ci gaba da yin tururuwa zuwagidajen, wasu ma daga wasu jihohi, sunayin gaisuwa. Duk inda wani ]an fim yaha]u da wani, sai ka ji ya ce, �Ya muka jida ha}uri?�

Ban da shirin fim, Aminu marubuci ne.

Maijidda ce a tsaye a tsakiyar wannan hoton. A hagunta, Abdullahi Alhassan Jalla ne,mai fim din Da Arziki Da Tashin Hankali... A gefensa kuma Maryam Mai-Idon-Bacci ce

Ga Maijidda nan (ta biyu a tsaye daga hagu, wadda wani yake nunawa dayatsa) tare da wasu ’yan wasan kwaikwayo na Gombe

rubuce-rubuce sukatsunduma a ciki. Yana dagacikin manyan furodusoshinKano, shi ya sa ma a lokacinda mujallar nan ta bugarahoto a kan mamayar da�yan Yakasai suka yi waharkar fim, Aminu yana cikinwa]anda muka gabatar.Wasu daga cikin finafinan damarigayi Aminu Hassan yayi wa darakta sun ha]a da:In Da So Da {auna, Munkar,Bakandamiyar RikicinDuniya, {arshen Kiya daKowa Da Ranarsa, ~angarena Bada}ala, da sabon fim]in nan da bai fito ba, watoAjizi.

Dangane da jimaminwannan babban rashi kuwa,Majalisar �Yan Wasa ta JiharKano ta ]age duk wani shirinfim da aka shirya yi ranarAsabar, 16 ga Yuni. Ita ma{ungiyar Furodusoshi taJihar Kano ta ]age taron tada ta shirya yi a waccan ranar.

{o}arin da wakilinmu yayi na ganin shugaban}ungiyar Tauraruwa,Abdullahi Alhassan Jalla, yaci tura. Sai dai wata}wa}}warar majiya tabayyana cewa hankalin Jallaya tashi matu}a cewasanadiyyar tafiya shirya fim]insa ne wannan mummunanal�amari ya auku.

Furodusan A�isha daDawayya na kamfanin �Iyan-Tama Multimedia,� Ahmad S.Alkanawy, yana daga cikin

]imbin �yan fim wa]andasuka bayyana ba}in cikinsua kan rashin da �yan wasa dakuma masu kallo gaba ]ayasuka yi dangane da rasuwarAminu. �Aminu mutuminkirki ne, wanda ba ya }aunartashin harkali. Kuna ba kata~a ganin ya tsoma kansacikin rikici ko wani abin dabai shafe shi ba,� inji shi.

Shi kuwa Shehu HassanKano, shugaban Majalisar�Yan Wasa ta Jihar Kano, yanuna cewa �babu shakka zaa da]e ana jimamin rashinwa]annan bayin Allah. Abinba}in ciki ne }warai.� Shehu

Hadiza, matar Aminu Hassan, tare dababban dansu, Muhammad Sani ...

bayan aukuwar hatsarin

A lokacin da akeyayin rubutal i t t a t t a f a nsoyayya, yawallafa littafimai sunaMadubi, kumaya rubuta wasuwa]anda bai kaiga bugawa ba.Hasali ma, shi nes a k a t a r e n} u n g i y a rmarubuta ta�Raina-Kama.�Da shirin fim yazo, yana dagacikin wa]andasuka watsar da

21

Page 18: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

ya yi addu�ar Allah ya gafartamasu, ya kuma bai wawa]anda suka ji ciwo sau}i.

Wallahi ban iya cewakomai.� Sai dai ta yi }arfinhali ta gode wa ]imbin

halayensa kuwa, Ibrahimcewa ya yi, �A gaskiyahalayen marigayi abin koyi

Tawagar tana }ar}ashinshugaban {ungiyarFurodusoshi ta Arewa reshinjihar, Alhaji Waziri Zayyanu.Sauran �yan tawagar sunha]a da Aminu Hudu (Alma),Magaji Mijinyawa da kumaIbrahim Isa Acimota.

Baya ga wannan kuma aranar Jumma�a, 22 ga Yuni,an yi wa wa]anda suka rasuaddu�ar neman rahamarUbangiji. A dandalin matasana Fagge aka yi taron, wanda�yan fim tare da sauranjama�a kimanin dubu ]ayasuka halarta. Shugaban}ungiyar �MurtalaMuhammed Za~i SonkaClub,� Malam [ahiru [anBello ne ya bu]e taron daaddu�a, yayin da MalamUzairu ya gabatar da karatunAl}ur�ani Mai Tsarki. Ankuma saurari }asidarta�aziyya daga bakinAbdulmunafi da Malam[anladi Maibulala. BayanAlh. Ibrahim Mandawari yafa]i tarihin marigayi AminuHassan, sai Nura Imam (nacikin Zarge) ya rufe taron daaddu�ar Allah ya ji}anmamatan. To amin.

Ana addu’o’i a wajen sadakar uku a gidan su Aminu

Mujallar Fim ta sami jin tabakin mai ]akin marigayiAminu Hassan Yakasai agidan mahaifinsa da keYakasai bakin MasallacinBela. A cikin damuwa, matar,Hadiza Umar Kurawa, ta ce,�Ai ni babu irin misalin dazan bayar kan wannan abinba}in ciki da ya same mu.

jama�ar da suka jajanta waiyalan mamacin, musamman�yan fim da sauran jama�a.

Shi kuwa babban }anenAminu, Malam IbrahimHassan Yakasai, ya bayyanacewa ba }aramin rashi ba neilahirin danginsu suka yi. Ya}ara da cewa ba za su ta~amantawa da Aminu ba. A kan

Aminu Hassan kan iringudummuwar da ya bayardon ha~akar finafinanHausa. A ranar 18 ga watakuma wata tawagar mutumhu]u ta wakilci �yan fim naJihar Filato domin yinta�aziyya da kuma dubawa]anda suka sami raunisakamakon ha]arin.

Yadda Abin Ya AukuBALA MOHAMMED YAKASAI ne mai motar da aka yi ha]ain

da ita. Ya ce tun a gida ya ga ishara...

TARE da BalaMohammed Yakasaine aka yi ha]arin

motar. Hasali ma motarsa ceabin ya ritsa da ita. Yanazaune a gidan gaba a gefendireba. Lokacin dawakilinmu ya ji ta bakin sa agidansa da ke unguwar[orayi, Bala ya bayyanayadda abin ya faru da kumawasu isharorin aukuwaral�amarin tun kafin �yan fim]in su bar Kano.

Da farko ya fara da cewaya ga alamun aukuwarha]arin daga isharar da wasukarnukansa suka nuna masa.�Amma ka san da yakemutum bai san gaibu ba,babu yadda zai yi ya gane,sai kuma }addara ce, dole sai

abin ya faru.�Ya nuna cewa shekararsa

uku da wata karya da kegidansa �amma ita da�ya�yanta uku da ta Haifabasu taba shigowa sittingroom si/na ba�. Alhaji Balaya kara da cewa ranar da zamu yi wannan tafiyar sai�ya�yan karnukan suka shigo]akina suka ri}e min }afarwando�. Ita kuwa uwar tasua kullum takan raka shi harkan kwanar bayan gidansa.�To a ranar da za mu yitafiyar kuwa sai da karyarnan ta shiga gaban mota inabin ta har bakin titin [orayi.Ka san kuma nisan ya kusankai kilomita ]aya,� inji Bala.

Alhaji Bala, wanda azaman yanzu shi ne jami�iAlh. Bala Moh’d Yakasai

mai bincike ku]i (InternalAuditor) na {aramarHukumar Warawa ta Jiharkano, ya ce tun a cikin 1971yake ajiye da labarin da za ashirya fim ]in a kansa, ammasai a wannan shekarar ne akayi nufin mayar da shi fim. Fim]in na Da Arziki da TashinHankali, Gara Tsiya DaKwanciyar Rai, an fara]aukarsa har sau hu]u.

Da ya juya kan aukuwarha]arin kuwa, sai BalaYakasai ya bayyana cewalokacin da abin ya faru, ]ansaUmar da Maijidda da kumaAminu Hassan duk barcisuke yi �Domin tun kafin akai garin Bichi suka farabacci,� inji Alhji Bala wanda]an shekaru 56 ne a duniya.

22

ne, na }waraine�.

Jama�a dadama sun cigaba da nunaj i m a m i nwannan rashida aka yi. Aranar 17 gaYuni, fitaccendaraktan fim]in Kallo YaKoma Sama,Bala AnasBabinlata, yasadaukar dafim ]in sa maifitowa, watoSalma SalmaDuduf, ga

Page 19: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Da aka tambaye shiko rami suka fa]akamar yadda wasu kehasashe, sai ya ce,�Ba rami muka fa]aba, kuma ba gudumuke ba. Illa iyakakawai na ga ya kaucehanya kuma da na yimasa magana,maimakon ya takaburki, sai ya takatotur ya }ure shi�.Wannan ne, inji Bala,ya sa motar ta yi tashisama ta yi ta watsarda su. �Ni ka]ai narage a cikin motar�.Haka ya fa]a kanhadarin nasu da yaauku a cikin motarsamai lamba Kano: AA534 WRA.

An dauki motar da janwai

DA yake yawancin �yanfim ba su san ta ba,mutane sun ri}a

tambayar shin wacece yarinyarne? A cikin gari kuma, wasu sunri}a baza ji-ta-ji-tar cewaMaijidda Abdul}adir ce, watoshahararriyar �yar wasan nanwadda ta yi aure kwanan nan,abin ya ritsa da ita.

Maijidda Mustapha bacikkakken sunanta ba ne. Hawwane sunanta na yanka, sai dai ko agidansu an fi kiranta da sunanMaijidda. Binciken da Fim ta yiya nuna cewa an haife ta aunguwar {ofar Na�isa cikinbirnin Kano. Mahaifiyarta maisuna A�isha �yar asalin garinIngawa ce ta Jihar Katsina,mahaifinta kuma, AlhajiMuhammadu, ]an asalin garinDawakin Kudu ne ta Jihar Kano.

Maijidda ta ta~a yin aure,kuma tana da �ya�ya biyu, Zainabda Ali. Ta rabu da mijinta shekarushidda da suka wuce, wanda taaura a unguwar da aka haife ta({ofar Na�isa).

Mustapha ba sunan mahaifintaba ne. Ta sami wannan suna nedaga wani saurayinta wanda sukayi matu}ar sha}uwa da juna aKatsina. Mustapha soja ne da keaiki a barikin sojoji na Katsina.[an asalin Jihar Adamawa ne.Wannan ne ya sa ake masa la}abida suna Mustapha [anAdamawa. Har zuwa lokacin daMaijidda ta rasu akwai al}awarin

Wacece Maijidda Mustapha?

Maijidda tana wasa a matsayin nas a ikin shirin Zanen Dutse na kamfanin‘Ummulkhairi Entertainment’ a Kano. Ishaq Sidi Ishaq ne yake ba da umarni.Sani Yusuf ne a kwance a matsayin majinyaci

aure tsakaninsu. Suna son junamatu}a.

Mahaifin Maijidda yana da rai;yana zaune a unguwar Shara]a� Hauren �Yan Wanki, Layin[an�iya. Da yake ya rabu damahaifiyar su Maijidda, itamahaifiyar tata sai ta komagarinsu inda har yanzu takezaman aure a can.

Maijidda shiga wasan fim neta hannun �yar wasan nan maisuna Maryam Mai-Idon�Bacci.Ta fara yin }ungiyar wasankwaikwayo ta Tauraruwa, dagabaya kuma ta koma }ungiyar

�Fagge Unity.� A wannan}ungiyar ne marigayiya Maijiddata shiga finafinai da dama. Dagacikinsu akwai Hanyar Allah, SaraDa Sassa}a, Zanen Dutse, [anHajiya, Rama Cuta da kuma [anHayis. Daga cikin wa]annanfinafinai, Zanen Dutse ne ka]aiya shiga kasuwa inda Maijiddata fito a matsayin jami�ar jinya aasibiti (nurse). Rashin fitowarfinafinan ne ya sa mutane dadama ba su san ta ba.

Kamar yadda BalaMohammed ya ce ya ga ishararha]arin nasu tun a gida, mujallar

Fim ta ji daga }wa}}wararmajiya cewa mahaifin Maijiddaya yi mafarki. Ba a nan mafarkinnasa ya tsaya ba, sai da kuma yagan ta jama�a suna ]auke da itatana cikin fararen kaya. Bayankwana uku da yin mafarkin saiya sami sa}on mutuwar ]iyarsa.

�Halayen Maijidda abin yabone,� inji Sani Lawan {ul}ul,shugaban }ungiyar �FaggeUnity,� }ungiyar da Maijidda tayi shekara biyu da rabi a ciki.�Maijidda ba ta ta~a fa]a dakowa ba, kowa ya yi ba}in cikinrabuwa da ita. Allah ya ji}anta.�

23

Page 20: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

MANDAWARI ENTERPRISES, KANO

Assalamu alaikum,

GASKIYA duk mutumin da ya ji labarin yaddaaka yi wannan rasuwa ta Aminu Hassan Yakasaida ita wannan yarinya Maijidda Mustapha, alalha}i}a zai girgiza. Ma�ana, zuciyarsa za ta ta~u

sosai saboda ha]ari suka yi kuma dole a kira shi mummuna. Na firgita da wannan rasuwa,

musamman saboda abu biyu da ba zan iyamantawa ba. Na farko dai, Aminu yanacikin wancan hali na lahaula wala }uwata,idonsa a rufe ba ya iya ganin kowa, yasamu rauni a ka, kuma }afarsa ta karye.Duk da haka ina zuwa ya mi}o hannumuka gaisa, ya tambayi matata da yarana.Har ya ce min in ba shi ruwa ya sha. Ammasaboda likitoci sun hana a ba shi, ba a bashi ]in ba.

Tun daga ranar da aka yi wannanrasuwa har zuwa yau ina cikin damuwarda kowane irin mutum ne nawa ya rasu, toirin wannan damuwar ce zan yi. Da fatanAllah ya ji}ansa shi da yarinyar da ta rasu.Su kuma wa]anda suka samu raunuka,Allah ya sauwa}e, amin. Mutuwar Aminua wurina dole in ce na rasa amini kuma narasa aboki matu}a. Farko dai ba zan iyamantawa ba da wata }ungiya ta �TumbinGiwa� ta shirya wasan kwaikwayo, wadda ita ce asalin kafawannan sana�a ta harkar finafinan bidiyo. A wancan lokacinakwai sa�ad da muka yi rikice-rikice da }ungiyar, mukasami sa~ani; kuma duk da irin abin da wasu �yan }ungiyarsuka yi min da abin da }ungiyar ta yanke hukunci a kaina,Aminu bai yarda mun rabu ba. Ya yi matu}ar }o}ari yanuna babu wani abin }yama tare da ni, yana zuwa wurinna,ina zuwa wurinsa. Ko a cikin �yan watannin nan ya zo nanofis ]ina mun samu kusan awa biyu da shi.

Aminu Hassan ya ba da gudummuwa cikin harkar fimbaki ]aya. In ban ce Aminu Hassan ne ya kafa sana�arfinafinan bidiyo ba, ba kuma zan ce ni na kafa ta ba. Tunyana Jami�ar Sokoto ni kuma ina banki ina aiki muke wayakullum, muna tattauna yaya za a mai da wannan shirinwasa zuwa bidiyo ta yadda zai zama sana�a? Duk da shimuka zauna na shirya fim ]in Turmin Danya na farko; shiya yi min mataimaki. Kullum kwanciya barci ke raba mu.

A wancan lokacin yana da wani babur Kawasaki. A wurinharkar yadda za a yi fim ]in aka sace shi amma bai damuba, muka ci gaba. A kan wannan babur ]in kullum yakezuwa banki ya ]auke ni ya kai ni Bagauda, lokacin danake shirin Aminu Mijin Bose. Kai, da shi muka ri}a zuwa

Nigerian Film Corporation don neman ilimin yadda za ainganta harkar fim, a wurin Adamu Halilu, wanda shi ne ]anNijeriya na farko da ya fara shirya fim. Kai, akwai wasu masai mun jira sun tashi daga barci muna }ofar gidansu a zaune.To a gaskiya ya ba da gudummuwa mai yawa, sai dai mu ceAllah ya saka masa da alheri.

Zan so in yi maganar zumuncin da ke tsakanin mahaifiyarAminu Hassan da mahaifiyata. Sunsha}u da juna. Kuma shi ya yi ta }o}arihar matarsa ta }ulla }awance da tawa. Harkuma ya yi al}awarin idan Allah ya sa�ya�yansa sun girma, zai ha]a su da nawadomin su saba. Lokacin da na je yi wamaihaifiyarsa da matarsa ta�aziyya,wallahi kasa amsa min suka yi. Ba sukomai sai kuka. Ni kaina ban san lokacinda hawaye suka zubo min ba.

Ni dai ban ta~a ganin mutum maijuriyar zama da jama�a kamar AminuHassan ba. Domin za ka ga abokai kamarbiyar ko goma sun zagaye shi sunatsokanarsa. Amma daga lokacin da na sanshi kusan shekaru ashirin da suka gabata,ban ta~a gani ko jin cewa ya yi zage-zage da wani ba. Yana da ha}uri sosai.Wannan ka]ai ta isa a yi masakyakkyawan zato da samun rahamarUbangiji.

Ina kuma so in yi amfani da wannan dama in nuna cewaMaijidda Mustapha �yar }ungiyar �Tauraruwa� ce da �FaggeUnity.� Ta yi wani fim a nan �Mandawari Enterprises� maisuna Uwa Tagari. Ta kuma yi wasan finafinai a wasuwurare.Wani abin mamaki da wannan yarinya shi ne, ranarda za a yi tafiyar ta ce wa mutane su gafarce ta. Mahaifintadattijo ne; ya damu kuma ya gigice. Dole a tausaya mata dakuma shi. Allah ya yi masu rahama!

Kuma ina so in nuna wa jama�a cewa mutuwa wa�azi ce.Mutum da }uruciyarsa ya mutu. Basarake ya mutuu. Maiku]i ko talaka ya mutu. Ya kamata mutum ya gane cewaha]ama ta rayuwa da rashin kirki da yawaita sa~o, duk yakamata mutum ya daina. Ya dace mutane su ri}a yi wa mutumkyakkyawar shaida kamar yadda wasu suka yi wa wanimamaci a gaban Manzo (SAW). Kuma mutum ya guji yinabin da za a yi masa mummunar shaida kamar yadda wasusahabbai suka yi wa wani mamaci a gaban Manzo (SAW).

Daga }arshe ina fatan Allah ya gafarta wa wa]anda sukarasu. Wa]anda suka ji ciwo kuwa Allah ya ba su lafiya, amin.

Sa Hannun: IBRAHIM M. MANDAWARI

24

“In ban ce Aminu Hassan ne ya kafa sana’ar finafinanbidiyo ba, ba kuma zan ce ni na kafa ta ba!”

RASUWAR AMINU HASSAN YAKASAI: BABBAN

RASHI NE GA AL’UMMAR HAUSAWA

Page 21: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 25

KANO STATE FILM

DIRECTORS GUILD

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un!

A madadin Cibiyar Masu Ba Da Umarni AFim ta Jihar Kano, ina mi}a sa}on ta�aziyyaga iyalan marigayi fitaccen daraktaMALAM AMINU HASSAN YAKASAI, da�yan�uwansa, da abokansa, da masoyansa,da ]aukacin al�ummar Yakasai cikin birninKano, da dukkan jama�ar ArewacinNijeriya wa]anda sun amfana matu}a daayyukan da marigayi Aminu ya yi.

Aminu abokin aikinmu ne, kuma babbanabokinmu, sannan ]an�uwanmu ne.Mutum ne wanda ya yi hul]ar alkhairi dajama�a. Mutum ne mai ha}uri da sanyin raida hangen nesa da sanin ya-kamata.

Irin gudunmawar da ya bayar ga harkarshirya wasannin kwaikwayo na Hausa,musamman na bidiyo, a gaskiya ba tamisaltuwa. Rasuwarsa ta sa an sami waniwagegen gi~i a wannan muhimmiyarsana�a wanda za a da]e ba a cike shi ba.Don haka mun yi babban rashi!

Duk da haka, mun san dukkan mai raimamaci ne. Saboda haka ba abin da za muce illa muna yi wa Aminu Hassan Yakasaiaddu�ar Allah ya ji}ansa, ya gafarta masadukkan kurakuransa, ya sa AljannaFirdausi ce makomarsa. Allah ya amsaro}onmu, amin summa amin!

Aminu Hassan Yakasai

Sa Hannun:

ISHAQ SIDI ISHAQ

Page 22: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200126

Advert:

Kazafi

I YAN-TAMA MULTIMEDIASabon Titin Mandawari, Kano

Aminu Hassan Yakasai

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un!

Mu, Shugaba tare da dukkan Ma�aikatan kamfanin �Iyan-TamaMultimedia�, muna mi}a sa}on ta�aziyyarmu ga iyalan abokinmu,masoyinmu, MALAM AMINU HASSAN YAKASAI, daabokiyar aikinmu MALAMA MAIJIDDA MUSTAPHA,wa]anda Allah ya yi wa rasuwa a ha]arin mota a ran Asabar, 16ga Yuni, 2001, a kan hanyar zuwa Katsina.

Mun san Aminu matu}a a matsayin mutum mai ha}uri, mai juriya,mai kula da addini, mai }aunar danginsa. Mun tabbatar rasuwarsababban rashi ne. Allah (SWT) ya ji}ansa, ya yafe masakurakuransa, ya sa Aljanna ce makomarsa, amin.

Sa Hannun:HAMISU LAMI[O IYAN-TAMA

Page 23: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Hajiya, kina so ki shirya fim naki na kanki? To, ki sani, akwai mata irinki wa]andasuka riga ki shirya fim. Wasu daga cikinsu matan aure ne, wasu kuma zawarawa, dasauransu. Don haka kul kika shiga harkar fim ba tare da jin yadda �yan�uwanki matasuka yi nasu ba. Shin sun wanye lafiya kuwa? Ki karanta wannan labarin a tsanake,

don Hausawa sun ce da na gaba ake gane zurfin ruwa!

L OKACIN da aka fara yin wasan kwaikwayona bidiyo, babu wanda ya ta~a tunanin matawa]anda ke zaune a gidansu ko gidajen

mazansu za su taka muhimmiyar rawa cikinharkar. Amma sai ga shi tun tafiya ba ta yi nisa bamatan sun shiga cikin harkar ta hanyar zamafurodusoshi, watau masu fitar da ku]a]ensu suna]aukar nauyin shirya finafinai. In ana wannanmagana, misali, dole a ambaci mata irin sumarubuciyar nan Hajiya Bilkisu Salisu AhmedFuntuwa, wadda ita ta ]auki nauyin shiryafinafinai kamar su Ki Yarda Da Ni, wanda harabada ba za a manta da shi ba a tarihin fim naHausa, da Sa�adatu Sa�ar Mata. �Anty Bilki� tanadaga cikin matan da suka shirya fim, amma a}arshe ba su jida]i ba. Shi yasa ma haryanzu ba tasake ba daku]inta an yifim ba, ga shikuwa tana so tayi ]in. Babbarmatsalarta itace, ita mataraure ce, kumaita sana�ar fim,a yadda take ayau, harka ceta maza, ko ace wadda mazasuka yi kane-kane a cikinta,suna cinkarensu babu

babbaka. Mata, musamman na aure, ba za su iyayin cu]anyar kasuwanci irin wadda sana�ar shiryafim ke bu}ata ba. Duk da haka, a gaskiya, mata sun taka rawargani wajen ]aukar nauyin shirya fim. Wata,sha�awa kawai ke sa ta fasa asusunta ta ba daku]in a yi mata fim. Wata kuma, wani labari netake so ta ga an yi fim ]insa, don haka sai ta ]aukinauyi, ya-Allah don labarin ya shafe ta ko kumakawai tana so a yi shi. Wata kuma tana hangen zata samu ku]i, wato a wurinta sana�a ce wadda ta fiadashe � ta zuba jari, ta sami riba bayan an fitarda uwar ku]i. To, kamar kowace sana�a, yadda ba ko dayaushe ake samun biyan bu}ata ba, haka ma abinyake a harkar fim. Akasari matsalolin da su matafurodusoshi ke samu sun danganta ne da jinsi �watau su mata ne ba su shiga suna gogayyakamar yadda maza furodusoshi ke yi. Wannankan jawo masu samun tangar]a da �yan wasamaza da mata, darakta, masu sayar da kaset kokuma wurin nuna fim ]in a gidajen sinima kafin asake shi a kasuwa. Mujallar Fim ta da]e tana nazarin halin }uncida furodusoshi mata suke a ciki. Domin za}ulohalin da suke samun kansu, mujallar ta shafewatanni tana bin wa]ansu daga cikin fitattun matafurodusoshi gida gida, tana tattaunawa da su.Bayanan da mujallar ta na]o sun tabbatar da cewaashe inda wani ya yi rawa aka ba shi ku]i, wani inya yi sai ya sha ]an karen kashi. To shi ya samuka baje wa masu karatu bayanan dalla dalladon a fahimci matsalolin da suka fuskanta, ya-Allah ko an yi yi masu shigo-shigo ba zurfi, kokuma su yi wa kansu hangen-Dala.Wa}a a bakin mai ita ta fi da]i.Bilkisu Salisu Ahmed Funtuwa

... zakaran gwajin dafi

RAHOTON MUSAMMAN

27

Page 24: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

RAHOTON MUSAMMAN

AISHATU GIDADO IDRISMujallar Fim ta sha kawo

rahoto a kan wahalhalun daHajiya A�ishatu Gi]a]o Idrista sha a }o}arinta na shiryafim ]in Rabi�at a Kaduna.Idan an tuna, ta kashe ku]inda sun isa ma a shiryafinafinai a}alla guda biyu,amma fim ]in ya }ikammaluwa. A }arshe tatattara komai ta watsar acikin damuwa da kumakarayar gwiwa. Wanda yajagoranci yun}urin shiryafim ]in shi ne shahararren]an wasa {asimu Yero. Shinko ta daddara?

Fim: Hajiya, mutane ba susake jin ]uriyarki kanyiwuwar kammala fim ]in kina Rabi�at ba. Ko an fasayinsa gaba ]aya ne?

A�isha: A gaskiya fim ]inna Rabi�at yana tattare damatsaloli masu yawa.Saboda haka ni na fi ganinya kamata a bar shi gaba]aya. Amma ina sa ran zan yiwani da wasu �yan wasanmuna nan Kaduna masu}ungiyar Farin Wata; sunayin wani fim wanda ina ciki,in sun gama nasu ina da waniscript na wani littafin nawaina son su yi mani shi a cikinwannan shekarar.

Fim: Sau da yawa matasukan fuskanci matsaloliwajen shirya fim a yayincu]anyarsu da mazan da zasu taimaka masu kamaryadda ke ]in nan za ki iyazama a matsayin misalinmu.Tun da har yanzu kina dawannan buri na shirya fim,ta yaya za ki magance irinwa]ancan matsaloli?

A�isha: To ni yadda zan yiwajen magance irinwa]ancan abubuwa� Ko dayake matsalar ba ta masushirya fim ce gaba ]aya ba,ya danganta da wanda ka yihul]ar da shi ne. Kamar niyanzu, zan shirya fim tundana da]a wayau, na da]adabara, zan yi hul]a dawanda yake jin maganata ne,ba wanda ya fi }arfina ashekaru ko wanda nake jinkunya ba. Zan yi harkar neda wa]anda suke ganina amatsayin babba, wa]anda in

na yi magana za su saurareni (dariya). Domin wannanshi ne kawai ya fi dacewagare ni har in kai ga cimma

nasarar wannan buri nawa nashirya fim.

Fim: Wace shawara za kiba mata masu sha�awar shiga

wannan harkar don kauce wairin matsalolin da kika cikaro da su?

A�isha: Shawarar da zan basu ita ce kar su karaya. Ko ni]in nan ba na karaya ne dashirya fim gaba ]aya ba. Inwani bai maka yadda kakeso ba, wani zai yi. Na yarda akullum mutum yana da za~i,don ban ta~a yarda mutaneduk ]aya suke ba. Har yanzuakwai wa]anda za ka ba suamana ba za su ci ba. Abinda ya sa na yanke hukuncinba zan ci gaba da yin fim ]inRabi�at ba shi ne yawansurutan da yake zagaye dashi. Amma ni tunda inasha�awa kuma na ga mutanesuna da sha�awar in shiryafim, zan yi }o}arin ganin nashirya ko da fim ]aya. Yanzuna san wa]anda zan ba a takecikin sati uku sun gama. Donhaka duk mai sha�awarharkar kada ta karaya. Ni maabin da ya same ni rashin sa�ane da kuma dalilin shi wandana bai wa aikin ]an�uwa nekuma ya girme ni ina jinkunyar shi. Nan gaba in nasamu wa]anda suke jinkunyata in Allah Ya yarda zasu yi mani. Kuma shi yin fimin ya cika burinka yana dariba kuma abu ne mai kyauga rayuwar jama�a. Duk daabubuwan da suka farutsakanina da {asimu Yerohar ake ambaton za a iya yinfim na naira miliyan ]aya kobiyu, na san akwai finafinaiwa]anda za ka kashemiliyoyin nairori,amma nasan irin wa]annan finafinannamu na Hausa dai da dubu150 zan iya shirya guda]aya. Don haka dubu 150zuwa dubu 200 shi zan sa afim ]ina na gaba, kuma zaifito in Allah Ya so!

Idan akwai wadda ta yi waharkar fim shiga da }afardama, to Hajiya HalimaIsma�il Almajir ce. Ko daakwai wasu kafin ita, totabbas dai wannanmatashiyar matar auren tanacikinsu. Za a iya lura dawannan kalami ganin cewa

fim ]in ta na farko da ta ]aukinauyin shiryawa, watau KaraDa Kiyashi, bai fito ba sai daya shirya. Ganin cewa kamarta shigo harkar da }afar dama,Halima ba ta yi wata-wata basai ta jefo }afar hagu ta fa]oruwa tsundum a cikin harkar.Ko da yake ruwan bai ha]iye

ta ba, to ya kama ta iya wuya.A yanzu haka ta yi wanisabon fim mai suna Alhini,wanda muka ba ku labarinsaa watan Afrilu na bana. Gadalili:

Fim: Hajiya, me ya ba kisha�awa har kika shiga

HALIMA ISMA’IL ALMAJIRFurodusar shirin Kara Da Kiyashi

A’ishatu Gidado Idris... rashin sa’a na yi

�Ni yanzu, zan shirya fim tunda na da]awayau, na da]a dabara, zan yi hul]a da

wanda yake jin maganata ne, ba wanda yafi }arfina a shekaru ko wanda nake jinkunya ba. Zan yi harkar ne da wa]anda

suke ganina a matsayin babba, wa]anda inna yi magana za su saurare ni...�

28

Page 25: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

]aukar nauyin shiryafinafinan Hausa?

Halima: Ka san al�amurranyau da kullum. Ina ]ayadaga cikin masu yi wawannan harka kallonfa]akarwa da kumailimantarwa. Koda yake daiwasu na ganin kamar shirmene, to ni a ganina ba haka bane.

Fim: Ba ki samun rashinjituwa da maigidanki? Ko dayardarsa kike yi?

Halima: Babu watamatsala ta ~angarenmaigidana.

Fim: Ya zuwa yanzu fimnawa kika yi wanda ya shigakasuwa?

Halima: Guda ]aya ne,watau Kara da Kiyashi.

Fim: Wanene daraktan fim]in?

Halima: IbrahimMandawari ne.

Fim: Ko kwalliya ta biyaku]in sabulu?

Halima: Sosai kuwa, saigodiya; kwalliya ta biyaku]in sabulu.

Fim: Ga shi ke a gida kikezaune. To ba a samunmatsala can wajen nuna shia sinimomi ba, watau a yimaki }wange?

Halima: Ai ni ina dawa]anda ke yi min komaikuma na yarda da su }warai.

Fim: To kin ta~a ba dagudummuwar gida don a yishirin fim a ciki?

Halima: Ai Alhini kusan agidanmu aka yi shi.

Fim: Ko kikan yi hira tareda wasu mata har su ba kilabarin suna sha�awa su masu shiga cikin harkar?

Halima: Ai ka san wannanharka ta mai ha}uri ce.Watau idan ta ji lokacin daake ]auka tun daga farkonfara yin fim har shigakasuwarsa, sai gwiwarta ta yisanyi. Wasu kuma gaskiyasuna sha�awar shiga amma basu da }arfin yi.

Fim: An ce labari kike saye.To zuwa yanzu kin sayikamar guda nawa?

Halima: Zuwa yanzu nasayi labarai sama da gudagoma amma a yanzu Alhinine ake so a kammala; daganan kuma sai a shiga wani.

Fim: A wurin wa kika sayilabarin Alhini?

Halima: Ai ka sani. A wurin

Maureen Ikram ne, kuma bata da]e da tashi daga nan b;,da ta san za ka zo to da kuwata tsaya.

Fim: Wace hanya kike bikike gane ingantaccenlabari?

Halima: Muna zama netare da mai labarin da daraktada ni da kuma dangina a yiwa labarin duba na basira.

Fim: To wannan harka

FATI H. MOHAMMEDBabbar furodusar shirin Ana Bikin Duniya...

Hajiya sai mai }arfi ke da}arfin yin ta. Ya kike gudanarda taki?

Halima: Da }arfina, saikuma na Allah yaketaimakona a kowane hali.

Fim: To fim ]in ki maifitowa nan gaba, watauAlhini, tun bai fito ba harsunansa ya game ko�ina.Wannan alamun nasara ne?

Halima: {warai kuwa.

Gaskiya ina gode wa daraktaTijjani Ibrahim da sauran�yan wasan da ke ciki. Kumain Allah Ya yarda sai na samu�Award� (kyauta), ko a kansako a wani!

Fim: A }arshe ko za mu iyajin farashin wasu labaran dakika saya?

Halima: A�a, gaskiya sirrine. Kai ma ka san bai kamatain tona ba.

Hajiya Fatima H. Moham-med ta shirya fim ]in ta nafarko, Ana Bikin Duniya...Daga kansa ba ta yi wani ba,amma an ce mana tana nantana jan ]amarar sake shiryawani, idan kashi na 2 na AnaBikin Duniya..., ya fito.

Hajiyar tana daga cikinmatan da suka }waci kansuda }yar daga hannun mazanda suka dan}a wa amanarshirya musu fim a Kaduna.Shin yaya aka yi ne?

Fim: Hajiya, Ana BikinDuniya... ya shiga kasuwa,amma mun samu labarin kinfuskanci matsaloli masuyawa kasancewarki mataraure kuma ba}uwa a harkar.Shin kina sha�awar ci gabada shirya finafinan Hausa?

Fatima: A gaskiya na samumatsaloli da dama, na samutangar]a da yawa. Ka sansha�anin mutane, da na luraabin kamar an yi mani dagayya ne don gobe kada insha�awar shirya fim, sabodahaka ko na ci riba ko ban ciriba ba kasancewar da manba na yi don kasuwanci bane, a yanzu haka a shiryenake da in sake shirya wanifim ]in.

Fim: Yawanci ku matanaure da kuka shiga cikinwannan harka ba ku iyahalartar ko�ina domin aikinshirya fim kamar yadda mazake yi, wanda hakan yake saake maku sakiyar da ba ruwaa wasu wuraren. Ya za ki yida wannan matsala a nangaba?

Fatima: Game da matsalarzuwa locations (wuraren

Fatima H. Mohammed... na hadu da maza maciya amana

]aukar wasa) gaskiya banwahala a wannan ~angarenba, saboda duk inda aka tafi}afata na wurin tunda ayanki guda na yi aiki. Ammana samu wasu matsalolisaboda rashin sanin abu.Kasancewar na farko ne agare ni, na dan}a wasuabubuwa ga maciya amana,suka ci amanata. Tundayanzu na karantu, nan gabada kaina zan ]auki matakitare da �yan�uwana da dukwanda na yarda da shi, tundaba duka aka taru aka zama]aya ba. A lokacin shirya fim]ina na Ana Bikin Duniya...,

akwai wa]anda na ji da]inaiki da su; zan iya gayyatarsua duk wani fim da zan shirya.Akwai wa]anda ko kyautasuka ce za su yi mani ba naso.

Fim: A }arshe waceshawara gare ki ga�yan�uwanki mata da suke dasha�awar shigowa harkarshirya finafinan Hausa?

Fatima: Shawarar da zanba �yan�uwana mata da sukeda sha�awar shiga wannanharka ta shirya fim, muwa]anda muka fara mukafuskanci matsaloli kada}yashi da kishi da mugunta

29

Page 26: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

su sa mu }i nuna wa�yan�uwanmu hanyar da ta fidacewa. Duk wacce za tashirya fim ina ba ta shawararta nemi �yar�uwarta mace data ta~a yi don ta ba tashawarar kauce wa wasumatsalolin. Kuma ina ro}onsu mazan da muke tare da susu ri}a kwatanta gaskiya ayayin cu]anyar mu da su.

Fim: Yanzu in wata ta nemeki da ki taimaka mata har tashirya fim, za ki amsagayyatarta?

Fatima: Wallahi, wallahi,zan taimaka mata ]ari bisa]ari yanda za ta ji da]i har tace ai wance ce sanadinsamun nasarata. Zan taimakada iya abin da zan iya dagaKaduna har Kano, da yinharkar. A }arshe ina kira gadukkan furodusoshi maza damata da mu ri}a shiryafinafinai masu ma�ana bakwashi-kwaraf ba. Kuma inason mu ha]a kai a daina fitarda finafinai barkatai akullum. Ya dace a yi tsari nafitar da finafinai daki-daki.

Duk wacce za ta shirya fim ina ba ta shawarar ta nemi’yar’uwarta mace da ta taba yi don ta ba ta shawarar

kauce wa wasu matsalolin. – Fati H. Mohammed

Malama Maryam HammaWabi ba furodusa ba ce (saidai buri!), to amma �yar wasace a rediyo da talbijin dakuma wasu finafinai }alilanda ta fara. Maryam wadda kezaune a Kaduna, ta cematsalolin da mata kefuskanta a }o}arinsu nashirya finafinan Hausa laifinmazan da ake ba aikin ne sukuma su cutar da matan bisatunanin sun fi su wayo,wanda yin hakan kasheharkar ce gaba ]aya da kumawayon rashin wayo da sumazan ke aikatawa, inji ta.�Ko ba komai, masu karinmagana sun ce cin dare ]ayakumburin ciki,� injiMaryam.

Ta ce da mazan da matanke jawowa a jiki don shiryafim suna aikinsu tsakani daAllah, to da an samu matamasu yawa ya zuwa yanzu a

wannan harkar, musamman aKaduna inda ita ta fi sani.Don haka a ganinta ya zamawajibi ga maza da suka yi

nisa a wannan harka su fitofisabilillahi wajen taimakawa mata masu sha�awar shigaharkar ba tare da zaluntarsuba.

�Yar wasan ta }ara da cewayadda aka bar mata masuharkar fim suna ta kame-kame a harkar da fuskantarmunanan matsaloli shi ne ke}ara kashe gwiwar yawancinmata irinta masu sha�awarshiga harkar. Wannan dalilinna yi wa mata dungu a harkarya sanya wasu matan da sukaci karo da irin wa]annanmatsaloli ba su sha�a war cigaba da harkar ko sun fara.

A }arshe ta yi kira dababbar murya ga mazan dasuka san harkar shirya fim,musamman a Kaduna, da suri}a tsare gaskiya a yayinhul]arsu da mata masusha�awar harkar ta yadda zaa gudu tare a tsira tare.

‘Yadda za a gudu tare a tsira tare’– Hira da Maryam Hamma Wabi

ZAYYA I. DANTATAFurodusar shirin Gwi Da Yara

Hajiya Zayya I. [antata ceshugabar kamfanin �[antataMotion Pictures,� Kano,kamfanin da ya shirya sabonfim ]in nan Gwi Da Yara. Itama, kamar kowa, ta fuskancimatsaloli wa]anda suka sahar ta yi tunanin kila ma tadaina shirya fim ]in kwata-kwata. Me ya faru?

Fim: Menene ya jawo}arancin furodusoshi matataa harkar fim na Hausa?

Zayya: Ni a ganina shi nesaboda mazan ba sa ba mutallafi da kuma ~ata fim ]ina idon mutane wanda kumababu wani abin ~atanci aciki.

Fim: Menene ra�ayiniyayensu bayan sun kalla?

Zayya: Iyayensu sun san�ya�yansu fa]akarwa suke yi,suna farin ciki da su, dominsabuwar hanya ce ta wa�azi.Saboda haka idan har akwaikura-kurai, sukan nuna wayaran su gyara nan gaba.

Fim: Kina ganin akwaiwani dalili da zai iya hanauba ya bar �yarsa ta yi fim?

Zayya: I to, babu wanidalilin da zai sa uba ya hana�yarsa ta yi fim illa dalilinwasu finafinai da wasu ba}ike yi wa]anda ba su ta~a yinfim ba, kuma su ba Hausawaba ne, ba su san al�adarmuba; idan ma ka bi salsalarwasunsu ma ba ma �yanNijeriya ba ne.

Fim: Kina ganin wannanka]ai na iya hana iyaye barin�ya�yansu su yi fim?

Zayya: {warai!Yawancinsu ba Hausawa bane. Al�adunsu kawai sukan

Maryam Hamma Wabi

Zayya I. Dantata... kila in daina shirya fim

Fim: Kina nufin mazan daba sa ba ku tallafa mazajenkuna aure ko kuma wa]anda kecikin harkar?

Zayya: Manyan masuku]i da kuma mazajenmu naaure. Akwai da yawa matamasu ku]i da suke son su]auki nauyin fim ]in, ammamazajensu sun }i. Abin dasuka dogara da shi kuwa shine tun usulin shirinfinafinan, mata ne masuzaman kansu suke yi. Ammasuna mantawa da cewa matanda suke yin fim a yanzukamilallu ne; yawancinsu agaban iyayensu suke. Niabin da yake da]a }arfafamin gwiwa a halin yanzu harnake da]a yin fim ]in (shi

ne) yawancin �yan matanidan muka gama yin fim ]insai sun kai wa iyayensu sunkalla.

30

Page 27: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

zuba su caku]a da namu subai wa mutane su kalla.

Fim: Wane irin labari yakamata a rubuta a shiryafinafinai da su kenan?

Zayya: Labarin da nake so,nake ganin kuma ya kamatamutane su dinga yi, shi nekowa ya san mu Hausawa dakunya da karamci da kara daal�adu; a ce duk wani wandazai shirya fim idan ya zo,muddin ba yarensa ba ne, saiya samu Bahaushe ya ba shilabarinsa ya duba, kumaBahaushen wanda ya san ya-kamata.

Fim: Akwai wasu ba}in dasuke zuwa suna ha]ashirinsu da Hausawan namuamma duk da haka sai ki gaan gur~ata lamarin. Me kejawo hakan?

Zayya: Ai ya kamata dukmutumin da ya yi wani abu acikin fim a daina ganinlaifinsa saboda sai abin dadarekta da furodusa suka cemasa su zai yi; laifin nafurodusa ne da darekta.

Fim: Su �yan wasan ba suda laifi kenan?

Zayya: �Yan wasa baruwansu. Ai duk abin da akaba shi zai yi. Ka ga misali,kamar Wasila, mutane na jinhaushin Ali Nuhu sabodawannan wa}ar, amma ai baikamata a ji haushinshi ba akan wannan wa}ar. Wanda yarubuta ne. Shi Ali ba shikawai aka yi ya kwaikwayafa. Yawancin mutane ba susan akwai wasa tsakaninmuda su (Zazzagawa); shi ya saaka yi, amma bai kamata a jihaushi ba har da mai damartani. Saboda akwai wasuwa}o}i da aka yi don mai damartani. Idan aka ci gabahaka sai ka ga abin ya jawogaba. Martani bai dace ba.

Fim: A lokacin shirya GwiDa Yara, kin yi wa �yan wasanda ma�aikatan fim ]inkyautar shaddodi da leshi-leshi. Me ya sa?

Zayya: Ina tunaninwatakila zan daina shiryafinafinai. Ka ga in aka yihaka sai mu yi rabuwar lafiya,ina tunawa da abin kirkin dasuka yi min, suna tunawa dani.

Fim: Gwi Da Yara ne fim]inki na }arshe kenan?

Zayya: Ina tunanin kilaidan na fitar da Gwi Da Yara

na 1 da na 2 da Harbi Ga [anJaki kashi na 2, zan dainashirya finafinai. Sai dai kumaban san ikon Allah ba!

Fim: Me ya sa za ki dainashirya finafinai?

Zayya: Saboda yauhar}alla sun yi yawa, masu~ata mana sana�ar sun yiyawa kuma idan an tashi ba

za a ce su wane da wane neba. Idan da za a bi ta mazanjiya wa]anda muka taras dasu a kai, kamar su {asimuYero, sun yi aiki }warai dagaske; muddin suka yi fimza ka iya ]aukowa ka kalleshi a gaban ko waye naka,babu batsa damakamantansu.

Fim: Wace shawara za ki

ba masu shirya finafinai?Zayya: Don Allah don

Annabi su daina ci da zuci.Harkar fim fa]akarwa ce bawasa ba ne ba, kuma a gabaamfaninmu ne, amfanin�ya�yanmu ne. Allah Yataimake mu jama�a damutanen gari da gwamnati suda]a fahimtar fim.

AMINA MOHAMMED LAMIDOFurodusar shirin Tagwayen Hawaye

Amina Mohammed Lamido... na yi zaton ba zan samu matsala sosai ba

Kamar yadda muka ta~akawo maku labarinta, AminaLami]o fitaccioyarma�aikaciyar talbijin ce,wadda har yau ]in nan takekaranta labaran duniya agidan talbijin na �NTA�Kaduna. Ba �yar wasa ba ce,amma tana tare da �yandirama na gidan talbijin ]in,wato irin su Samanja.Sha�awa da son fa]akarwa yasa ta shirya fim ]in ta �maiaji�, wato Tagwayen Hawaye.Kamar kowace ba}uwarfurodusa, ita ma ta sha tasku:

Fim: A matsayinki na mataraure kuma sabuwa a harkarshirya fim, ya kika samukanki a wannan harka?

Amina: (dariya tare dajinjina) A gaskiya, harkartana da wuya ba yadda nazata ba! Da ganin cewa inaaikin talbijin kuma na sanyadda production yake sai nayi zaton ko da zan samumatsala, to ba zai zama maiyawa ba. Amma sai na ga abinba haka yake ba. Don munfuskanci matsaloli masuyawa. Sai dai matsalolin inAllah Ya so ba za su sa mu yi}asa a gwiwa ba. Kai, sun ma}ara mana zumma ta yaddaza mu fito a yi da mu.

Fim: Ko za ki ]an labartamana ka]an daga cikinmatsalolin da kika fuskantaa lokacin shirya fim ]inki?

Amina: Farko dai matsalata ku]in sannan matsala tahul]a da jama�a � abin da basai na fayyace komai ba,musamman wa]anda aikinna bu}atar gudummawarsu.Da man ka san hul]a dajama�a akwai wuya, sai kala}ance su kuma ka yiha}uri.

Fim: Akwai matsala tayawanci mata da ke cikinwannan harkar: ba su iyashiga dumu-dumu cikinaikin sai dai wasu maza suwakilce su, kuma in aka yirashin sa�a su ri}a yi masuwasa da hankali. Ke ya kikayi naki?

Amina: E, kamar yadda kafa]a, kamar batun zirga-zirga, ka je nan, ka je cankamar yadda namiji zai yifa]i-tashi, mu zai manawuya; sai dai ka zaunawanda kake bu}atar aikinnashi sai ya biyo ka. Kai,akwai wanda na ba aiki maban san inda yake ba kumana samu matsala da shi sosai,sai dai abin ya wuce. Ina da}anne maza da kuma wa

wa]anda sukan je wasuwuraren a madadina, ammasuna da matsala tunda basanin harkar suka yi ba.Kuma ni saboda kula da gidada kuma aikina ka ga ba zaniya zuwa ko�ina ba.

Fim: Saboda matsaloli dakika fuskanta, ba kya jinhakan ya kashe maki gwiwakan ci gaba da wannanharkar ?

Amina: Kasancewar akwaimu da saurin karaya mumata, akwai lokacin da zanji kawai ni ma na dainawannan harka. Sai kuma inna je na kwanta na yi tunanisai in ce, �Ba ma zan dainanba!� Saboda a NTA Kadunainda nake aiki, kusan nika]ai ce mace. Kuma irin

31

Page 28: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

gwagwarmayar da nafuskanta a shirya wannan fimna Tagwayen Hawaye, hakanake fuskanta a can. Aiki newanda yawancin maza sukafi yin shi, don haka ke macein kika shigo dole ki samumatsaloli don haka wannanwani }alubale ne a gare mu.Koda yake ni ba ina irinfariyan nan wai duk abin damaza suka yi za mu yi batunda ba irin tsarinhalittarmu ]aya ba, amma shiirin wannan aiki ina ganinbai fi }arfina ba; zan iya.

Fim: Idan wata maisha�awar wannan harka tanemi shawararki kan yaddaza ta magance wasu cikinmatsalolin, me za ki fa]a

Aiki ne wanda yawancinmaza suka fi yin shi, don

haka ke mace in kika shigodole ki samu matsaloli

– AMINA LAMIDO

mata?Amina: A gaskiya, mace ita

ka]ai ta fito ta ce za ta shigacikin wannan harka akwaiwuya. A gaskiya, kamaryadda na fa]a kan hul]a dajama�a, in ba tana da wasutsayayyun maza ba a gefenta

wa]anda ko don shakkarsuza a raga mata, musamman awannan loaci namu na komaisai a ce cuwa-cuwa, za tafuskanci matsaloli. Kodayake an ce Bature ya hanaaikin banza, haka yake, saidai wani lokaci ana yin abin

da zai cutar ne.Fim: To in ta ba da

kwangilar aikin gaba ]aya fasai dai ta ga an shirya mata.Menene ra�ayinki kan haka?

Amina: E, to wannanmagana ce ta aminci. Ai intana ganin akwai amintaccensai su shirya ta ba shi. Ammani dai abu ne da ba zai yiwuba a gare ni. A gaskiya ni daizai yi wuya in dun}ula ku]iin dam}a ma mutum don yaje ya shirya mani fim, ko donna saba hul]a da jama�a nena san halayen yawancinsu?Don haka maganar mace tazauna ta dun}ula ku]i ta bada a yi mata fim, ko]an�uwanka na jini ne akwaitunani a kai.

RABI SULEIMAN da RAHAMA YUSUFFurodusoshin shirin Dukiya

RABI Suleiman sananniyace a duniyar finafinan Hausa.Domin ta yi finafinai dadama baya ga diramomi data yi a gidan talbijin na JiharKano (CTV). �Yar�uwartawadda suka ha]a dangi tawajen uwa, Rahama Yusuf,ita ma ta fara cirar tuta afagen fa]akarwa ta hanyarwasan kwaikwayo a kasa-kasan bidiyo na Hausa.

Dukkansu ba �yan mata bane duk da yake ba kowa neya san hakan ba saboda dukwanda ya kalle su, tsammanizai yi �yan mata ne irinwa]anda Bature ke ce wa�sweet sixteen� watau �yanshila �yan shekaru shashidda. Amma sun fa]a wamujallar Fim cewa sun ta~ayin aure har kuwa da }aruwa.Kowace tana da �ya�ya gudabiyu.

Ita dai Rabi, mutunniyarJihar Bauchi ce, daga garinAzare, yayin da RahamaBaha]ejiya ce daga JiharJigawa, amma a birnin Daboaka haife ta a Fagge. Yanzutana zaune a Rijiyar Lemo.

Wa]annan }awaye kuma�yan�uwa sun bi sahun abintarihin nan da mata ke yi nazama furodusa.

Su ne furodusoshin sabonfim ]in nan, watau Dukiya.Kuma sun ce sun yankehukuncin shiga a dama da sune a fannin samar da finafinai

saboda kasancewarsu a cikinharkar, wadda sun san sirrintaciki da waje domin �munacikin harkar muna }aruwa,muna samun alheri, sabodahaka duk da kallon hadarinkajin da al�umma ke yi wamatan da ke cikin wannanharkar, muka ga ya dace mushiga mu ma a dama da mu.�

Kuma sun ce suna sane dairin maganganun da aka yi

na cewa ina suka samu ku]inda suka shirya fim? Jarumansun ce hanyar Allah cewadda Hausawa kan ce ta fida cali. �Mun yi }o}ari muntara ku]in da muke samu afim. Kuma akwai wa]ansuabubuwa da muka sayardomin yin wannan fim,� injisu. Amma sun ce sun samutaimako daga abokan arziki,ciki kuwa har da samarinsu,

amma sun ce abin da sukasamu ba wani wanda ya takayara ya karya ba ne.

Da aka tambaye su kowa]anne irin matsaloli sukafruskanta yayin }o}arin fitarda wannan fim nasu? saijaruman suka ce ba sufuskanci wata gagarumarmatsala ba, illa dai a ranarfarkon ]aukar shirin sabodarashin halartar wasu dagacikin �yan wasan a wurin]aukar shirin. Amma dagabaya ba su sake fuskantar irinwannan matsala ba domin�yan wasan sun ba su ha]inkai }warai da gaske.

Sun danganta rashinsamun matsala gakasancewarsu suna cikinharkar domin �kar ta san karne.�

�Muna cikin harkar, munsan komai, mun san sirinharkar � da]inta da rashinsa,ka ga ko da wuya a ce anlayance ma mutum ko a cuceshi,� inji jaruman biyu.

Jaruman, wa]anda suka cesuna sa ran kwalliya za tabiya ku]in sabulu, sun yi kiraga �yan�uwansu �yan wasamata da su ]auki halayyartsimi da tanadi don su ma susamar da nasu finafinan, susan cewa ba wahala suke yiba. Sun }are da bayar databbaccin sake yin aure dazarar Allah ya kawo masumazan }warai.

Rahama Yusuf... kar ta san kar, ba za a layance mana ba

32

Page 29: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 33

BALARABA Ramat Yakububa ba}uwa ba ce a harkar fim.Duk da cewa har yanzu fim]aya ta yi, sunanta ya yi fice,musamman a cikin }ungiyarmasu shirin fim ta Jihar Kanoda kuma ta �Arewa Filmmak-ers� inda take a matsayindattijuwa (elder). Sai ALahira na 1 da na 2 su nefinafinanta wa]anda tunisuka shiga kasuwa. Ammatana nan tana shirin yin wanim ai suna Ina Son sa Haka.

Tun kafin ta fara yin fim]in a 1999, da ma tana dasha�awar finafinan Hausa.Takan je inda su Ado AhmedGidan Dabino da [an�azumiBaba suke shirya fim tanakallo. Daga nan sai ta fasoruwa.

Hajiya Balaraba tabambanta da sauran matafurodusoshi. Yayin da saurake zaunawa a gida suna turamaza don gudanar masu daharkoki, ita da ita ake zuwako�ina. �Ka ga ni inda nabambanta da sauran mata, dani ake komai, hatta raba

BALARABA RAMAT YAKUBUFurodusar shirin ...Sai A Lahira

Balaraba Ramat Yakubu... za mu kafa kungiya ta furodusoshi mata

kwalaye wurin �yan kasuwaduk da ni ake yi, � inji ta.Amma ba ta zuwa sinima.

Wannan kalami ne da ta yiya sa ita ba ta fuskancimatsalolin da wasu mata kanfuskanta ba. Sai dai tatabbatar da cewa wasumatan kan ha]u da matsaladomin, a ganinta, shi kesanyawa suna canza daraktaidan sun tashi shirya wanisabon fim. �Ai kowar tunabara, bai ji da]in bana ba,�inji babbar furodusar, waddatun tuni ta ciri tuta a fagenrubuta littattafan }agaggunlabarai. Ma�ana dai, samuntangar]ar da ake yi idan an]ora wani ne kan haifar dacanjin.

Yanzu haka tana da labarairubutattu guda hu]u. Takuma bayyana cewa cikinwatan Yuli ko Augusta za tafara shirin fim ]in ta na InaSonsa Haka. A }arshe kumata nuna cewa su matafurodusoshi suna nan suna}o}arin }afa }ungiya tasu takansu don kare martabarsana�arsu, musammansaboda irin matsalolin da susuke fuskanta a matsayinsuna mata.

HINDATU BASHIRFurodusar shirin Maula

Hindatu Bashir... babu wanda ya cuce ni don na san komai a harkar

AN fi sanin HindatuBashir a matsayin fitacciyar�yar wasa. To kwanan nan tariki]a, ta zama furodusa.Sunan fim ]in da ta shiryaMaula, wanda zai fito a nangaba ka]an. Shin me ya bata }warin gwiwa har ta ga itama ya kamata ta yi fim nakan ta? Wannan ita ce tambayar farko da mujallar Fim tayi mata. Hindatu ta ce: �E to,a gaskiya abin da ya ba ni}warin gwiwa har na yitunanin yin wannan fim nakaina shi ne kishin abin (fim)kuma ina ganin na da]e cikinharkar nan, ya kamata a ceiri irinmu da suka da]e cikinharkar nan muna ]an }o}ariko dai yaya ne muna ]an yinnamu production ]in.�

Fim ]in Maula yana nunaillar almajiranci ne aArewacin }asar nan. �Sabodasai ka ga mace lafiyarta }alau

ta zo da katin asibiti na }aryata ce mijinta kaza, ta yi ta]ora ma kanta bala�i damasifa. To ana so a nuna illarwannan. Kuma uwa da ]antayana yi mata komai a duniyatana bara duniya kuma nazagin ]an, ana cewa ba ya yimata abin da ya kamata, nanko rashin wadatar zuci kejawo irin wa]annanabubuwa da suka gallabe mua Arewa. Kuma }abila ba yada abin da yake zaginmu dashi da ya wuce wannan bara.Shi ya sa saboda kishinArewa, saboda ni �yar Arewace gaba da baya na ga yakamata in bayar da dagudunmawata gashugabannina. In kuma nunacewa ni mai fa]akarwa ce,wannan gudumawar ita yakamata in bayar a Industryga }asa baki ]aya,musamman Arewa.�

Page 30: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200134

Da yake wannan wanibabban al�amari ne da yashafi rayuwar mutanenmu,shin ko furodusar ta yi wani}o}ari na tuntu~a jami�angwamnati domin a taimaketa? A cewar Hindatu, da farkota so ta yi haka ]in, to ammasai ta ga tunda ta yi nesaboda Allah, in ta gamaalabasshi tana iya sanar dasu ga ]an kokarinta da ta yia zo a gani. Mun ji cewawata}ila Hindatu ta kira tarota }addamar da fim ]in donjawo hankalin jama�a zuwaga jigon fim ]in. Kuma dukda yake wasu suna gulmarwai ina ta samu ku]i har tashirya fim ]in, Hindatu ta ceita ta ]auki nauyin abinta,ba wani ne ya ba ta ku]in ba.Ta ce: �Ka san na da]e cikinwannan harkar. Kumaku]a]en da ake biyana ina]an adana su saboda ni maina sa ran nan gaba zan yi}o}arin yin nawa fim ]in. Tahaka ne na samu sukunin yinnawa fim ]in.�

To wace matsala tafuskanta a }o}arin da ta yina yin wannan fim? Hindatuta amsa: �Ka san shi harkarjama�a sai dai a yi ha}urikawai, amma gaskiya banfuskanci wata matsala bawata}ila saboda ni �yar wasace, akwai mutuncitsakaninmu da girmamawa.Saboda haka ban fuskanciwata matsala ba, sai dai taaljihu da ku]i suka yi tafita.�

Ta ce ba ta fuskanci irinmatsalar nan ta cutarsababbin furodusoshi mataba. �Saboda tun kafin in farasai da muka zauna mukazana abin da fim ]in zai ci,duk da cewa ya ci biyun abinda muka }iyasta kashewa.Amma ko me za a yi na sani,kuma daga aljihuna yakefitowa. Saboda haka ba azalunce ni ba.�

Furodusar tana da niyyarfassara wannan fim zuwaTuranci (sub-title)musamman don �yan Kudusu fahimci sa}on da take sonya]awa. A game daambaliyar da mata ke yicikin harkar shirya fim a �yanwatannin nan Hindatu ta cegaskiya wannan abin farinciki ne }warai. �Da ma hakaake so, mu �yan wasa,

musamman mata, mu tasomu rin}a yin ]an namu.Kada mu zauna sai dai akira mu mu yi wa wa]ansu.Gara kome }an}antarsa muyi namu. Ina yi masu fatanalheri.�

Mujallar Fim ta nuna waHindatu cewa idan akagama wannan ganawa ba ata~o maganar aure ba masukaratu za su ce mujallar bata yi aiki ba. Ina aka kwanakan maganar aure dominga shi maimakon a yimaganar aure sai }aratsunduma take yi cikinharkar fim? Sai Hindatu tayi dariya, ta ce, �Kamaryadda na saba fa]a kowanelokaci, komai yana dalokacinsa, kuma aure nufinAllah ne. Saboda hakakamar yadda nake fa]a ne:a ci gaba da yi manaaddu�a ta gamawa daduniya lafiya. Dominkowace mace babbanburinta a duniya shi neaure, a ce ga ta a gidanmijinta. Kowa akwailokacinta. Saboda haka niba zan fa]i komai ba gameda aure a yanzu. Ko yau nasame shi ina murna. Ammayanzu tunda bai zo ba bani da yadda zan yi.�

Da aka tambaye ta komenene burinta a yanzu,sai Hindatu ta amsa: �Saiabin da Allah ya tsaramani. Kuma ka san saningaibu sai Allah. Idan nafa]i abin da Allah ya tsaramani kamar na yi sa~okenan. Amma ina ganin yatsara mani ]aukaka da cigaba.�

Handatu ta yi kira ga�yan kallo da za su kalliMaula, ta ce, �Farko daiina so in yi kira da babbarmurya gare su da cewa donAllah duk wanda ya kallifim ]in, aka kuma samusa�a al�amarin ya yi daidaida tasa rayuwar, to kada ya]auka da shi ake. Ka sanakan samu akasi haka, kaga fim ya fito amma ya farua gidan wani. Mun yi nedomin fa]akarwa da kumawayar da kanal�ummarmu.�

Kuma ta ce kada su sakea ba su labarin Maula.�Don gaskiya yana da aikiwanda yake da kyau!�

RUMASA’U ABDULLAHIBabbar furodusar shirin Tarkon Mugunta

RUMASA�U Abdullahi �yarwasa ce, kuma ba ba}uwa ba cea finafinan Hausa. Ta fito afinafinai kamar su Jimami,Makashinka, Matsala, GarinmuDa Nisa, Sake, Wake [aya na 2,Dan fillo, da sauransu.

Wannan Bakatsiniyar yarinyadai an haife ta a cikin 1975. Tayi karatun firamare ta Bariki dake Gumel, Jihar Jigawa. Takuma yi karatun sakandare amakarantar �yan mata ta Gezawacikin Jihar Kano. A cikin 1999ta fara harkar fim. Kuma cikinwannan shekara ta 2001 ta yifim na }ashin kanta mai sunaTarkon Mugunta wanda zai fitonan gaba ka]an. Rumasa�uAbdullahi ta jaddada cewa fim]in ta ba chamama ba ne, dominta kashe ku]i ma}udai a kansa.

An tambaye ta dalilin da yasa ta yin fim. Sa ta ce, �Ni na yine kawai don mata su amfana.�

Ta }ara da cewa ita dai basayen labari ta yi ba, ita tarubuta da kanta. �Shi ya saidan ma ana }wararfurodusoshi mata wurinsayen labari, to ni dai ba a}ware ni ba,� inji ta. Ashe itace ta }ir}iro labarin TarkonMugunta? �Sosai kuwa ni cena }ir}iro Tarkon Mugunta.�Da ta juya kan mata masu bada ku]i a boye ana shiryamasu fim, sai ta nuna cewatana ro}onsu da su fito fili ayi gogayya da su.

Shi dai fim ]in TarkonMugunta, yana magana nekan cin dukiyar marayu,ha}uri da zamantakewa.

Yanzu me ya rage a fim]in? Rumasa�u ta ce an gamakomai, har kwali an buga. Dazaran ta ya haye sira]inhukumar tace finafinai saikawai a sake shi.

Rumasa’u Abdullahi... tana so mata su yi goyayya a sana’ar fim

Page 31: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

UMMA ALIBabbar Furodusar shirin Kaddara Ta Riga Fata

Za mu iya kiran HajiyaUmma Ali da cewa ita ma�yar �Yakasai Mafia�ce afinafinan Hausa. Dalili kuwashi ne a unguwar Yakasai,Kano, aka haife ta, unguwarda �yan cikinta suka yi waharkar fim kaka-gida. Har ilayau ita ce mace ta tarkofurodusa a Kano.

A cikin 1973 ne aka yimata aure, daga nan kuma saimijinta ya ga ya kamata tawuce ta }ara karatu a kan nafiramarr da ta yi. Sai ta daureta yi shekaru biyar asakandare, daga nan kuma saita zarce ta shiga makarantarkoyon unguwar zoma.

Da ta gama sai aka tura taAsibitin Murtala na Kano tayi aiki har na shekaru biyar.Ganin cewa nauyin iyali yafara hawa kanta, sai HajiyaUmma ta yi ritaya daga aiki.Da dai ta fahimci zaman gidaba zai yiwu haka ba, ita kumaba ta iya ]abi�ar Kanawa ba(kasuwanci), sai ta nemishawarar }anwarta HauwaAminu. Daga nan sai tashiga harkar ]aukar nauyinshirya fim.

Fim ]in da ta fara yi daishi ne {addara Ta Riga Fata,wanda labari ne daga littafimai wannan suna da itaHauwa Aminu ta rubuta. Gata}aitacceyar hira da UmmaAli ta yi tare da mujallar Fim.

Fim:Ya zuwa yanzufinafinanki nawa ke cikinkasuwa?

Umma: {addaraTa Riga Fata l & 2 da na 3sune ke kasuwa. To bayanshi kuma na yi yun}urin yinwani fim can a baya ammasai aka ce min fim ]in ba zaikar~u ba. To yanzu sai UmarBankaura ya kawo min waniscreenplay (rubutaccenlabarin fim) ya ce in saya. Nikuma na saya. Shi ne yanzuake yin fim ]in.

Fim: Yaya sunan fim ]in?Umma: Sunansa Romon

Rogo.Fim: Lokacin da kika yi

{addara Ta Riga Fata ko kinfuskanci matsaloli ganin

kuma wannan ni ban ]auketa matsala ba. Dalili kuwasu �yan wasan nan idan munkula duk abin da za mu basu, to ba mu biya su ba,domin mun yi anfani da�yancinsu ne. Ai ]an wasakamar mai kitso yake. Kasan Hausawa na cewa wai baa biyan ku]in kitso. Tomatsalar da na samu ita cerashin halartar (�yan wasa)kan lokaci ko kuma sa~aninda aka ri}a samu kan zuwan�yan wasa idan za a tafi shoot-ing. Ni kuma a fahimtatagani nake to wanda ya yimaka haka, ai yana da dalili,shi ya sa ban yi fushi bakuma ban canza �yan wasaba.

Fim: Kamar nawa kikakashe wurin {addara Ta RigaFata?

Umma: A }ididdiga inaganin na kashe kamar nairadubu ]ari uku, daga na 1 dana 2 da na 3. Amma cikin

kwanta saboda yanzua}allala akwai furodusakusan guda saba�in a JiharKano. Kowa idan ya yi nasa,fitar da shi zai yi. Ni kuwalokacin da na yi {addara TaRiga Fata akwai wani tsarina cewa duk sati akwai fim]in da zai fita. To wannan yakawo mana ciniki.

Fim: Da aka nuna {addaraTa Riga Fata a sinimomi ansami ku]i?

Umma: Lokacin ba a faranuna finafinai a sinima ba.

Fim: Akwai wa]ansumatan da suka nuna makisuna sha�awar zama furodusasu ma?

Umma: Ai ko sati ba a yiba wata mata ta yi min wayaamma na fa]a mata cewaharkar fim tana da da]imuddin za ta iya toshekunnenta daga dukkankowa]anne irin maganganu.Kuma na fa]a mata yanzukasuwa ta canza ba kamar da

Fim: Wa]anne nasororikika samu kan {addara TaRiga Fata?

Umma: Na sami nasarorida yawa, musamman dagaMaiduguri. Kai, MaryamAbacha ita kanta sai da takalli fim ]in kuma ya burgeta. Kuma wata uku da yawuce �yan Jami�ar Abuja sunnemi a sayar masu da fim ]in{addara Ta Riga Fata dominsu sanya shi cikin syllabus(manhajar karatu) a yijarabawar fita da shi. Ka gawannan in har haka ta faru aina sami nasara sosai.

Fim: Daga }arshe, Hajiya,kin ta~a yin tunanin kafa}ungiyar mata furodusoshi?

Umma: To ka san mu acikin gida muke, kuma ba muda yawa, don ban da irin suHajiya Zayya, BalarabaRamat da nake tare da ita,ban san mata furodusa dayawa ba, sai Hajiya A�i wacceta yi Gwagwarmaya.

cewa a gida kike zaune saidai ki tura a yi makiwa]ansu abubuwan?

Umma: Wallahi matsala]aya ce zan iya cewa nafuskanta wadda yake ita

yardar Allah na samu samada naira dubu ]ari bakwai.

Fim: A matsayin riba kociniki da riba gaba ]aya?

Umma: A�a ciniki da riba,saboda lokacin da na fitar dakwalin kashi na 2 na fim ]inhar guda dubu goma, cikinkwana ]aya suka }are.

Fim Har yanzu ana cinikiko ba a yi?

Umma: Gaskiya ciniki ya

ba.Fim: Wane kira za ki yi wa

mata furodusoshi?Umma: Ni a nawa ra�ayin,

mu ]auki �yan wasannan muri}e su hannu biyu. Ba nanNijeriya da ake finafinanHausa ko na lnyamurai ba,duk }asar duniya, kamarAmerika da Indiya, akwaitsegumi a cikin film indus-try.

Hajiya Umma tare da sauran furodusoshi a taron kungiyar masu shirya fim ta Nijeriyareshen Arewa (MOPPAN). Tare da ita akwai Balaraba Ramat

35

Page 32: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

ZAINAB WADA YAKASAIBabbar Furodusar shirin Tangaran

Ba matan aure na cikingida ka]ai ne suka taunagar]in shirya fim a matsayinfurodusa ba. Kwanan nanwata ]aliba ta bugi }irji tafito da wani sabon fim wandake cin kasuwarsa har yanzu.Fim ]in, wanda Zainab WadaYakasai ta yi mai sunaTangaran, shi ne fim ]in tana farko. Zainab dai ]alibace a makarantar share fagenshiga jami�a (�College of Artsand Science,� CAS) ta Kano.

Lokacin da wakilinmu ketattaunawa da ita ta wayartarho, ]alibar ta nuna cewaba wani abu ne ya sa ta farashirya fim ba sai don kawaitana so ta isar da wani sa}one ga jama�a. Ta ce wanisa}on ko ka fa]e shi da bakiba zai yi amfani ba, sai ka

aika da shi ta cikin fim.Furodusar ta nuna cewa

mugayen ]abi�u kamarmugunta da wula}anci ayanzu ko an yi nasiha da bakiba ]auka jama�a ke yi ba. Acewarta, �Yanzu kuwa harmugum kishin da matan aureke yi ya fara raguwa, ba donkomai ba kuwa sai donfa]akarwar da ake yi a cikinfim.�

Da aka koma kan fim ]inta Tangaran, wanda ya fito a}ar}ashin kamfanin �AmgeFilm Treasury,� Kano, Zainabta ce ba ta fuskanci matsala

ba a wajen gudanar da shi.Ta }ara da cewa �yan�uwantamaza su ne suka ]aukinauyin nuna shi a sinimomikuma komai a rubuce ake yi.Sai kuma ta yi godiya ga Al-lah cewa tun kasuwa ba ta yinisa ba, har ta fara samunnasara. �Ga shi kuma ana taaiko min da yabo cewa donAllah in fiddo na 2 da wuri.�

Da aka tambaye ta kofurodusoshi mata suna cikinmatsaloli? sai ta ce, �Ai niyanzu a wannan harkamakauniya ce, sai na }arakwana biyu ne idanuna za su

bu]e.�Ban da Tangaran, Zainab

tana nan tana }o}arin farashirya wa]ansu finafinanwa]anda suka ha]a daCefane da kuma Kisisina. Saidai duk da wannan yun}urida ta yi, wani abin da ke bata tsoro a harkar shi necunkoson finafinai a kasuwa.Wannan ne ya sa ta yi ro}oga }ungiyar furodusoshi data tashi tsaye ta ragecunkoson finafinai ta hanyarkafa }a�idar yawan finafinanda za su ri}a fitowa a makoko a wata.

MARYAM MOH’D DANFULANIBabbar Furodusar shirin Ajali

Maryam Mohammed Danfulani... maza, ku rike amana!

Finafinai biyu MaryamMohammed [anfulani tashirya ya zuwa yanzu:Bayan Wuya..., da na kwana-kwanan nan, wato Ajali. Donhaka ba mamaki ba ne jinwannan sananniyar �yar wasatana bugun }irji tana cewa,�A gaskiya yanzu in dai bawani accident (hatsari) akasamu ba, da wuya wani yacuce ni a harkar a yanzu.� Ta}ara da cewa, �Yanzu yaddana san harkar, musamman dayake na samu shugaba, inaganin komai yana zuwa dasau}i.�

�Shugaban� da Maryamtake nufi shi ne furodusantaSalisu Mu�azu, wandafitaccen ]an wasa ne wandata ri}e kamkam, yana yi matajagora a harkar.

A cewar babbar furodusar,matsala guda ]aya ce waddaidan mace tana sabon shigaharkar fim za ta iya fuskanta.Ita ce: �Ka ]ora wani ya yimaka fim ]in, kai ba damaka je ka ga me ke faruwa. Tokafin ya yi maka (abin da kasa shi) sai ka ga har rai ya~aci.�

Ta ba da misalanabubuwan da ake yi, su netattaro �yan wasa kafin a yiwasa, tsara fim (editing) zuwa

wurin tace fim a Abuja, bugakwali da fosta, da sauransu.�Za ki sa namiji duk ya yi

maki wa]annan. Idan kikabiya shi, zai ga kamar kyautayake yi maki aikin,� inji

Mashahama, wadda ita ceshugabar kamfanin�Mashahamatic Production�da ke Kano.

Da muka nuna mata cewaai mace mara aure irintya tanaiya yin duk wa]annanabubuwan, sai ta ce, �E, toamma ka san ko ba ta da auredole fa sai ta san abin. Idanba ta san shi ba dole ta saminamijni ya shiga mata gaba.To idan aka samu matsala saika ga tana samun matsala itama. Amma in mutum ya yifim ]aya ko biyu, na gaba yasan yadda zai yi.�

Haka ne. To yaya Maryamtake ganin cutar da wasumazan suke yi wa matafurodusoshi? �Duk mutuminda zai harka ta kasuwanci,�inji Maryam, �idan aka cefarkonshi ne, sai ya fuskanciirin wa]annan abubuwan.Don haka dole a }warimutum ta wani ~angaren.�

Furodusar ta yi kira gamaza masu kar~ae aikinshirya fim daga gun matamasu son a juya musu ku]i aharkar da su ji tsoron Allah.Ta ce, �Ina kira ga irinwannan namijin, ba sai ankira masa an ce amana ba. Yasan amanar ce. Ya yi yaddaya kamata kamar yadda zaiyi wa kansa, ba ha�inci.Saboda amana guda ]aya ce.Idanm ba haka ba Ubangijisai ya saka mata.�

To, Maryam, Allah ya sasun ji ro}on naki.

36

Page 33: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

ZAINAB IBRAHIM KANYABabbar furodusar shirin Uwa

Zainab Ibrahim Kanya ... daraktana da furodusana sunba ni matsala

An fi sanin Zainab IbrahimKanya a matsayin �yar wasa, indata yi tashe da sunan Kyauta. Toamma ta fara riki]a, domin kuwata zama furodusa. Sunan sabonkamfaninta �Kanya Communica-tion Network.� Fim ]in ta nafarko, wanda zai fito kwanannan, sunansa Uwa. Shin ta hangoromo ne a matsayin furodusawanda ya fi na ]an wasa?

Fim: Ga shi kin fara shirya fimnaki na kanki. A matsayinki nababbar furodusa, wa]anne irinmatsaloli kika fuskanta a lokacinshirya fim ]inki na farko maisuna Uwa?

Zainab: (dariya) Matsalolin dana fuskanta, da �yan wasa na fisamu, domin bayan mun gamashiryawa za mu je aiki sai ka gana nemi mutum an rasa. Ba waiina nufin dukkansu ba ne. Ammain ban da wannan, a gaskiyarikodin ]in ya tafi yadda yakamata.

Fim: Wacce gudunmuwa wasu�yan wasan suka ba ki a wajenganin an samu nasarar aikin?

Zainab: Na samu gudunmuwaa wurin wasu �yan wasan. Dayawa daga cikinsu ba don ku]ine suka yi min aikin ba. Sabodani ma �yar wasa ce �yar�uwarsuba su caje ni kamar yadda za sucaji manyan furodusoshi ba.

Babu abin da zan ce masu sai daigodiya.

Fim: Me ya sa kika yi sha�awaryin fim naki na kanki bayan kumake �yar wasa ce?

Zainab: Na ga ya kamata nima in ba da gudunmuwata ne ta

kowanne ~angare na harkardomin bun}asa sana�ar, ba waikawai in tsaya a �yar wasa ba,don rage koma-bayan da mukansamu a harkar shirya finafinai.Ba wani dalili ba ne wanda yawuce }arancin masu ]aukarnauyin harkar. Sannan amatsayina na �yar wasa nafahimci masu ]aukar nauyin sunaamfani da mu ne suna tara ku]i.Kuma ka san yanzu mafiyawancin mazaje ba sa son aurenmace da za ta zauna haka sunaciyar da ita; daidai da ciwon kaisai ya saya mata magani. Wanimutum ]aya ne ya fara ba nishawarar in yi wani abu nawa nakaina.

Fim: Wanne mutum newannan?

Zainab: Wannan kuma sirri ne,ba zan fa]a ba. Shi ma mutumindon kar ya tuna ne in ya karantawannan hirar ya ce, �ShegiyaZainab, ni na ba ta shawararashe!�

Fim: Menene ya ja ra�ayinki akan labarin da kika shirya fim]in ki da shi? Na san dai ba shika]ai kika samu ba, amma kuma

shi kika za~a.Zainab: [an jarida, kada dai

ka tambaye ni ta yaya aka yi akahaife ni! (dariya) Na ga yawancinfurodusoshi suna yin finafinai neda suka shafi soyayya. To nikuma sai na ga ya dace in ]aukiwani sabon abu� shi fim ]inaUwa labari ne da ya shafisoyayya tsakanin uwa da ]anta,ba wai soyayya ba da za ta kai gaaure.

Fim: Akwai wasu matsaloli dakuka fuskanta da ma�aikatanfim]in naki?

Zainab: Akwai babba kuwa!(ta yi kashingi]e a kan kujerata]ora }afa ]aya kan ]aya) Babbakuwa! Gaskiya na ]aya na samumatsala da furodusana. Mun rigamun fara fim ]in da shi sabodawasu matsaloli da suka shafe shisai ya }i bari a }arasa da shi.Daraktan nawa kuma ya zo ya yitafiya ya }i dawowa. Saiwa]ansu mutane ne suka taimakamin har na }arasa. A lokacin daya tafi, na aika na aika bai zo ba.Haka dai. Ni ba furodusa ba ce,ni ba darakta ba ce, wasu ne daisuka taimaka min aka }arasa.Sannan da na jira shi domin muyi editing ban gan shi bafurodusan ma ya }i zuwa. To kasan shi editing sai da darekta kofurodusa. Haka dai na shiga nayi editing ]ina ni ka]ai saieditana.

Fim: Su waye suka taimakamaki a kan fim ]in har ya kai ganasara?

Zainab: Akwai MuhammedSani Abdullahi, Shu�aibu YawaleYakasai, sai kuma SaniMuhammed Sani wanda shi nedaraktan ]aukar hoto. Babu abinda zan ce sai dai Allah Ya biyamasu bu}atansu, amin.

Fim: A yanzu da kika gamaediting wa]anne matsaloli kikefuskanta kafin ya shiga kasuwa?

Zainab: A gaskiya ba nafuskantar wata matsala dagagamawata zuwa yanzu; censor-ship na Abuja na riga na yi, naKano ma na riga na yi. InshaAllahu zuwa wata mai zuwa zaishiga kasuwa (wato watanMayu).

Fim: Wa]anne finafinai newa]anda kike ciki za su fito nangaba?

Zainab: Akwai TarkonMugunta, Tagwaye da Girgizar{asa.

Darakta Magaji Mijinyawa yana yi wa Sa’adatu Umar Faruk,Auwalu Dangata da Rabi Mustapha bayani a lokacin daukarwakar “Uwa”

37

Page 34: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

KOLI TRADING COMPANYNo. U.8, Katsina Road by Roundabout, Kaduna

Mu, KOLI TRADING COMPANY, dillalai ne nakowane irin finafinai � na Hausa da na

Kudancin Nijeriya, na }asashen waje dana wasanni kamar }wallon }afa, kokawa

(wato wrestling) � da kuma sababbinkaset-kaset na bidiyo da rediyo, har ma da

na CD.Muna maraba da masu sari da kuma masu

sayen ]ai ]ai.

SAI KUN ZO!A tuntu~e mu aBabban ofishinmu da ke:Lamba U8, Katsina Roadby Roundabout, Kaduna

ko a Reshenmu da ke:Lamba U4, KatsinaRoad, Kaduna

ko kuma ta wayar tarho: 062-241170 ko 062-240228

Sayen nagari, maida ku]i gida!

BIZ CENTREA DIVISION OFSARAUNIYA

PRODUCTION

In dai aiki mai nagarta da }warewa a kan farashimai rahusa kuke bu}ata, to ku zo KBC.Ayyukanmu sun ha]a da:

* Photocopy* Lamination* Computer Graphics

KK B C

C

Head Office:

Opposite Dala Orthopaedic Hospital,Gwammaja, Kano - Nigeria

Tel.: 064 - 640196

38

L A B A R A I

Daga WAKILINMU,a Kano

KO shakka babu, watan Yunina wannan shekara ya zame

wa �yan wasan fim watan ba}inciki. Tun ba a gama jimaminha]arin da wasu �yan wasa sukayi ba wanda ya jawo sanadiyyarmutuwar wasu, sai ga shi kwanatakwas kacal bayan ha]arin wasu�yan fim kuma sun ha]u dawa}i�ar �yan fashi.

Da asubahin wayewar safiyarLahadin ranar 23 ga Yuni, 2001,wasu �yan fashi suka auka gidanda �yan fim ]in suke kwancesuna barci bayan sun raba daresuna ]aukar wani fim.

An dai je ne wata unguwa dake Kano mai suna Janbulo waddake can titin sabuwar Jami�arBayero (hanyar zuwa Gwarzo)inda aka ke~e wani gida ana]aukar wani fim na furodusa

}ara da cewa, �Daga cikinwa]anda zan iya ri}ewa akwaiTahir Fagge, A�isha [ankano(Sima), Hauwa Ali Dodo (Biba),Usaina Gombe (Tsigai), Ibrahim�Big Joe� da [anladi wanda shine jami�in sarrafa na�urar ]aukarfim ne.�

Ba su kenan ba. Bincike yagano cewa abin ya rutsa da shikansa furodusan fim ]in, AlhajiSani Abdurrashid, da kuma mai]aukar hoton bidiyo na shirin,Yahaya Skito, wanda ya zo dagaKaduna.

An ce ~arayin wa]andayawansu ya kai su goma, sunhaura katangar gidan, inda ba suyi wata-wata ba sai suka tashimafi yawan �yan fim ]in dagabarci. Sun kar~e ku]i har N9,000daga hannun Tahir Fagge, saikuma Sani Abdurrashid wandasuka }wace wa N26,000.

�Sauran �yan wasa kuma,

�Yan fashi sun kai wa �yan fim �ziyarar ba-zata�... sun raba Tahir da N9,000

Tahir Mohammed Fagge Sani Abdurrashid

Sani Abdurrashid (wanda ya yiTsumagiya da kuma Alaqa).

Wani wanda aka yi abin yanawurin ya labarta wa wakilinmucewa wajen �kimanin }arfe 4 da

�yan mintina na asuba ne �yanfashin suka dirar mana munabarci.�

Mai ba mu labarin ya ga�balbalin bala�i ido da ido.� Ya

Page 35: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 39

L A B A R A Imusamman Sima, an kar~e matasar}ar gwal, an kuma }waci �yanku]a]e daga sauran wasu �yanwasa.�

Haka kuma �yan fashin sun yibarazanar harbin furodusan fim]in, inda suka umarce shi da yabude firjinsa su auno shi. Shikuwa Tahir Fagge an li}a masa}ofar bakin bindiga a kansa yayinda ake masa �yan tambayoyi.

Dukkan �yan wasan, dai bawanda cikinsa bai ]uri ruwa ba,musamman da suka ga wani ]anfashi ya gaura wa ]aya dagacikinsu }afa a ka.

Sai dai wani abu da ya ]aurewa kowa kai shi ne yadda �yanfashin suka tambayi ]an wasannan Ibrahim Y. Ibrahim(watoDumbadus ]in cikin Badali).

Majiyarmu ta bayyana cewagidaje hu]u aka yi wa fashi awannan asubahi. Amma kumaabin da jama�a da dama kemamaki shi ne, me ya sa �yan

fim ]in, musamman Tahir dafurodusa Sani, suke ]auke dama}udan ku]a]e a garinsu bawani gari can suka tafi ba?

Lokacin da wakilinmu yatuntu~i Tahir Fagge, jarumin ya

tabbatar masa da aukuwaral�amarin. Ya kuma yi ro}o ga]aukacin furodusoshi da su}aunaci Allah su ri}a ]aukarshirin finafinai a cikin otal, indaakwai tanajin tsaro sosai.

Daga ASHAFA MURANIBARIKYA

BABBAN DaraktanHukumar Tace Finafinai ta

Nijeriya (Nigerian Film andVideo Censors Board, NFVCB),Mista Ademola James, ya yiritaya daga aiki. Daraktan, wandayana ]aya daga cikin wa]andasuka assasa hukumar, ya bar aikine don }ashin kansa bayan yabauta wa hukumar a matsayinbabban darakta har tsawonshekara bakwai.

Cikin wata takarda waddajami�in hul]a da jama�a nahukumar, Mista Ferdinand Abua,ya sanya wa hannu, an bayyanaMista James da cewa shi neginshi}in ci gaban finafinai daake shiryawa a }asar nan (homevideos). Takardar ta }ara dacewa ya zuwa tsakiyar wannanshekara, finafinan da akeshiryawa a }asar nan sun samiku]a]e wa]anda aka }iyastasun kai kusan naira biliyanbakwai. �An kuma sami wannangagarumar nasara ne ta hanyar}wazo da sadaukar da kandukkan ma�aikata hukumar.�

�A shekaru bakwai da suka

shu]e, an shirya a}alla finafinanbidiyo har 3,000 a }asar nankuma duk an yi musu rijista daita hukumar tace finafinai,� injisanarwar. Ta }ara da cewayawancin wa]annan finafinaikuwa sun sami shiga kasuwannin}asashen Turai da Amerika da

Afrika.Baya ga ha~aka harkar finafian

bidiyo, Mista Ademola James yakafa tsari na bayar da ku]a]enfansho ga ma�aikatan hukumarta tace finafinai. Ya kuma ha]abiyu daga cikin ofisoshi uku nashirya fim a hukumar dana�urorin komfuta. Har ila yau, a}ar}ashinsa hukumar ta farashirya kundin tattara bayananfinafinai 2,500 da aka shirya a}asar nan (wato directory).

{asidar ta ci gaba da bayyanacewa ba za a ta~a mantawa dagudunmuwar da daraktan yabayar ba. Yana daga cikinmarubutan shirin fim na farko(scriptwriters) da akan nuna agidan talbijin na }asa (NTA) maisuna �Village Headmaster.� Yafara aikin gwamnati, ya ri}emu}amin babban daraktanhukumar har tsawon shekaruhu]u, sai kuma a cikin 1998gwamnatin AbdulsalamiAbubakar ta }ara sabunta masawasu shekaru uku.

Sai dai duk da wannan ritayada ya yi, Mista James zai zaunacikin kwamitin amintattunhukumar. Tun da farko a wurinbikin yi masa bankwana sai da

Daraktan hukumar tace finafinai ya yi ritayi... Roseline Odeh ta maye gurbinsa

Ministan Ya]a Labarai da Wayarda Kan �Yan {asa, FurofesaJerry Gana, ya bayyana shi amatsayin �jami�in ya]a labaraimai tarin hangen nesa kanal�amurran da suka shafirayuwa.�

Wani labari kuma da MujallarFim ta samu na baya-bayan nanshi ne kama aikin sabuwarbabbar daraktan hukumar. Waddaaka na]a ]in, mai suna Mrs.Roseline Odeh, ta kama aiki ne aranar Litinin, 12 ga Yuni, 2001.

Mujallar ta tattauna ta wayartarho da daraktan shiyyar Abujana hukumar, Mista E. Njoku,wanda ya tabbatar da wannanbatu. Ya kuma yi amfani dawannan dama ya yaba da namijin}o}arin da tsohon babbandaraktan ya yi na ciyar dahukumar tace finafinan gaba. Yace, �Yana daga cikin aikin MistaAdemola James na kafaofisoshin shiryar hukumar agaruruwan Legas da Anacha.�

Mista Njoku ya kuma shaalwashin ba da cikakken goyonbayansa ga sabuwar daraktar donganin an sami biyan bu}ataraiwatar da ayyukan da aka sa agaba.

sauran }asashen duniya. Wannanya jaddada cewa Nijeriya cejagaba wajen shirya finafinai a

Mista Ademola James

Sa�annan ya jawo hankalinsu dasu daina kwasar �yan wasabataliya guda ana tafiya �location�da su. To, ko me ya faru dai yawuce, sai a yi addu�ar kada Allahya maimaita.

A WATA sabuwa kuma, wasu�yan fashi ]auke da gora (ba

bindiga ko wu}a) sun kai hari gafitattun �yan wasan nan biyu, AliNuhu da Aminu A. Shariff(Momo). Harin ya auku ne adaren ranar Litinin, 26 ga Yuni,2001 a wani otal da ke garin Joscikin Jihar Filato.

Momo da Ali suna tare daSama�ilan Isyaku Koli, sabonfurodusa wanda ya je tace fim]insa Juriya, da MudassirHaladu (�Young Producer�),mataimakin babban furodusanfim ]in Badali. Momo daMudassir sun tabbatar wamujallar Fim da wannan labarin.

Ali da Sama�ila sun je Jos nedomin tace finafinansu (editing)a kamfanin �Lenscope Media,� Alizai tace {uduri, shi kumaSama�ila zai tace Juriya.Mudassir ya raka Momo nemanwurin da zai ]auki wani sabonfim a nan gaba (location).

Mutum biyu suka fasa ]akinsuda daddare a wani }aramin otal,]aya ya tsare mai gadi a waje,kuma ana zargin wata}ila daicinno su aka yi. �Fataken dare�]in sun }wace ku]a]e da yawaa gun �yan fim ]in. Bugu da }ari,sun ta~a lafiyar jikin Sama�ilasaboda ihu da ya yi ta yi a lokacinda ya ji za su karya }ofa su shigo.

Shi ma Momo ya ji jiki a gun sudomin wai �ya yi musugardama,� har ma aka ]ankwantar da shi a asibiti na tsawon�yan awowi a Jos.

Momo da Mudassir sun dawoKano a jigace washegarin kaiharin, suka tarar duk labari yawatsu. Sai jaje ake ta yi musu.

Su kuma su Ali suna can Jos.Al�amarin ya }ara jefa tsoro a

zukatan �yan fim a Kano, dominkamar yadda wani ya ce, �abinya fara yin yawa, kila saboda �yanfashi suna zaton muna da ku]ine.� A yanzu �yan fim sun farayin kaffa-kaffa. Da yawa sun cesun daina kwana a otal.

...Sun kai wa su Ali Nuhu da Momo hari!

Page 36: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

L A B A R A I

�Gwamnan Zamfara bai sa a kama ni ba�… inji sakataren kudin kungiyar furodusoshi

Aliyu Abdullahi Gusau

Daga ALIYU A. GORA IIa Kaduna

SHUGABAN }ungiyar �yanwasan fim na Jihar Kano,

Shehu Hassan Kano (Tindir}i),ya bayyana cewa rikicin da ketsakanin furodusoshi da dillalankaset a Kano zai iya shafar �yanwasa. Da yake tsokaci a kanrikicin nan wanda ake yi a kanbatun }arin ku]in kwalin kasetna fim wanda furodusoshi sukesayarwa ga dillalan, Shehu ya cematu}ar hankalin furodusa ba akwance yake ba, babu yadda za ayi ya samu damar tsayawa yashirya fim, ballantana ya nemi�yan wasa, wa]anda su da bazarfurodusa suke rawa.

A hirarsa da wakilinmukwanan nan a Kaduna, Shehu yatofa albarkacin bakinsa a kanmatsayin jaruma MaryamMohammed [anfulani a fagenshirya finafinai bayan korarta da}ungiyar furodusoshin JiharKano ta yi mata a kan laifin wai

Rikici da dillalan kaset zai iya shafar ’yan wasa

Shehu Hassan Kano

40

ta sa~a wa dokar }ungiyar.Fitaccen ]an wasan ya kada bakiya ce, �Ni abin da na sani sh ne,}ungiyar furodusoshi ta JiharKano sun dakatar da MaryamMashahama a matsayinfurodusa, amma ba a hana ta shigafim a matsayin �yar wasa ba.� Ya

Daga IRO MAMMANda SANI MUHAMMED SANI

SAKATAREN Ku]i na{ungiyar Furodusoshi ta

Arewa kuma furodusan shirinBabu Maraya..., Aliyu AbdullahiGusau, ya }aryata ra]e-ra]in daake yi cewa wai gwamnatin JiharZamfara ta kama shi saboda waiya shirya fim wanda ya sa~a waShari�ar da aka }addamar a jihar.Ya ce sam, wannan magana ba tada }anshin gaskiya ko ka]an.

A cikin �yan kwanakin nan, ji-ta-ji-ta ta cika garin Gusau indaAliyu yake da kamfanin shiryafinafinai, ana cewa wai an kamafurodusan an kulle shi a kanumurnin Gwamna Ahmed Sani(Yariman Bakura). A cewarAliyu, mutane sun yi ta tururuwazuwa ofishinsa da gidansa donsu yi masa jaje, abin da ya ba shimatu}ar mamaki.

Ya ce ai maimakon magwamnatin ta yi masa haka,karrama shi ta yi a lokacin}addamar da fim ]insa na BabuMaraya... wanda aka yi kwanan

baya. A lokacin }addamarwar,gwamnan ya nuna wa �yan fimna jihar }udurinsa na agaza masu,domin har kyautar N100,000 yaba furodusan na Babu Maraya...

Bugu da }ari, ya ba furodusanagajin mota }irar safa �Hiace� a}ar}ashin shirin ba da rance nagwamnatin jihar, don ya taimakamasa.

Wata majiya tamu ta ce daraktamai ba gwamna shawara kanharkokin ya]a labarai, MalamBashir Sanda Gusau, shi newanda ya ]auki nauyin shirin naBabu Maraya...

A lokacin }addamarwar,Yarima ya ja kunnen masu sayarda kasa-kasai a duk fa]in jiharda su guji shigo da finafinai kohotuna masu nuna tsaraici. Yakuma bayar da dama a bu]egidajen sinima wa]anda aka rufea da, domin ci gaba da nunafinafinai, amma sai malamai masura�ayin ri}au suka yi bore a kana rufe.

Gwamna Ahmed Sani ya da]aneman masu shirya finafinanHausa da su bai wa Musulunci

}arfi a cikin finafinansu, su gujiabin da ya sa~a wa Shari�a sannankuma su yi }o}arin ya]aal�adunmu.

Wakilinmu ya ji cewa masugidajen sinima a jihar sun yial}awarin ba za su nuna wanifim a sinimominsu wa]anda sukasa~a wa Shari�a ba, kuma ba zasu yarda yara }anana suna shigagidajen ba. Har yanzu dai masusinimun na da]a ro}ongwamnatin ta yi wa Allah ta dubigaskiyar lamarin ta taimake su tabu]e masu wannan hanya tasuda suke cin abinci suna ciyar daiyalansu da ita.

Shi ma Mataimakin Gwamnagudunmawar N30,000 ya bayara lokacin }addamar da fim ]in;Alh. Hassan Tafidan MaradunN200,000 ya bayar. Sannanmanyan mutane masu dubusaba�in dubu hamsin Allah Ya yiyawa da su.

}ara da cewa shi a matsayinsa nashugaban �yan wasan JiharKano, babu wani laifi da Maryamta yi masu, wanda har ya kai gadakatar da ita ana cewa ba za ta yiwasa ba. Ya ce saboda haka haryanzu Maryam tana nan a

matsayin memba a }ungiyar �yanwasan kwaikwayo ta Jihar Kano.

Shehu ya ba da shawarar cewakada wasu furodusoshi su yiamfani da abin da ke tsakaninsuda Maryam su ce ba za su ]auketa ta yi masu wasa ba.

inji Shehu Kano

SHUGABAN }ungiyarfurodusohi na Jihar

Kaduna barin gado, MalamAliyu Abdullahi, ya yaba dairin namijin }o}arin damujallar Fim ke yi wajenbuga ingantattun labaraimasu ma�ana, da ketaimakawa wajen wayar wajama�a da kawunansu a kanharkar finafinai. Shugabanya yi wannan tsokacin ne awata hira da ya yi dawakilinmu kwanan nan.

Shugaban }ungiyarfurodusoshin ya ce itamujallar Fim, ba a kanlabaran nisha]atarwa kawaita tsaya ba, a�a, ta taimaka}warai wajen ya]a al�adu da

kuma harshen Hausa, wandaya jawo a halin da ake cikiyanzu }abilu da yawa sunkarkato hankalinsu wajenkallon finafinan Hausa.

Aliyu ya ba da shawararcewa idan da hali ya kamatamawallafin mujallar ya farabuga ta da Turanci sabodaakwai mutane da yawawa]anda ke sha�awar karantata, amma dole sun ha}urasaboda rashin iya Hausa.

A }arshe, Aliyu Abdullahiya jawo hankalin duk maison ci gaban al�adu da kumaharshen Hausa, ya bamujallar Fim goyon baya, yakuma kasance yana ta}amada ita.

Mujallar Fim ta wuce duk inda aketsammani, inji shugaban furodusoshi

Page 37: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

L A B A R A I

41

Auren Fati: �Ran 15 gawannan watan za a yi�SHIN an fasa auren fitacciyar

jaruma Fati Mohammed daSani Musa (Mai Iska) ne?

Wannan tambayar ce aka dingayi cikin �yan kwanakin nan, dabda za mu wurin buga mujalla tawannan watan. Masu yintambayar suna tunanin ko waniabu ya faru ga batun auren, ganincewa lokacin da masoyan biyusuka ]ebar wa kansu ya kusashigewa.

Idan an tuna, a Fim ta 17 munruwaito Sani yana cewa,�Kyakkyawan zaton da muke yishi ne zuwa Maulidi in Allah yayarda za a ]aura mana aure.� Ita

ma Fati ta shaida mana cewa, �Baa tantance ranar da za a ]auraauren ba. Amma dai insha Allahumuna nan a kan bakanmu inshaAllahu Rabbi a watan Maulidi.�

To, binciken da Fim ta yi yagano cewa ran Asabar, 15 gawannan watan ce aka tsayar don]aura auren. Za a yi bikin Gala aran jajibirin ranar.

Wata majiya }wa}}wara tatabbatar mana da cewa a yanzuan kammala komai don ]aurinauren, kuma isha Allah �ba guduba ja da baya za a ]aura shi awannan rana.�

Mun tuntu~i Sani Musa kanFati Mohammed

SHUGABAN kamfaninshirya finafinai na �A.M.D.

Film Productions� da ke Kaduna,Auwal Muhammad [angani, yace fim ]insa na farko mai sunaHassan Da Husaini ba ya da wataala}a da wani fim da aka yi aKano mai suna Hassana DaHusaina.

A lokacin da yake zantawa dawakilinmu a Kaduna kwanannan, Auwal ya ce, �Fim ]ina baya da wata dangantaka da wancan.Abin da fim ]ina yake magana akai daban da na Hassana DaHusaina.�

Ya ce labari fim ]in nasa labarine na wani al�amari da ya ta~afaruwa a zahiri, kuma wasutagwaye, Hassan Da Husaini, nagaskiya ne suka yi wasan, bamutum ]aya ne kawai aka sarrafaba. �Na shirya shi ne a kansoyayya da kuma cin amana,� injishi. �Cin amana ce tsakaninmaigida da yaranshi.�

A kan abin da ya jawora�ayinsa zuwa harkar shirya fim,Auwal ya ce tun kafin harkar fimta bun}asa a }asar nan yake dara�ayin shirya fim, amma Allahbai nufa ba, sai a wannan karon.

Kuma ya ce bai fuskanci watamatsala mai yawa ba amatsayinsa na sabon furodusa,�sai dai abin da ba a rasa ba.�

�Tun tuni nake da burin shirya fim,inji furodusan Hassan Da Hussaini

A lokacin hirarmu da shi,Auwal ya ce fim ]in an kammalashi baki ]aya, kuma ana sa ranzai fita a cikin watan Yuni.

Kamfanin �D.M.D.� dai ba subu]e ofis nasu na kansu batukuna. �Ba mu bu]e namu batukun, muna amfani ne da nawasu, a nan kasuwar AbubakarGumi, ta Kaduna,� injifurodusan, wanda ]an asalinJihar Filato ne.

abin da zai ce game da labaran daaka ri}a ya]awa kan batun auren,sai ya ce gaskiya ba zai ce komaia yanzu ba. Shi da don ta sonsane ma, da kawai sai dai mutanesu ji an ]aura auren.

Wata majiya ta gaya mana cewaSani da Fati sun damu kan yaddaake ya ya]a }arairayi game daauren nasu, wa]anda suka ha]ada cewa wai iyayen Sani sun ceba su amince da yin aure atsakanin �yan wasan biyu ba.Majiyar ta ce sai da ta kai Fati taro}i Sani don Allah su kammalakomai da sauri a yi auren sabodata huta da masu yi matatambayoyi �na ba gaira ba dalili.�

Wakilanmu sun tsinci labarincewa a yanzu kam har Sani yabuga katin gayyata, kuma yananan yana ta shige-da-fici donganin komai ya daidaita.

Ita ma Fati, mun ji an ce tarage fita saboda auren.

Auwal Moh’d Dangani

Abdu Haro zai shirya taro don’yan fim su cire Indiyanci daAmerikanci daga cikin finafinai

Alh. Abdu Haro Mashi

Daga ALIYU A. GORA II,a Kaduna

AN yi kira ga furodusoshinfinafinan Hausa da su maida

hankali wajen shirya finafinaimasu inganci tare da karemartabar al�adun Hausa.Sardaunan masu shirya finafinaia arewacin Nijeriya, Alhaji AbduHaro Mashi, ne ya yi wannankiran ya yin da yake zantawa da�yan jarida a wajen bikin bu]ekamfanin �Bazanga Films Pro-duction� kwanan baya a kan TitinDutsin-ma da ke Tudun Wada,Kaduna.

Sardaunan ya nuna matu}artakaici game da yaddafurodusoshi suka karkatar daaniyar da aka san su da ita nawayar wa jama�a da kawunansu,tarbiyyantarwa tare da ha~akadarajar al�adar Bahaushe zuwawasu al�adu na }asashen }etare,wa]anda ba su ma da nasaba danahiyar Afrika, ballantana suamfani Bahaushen da keArewacin Najeriya.

Alh. Audu Haro Mashi,wanda wakili ne a MajalisarTarayya, ya }ara da cewa amfanida Indiyanci da kuma Amerikancida ake yi a cikin finafinanmu ba

burgewa ba ne, illa ma ya }arataimakawa wajen gur~atatarbiyyar �ya�yan mu, maimakongyara halayensu, tare da koyamasu darasi domin amfaninal�ammar Hausa da kumaNijeriya baki ]aya.

Da �yan jarida suka tambayeshi ko akwai wani }o}ari da sukeyi don ganin sun kawar daIndiyanci da Amerikanci da akeyi a cikin finafinan, sai ya ce, �Toalhamdu lillahi, ka ga kamar awajen wannan taro a yau na so inisar da wannan sa}o, to ganin

Page 38: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

cewa shi shugaba (na {ungiyarFurodusoshi) bai zo ba, shi kumababban sakatare AbdullahiMaikano Usman bai zo ba, yanacan ana ta shirye-shirye, ban ]anbayyana mashi ba, ka ga ba zanso abin a ji shi kwatsam ba.

L A B A R A IAmma na san za a yi taro nashuwagabanni.

�Kuma za a yi taro na kowa dakowa zuwa }arshen wannanwatan. To a wannan lokaci ne, na]auki al}awari, kuma na yiniyyar cewa za ni bayyana ma ita

wannan }ungiya tamu cewa takira furodusoshi da ke duk fa]inarewacin }asar nan, a ha]a dadaraktoci, a ha]a da su kansu�yan wasa, ni zan ]auki nauyinsu,ko da ya kai nira miliyan ]aya nezan iya kashewa domin a

gudanar da taron }ara wa junailimi; to iyaka su ne zan bayyanamawa, su suka san yadda za sushirya, a shawo kan matsalar daake fuskanta game da Indiyancida Amerikanci da ake amfani dasu a cikin finafinan Hausa.�

Katsinawa sun yi ruwan naira a bikin}addamar da Aminan Zamani

Wakilin Gwamna, Alh. Muntari Lawal, yanagabatar da jawabin Gwamnan Jihar Katsina

WASU KU[A[E DA AKA TARA NA GUDUNMUWA1. Alhaji Dahiru Barau Mangal (Kaset 10) N100,000.002. Gwamnatin Jihar Katsina (Kaset 5) N200,000.003. Karamar Hukumar Danja (Kaset 21) N210,000.004. Alh. Audu Haro Mashi (Kaset 3) N50,000.005. Hajiya Mariya Abdullahi (Kaset 5) N50,000.006. [anja Consultative Forum (Kaset 10) N20,000.007. Alh. Bashir Lawal [anja (Kaset 1) N10,000.008. Hakimin [anja (Kaset 1) N5,000.009. Alh. MUsa Moh�d {an}ara (Kaset 1) N5,000.0010. Fhauzy Communications, Gombe (Kaset 1) N5,000.0011. Sa�ad Uba Muh�d (Kaset 1) N4,000.0012. N.U.J Katsina Branch (Kaset 1) N2,000.0013. Ado Gidan Dabino (Kaset 1) N2,000.0014. Alh. M. M Liman (Kaset 1) N1,000.0015. Dan Galadiman Zazzau (Kaset 1) N1,000.0016. Deputy Concil Leader Charanci (Kaset 1) N500.0017. Hajiya Jummai Garanti (Kaset 1) N500.00

Daga ALIYU GORA II,a Kaduna

A RANAR Lahadi, 10 gaYuni, 2001 ne a ka y i bikin

}addamar da fim ]in AminanZamani a ]akin taro na gidanSardauna da ke Kaduna (ArewaHouse), fim ]in da kamfanin�Bazanga Communications Lim-ited� ya shirya a }ar}ashinjagorancin Alh. Ashiru SaniBazanga (Sawun Keke).

Bikin ya yi farin jinimusamman domin ]akin taronya cika ma}il da jama�a, kumamanyan ba}in duk da akagayyata kusan babu wanda baihalarci taron ba; wa]anda kumaba su samu damar zuwa ba sunaiko da wakilansu. Ka]an dagacikin manyan ba}in ha]a da:

* Mai Girma Sardaunan Masushirya finafinan Hausa, Alh.Abdu Haro Mashi;

* Gwamnan Jihar Katsina,Alh. Umar Musa �Yar�Aduwa,ya samu wakilcin babban mai bashi shawara a kan harkokinsiyasa, Alh. Muntari Lawal;

*. Mai girma Sarkin KudunKatsina kuma hakimin [anja,Alh. M.T. Bature;

* Babban mai }addamarwaAlh. [ahiru Barau Mangal wandaya samu wakilcin daraktan ya]alabarai na Jihar Katsina, Alh.Aliyu Garba Gangara;

* Shugabar {aramar Hukumar[anja, Alh. Sani Dabai;

*. Sannan kuma sai [anGaladiman Zazzau, HakiminRigasa, Alh. Ummar Idris, wandaya samu wakilcin ]ansa, Alh.Muhammed Umar Idris.

Haka kuma daraktoci dafurodusoshi ha]e da wasu dagacikin shahararrun �yan wasa sunsamu halartar taron.

Da yake gabatar da jawabinmaraba a matsayinsa na maimasaukin ba}i, Alh. Sani Dabaiya bayyana matu}ar farin cikimatu}a dangane da irin namijin

shirya finafinai.Shi kuma Abdu Haro Mashi,

kira ya yi ga furodusoshi,daraktoci, �yan kasuwa da kuma�yan wasa da su yi }o}arin ganincewa suna kyautatawa wajenshirya finafinan da za su ]agamartabar al�adun Hausa. Ya }arada cewa a tabbatar da karemutuncin addinin Musulunci acikin finafinai.

Sardaunan ya }ara nuni dacewa wa]annan finafinan da akerainawa suna iya gur~ata halayen�ya�yanmu kuma suna iya gyaragur~atattun halayensu. sabodahaka ya yi kira da cewa a yi taka-tsantsan don a ri}a tace labarikafin a maida shi fim. A }arsheya yi kira ga �yan kasuwa,furodusoshi da kuma �yan wasada su tabbatar da cikakken ha]inkai a tsakaninsu matu}ar ana sona ci gajiyar sana�ar shirya finafinaimasu inganci.

A cikin jawabin babban mai}addamarwa, Alh. [ahiru BarauMangal, wanda babban ]ankasuwa ne a Katsina, cewa ya yishi kam alhamdu lillahi kumayana }ara addu�a cewa Allah ya}ara ]aukaka wannan sana�a tashirya finafinan Hausa.

Ha}i}a dukkan manyan ba}inda suka halarci wannan taron sunyaba ainun, musamman ma ganincewa ]ansu ne Bakatsine ya tarasu a wannan rana. Ita kuma HajiyaMariya Abdullahi, wadda ta ta~azama shugabar {aramarHukumar Bakori a zamaningwamnatin Babangida, a cikinnata jawabin ro}o ta yi gakamfanin �Bazanga Films Pro-ductions� da su shirya fim a kanrayuwarta.

Shi ma Gwamna Umaru�Yar�aduwa, a nasa sa}on, cewaya yi akwai bu}atar furodusoshisu yi tunani su dainakwaikwayon finafinan Indiya. Yace kamata ya yi su yi }o}arinya]a kyawawan al�adunmumaimakon ya]a na wasuwa]anda ba su da wani amfaniilla su taimaka wajen gur~atatarbiyyar �ya�yanmu.

} o } a r i nda AshiruS a n iBazanga,w a n d akamsila nea }aramarhukumarsa,ya yidanganeda shiryaw a n n a n}asaitaccenfim.

Ya ceb a b us h a k k aA s h i r uS a n iBazangaya zamaa b i nta}ama gad u k k a n] a n}aramarhukumar,musammans a b o d ayun}urinda ya yi naganin yafito damartabartaa fagen

42

Page 39: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

L A B A R A I

SAKAMAKON hirar dasakataren ya]a labarai na

}ungiyar furodusoshin jiharKaduna ya yi, aka buga a Fim tawatan jiya, furodusan fim ]inWasila, Yakubu Lere, ya }ararsakataren, Adamu MohammedBello (Ability) a gaban }uliya.

Idan an tuna, Ability ya zargiLere da laifin cin ku]in }ungiyar,a madadin martaninsa ga wanii}irari da shi Lere ya yi a Fim tawatan Mayu. Hirarmu da Abil-ity, wadda aka buga a shafi na 42a cikin mujallar, ta haya}a Lere,har ya shigar da }ara a kotunmajistare da ke Daura Road,Kaduna, a ranar Laraba, 6 gaYuni, 2001. Kotun ta aika waAbility da sammace, inda akegayyatar shi da ya bayyana agaban kotun a ranar Jumma�a, 8ga Yuni, 2001.

Da aka shiga kotu a ranar,Ability ya je tare da lauyoyi biyuda wasu furodusoshi guda biyar.A lokacin Lere bai zo da lauyaba, to amma ganin halin da akeciki sai shi ma ya gayyacilauyansa ta hanyar tarho selula.

{arar da ya shigar ana kiranta�criminal defamation,� wato ~atasuna ta hanyar laifi mai }arfi. Donhaka kotu ta bu}aci Ability yakare kansa a kan zargin da mai}ara yake yi masa. Sai ya kasakawo takamammiyar hujjar cewa}ungiyar furodusoshi ta ba Lereku]i ya cinye bai yi aikin da ta sashi ba. Amma ya ce Lere ne yafara zargin shugabannin}ungiyar da cewa sun ci ku]i.

An ]age sauraron }arar zuwaran Litinin, 2 ga Yuli, 2001,bayan da kotu ta ba da belinwanda ake }ara a kan N50,000.To amma har zuwa lokacin dakotu ta tashi wa]anda za su kar~ibelin nasa ba su dawo daga indasuka nufa ba. Wannan ya sa �yansandan kotu suka tafi da Abilityzuwa gidan yari don ajiyarsazuwa ranar Litinin, da yake ba aaiki a ranakun Asabar da Lahadi.

Haka Ability ya zauna a jarunhar Litinin, kafin ya }waci kansa

daga hannun hukuma.Al�amarin ya jawo ka-ce-na-

ce a tsakanin �yan fim na JiharKaduna. Shugaban }ungiyarfurodusoshin jihar, AliyuAbdullahi, tare da wasufurodusoshi, sun yi iyakar

}o}arinsu wajen ba Lere ha}uridon ya janye tuhumar da yake yiwa abokin aikinsu. Shi kuma yace ba nufinsa ba ne ya tozartaAbility, illa dai a gane gaskiyarlamarin, kada mutane su ri}akallonsa a matsayin maciyinamana.

A wata zantawa da Lere ya yida wakilinmu a kan maganar, yace ya amince da ha}urin da akaba shi, to amma sai an cika wasusharu]]a da ya bayar, wa]andasuka ha]a da buga bayanin ba daha}uri daga Ability a cikinmujallar Fim, da biyansa ku]inda ya kashe wajen ]aukar lauya.

Sardaunan FurodusoshinArewa, Alh. Abdu Haro Mashi,ya kira wani taro na shugabanninshirin fim a Jihar Kaduna, don asasanta al�amarin, a kuma samomaganin rikice-rikicen da ketsakanin �yan fim a jihar.

Ranar Alhamis, 21 ga Yuni,aka yi taron. Taron, wanda akagudanar a ofishin Ashiru SaniBazanga (�Bazanga Communica-

Wasa ya ~aci: an kulle furodusa,* {ungiya ta wanke Yakubu Lere, shikuma ya yi tawaye, ya kafa }ungiya

tion� ) ya sami halartar AliyuAbdullahi, sakatare AbdullahiMaikano Usman, AbdurrasheedMohammed Kankia, GarbaShehu da kuma Abubakar Ishaq.Sauran su ne Lere, Ability, dakuma [an� azumi Usman (Dafe-dafe).

An dai yi amfani da wannandama inda aka ]inke ~arakar dake tsakanin Lere da Ability. Ansami rashin fahimtar junatsakanin }ungiya da Abilitylokacin da kowa ya nemi ]orawa shi Ability laifin kato~arar dasuka ce ya yi na hirar da Fim.Bayan an yi cacar baki mai zafisai }ungiya ta ]auki nauyin laifinda Ability ya yi.

Tun da farko dai a wajen taronsai da Ability ya tashi ya bayyanadalla-dalla hujjojin da ya dogarada su na cewa da yawun}ungiyar ne ya yi hirar da ta kaisu kotu da Lere.

Sai dai an tashi baran-barantsakanin }ungiya da Dafe-dafe,wanda ransa ya ~aci matu}alokacin da aka ayyana masa cewaakwai ku]in rijista N1,200 ahannunsa. Ya tashi ya yi ~a~atu.Da abin ya yi }amari, sai ya ficedaga ]akin yana fa]ar ba}a}enkalamai. �Shugaba akwai ku]in}ungiya N1,200 wajena, ka sameni ka kar~a, kuma daga yau na

Daga ALIYU A. GORA II

WANI ]an wasa, NasiruAula Da~~akal, ya ce

fitowar da ya yi a cikin fim ]inWasila 3 ta ba shi }warin gwiwarci gaba da taka rawa sosai a cikinfinafionan Hausa.

Nasiru, wanda ya yi tattakizuwa kamfanin mujallar Fim aKaduna, ya bayyana farin cikinsatare da nuna jin da]in irin rawarda ya taka a cikin shirin Wasila 3]in.

Duk da kasancewar fim ]inshi ne fim ]insa na farko, Nasiruya ce abin ta}ama ne a gare shitun da yake shi ka]ai ne aka faragani a fim daga jiharsu taZamfara. [an wasan ya }ara dacewa duk da yake fita ]aya kawaiya yi a fim ]in, inda ya fito amatsayin malami, wanda shi neya ba Salaha laya don ta mallaki

Jamilu, ya ce wannan fita ]ayakacal da ya yi ta jawo masakwarjini da farin jini da kuma}auna daga ma�abota kallonfinafinan Hausa a Zamfara ]in.

Da wakilinmu ya tambaye shi

Fitowa a Wasila ta ba Nasiru Aula }warin gwiwaabin da ya sa masa ra�ayin shigaharkar fim, sai ]an wasan ya ceshi tun yana makaranta yake dara�ayin wasan kwaikwayo. Alokacin kuma da ya gamamakaranta, ya da]e cikin takaicinrashin samun hanyar da zai shigaharkar fim a matsayin ]an wasa.Nasiru Aula ya ce }unar bakinwake ya yi, inda ya tasomusamman daga Gusau yatunkari kamfanin �Lerawa Films,�ya kuma ci sa�a ya tarar da dashugaban kamfanin, watoYakubu Lere. [an wasan ya ce,bai tsaya ~ata wani lokaci ba, yabayyana wa Lere bu}atarsa, shikuma Leren ya share masahawaye, nan take ya sanya shicikin �yan wasan Wasila 3.Nasiru ya ce shi kam alhamdulillahi, ko banza dai shi ne ]anwasa na farko da ya fito dagaJihar Zamfara.Nasiru Aula Dabbakal

43

Ci gaba a shafi na 56

Adamu Moh’d Bello (Ability)

Page 40: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

L A B A R A I

Masoyan Fim zun kawo mana ziyara

Zumunci a kafa yake: Jagoran maziyartan, Zubairu Garabasa, shi ne na farko dagahagu a zaune. Ashafa Murnai Barkiya ne a zaune a tsakiya

A RANAR Lahadi, 10 gaYuni ne wata tawagar

mutane su 13 suka kai ziyara a}aramin ofishin mujallar Fimda ke Kano. Tawagar, waddata zo daga garin Kazaure cikinJihar Jigawa, tana }ar}ashinjagorancin Alhaji ZubairuGara~asa wanda shi ke dadan}areren kantin sayar dakayayyaki na zamani mai suna�Gara~asa Store� a Kazaure.

Da yake gabatar da jawabingoyon bayan mujallar, AlhajiZubairu ya ce dalilin da yakawo su shi ne don su nunairin jin da]in karanta mujallar.�Mujallar Fim ita ce madubinda masu kallon fim ke dubawadomin ganin �yan wasa,� injiZubairu. Ya ce ta hanar mujallarjama�a na nesa suke saninha}i}anin abin da �yan wasake ciki.

Da ya koma kan shawara gamujallar kuwa, bayan ya yabada irin aikin da wakilanta kegudanarwa, sai ZubairuGara~asa ya yi ro}o da cewa,�Don Allah ku daure ku }arayin shafi mai kala domin }aramata armashi. Gaskiya idan akayi haka, to ko naira ]ari ukuaka sayar da ita ta ci ku]in ta.�

Shi kuwa Habibu Magaji[anjuma Aci Lafiya, cewa yayi abin da ya fi ba shi sha�washi ne labaran gaskiya damujallar ke bugawa kan �yanwasa. Domin idan mun bincikasai mu ji gaskiya ne.� Ya kumabayyana cewa yana ro}omujallar ta ci gaba da tsaregaskiya kuma ta ri}a shigalunguna da }auyuka sosai.

A nasa ~angaren, BashiruAhmed, wanda shi ne manajan�Gara~asa Provision Store,�cewa ya yi suna jin da]imujallar. Ya ce Fim tana }arawayar masu da kai kan abinda ke gudana cikin harkarwasan Hausa. �Gaskiya ba donmujallar Fim ba da ji-ta- ji-ta daru]u sun game ko� ina. Ammayanzu da an fara ya]a ji-ta- ji-ta kan wani ]an wasa, sai kaji ana cewa �a jira mujallar Fimta fito, za ta raba managardama�� inji shi.

Da yake masu jawabingodiya dangane da ziyarar da

suka kai, Mataimakin Editanmujallar, Malam Ashafa MurnaiBarkiya, ya nuna farin cikinsaganin cewa jama�a sun yintakakka domin kai wa mujalarziyara. Ya yi kira da cewa �Ako da yaushe ma�aikatanmujallar Fim a shirye suke dayin maraba da duk wasu

shawarwari da masu karatu zasu bayar.�

�Yan tawagar sun ha]a daAlhaji Zubairu Gara~asa,Lawan [anjuma A Ci-Lafiya,Habibu Magaji A Ci Lafiya,Sani Safiyanu S/Jawo A CiLafiya, Salisu Umar A CiLafiya, da Bashiru Ahmed A

Ci Lafiya. Akwai SardauWaima Kazaure, IsyakuIbrahim Gara~asa, IdrisBalarabe Gara~asa, Masa�uduSalisu S/Jawo, Yahaya[ayyabu, Iliyasu Rabo da IdrisIbrahim Gara~asa. Sun zo ne acikin mota }irar Model F mailamba �Gara~asa-1�.

An kafa }ungiyar makaranta mujallar Fim a Wudil

WATA }ungiya ta masukaranta mujallar Fim mai

suna �Fim Magazine ReadersAssociation� da ke Wudil, JiharKano, ta taya mujallar murnarcika shekara biyu da kafuwarta.

A cikin wata wasi}a dasuka aiko wa kamfanin waddaaka rubuta ranar 9 ga Yuni

mai ]auke da sa hannunshugaban }ungiyar, takardar tabayyana cewa dukkan �yan}ungiyar su 48 sun da]e dakafa }ungiyar a garin na Wudil.

A ta bakin shugaban nasu,Aminu Muktar Wudil, wandaaka fi sani da �Manaja,�}ungiyar tana da membobi

maza da kuma mata. Sai dai yayi }arin haske da cewa}ungiyar tana }ar}ashin wata}ungiya mai suna �FriendshipGroup of 95,� Wudil.

{ungiyar ta yi amfani dawannan dama inda ta yi kira gama�aikatan wannan mujallar dasu }ara zage damtse domin

ganin ta }arasamun kar~uwa.

S h u g a b a n}ungiyar ya mi}asa}on gaisuwa gailahirin wani maiba da gudunmuwawajen ha~akamujallar Fim dadukkan masushirya finafinai.

Aminu Muktarya }arasabayanansa dakalmomi kamarhaka: �Allah yaja zamaninmujallar Fim,amin!�Aminu Mukhtar Manaja (a tsakiya daga kasa) da sauran membobi

44

Page 41: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

T AT T A U N A WA

In har anason a kawogyara sai

an cire sonzuciya

– BankauraDaga KALLAMU SHU’AIBU

WAYE bai san BANKAURA ba? A gaskiya, saidai wanda ba ya kallon finafinan Hausa. Sunan daBankaura ya yi ya sa wasu ma ba su san cewa UmarYahaya Malumfashi ne sunansa na ainihi ba. Ya fitoa wasannin kwaikwayo sun fi a }irga, tun daga natalbijin har zuwa na bidiyo.

Shi dai Bankaura, an haife shi ne a garinMalumfashi cikin Jihar Katsina. A nan Malumfashiya yi karatun firamare da na sakandare. Halinrayuwa, tafiya ta yi tafiya har Allah ya kawo shiKano inda a halin yanzu nan yake zaune ake tadamawa da shi a kan harkokin shirye-shiryenfinafinan Hausa.

A lokacin da muka zanta da Bankaura, mun nunamasa cewa mun san ba haka kawai ya tsinci kansaa garin Kano ba, kila sana�a ko aiki ya kawo shi.Mun nuna masa cewa mutane za su so su san shinbaya ga wasan kwaikwayo yana da wata sana�a?Da wannan tambaya hirarmu da Umar YahayaMalumfashi ta ci gaba, kamar haka:

Bankaura: E, ina da sana�a. Akwai mutane na arziki da

muke harka ta kasuwanci dasu. Kuma da can asali a cikingarin Kaduna nake zaunesaboda akwai �yan�uwanasha}i}ai a can. Allah Ya yimasu zama a can ina tare dasu, don Allah ya yi wamahaifina rasuwa ranar 14/1/74. To zaman da na yiKaduna ina wasankwaikwayo a wata }ungiyada ake kira �Zumunta Za~iSonka Social Club� aUnguwar Shanu a gidanajiye kayan tarihi (�NationalMuseum�). A nan wanifurodusa ana ce masaMohammed Umar Hassan yagan ni a 1982 ya ba nitakardar gayyata tamusamman zuwa gidantalbijin na }asa (NTA)Kaduna inda na fara shirinTambari tare da su {asimuYero a 1982. A wannanlokacin Joe Ajiboye shi nefurodusan wannan shirin,kuma a dai shekarar 1982 ]inne Samanja ya fara sa ni acikin shirinsa ina fitowa amatsayin Sauran Mazan Jiya.

A 1985 aka ba ni wani shirinawa na kaina ina fitowaShegen Sama. Ina nan inawannan shirin, Garba Ilu([ankurma) na nan (Kano) yaaika mani Kaduna cewa inzo akwai wani shiri wandaza su fara tare da ni mai sunaNadakama. Da na zo ya cega yadda ake so a shiryashirin; wasa ne dai na bandariya. Ya ce shi yana nan aNadakama, sai ya tambaye niwanne suna na ga ya dace?Na ce mashi, �Bankaura.� Ayayin da muke wannan wasa,hukumar gidan talbijin naJihar Kano suna }aunata}warai da gaske; sai sukanuna mani cewa to in zomana in zauna tunda ga shiina ta abubuwa da su. Shi nesai na zauna na fara sana�arsayar da kaset-kaset haka. Kaji yadda Allah Ya kawo niKano kuma har yanzu nakecikinta.

Fim: Shi wasa na kaset ]inbidiyo, yaushe ka fara shikuma za ka iya tunawa da fim]in da ka fara? Kuma za ka

Umar Yahaya Malumfashi

47

Page 42: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Umar Yahaya Malumfashi (a matsayin Alh. Bashir) tare da dattijo Alh. Daudu Galadanchi(a matsayin mahaifin Alh. Bashir) cikin shirin Sai A Lahira

iya }idaya iya finafinan da ka fito cikinsu?Bankaura: To idan na fahimce ka kana nufin na kaset na

sayarwa wanda ake ce ma home video, ko?Fim: E.Bankaura: To akwai wani fim da muka ta~a yi da Tijjani

Ibrahim a 1990 ko 1991, in na tuna ina jin sunanshi WaiwayeAdon Tafiya. Wannan ina ganin shi ne na fara da shi. Daganan su Mandawari suka yi wani wanda ya fara ]agawa, shine Gimbiya Fatima, to ba ni a cikinshi. Sai kuma suka yiHo]ijam, shi ma ba ni a cikinshi. To daga nan kwatsam, inazaune a nan Kano, sai aka kawo bayanin cewa ga wani fimda za a yi, Alhaki Kuikuyo, wanda Balaraba Ramat Yakubuta rubuta littafin, kamfanin �FILABS� suka ]auki nauyingudanar da shi. Air Vice Marshal Muktari Mohammed shi neya ]auki nauyin aiwatar da shi. Sai aka ga cewa ni ne babbanjarumin wannan fim da za a nuna. Ina ganin shi ne fim ]in daya zama tauraro a gare ni, ya ]aga ni.

Fim: Kuma wannan fim shi ne aka fi tsokaci da ka-ce-na-ce a kansa, ana cewa rawarda ka taka a ciki ta yi hannunriga da al�adunmu. Me za kace game da wannan al�amari?

Bankaura: To alhamdulillahi, ni abin da zan ce ]ayane. Ka ga kada ka jahilciAl}ur�ani, akwai inda AllahUbangiji (SWT) yake cewa,�Innal insana lirabbihi lakanudun.� To ka ga wannanAllah da kanshi yake fa]acewa, �Duk ni�ima da mukayi wa bawa ]an�adam haryanzu ba mu iya masa ba.�To ni kuma me zan yi in iyawa wani mutum? Babu! Illaiyaka dai kar ka manta niMusulmi ne, na biyu inatsoron Allah daidaigwargwadon iyakar iyawata.Kuma ba ni wasa daaddinina; duk mutumin daya yi hul]a da ni ya sanwannan. Saboda haka bamutum ba ne yake rubutawawa kansa la�adar aikinsa nazunubi ko na lada, Allah kewannan. To ni na san abin dake tsakanina da Ubangijina, sai kuma Shi. Abin da dukmutane za su ce game da ni bai dame ni ba, kuma ai daidai]in wani karkatar wani ce. Na ga rubuce-rubuce da yawa � ace ban kyauta ba. Ni dai ban yi magana ba. Kuma sai ga shiwasu na rubutowa suna wanke ni suna cewa wai me ma na yine wai? Me na yi wanda za a ce ban yi daidai ba? Ni dai nayi iyakar iyawata. In har akwai wa]ansu abubuwa wa]andasuka sa~a wa wa]ansu rai daga cikin Kuikuyo, to abin dazan ce masu shi ne kowane mutum fa ajizi ne. Kowane mutumya tsaya ya dubi kansa tukuna; kar ka yi la�akari da UmaruYahaya kawai. A�a ni na yi Alhaki Kuikuyo na yi rashinkunya na yi menene. In ko har abin bai yi maka da]i ba, tosai in ce Allah ba da ha}uri. Abin da kawai zan iya cewakenan. Amma ni babu wani abu wanda ya dame ni ko ya yimani ciwo ko kuma na yi da na sani daga duk rawar da nataka cikin Alhaki Kwikuyo.

Fim: Wa]anda suka fahimci fim sun san ka taka wannanrawa ne a matsayin mai fa]akarwa. Ba ka ganin }ila irinwasi}un da ake samu yanzu na nuna irin }o}arin da ka yi zaa iya danganta shi ga irin wayewar da mutane ke }ara samu

kan menene fim?Bankaura: To ai da ma abin haka yake. Ina ganin ai ka ga

wani fim mai suna Umar Mukhtar. To ni ka dubi wannan fim,rayuwa ce da tarbiyya ta Larabawa zalla aka nuna, sannankuma da kishin addinin Musulunci, kuma da yaddaMusulunci ya sanya kishi ga zukatan Musulmi. Amma abinban mamaki, wanda ya fito a matsayin Umar Mukhtar ]inBature ne, sunansa Anthony Quinn. Shin da wannan fim maisuna Umar Mukhtar ba za ka iya ya]a addinin Musulunciba? To shi ke nan haka al�amurra suke tafiya; ga shi ya baraddininsa ya bar al�adarsa ya zo ya yi ya}i iyakar ya}i sai ya]aukaka kalmar Allah kuma shi har yanzu bai Musuluntaba. Ya ]aukaka al�adar Labarawa duk da yake shi Bature ne,zanzaro yake yi, ya yi fitsari a tsaye. Saboda haka shi fimyanzun nan fa muke koyo. Mutane su rin}a yin ha}uri dairin yadda suke ganin muna taka rawa. Tunda abubuwanmufa in an lura suna ta gogewa suna canzawa; rawar da aka takabara cikin harkar fim in kun lura bana ba ita aka taka ba. Fim

]in da ka yi shooting cikin watan da ya shu]e yanzu in kanahalartar gurin da ake ]aukar wani shirin za ka ga ba irinwanda aka yi ba ne, wancan ake ta gyaggyarawa.

Fim: In aka yi la�akari da irin gunagunin da jama�a sukayi dangane da irin rawar da ka taka a Alhaki Kuikuyo, wata}iladon rashin fahimta mene ne ra�ayinka dangane da wannanal�amari?

Bankaura: Iyalina da �yan�uwana � ka ga ina da iyaye inada surukai da �ya�ya, ina da mata ina da }anne � dukkansubabu wani mutum ]aya wanda ya ce tir da abin da na yitunda ni mai biyayya ne ga na-gaba da ni. Inda an samudaga cikin yayyena ba ma iyaye ba, wani ya ce, �Me ya sa kayi haka a cikin Alhaki Kuikuyo? Gaskiya ba mu ji da]i ba.�Wallahi, yin fim da ma ai ni na sa kaina nake yi, ban mai dashi wai shi ne abincina na yau da gobe ba. A�a, kamar yaddaka ce, fa]akarwa nake. Alhaki Kuikuyo ku dubi littafin manaku ga sunansa. Shin wadda ta rubuta littafin nan fa mace ce.Macen nan kuma gidansu fitacce ne, hasali ma ]aya dagacikin �yan�uwanta da suka fito ciki ]aya ya ta~a ri}emu}amin shugabancin }asar nan, Allah Ya jikansa Janar

HO

TO

: R

am

at

Film

Pro

du

ctio

n

48

Page 43: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Murtala Ramat Muhammed. Kowa ya san shi. {anwarsa dasuka fito ciki ]aya ta zauna ta rubuta littafin nan; ga iyayentaba su }alubalance ta ba, kuma sun karanta littafin nan. Ga�ya�yanta ba su }alubalance ta ba, sun kuma karanta littafinnan, ga masoyanta ba su }alubalance ba, sun kuma san cewaita ta rubuta wannan littafi; har sai ga shi wani bawan Allah,Air Vice Marshal Muktari Mohammed, ya ]auki littafin nanya karanta ya ce wannan littafi a yi fim ]in shi. Aka zaunaaka tace aka ga ni ]in nan ni na fi dacewa da in je in takawannan rawa. Duk wanda yake yin fim a cikin garin Kano,wanda tauraronsa ya ]aga a wancan lokaci, ka ga a cikinza~a da aka yi cewa a zo a gwada a ga wa ya fi dacewa (yafito a matsayin) Alhaji Audu ka ga marigayi Mansir {walliya taka rawa ya fa]i; Alhaji Ado wanda ake cewa �Kuturun

Umar tare da Hajiya Amina Garba

Danja,� ya taka rawa shi ma ya fa]i; Ado Ahmed Gidan Dabinoya taka rawa shi ma ya fa]i. Duk kuma Alhaji Audun nan akenema dai a zama. Sai Umar Yahaya Malumfashi na zo nataka aka ce, �Af, ai wannan shi ya fi dacewa da ya zo ya ri}ewannan wuri na Alhaji Audu,� a cewar darakta Galadima.Saboda a auditioning ]in nan da aka yi, Tijjani Ibrahim neya kafa kyamara ya yi auditioning ]in mu. Wallahi wa]ansuna manta su; a duk wa]annan da na gaya maka na san duk anha]u a wurin nan an cika (kamfanin) �FILABS,� kowa yanarububin ya zama Alhaji Audu

Fim: To Alhaji Umaru ka ga shekaranjiya, ka ga jiya, kanakuma ganin yau, da fatan a ga gobe da kai a cikin harka fim.Shin wane bambanci za ka iya cewa an samu tsakanin irinwasanninmu na da, da na yanzu?

Bankaura: Abu ne wanda yake bayyananne, watau shizamani da kake ganinshi kamar wani shiri wanda gidanrediyon Kano suke yi ne, mai suna �Zamani Riga,� duk irinyadda rigar nan ta zo ta same ka sai ka ]auka ka sa ka shigajama�a a yi ta yi tare da kai. In na fahimce ka, ai wannan abune ma mai sau}i. Harkar fim bari in gaya maka ita, ni atashina fim na Hausa wanda ake kira da home video da Hausada na sani da ya yi kwarjini kuma har yanzu ba a yi kamarsaba. Fim ]in nan ya fito da martabar matar aure. Ya fito damartabar miji mai aure. Ya fito da martabar talaka da kebiyayya ga sarakuna. Ya fito da martabar ma�aikaci ya zuwa

]an sanda tafi soja ka dawo har mai aikin kurkuku. Ya fitoda martabar �yar shara. Ya fito da martabar ababen hawanmukamar ra}uma, jakuna, dawakai, ban ce maka mota zuwamashin ba. Ya fito da martabar jinka da ]an boto gini na}asa, danni, da sauran abubuwa. Ya fito da martabar maduguda ake kira uban tafiya wa]anda suke fatauci a da kan }afa,su tashi tun daga nan har zuwa Ghana, zuwa }asar Larabawasu ciwo kasuwarsu su dawo gidajensu. Malam wasu su yitafiyar shekara biyu wasu watanni. Wannan fim ya fito dawannan martaba. Sannan bugu da }ari ya fito da kwarjini damartaba ta almajirci wadda ake kira makarantar malamanda, gardawa da alaramma da }olo da gardi da ko ma wanene.Fim ]in nan ya nuna tarihinsu, kuma wai fim ]aya ne nakeso in gaya maka shi wanda har yanzu ba a yi kamar shi ba. To

fim ]in Shehu Umar! Ka gashirin da aka yi wa fim ]inShehu Umar abin duk da nafa]i maka to ka gaya maniguda ]aya wanda ba hakayaken ba. To yanzu gayamani wani fim tun daga 1998kama ya zuwa yanzu, yaunawa ga wata ne?

Fim: 2 ga wata.Bankaura: Wane wata?Fim Watan biyu.Bankaura: Na wace

shekara kuma?Fim: 2001.Bankaura: To tace wani

fim tun daga 1998 zuwa yauwanda ya yi kama da ShehuUmar. [aya tak gaya manishi.

Fim: Zai yi wuya.Bankaura: Babu ko? To

shikenan. Ka ga kayan ma daaka yi aikin da su ka ga bairin wa]anda ake aiki da suba ne yanzu. Masu }wari nemasu kuma kamala ne. Ka ji]aya. Ma�aikatan yanzu

kamar yadda ake da Tijjani Ibrahim a nan shi ]aya yakedarektin fim yana ta }o}ari a ha]a a tafi. A fim ]in ShehuUmar irin su Tijjani Ibrahim sun kai guda biyar ko shida.Don saboda an ba abin muhimmanci. Ina gani a}alla an yiwata biyu ana shooting wannan fim ]in. Yau idan furodusaya shirya da darektansa aka fita, an da]e ana shooting fimkwana biyar an gama an shiga wani. Ka san dalili? Fim ]inkamar tafiya yake hannu-baka-hannu-}warya, a yi ku]in daka kashe a sa wannan fim ya shiga kasuwa ku]i su dawo a cigaba da aiwatar da wani. Saboda haka akwai bambanci dayawa malam! Mutane da suke dirama a da akwai natsuwa atattare da su. Babu son kai! A ce kaza! A�a, wanda duk yacancanci wannan abu to shi zai yi. Saboda ba zan manta ba,akwai wani fim mai suna Ko Biri Ya Karye, {asimu Yeroyana karyensa, a rugurguje, yana jinya a nan asibitin }ashina Dala, suka yi fim ]in nan a nan Kano. Ya baro Kaduna. Kaga Samanja ai Kaduna yake; ]auko shi aka yi ya zo nanKano ya ha]u da Malam Mamman da marigayi Doron Mage,Alhaji Uba Garba, watau Alhaji Buguzun. Aka ]auko KaroDa Goma, aka tafi Zariya aka ]auko Hassan Wayam ya zo dakayan ki]ansa nan aka yi dabdala aka }are. To amma inyanzu ne ya kake tsammanin za a yi? Cewa za a yi dukwa]annan mutane ana da su a Kano ba sai an je an ]auko naKaduna ba. In a Kadunan ne ba sai an je an ]auko na Kanoba. Yanzu sai ka ga finafinai ka]an ne ake ]auko wa]ansu

49

Page 44: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

daga Kaduna su zo su yi. Kaga kenan ba a ba mutaneha}}insu ba. Sai ka gamutum ya kawo labarinsamai kyau amma son zuciyaya sa ya ]auko wanda baidace ba ya li}a a wurin. Kaga ai abu ba zai ti daidai ba.

Fim: Ina mafita?Bankaura: In har ana son a

kawo gyara sai an cire sonzuciya. Kama tun dagafurodusoshi, nan son zuciyayake. Saboda kai ne kake dafim ]in ka kuma kai ne za kaaiwatar da shi. To kai kakeda alhakin tsamo wa]anda kaga sun dace su yi maka fim]in. To shi ke nan ko da naba ka shawara: �E! ]aukowane ko wance,� a�a shi yakafa tunga wanen nan kowance shi ba zai canza ba.Abu ya tafi haka babushawara? In za a iya cire sonzuciya a tsaya tsaf a waremutanen da suka dace sutaka rawa a kowane irin fim,ina ganin insha Allahu za aiya samun cimma buri agyara al�murra. Kuma ka gakamar Tijjani Ibrahim, IshaqSidi Ishaq da Hafizu Belloda su Auwalu MohammedSabo, fisabilillahi rawar dasuke takawa wajen ha~aka kalmomi na Hausa da al�aduntaa gaskiya rawar ba ka]an ba ce ba. Ina kira ga kowaneartiste, don Allah mace ko namiji, su ba daraktocin da akeda su goyon baya. Su kuma daraktoci don Allah su ri}akar~ar shawara mai amfani domin su gudanar da aikinsu.

Fim: To har yanzu dai a kan irin rawar da kakan taka. Kasake taka wata rawa kwatankwancin irin wadda ka taka aAlhaki Kwikuyo a cikin fim ]in Fallasa, har wasu sukeganin shin wai wannan ra�ayinka ne ko kuwa ra�ayinfurodusoshi ne na su sa ka irin wannan rawa mai sar}a}iya?

Bankaura: Kamar ban gane Hausar ra�ayi ba. Kana nufinni nake cewa a rubuta mani irin wannan labarin ko kuwa a�anake cewa duk wanda ya rubuta irin wannan rawa da nataka cikin Alhaki Kwikuyo ya zo ya neme ni zan taka masa?

Fim: A�a. Masu lura da harkokin finafinan ne suke cewarawar da ka taka a Alhaki Kwikuyo irin ta Fallasa ce. Misali,Wasila Isma�il ita ma ta taka irin wannan rawar a cikin fim]in Wasila kuma har ila yau kuma ta zo ta sake takamakamancin ta a cikin Fallasa. Akwai irin wannan tunaninna mutane.

Bankaura: Gaskiya in wannan suke tunani ban sani ba.Ni abin da nake da shi ne mutum ya yi labarinsa a rubuce ayi screenplay, in ya ga na dace da wannan to sai ya zo yasame ni a gida ko kuma ya bar mani sa}o in na zo in sameshi. In takarda ce ka ce in zo mu yi meeting game da fim. Inzan yi sai in ce yaushe za a fara, ya gaya mani. In kuma naga ba wanda zan yi ba ne sai in ce a�a. Ai akwai finafinai dayawa da aka neme ni in yi, amma ban yi ba, ba wai donwa]anda suka neme ni ba su isa ba ne, a�a! Idan ka dubi fim]in Fallasa da kyau, babu wani abu wanda na rage danganeda irin mutanen da ke da irin wannan halayya, saboda hakani ba wani abu takaici ba ne da zan ce na tuna shi na ji zafi.To me na yi? Fim ]in Fallasa in ka lura sunansa ma yawa

gare shi, bayan Fallasasunansa �Kukan kurciya majawabi ne, mai hankali shi keganewa.� Yanzu ai ka gawani bawan Allah ranar damuka saki Fallasa ]in,washegari ya buga wa(furodusa) Hamisu Lami]oIyan-Tama waya ya tambaya:na farko ma dai a ina nake?Aka ce ni ba nan (ofishin)Iyan-Tama nake da zama ba,na yi dai fim ]ina na gamana tafi. Ya ce a neme ni a gayamani yana yi mani fatanalheri. Ya ce ya ga dukabubuwan da na yi cikinFallasa, da (a ce) mun ha]aunguwa da shi zai ce wallahitallahi shi nake bi (ina ganin)duk abubuwan da ya faru dashi, na zo na yi fim ]in nan.To ni ba unguwar nake ba.Saboda haka (ya ce) yau baifito ba sai da ya sanya guesthouse ]in shi kasuwa, yatuba, yana ta istigifari.Billahillazi sai da na yi kukada hawayena. HamisuLami]o ya aika da mota akaje aka kirawo ni ya ce mani,�To ga waya ka ji abin da yafaru.� To kuma ni har na ceakwai wani abu da na takarawa a cikin Fallasa da zan ji

ban ji da]insa ba? Wallahi duk abin da na yi cikin Fallasaina sane na yi shi, kuma sa}o na isar. Allah Ya ga niyyata.

Fim: Shin ka ta~a zuwa wani guri aka nuna maka }yamasaboda irin rawar da ka taka a finafinan biyu?

Bankaura: Tun da nake yawo a cikin sararin nan naSubhana ban ta~a zuwa wurin da aka ce mani �Mun ga abinda ka yi, ba ka kyauta ba; tashi ka ba mu wuri.� Ko kuma ace, �A�a wannan wane ]an iskan nan ko wani abu mai kamakaza.� Duk inda nake zuwa kuma babu wata rana da za ta zota koma da ban tarar da mutane a cikin gidana suna jiranaba, wasu su same ni wasu su bar sallahu. Haka nake a kullum,ana ta murna da abubuwan da nake gudanarwa. Misali, kaga yau Jumma�a, to ga shi yanzu mutum ne tun dagaMaiduguri ya zo garin nan domin ya gan ni.

Fim: Daga cikin ]imbin finafinan da ka yi, wane ne za kaiya cewa shi ne bakandamiyarka, ya fi kwanta maka a zuciya?

Bankaura: Yana da wahala in iya nuna wani fim tilo in ceshi ne bakandamiyata, sai dai da yake mutane ne suke kalloban san wanne ya fi yi masu da]i ba. Wanda mutane suka ceshi ne ya fi daga cikin finafinaina, to shi ne bakandamiyata.

Fim: Ka ta~a jin wani wanda suka za~a suka ce shi ne?Bankaura: To a kullum sai misali; sai a ce, �A gaskiya fim

]in ka babu kamar Alheri,� sai wasu su ce, �Taf]ijam! Ba kaga rawar da ya taka a �Yanci ba!� sai wasu kuma su ce,�{addara Ta Riga Fata ya fi!� Saboda haka duk bayanin daake yi na ~atanci a kaina ba su ru]a ni.

Fim: Za ka iya gane iya yawan finafinan da ka yi?Bankaura: A gaskiya ba zan iya ba saboda abin da yawa.Fim: A }iyasce.Bankaura: Zai yi wuya, amma }iyasce mu bar shi a guda

]ari biyu.Fim: To daga cikin abokan sana�arka, musamman wa]anda

kukan yi wasa na manya, kamar da wa ka fi son ka fito a

Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura)

50

Page 45: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

da]ewarka a fim, kana da wata niyya ta shirya fim na }ashinkanka, domin }ila isar da wani sa}o ga al�umma?

Bankaura: {warai da gaske, wannan shi ne a cikinzuciyata. Akwai shirye-shiryen da nake yi, in Allah Ya yardazan yi. Ka san abin daga Allah yake.

Fim: Idan ka dubi yadda wannan sana�a ta fa]akarwatake, za ka iya barin �ya�yanka maza da mata su shiga harkar?

Bankaura: To ai sana�a ta Allah ce; kakan haifi ]a ba kahaifi halinsa ba. Idan a cikin �ya�yan da Allah Ya ba ni waniya ga cewa wannan harka ta yi daidai da ya yi ta, to in daialheri ce ni kaina ina taya shi addu�a Allah Ya inganta ta.Amma ni ban ce maka a cikin �ya�yana akwai wani wandana ke kama hannunsa in nuna masa wasan kwaikwayo ba.Kuma bari in fa]a maka wani abu, ban ta~a ]aukar kasetwanda na yi wasan kwaikwayo cikinsa na sa a gida munkalla da iyalina ba.

Fim: Ko da mace ce Allah Ya za~a wa wasan daga cikin�ya�yanka za ka bar ta ta yi?

Bankaura: (Shiru na wani lokaci) Idan ka yi magana gameda mace, duk �ya�yana ba ni da mace. Duk maza ne, to bance wai ba na son in haifi macen ba. Ka san abin na Allah ne.Amma in Allah Ya ba ni, ta ga za ta yi, ta zo bismillah ga filiga mai doki nan. Amma babban za~ina ga �ya mace ai aurene.

Fim: A cikin harka irin wannan na san ba za ka rasa samunalheri ba. Wane alheri ne ka samu ta sanadiyyar wannansana�a da ba za ka manta da shi ba?

Bankaura: Gaskiya ne. Ni har ma ba zan san abin da zanfa]a ba, amma akwai. A nan cikin garin Kano, ban san hawaban san sauka ba, Hajiya Rabin Mato ta aiko Hajiya LadinCima, wacce ita ce matata a fim ]in mu na Bankaura, cewatana nemana. To Allah da ikonsa ba mu ha]u da ita ba sairanar da aka }addamar da kalandarmu ta fitattun �yan wasa,ta ce tana nemana, domin wasana yana burge ta. Ta ce tanaso mu gaisa da ita a gidanta. Na ga wannan baiwar Allah ahaife dai ta haife ni. Duk da haka na taka na je gidanta. Inadu}awa na gai da ita, ta mi}a mani makullin Vespa, da daisauran kyaututtaka da dama wa]anda ni ma ban san iyakarsuba. Misali, Sa�in Katsina (Alh. Ahmadu Na-Funtuwa) yata~a ba ni kyautar ku]in da ni kaina ban san nawa ba ne.

Umar tare da Hajiya Hajara Usman a cikin shirin Fallasa

wasa?Bankaura: A

gaskiya IbrahimMandawari shi negaskiya tun da mukeshooting fim, in daiabu ya ha]o mu dashi, ban ta~a samuntake two ba; ma�anaa samu wani ]an abuya zo ma darakta yace, �Dakata, a sake;kaza za ka c,e ka cekaza! Kun gane ko?��Mun gane!� IbrahimMandawari shi ka]aina cire wa wannantutar. Saboda hakaina son mai irinhaza}arsa.

Fim: A mata fa?Bankaura: Amina

Garba; Hajiya Amina.E! Inda duk na nufato ta san inda za takamo ni.

Fim: Idan aka yila�akari da

Fim: A matsayinka na dattijo a wannan sana�a, wace shawaragare ka ga yara matasa wa]anda suka ]auki wannan sana�aa matsayin abin rayuwa?

Bankaura: Su zage damtse, su lura wace irin guguwa cetake bugawa, su ci gaba. Saboda fim kamar hira ne ga mutane:su zo su zauna suna ji a yi abu na nisha]i, a ji da]i abu nafa]akarwa kuma. Saboda haka su ba abin muhimmanci.Amma har abada ina kira ga masu shirya mana finafinanHausa kada su manta da al�adunmu na Hausa, a rin}a}o}arin nuna su. Domin ko�ina a duniya ana sha�awar al�adarBahaushe.

Fim: To a gurguje, mutane suna ganin ku masu fa]akarwa,musamman yaran da ke ciki yanzu, kuna yin kishiyar abinda kuke nunawa a cikin wasanninku. Misali irin shigar dawasu daga cikin �yan mata matasa da ke cikin wanna harkasuke yi wanda yake yana ]aya daga cikin abin da ya sakuke neman ku isar ]in ba ya yin tasirin da ya kamata. Meza ka ce kan wannan?

Bankaura: Gidan malamai babu masu shan taba?Fim: Ban sani ba. Bankauran: To ka bincika za ka gani. A cikin �ya�yan

malamai za ka ga wa]ansu na shan giya, a matan wa]ansuga su nan dai kara-zube; gashi a tsefe sama, wasu ma har sudasa gashin a kawunansu. A kowane gida, in dai babbangida ne, sai an samu irin wa]annan matsaloli, balle wa]andakusan ina iya cewa harkar fim ]in ce ta ha]a. Kowa da yaddayake rayuwarsa. Ni in za ki zo man daga ke sai siket in]auke ki in ba ki zane ki ]aura har zuwa sawun }afarki ki yimani lullu~i ki yi shiga irin ta Musulunci wadda ta yi daidaida al�adata, shikenan, in kin gama ki ]auki siket ]inki, inkin koma can wannan ke da iyayenki. Domin ita tarbiyyadaga gida take fitowa.

Fim: To daga }arshe, me ke burinka? Ko kana ganinburinka ya cika game da wannan sana�a?

Bankaura: To, ni ko a yau aka ce an dakatar da fim ai nialhamdu lillahi, da an }i da an so da ana so da ba a so, sai daia yi ha}uri ganin a faya-fayai barkatai Allah ka]ai ya sani.Saboda haka, alhamdu lillahi, ina ganin na cimma burinadomin na yi ma NTA da CTV wasa a baya, ga ]imbin nahome video.

HO

TO

: Iy

an

-Ta

ma

Mu

ltim

ed

ia

51

Page 46: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

A MINU MOHAMMED SABOfitaccen darakta ne wanda ya yisuna da finafinai kamar su

Daskin Da Ri]i, Sangaya da LinzamiDa Wuta, wa]anda kamfanin �SarauniyaFilms� suka shirya. Hasali ma dai, shiMalam Aminu tare da wansa AuwaluMohammed Sabo, su ke da kamfaninna Sarauniya.

Mutane suna yi wa su Aminu waniirin kallo, kuma gunagunin suna zuwaga kunnen mujallar Fim. Misali, me yasa Aminu bai ta~a yin darakta a wanifim wanda ba na Sarauniya ba? Me yasa suke yin finafinai wa]anda tushensutatsunniyoyin Hausa ne? Me ya sa suka}i yin Sangaya na 3 kamar yadda �yankallo ke bu}ata? Da dai sauransu.

To, don jin yadda wa]annanabubuwa suke, wakilinmu ASHAFAMURNAI BARKIYA ya tuntu~i hazi}iAminu, wanda bai da]e da auren�yar�uwarsa, shahararriyar zabiyarfinafinai ]in nan Fati Abubakar ba, donsamun amsoshi.

Fim: Darakta, sai ka ba masu karatunmujallar Fim ta}aitaccen tarihinka.

Aminu: Ni dai sunana AminuMohammed Sabo. An haife ni a nanKano, a Fagge. Kuma na yi firamare anan Gwammaja (1975-1981), dasakandare a G.S.S. Gwammaja (1981-1986). Daga nan na je makarantar horonmalamai, A.T.C., Gumel, a shekarar1989-1992, na samu takardar shaidarNCE. Yanzu haka ina Jami�ar Bayero, ashekarar }arshe, ina karatun aikinsadarwa, watau Jarida, da kuma Hausa.

Fim: A wace shekara ka fara shigaharkar fim?

Aminu: Ni dai harkar dirama na farata ne tun a ATC Gumel. Lokacin damuna karatu sai aka ce mu karancidirama a matsayin minor subject (wataukwas mai zaman ]an rakiya ga kwas]in da mutum ke karantawa). To da maa ~angaren da nake ina yin dirama taTuranci. Daga nan sai muka fara samungoyon baya saboda ana sha�awa. Saiya zamana a makarantar, daga shekarar1990-92, ni da abokin aikina BalaAhmed, mu ke ]ebe kewa danisha]antar da mutane. Bala da nakenufi, shi ne wanda ke da kamfanin�Sarauniya Films� da ke Sabon Titi.

Fim: Ga shi kamfaninku ya zamatamkar gidan gado a harkar finafinanHausa. Me ya kawo haka?

Aminu: E to, alhamdu lillahi, gaskiya

kam duk abin da muka dinga yi nadirama muna samun shawara daga gida.Wani lokaci ma mahaifiyarmu ke bamu shawara na abin da za mu yi. Kaikusan duk fim ]in da za mu yi sai munnemi shawararta. Kuma }anwarmuLubabatu Mohammed Sabo tana ]ayadaga cikin wa]anda suka fara kafaharsashen yin dirama. Don tun tanamakaranta takan rubuta littafi, daganan in ta rubuta mukan zauna da shi agaban mahaifiyarmu. A Daskin Da Ri]iduk mahaifiyarmu ce ta ri}a ba mushawara.

Fim: Me ya sa wani daga waje baishigo ya zuba jari a ciki ba?

Aminu: Abin da ya sa ba mu bar waniya shigo ba, mu muka san irin wahalarda muke sha. Babu irin }orafe-}orafeda zagin da ba mu sha ba a harkar fim.Tun ana cewa aikin banza muke yi,shashanci ne, ba mu da aikin yi, mukadai daure har muka kawo yanzu. Natabbatar maka kafin mu kawo yanzumun sha wahala sosai. To amma ba mufara sanin da]in abin ba sai da muka yi

fim ]in Gagare. Daga nan har dai AllahYa sa mutane suka }ara saninmu. To kaga yana daga cikin abin da ya sa mukari}e mu ne cikin kamfanin ka]ai. Ammafa mu kowa namu ne.

Fim: To yanzu ba ku maraba da dukwanda zai zo ya zuba jari a gidan gadon�Sarauniya Films�?

Aminu: To ai ban ta~a ganin wanikamfanin fim da wani ya zo ya zubajari nan Kano cikinsa ba. Ka gaMandawari shi ka]ai ke tafiyar da�Mandawari Enterprises,� Hamisu shi nemai �Iyan-Tama Multimedia,� Mansirshi ne mai Ibrahimawa. Ai ka ga wanibai shiga harkar wani.

Fim: Daga ina kuka sami wannansuna na Sarauniya?

Aminu: Ni dai ni na ba da wannansuna tare da Bala Ahmed. Lokacin damuna makaranta a Gumel, shekarar}arshe, muna da sha�awar dirama, saimuka ce mu yi }o}ari idan mun komaKano mu kafa }ungiya. Sai aka ce wanesuna za a sa mata? Wannan ya ce a samata kaza wancan ya ce wani suna. Toni sai na ce a sa mata suna Sarauniyatunda yawancin }ungiyoyi sai ka gasunan mace ne, kamar su Tauraruwa,Mikiya da sauransu. Mun sa wannansuna ba don muna ganin mun fi kowaba, a�a mun ga dai cewa shi ne sunan daya dace.

Fim: Ya zuwa yanzu finafinai nawakuka yi?

Aminu: Ni dai na san akwai Gagare,Sumbu}a, Daskin Da Ri]i, Tantiri,Kainuwa, Allura Da Zare, Zarge,Sangaya, Linzami Da Wuta, Nagari, saikuma Sartse.

Fim: Wasu masu rubuto wasi}u amujallar Fim suna tambaya cewayawancin finafinanku duk tatsunniyoyine. Shin haka ne? Kuma me ya sa kukefassara tatsunniyoyi?

Aminu: E, ai da ma an ce kowar bargida, to gida ya bar shi. Ai da ma fim datatsuniya ya fara. Ba an ce ka kwaikwayiabin da yake faruwa ba ne? Kuma damuna }ungiyar dirama da shi ma fimmun shiga ne domin mu bun}asaal�ada. Mutane da dama sun manta da

Taimakon damahaifiyarmu kebayarwa a finafinanmu

Aminu Mohammed Sabo

HIRA DA DARAKTOCI

– Hira da AMINU MOHAMMED SABO,daraktan ‘Sarauniya Films’

52

Page 47: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 53

tatsunniya, yaranmu da yawa yanzu basu san ta ba. Saboda haka sanin darajaral�ada, hukuma ta }asa da ta jiha sukakafa hukumar da ake kira �History andCulture Bureau,� watau Hukumar RayaAl�adun Gargajiya.

To shi ne mu ma domin mu bayarda tamu gudunmuwar sai muke ]aukotatsunniyon gargajiya muke fito da sumu nuna wa mutane wa]anda da damaba su san su ba. Ka ji dalilin da ya samuke yin tatsunniya. Amma kuma gaba]aya ina jin tatsuniyar da muka yi gudauku ce: Daskin, Da Ri]i, Allura Da Zare,sai Sangaya.

Fim: Wasu kuma na cewa tun da kukayi Sangaya har yanzu kuna yin }o}arinsake kamarsa amma abin bai yiwu ba,sai ga shi har wani ya yi Wasila, fim ]inda shi ma ya ci kasuwa kamarSangaya�

Aminu: Mutane ke ganin haka cewafitattacen fim ]in da muka yi shi neSangaya. To gaskiya har yanzu ba muyi kamar Daskin Da Ri]i ba. Komai dakomai Daskin Da Ri]i ya fi Sangaya]ari bisa ]ari. Na farko tun da muka yiDaskin Da Ri]i har yanzu wani bai zoya ce mana bai yi ba. Na biyu kuma inana batun samun alheri ne, to mun fisamun a cikinsa bisa ga Sangaya.Tunda ka ga shekaru uku da yin sa,amma har gobe muna cinikinsa, munasai da shi, muna kuma samun yabo.Yanzu haka da za a ce a fito takararfinafinai, to mu Sarauniya Daskin DaRi]i zai wakilce mu. Shi ne best filmnamu, ba mu da wanda ya kai shi ko yafi shi.

Fim: Ana kuma yin }orafin cewa baku }arasa wasu finafinanku. Gaskiyane? Me ya kawo haka?

Aminu: E, to, mutane sun}alubalance mu a kan wasufinafinanmu kamar Daskin Da Ri]i daSangaya. Sai dai mu ganinmu labarinya dire. Abin da mutane suke nema aSangaya, su burinsu lallai sai Zubainata dawo an wula}anta Kilishi. Wannankuwa ba zai ta~a yiwuwa ba a ce baiwata wula}anta �yar sarki. Wannan }aryane. Wannan yana ]aya daga cikin abinda ya sa mutane ke so a yi Sanygaya na3. Mu kuwa in har za mu yi shi don mununa an wula}anta Kilishi sabodaZubaina, to ba zai ta~a yiwuwa ba. Idanmukayi na 3 yanzu mutane ba su gaabin da suke son gani ba, za mu shazagi.

Fim: Da gaske ne kun fi kowanekamfanin shirya finafinai samun ku]i?

Aminu: Gaskiya ni na musa. Kafinmu akwai manya, na farko Mandawariyana nan. Ki Yarda Da Ni ai ya zamazakaran gwajin dafi a finafinan�Mandawari Enterprises.� �Iyan-TamaMultimedia� sun yi finafinai da yawa,wa]anda kuma sun yi kasuwa. YakubuLere ya yi Wasila. Mu dai alhamdulillahi mun gode, muna kuma samunyabo daga mutane cewa finafinanmu

sun shafi al�ada.Fim: To ko don kuna yin na al�ada

shi ya sa wasu ke cewa, �Su �yanSarauniya har yanzu ba su shigo birniba, a daji shirinsu yake�? Yaushe za kushigo birni?

Aminu: In dai a kan finafinan damuka yi ne ake cewa mun shiga daji, toAllah Ya }arasa tura mu daji! Mu daimun ce a kan al�ada muke, kuma haryanzu a kanta muke. Mu tunaninmu shine fim ya fito da ma�ana yadda za akoyi darasi a kansa, ba sai mun aromotoci da kayan sanyawa ba ne za muiya koya darasi. Ana iya yin haka kumamutane su ce fim ]in bai yi ba. Duk dahaka dai, don kada mutane su ce fushimuka yi, muna nan muna }o}arinshirya fim na zamani, in Allah Ya yarda.Kuma a Abuja za mu je a yi shi. (SuAminu sun je Abuja sun yi fim ]inGarwashi bayan wannan hirar � Edita).

Fim: Menene dagantakarku dakamfani �Sauraniya Films� na SabonTiti cikin birni?

Aminu: Da waccan da wannan duk]aya ne. Tun farko ai na fa]a maka maiwaccan Sarauniya, watau Bala Ahmed,abokina ne; tare da shi muka zaunamuka sa wa kamfanin suna, ya riga bu]etasa kafin tamu. Kuma duk finafinaiidan za mu yi, to sa shi muke yi. Za kaga muna sa �Jagoran shiri: BalaAhmed.� Shi ma idan zai yi, wani zubinyakan gayyace mu. Shi ma ya yifinafinai kamar Ragayar Dutse daHasana Da Usaina, da sauransu.

Fim: Watau ba reshe ba ne kenan nawannan kamfanin naku?

Aminu: A�a, gaskiya tushenmu gudane, bishiya ]aya ce, amma sai ta yi rassabiyu.

Fim: To da ta yi rassa, me ya sa aka sawa rassan suna iri ]aya?

Aminu: Ai na fa]a maka, ni da shi

muka dasa bishiyar. Kamata ya yi mutafi tare. Amma da Allah ya yi shi yanaSabon Titi mu kuma muna Gwammaja,sai suka ha]u da amininsa BalarabeAlasan, ni kuma na ha]u da ]an�uwanaAuwalu Mohammad Sabo, muka ri}ayin production tare. Ka ji yadda abinyake.

Fim Mun ji ana cewa da tare kukeamma daga baya sai aka ~ata, aka rabu.

Aminu. Ai wallahi har yanzu munatare. Kuma duk fin ]im da za mu yi saimun nemi shawararsa. In fa]a ma,gudummawar da Bala ya bayar a DaskinDa Ri]i, ta fi ta kowa yawa.

Fim: A matsayinka na darakta, me yasa ba ka yi wa kowa aikin fim sai fim]in ku na gado a daular Sarauniya?

Aminu: Gaskiya koyo nake yi. Kumamutane masu zuwa suna cewa mu ri}ayi wa wasu, to wasu su ba don Allahsuke fa]a mana haka ba. Wasu kumadon sun ga Sangaya da Daskin Da Ri]ishi ya sa suke zuwa. To ni abin dagaAllah ne. Kada ka yi mamaki in yidarakta a fim ]in mutum bai kyau ba,ka ga sai ya ce da ma mugunta na yimasa. Idan kuma ya yi nasara, to camfani zai yi kenan. Ni dai zan iya ba dashawara kawai. Muna da aminaiwa]anda idan za su yi fim sai sun nemishawararmu.

Fim: Ko kana da sa}o zuwa ga masukallon finafinan �Sarauniya Films�?

Aminu: Ina gode masu }warai,musamman masu aiko mana da wasi}u.Sai dai kuma ina son in fa]a wa masucewa ya kamata mu yi Sangaya na 3, toba za mu yi ba. Sangaya na 3 babu shibabu labrinsa. Akwai ma wani mutumdaga Katsina da ya zo ya ce ko nairamiliyan ]aya ne zai iya kashewa a yiSangaya na 3. Daga }arshe ina kira ga�yan fim da a ri}a mutunta kai, kuma ari}a auren juna.

Aminu (a tsakiya) da Auwalu Mohammed Sabo suna daukar shirin Zarge

HO

TO

: S

ara

un

iya

Film

s

Page 48: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200154

Kamar yadda muka ba da labari a watan jiya, fitacciyar’yar wasa Halima Adamu Yahaya ta haifi da namiji. Anrada masa sunan Muhammad Al-Amin. A nan, maijegonce da jaririnta

Halima da wakiliyarmu Sadiya Abdu Rano rike da Al-Amin

Haihuwar da Halima ta yi...

Halima tare da babbar aminiyarta Aishatu Danladi

AUREN WANSANI DANJA

�Yan fim na Kano sun nunazumunci a bikin aurenAbdulhameed Musa, wan jarumiSani Musa (Danja), lokacin da yaauri Binta. An yi shagali a ran

Lahadi, 17 ga Yuni, 2001. Dukda yake an go da amaryar ba �yanfim ba ne, furodusoshi dadaraktoci da �yan wasa dasauransu sun cika �Sani Abacha

Youth Centre,� inda aka yidabdala. Maza da mata sun yirawa duk da yake ana Shari�a.Amma fa shugaban taron, NuraIlu, ya }i takawa don kunya!HOTUNA DAGA: M.Z. FARU

RANAR FARINCIKI: AngoAbdulhameeddaamaryarsaBinta (ta sa‘ture-ka-ga-tsiya’) tareda babbarkawa a wurinwalimarauren

ABU NAMU: Balaraba Mohammed da SaniDanja suna cashewa... ana yi musu liki

’YANKALLO:Nura Ilu(furodusanMuradi) dadaraktaIshaq SidiIshaq sunki takawasab odakunya!

Page 49: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 55

FURODUSAN fim ]in Wasila 1-3, Yakubu Lere, ya ce nan ba dajimawa ba kamfaninsa na �Lerawa Films� da ke Kaduna zai fito dairin littafin nan na hikaya (wato �novel� a Turance) mai ]auke dalabari dalla-dalla daga fim ]in Wasila. Wannan sabuwar dabara ce anan }asar, amma ta da]e a Amerika da Turai. Wakilinmu IROMAMMAN ya sadu da furodusan a Kano, suka tattauna a kanwannan sabon yun}uri nasa da sauran al�amurra.

Fim: Mun samu labarin kana }o}arin fito da littafi na hikaya, watonovel, a kan fim ]in Wasila. Shin da gaske an rubuta wannan littafi,kuma wa ya rubuta shi?

Lere: Babu shakka da gaske ne. Wanda ya rubuta shi shi neshahararren marubucin nan na Kaduna, wato Ibrahim Musa Kalla,wanda ya rubuta littattafai da yawa. Masu sha�awar karanta littattafanHausa sun san sunanshi, kuma kamfanin buga littattafai na �Informart�da ke Kaduna muka ba kwangilar wallafa wannan littafi.

Fim: Shi wannan littafi, meye a cikinsa? Labarin rikice-rikicenkuda irin su Wasila Isma�il ne ko ko labarin da ke cikin fim ]in dagakashi na 1 zuwa na 3?

Lere: Wato kamar yadda ka sani ne, a }asasen da suka ci gaba afannin shirya finafinai, wato kamar a Amerika da Indiya, akan rubutalittafi sannan daga baya a yi fim ]in shi ko kuma bayan an yi fim saia rubuta littafinshi. To labarin littafin Wasila labari ne na ainihin fim]in Wasila ]in da wasu ba da wasu bayanai masu gamsarwa da za suda]a bayyana yadda labarin fim ]in yake.. Babu wani rikici. Yadda]auka ta farko take har }arshe. Misali, an yi bayanin wane kaza yanajan mota kaza ya yi tari; ko tari aka yi a fim ]in shi wanda ya karantazai ga cewa a waje kaza ya ga an yi tari.

Fim: Yaushe kake sa ran masu karatu za su karanta wannan littafi?Lere: E, to, wannan ya danganta. Ka san ana so a yi tsari ne mai

kyau. Insha Allah ba zai wuce nan da cikin watan Agusta ba. Yadanganta da kamfanin da muka ba kwangilar buga wannan littafi.

Fim: Da gaske ne za ka fito da kaset mai suna Sirrin Wasila, wato

ka nuna abubuwan da suka ri}a faruwa a lokacin shirya fim ]in?Lere: To babu shakka muna da wannan niyya.Fim: Yaushe ne ake sa ran za a yi shi?Lere: Insha Allah daga ran 15 ga Yuli zuwa }arshen watan Sirrin

Wasila zai fito.Fim: Wa]anne irin abubuwa ne mutane za su gani a cikin?Lere: Za su ga kurakuran da duk aka samu a lokacin ]aukar shirin

da kuma sirrin nasarorin da muka samu a cikin shirin, sa�annan daduk ilahirin nasarorin Wasila na 1, na 2 da na 3, da kuma wa]andasuka rubuta wa}o}in, da yadda aka rubuta wa}o}in da yadda aka]auke su, da yadda aka koya rawar wa}o}in. Sa�annan akwai wanibabban albishir da zan yi wa �yan kallo, shi ne asalin tarihin wasanZagezagi da Kanawa wanda ya janyo wa}ar Wasila ta tada }ura. Toinshe Allahu mun yi magana da mai girma. Mun ji [anmasanin Kanoya ba mu ~angaren Kanawa, sannan kuma akwai wani babban mutumda muka samu a Zazzau shi kuma ya ba mu ~angaren Zagezagi. Duka sirrin Wasila za a gani, insha Allah.

Fim: Fim ]inka na Adali na 1 ya bambanta da sauran finafinan daka yi ta fuskar jigo. Yaya kar~uwarshi yake a wurin jama�a dagacinikin da ka yi da kuma bayanan jama�a?

Lere: Wallahi ban ta~a jin wanda ya kushe script ]in Adali ba. Dukda ]aukakar da Wasila ya samu wa]anda suka kushe fim ]in tun apart one da two ballantana part three da aka sa ni ta}addama a kan shi.Amma har yanzu in ka ga yadda manyan mutare suke mana wayasuna yaba mana a kan Adali, ni ko da ban ci riba ba wallahi na godeAllah ballantana ma an ci riba. Don in da wani furodusa ne ba wandaya yi Wasila ba yai fim ]in Adali ya sami kar~uwa haka a kasuwa,babu shakka da an ji sunanshi. Irin haka ne ma ya sa har ro}on dajama�a ke yi ya sa za mu yi Adali na 2, amma da ban yi niyyar yi ba.

Fim: Yaushe ne kake hangen Adali na 2 ]in zai fito?Lere: Gaskiya ba mu sa rana ba saboda ko ]auka ]in ma daga

ranar 30 ga watannan da muka ciki ( Yuni) za mu fara ]auka. Sa�annankuma ka san akwai ayyuka da yawa wa]anda za a yi kafin fim ]in yafito. Insha Allahu dai nan ba da da]ewa ba cikin Sirrin Wasila masukallo za su fara ganin tallar Adali na 2.

Fim: Ya kake ganin nasarar da part two zai samu idan ka yi tunaninnasarar da part one ya samu?

Lere: Hausawa sun ce Jumma�ar da za ta yi kyau, tun daga Larabaaka ganewa. Ina kyautata zaton zai kar~u, saboda jama�a suka ro}emu mu yi, ba wai yin kanmu ba ne.

Fim: A kan hayaniyar da aka yi kan fim ]in Wasila, wani mawa}infinafinai Alkhamis Bature ya ba ka martani cikin mujalla. Shin menenera�ayinka game da abubuwan da ya fa]a a cikin martaninsa?

Lere: Na gani, na yi mamaki saboda na ]auka yana da tunani dahangen nesa. Ban ]auka zai shiga wannan rikici ba saboda ba abin daya shafe shi. Kuma in maganar wa}a ce, in dai ana maganar gaskiyana san masu karanta wannan mujulla ba su san wani Alkhamis Batureba. Na dauka zai bari ko su Mudassir {asim ko Musbahu Ahmed koYakubu Muhammad ko Sadi Sidi Sharifai su yi magana. Amma shidon katsalandan ya yi magana.

Fim: Su wa]annan da ka ambace su kana mi}a masu takardargayyata ne?

Lere: Ba wata gayyata.Ai ko mai kallo ya san sunansu. Matata data karanta sai ta ce, �Wai waye Alkhamis ]in nan da ya yi maganarnan?� Shi ne na ce, �Wani mawa}i ne amma na zamanin da.� To, ai nama ji ya zagaya gari ya fa]a cewa kada a yi mani wa}a. To ina ganincewa ingiza-mai-kantu-ruwa yake yi masu. Na ce kasuwarsu ba ta yida shi, kuma ma rumbunshi ya }one. Amma ina mai ba shi ha}uri, bada shi nake yi ba; abokin fa]anmu shi ne Gali, ba wai da sauranmawa}an finafinai ba, muna }aruwa da juna.

Fim: Kwanan nan ka kai }arar wani ]an wasa a Kaduna mai suna

Za mu fito da littafin hikayar shirin Wasila– inji Yakubu Lere

Lere: ‘Kishi da wanda Allah ya daukaka, ja da Allah ne!’

Page 50: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Muna dab da zuwa gun buga mujalla, sai labari ya zo cewaan rushe kwamitin zartaswa na {ungiyar Furodusoshi taJihar Kaduna. An kuma za~i Adamu Moh�d Bello Ability amatsayin Shugaba na wucin-gadi kafin a yi za~e nan dawata biyu. Wannan ya biyo bayan taron gaggawa na}ungiyar wanda aka yi a Zariya a ran 27 ga Yuni. Da matun da aka kafa }ungiyar, ba a sake yin za~e ba. An watsedaga taron kowa yana fatan Allah ya sa rikici ya }are.

An rushe shugabannin furodusoshin Kaduna

56

fita }ungiyar,� inji shi.A gefe ]aya kuma bayan }ungiya ta ]auki nauyin laifin da ta yi wa

Lere, sai ta rubuta wa Lere takardar neman gafara. Takardar, waddaaka rubuta a ranar 21 ga Yuni, tana ]auke ne da sa hannun Maikano.Takardar dai ta nemi Lere da ya yi ha}urin ~ata masa suna da aka yi.Sai kuma ta yaba da }o}arin da Lere ya yi inda ya amince ya janye}arar da ya kai Ability a kotu. A }arshe dai takardar ta nuna ba}incikin }ungiya kan duk wata damuwa da Lere ya shiga sakamakonlabarin da aka buga kan batun.

Sannan }ungiyar ta aika wa Lere da wata takarda inda ta yankeshawarar maido shi cikinta bayan ]an dakatar da shi da aka yi natsawon watanni biyu. Amma }ungiyar ta ce Lere ba zai koma cikin}ungiyar ba har sai ya biya harajin N5,000 da kowanne furodusa yabiya wanda shi Lere bai biya ba. Ana kuma bu}atar ku]in ne dagaran 21 ga Yuni zuwa ran 6 ga Yuli.

Ana wata sai kuma ga wata. YakubuLere ya tuma tsalle gefe ]ayaya yi jagorancin kafa wata }ungiya mai suna Filmmakers Associa-tion of Kaduna State. Wannan ba }ungiyar furodusoshi ba ce. {ungiyace da ta }unshi �yan wasa tun daga furodasa, darakta, ]an wasa,masu ]aukar hoton fim, da sauransu.

Abin da kowa ke tambaya shi ne: shin ba an kafa wannan }ungiyarba ne don yin hamayya da ta furodusoshin Kaduna? Idan aka yila�akari da cewa furodusoshin da aka dakatar suna cikin sabuwar}ungiya, to za a iya yarda da wannan hasashe. Sai dai shi Lere,wanda shi ne aka za~a shugaban }ungiyar, ya bayyana wa wakilinmucewa ba su kafa wannan }ungiya da nufin ci wa kowa mutunci ba.Yace sun kafa ta ne don inganta hanyar da �yan wasa za su ci moriyarharkar .

Ya ce, �Waccan }ungiya ai daban ta furodusoshi ce, mu ma tamuduk furodusan da ke so ya shigo sai ya shigo.�

An ci gaba da tambayar ko taron da }ungiyar furodusoshin ta yizai iya kawo }arshen tirkaniyar da ke cikinta? Kuma tsallen da Lereya yi na kafa wata }ungiyar gangamin masu shirya fim ta Kadunashin abin zai ]ore ko kuma tsalle ne ya yi irin tsalle da �yan maganake ce wa �tsallen ba]ake�?

SHUGABANNIN {UNGIYAR DA YAKUBU LERE YA KAFA:1. Yakubu Lere � Shugaba2. Al�amin Ciroma � Sakatare3. Mohammed Inuwa � Ma�aji4. Abdurrashid M. Kankiya � Sakataren Ku]i5. Aliyu Abdullahi Gora II � Sakateren Ya]a labarai6. Mukhtar Abubakar � Sakataren Shirye-shirye.7. A�isha Ibrahim (Saliha) daAbdullahi M. {waya � Masu Binciken Ku]i

Ci gaba daga shafi na 43

Lere ya kafa }ungiyar �yan fim

Adamu Mohammed Bello Ability wanda muke da labarin kotu ta saan tsare shi a gidan wa}afi har tsawon kwana uku. Shin me ya faru?

Lere: Kamar yadda masu karanta mujallar nan suka gani, bakunya ba tsoron Allah ya ce na cinye ku]in }ungiyar furodusoshi taKaduna wanda Allah shi ma ya sani }azafi ne, da fatan ~ata manisuna. Don haka na bi bahasi a kotu. Kamar Wasila Isma�il ko GalinMoney, abinda kotu ta yi wa Ability ha ka za ta (iya) yi musu. Ammamisali Gali yaro ne, mawa}i ne, na kira yaro ya yi min wa}a, in kumana kai shi kotu na kulle shi ai girmana ya fa]i, ballatama ita Wasila.Kuma ba wanda ya san ta (Wasila), Allah ya ]aukake ta ta hanyata,sai kuma a ji na kama ta na kulle? Ka ga wannan bai dace ba. Kumasu sun yi magana ne sun ce na sa~a masu ne. Shi Ability yana kirankansa furodusa duk da yake dai shi ba furodusa ba ne tunda bai ta~ayin wani fim ba. Ya ce da yawun }ungiyar furodusoshin Kaduna yayi. Shi ciyaman ]in ya zo ya yi min magana. �Yan�uwa da abokanarziki sun ro}e ni. Amma shi kuma yana ta tada jijiyar wuya, yanaganin kamar yana da gaskiya ne.

Dalilin da ya sa nasa har aka ]auki wani mataki a kansa, na ]ayaya kamata a tsaftace wannan harka tamu. Idan mun sami sa~ani yakamata mu zama �yan�uwa kamar yadda lauyoyi da �yan jaridu dalikitoci suke. Idan mun sani sa~ani kada a je ana zagin wani a mujalla,wadda sarki da mai ku]i da talaka da yara ke karantawa. Mu ganecewa �yan�uwa ne, muna tafiya tare. Na biyu, ya kamata a san cewaakwai doka yanzu. Da na ga dama na kai Wasila }ara da ta ce min bani da mutunci, kotu za ta ce mata, �Wane irin rashin mutunci ya yimaki?� Idan ba ta tabbatar da rashin mutuncin ba, za a kama ta dalaifin ta ~ata min suna.

To ya kamata mu �yan �film industry� yanzu mu san cewa ba komaine za ka je ka fa]a a kafafen ya]a labarai kan �yan�uwanka ba. Idanan samu sa~ani ne a bi hanyoyi da dama na sasantawa. Wa]annandalilai ne ya sa na ]auki wannan mataki wanda alhamdu lillahi na sanduk �yan�uwa da abokan arziki suna ta ro}ona. Kuma na san za asasanta.

Fim: To an ]age ranar ci gaba da wannan }ara zuwa wani lokaci.Da gaske ne cewa wani sarkin yanka a }asar nan ya shiga cikinmaganar?

Lere: Haka ni ma na ji. Amma tunda ban ga takardu tabbatattu ba,sai in ce wai. Amma na ji daga majiya mai }arfi cewa Ability ya kaikukanshi ga wani babba da yake ganin zai taimaka masa. Ni abin danake so ya gane shi ne, ni ne matsalar ba wani babba ba. Ko ya kaiwajen babban ya zo ya ce kai me ya faru? To kai ka yi ha}uri. Shiciyaman Aliyu ban san iyakar zuwan da ya yi gidana ba yana cewa inyi ha}uri an sa~a min. Sharu]]an da na bayar shi ne, shi (Ability) yaje mujallar Fim inda ya fa]a ya ce na ci ku]i, ya ce }arya yake. Nabiyu, kuma ya rubuto min takarda cewa yana nemana gafara. Na uku,ya biya ni ku]in da na ]auki lauya domin wannan shari�a. Ba waniabu mai matsala ba ne. Tunda ni ba wai ba, har ga Allah, Ability na]aya daga cikin mutanen da na sani da da]ewa, tun kafin a faraharkar fim. Kuma har ga zuciyata wallahi ba }arya nake yi ba, Abilityyana ]aya daga cikin mutanen da nake }auna a zuciyata. Na yimamaki yadda nake samun irin wannan matsalar da shi. Wannan shine karo na biyu da na samu matsala da shi. Kuma shi ke ja. Har gaAllah idan jama�ar nan suka zo kuma ya yi al}awarin amincewa dawa]annan sharu]]a da na bayar, wallahi maganar nan ta }are.

Fim: Ya kake ganin wannan abu zai shafi batun ha]in kai a {ungiyarFurodusoshi ta Jihar Kaduna?

Lere: Gaskiya su furodusoshin ban san abin da ke damunsu ba.Ban sani ba ko suna da matsala da ni ko yaya? Saboda duk abubuwannan da suke faruwa ba wanda ya jajanta min ko ]aya. Wannan abinsun san an min }arya ne. Ko shi ciyaman da yake zuwa zuwa wurinakan maganar, yana zuwa ne a matsayinsa na dattijo kawai, wanda yasan abin da yake yi. Ga furodusoshin nan da yawa. Kamar Nata�alaAliyu, Ability ya ta~a kai masa �yan sanda da sha biyun dare. Ya zoya ro}e ni. Amma da sai su zo gaba ]aya (su ce): �E Lere, wannanabu da Ability ya yi ba da yawunmu ba ne, sannan kuma bai kyautamaka ba, ka yi ha}uri.� Ya kamata lokacin da Wasila ta yi wannanabu su zo su ce min, �Lere wannan abu da Wasila ta yi bai dace ba, ayi ha}uri. Shin yanzu me zai }arfafa wa mutane su zama �committed�cikin }ungiya tunda }ungiyar ba ta tsinana masu komai? Sai dai a

koma gefe ana yi maka dariya. Ina kira gare su a cire ba}in ciki dakishi, mu taru mu tafi tare. Idan Allah ya ce a yi da mutum, idan katsaya kana yi masa kishi to kana kishi da Allah ne ba da shi ba. Kumaka san mutum bai isa ya yi kishi da Allah ba.

Fim: Haj Lere, mun gode.Lere: To madalla.

Page 51: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 57

ASSOCIATION OF FILM PRODUCERSKADUNA STATE

c/o Iman Ventures, Kaduna57, Market Road, KabalaCostain, KadunaTel.: 062- 241170,069-34591,069-335048

1st June, 2001

YAKUBU LERE,LERAWA FILMS KADUNA.KADUNA.

Sir,

APOLOGY

I have been directed by the general meeting of the association held on 21st June, 2001 totender its apology on a publication in FIM magazine in which it was claimed that youmisappropriated funds.

In the interview granted by the PRO on the mandate of the association, facts were misrepresented.

The association hereby commends your decision at the above meeting to which you were inattendance to withdraw a legal suit you instituted on the condition that this letter be writtento you.

The association regrets any inconvenience the publication might have caused you.

Yours faithfully,

Abdullahi Maikano UsmanSecretary

Our Ref----------------------------Your Ref---------------------------Date-------------------

Page 52: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 59

Daga MUKHTAR MUSA DIKWAa Gusau

I DAN ana maganar shirya fim a JiharZamfara, to dole a sa sunan AliyuGarba. A Gusau, babban birnin jihar,

Aliyu furodusa ne kuma shugabankamfanin �Video Mark,� wa]anda sukashirya fim ]in Ki Yafe Ni.

Ban da shirya fim, Aliyu kuma ]ankasuwa ne. [an kimanin shekaru 30,an haife shi a cikin Gusau. Ya yimakarantar firamare a �Ibrahim GusauPrimary School�, Gusau. Ya kammalasakandare a �G.S.S. [ansadau� a cikin1990. Ya yi zaman kimanin shekara]aya a gida, daga nan kuma sai ya shigaharkar kasuwanci. Bayan �yan shekaruda shiga harkar kasuwanci, sai kumaya kutso harkar fim. Ga yadda sukazanta da wakilinmu cikin watanFabrairu na bana:

Fim: Malam Aliyu, yaya ake ciki agame da harkar fim a nan Jihar Zamfara?

Aliyu: Duk da cewa mu nan Gusauyanzu muka fara shiga harkar fim, inshaAllahu a hankali za mu ci nasara dukda matsalolin da muke fuskanta.

Fim: Wa]anne irin matsaloli ne kukefuskanta?

Aliyu: Gaskiya mun fuskanci wasumatsaloli, kamar lokacin da muke shirinfim ]in (Ki Yafe Ni) mutane sun }i bamu ha]in kai, su kamar ba mu taimakota wajen gidaje da motoci. Ta kai dukgidajen da muka yi amfani da su otalotal ne muka biya, to a nan mun kasheku]i sosai koda yake fim ]in mu nafarko kenan. Amma muna sa rai nangaba za mu samu ha]in kai gun mutane.

Fim: Me ya hana ]in naku fitowa?Aliyu: Yanzu kam mun ]an samu

wani matsala ne, amma a yanzu yana

wurin editing kuma mun ma ba da abuga mana kwali.

Fim: Zai fito kwanan nan kenan?Aliyu: Insha allahu zuwa }arshen

Maris.Fim: Me za ka ce a game da soke

shirin fim a Kano bayan an }addamarda Shari�a tunda ku ma nan akwai

Aliyu Garba

Shari�a a Zamfara ba ta hanamu yin fim ba � Aliyu Garba

Shari�ar?Aliyu: E, to wannan sun yi shi ne a

bisa son rai, saboda ko mu da muke nanZamfara ba a hana mu mu yi fim ba,kuma Shari�a ai a wurinmu aka somata, ta kuma fi ta ko�ina }arfi. Bugu da}ari, ai ba a da]e ba aka }addamar dawani fim mai suna Babu Maraya SaiRaggo (a nan Gusau), wanda manyanmutane sun halarta, ciki har damu}arraban gwamnati, kwamishinan�yan sanda ma ya sami halarta.

Fim: Ko kun gayyaci �yan wasa dagawasu garuruwa don yin fim ]in ku,kamar daga Kano ko Kaduna?

Aliyu: {warai dagaske.Fim: Kamar su wa da su wa?

Aliyu: E, cikiakwai [an Ibro,Ciroki da SanusiBurhan; akwai BibaProblem, HindatuBashir, Hajiya AminaGarba da FatiSulaiman, saiHabiba, da daisauransu daga Kano.Kuma daga Kaduna,Wasila Isma�il cemuka gayyata. Bacinna gayyato su nemuka ha]u da �yannan Gusau muka yifim ]in.

Fim: Ko kuna da}udurin ci gaba dayin wasu finafinaibayan wannan?

Aliyu: {warai dagaske. Yanzu hakamuna nan muna}o}arin shirya gudauku. Wanda za musoma fitarwa cikinukun kuwa shi nemai suna Shari�a AZamfara.

Fim: Ko kana dawani abu da za ka cea }arshe?

Aliyu: Ina son inba �yan kwamitinShari�a na Kano

shawara da su yi nazari a kan wannanhukunci da suka yanke na hana yin fimda sayar da kaset-kaset.

In aka duba a halin yanzu dubannanmutane na samun abinci ta wannanhanya. To ko ka ga yana da wuya a cean hana su kwatsam. In har wani abu nemuke yi (mu masu yin fim) kamar nabatsa ko abin da ya sa~a wa Shari�a, toa nan sai su yi mana dokoki wa]andain muka sa~a, sai a hukunta mu. Anaiya ma soke wa mutum rajista.

* (Mun yi wannan hira da Aliyu kafingwamnatin Jihar Kano ta ]age dokarhana yin fim. � Edita)

In har wani abu ne muke yi (mu masu yin fim) kamar nabatsa ko abin da ya sa~a wa Shari�a, to a nan sai su yi mana

dokoki wa]anda in muka sa~a, sai a hukunta mu

Page 53: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200160

idan sa~ani ya shiga tsakanisai ka ga cewa }asar da akayi shekaru an tarawa dacokali, an ]auki cebur anbaje ta a cikin �yan kwanaki.

Misalin wannan bayanitamkar misalin abin da yafaru ne yanzu haka tsakanintaurarin �yan wasan finafinanIndiya ]in nan guda biyu �Bobby Doel, ]an gidantsohon jarumi Dharmendra,da kuma Kareena Kapoor,�yar gidan Randir Kapoor.Iyanyansu dai abokan junane. Abin kuwa har ya nemiya shafi iyayen biyu.

Kafin faruwar al�amarinkuwa, akwai zumunta sosaitsakanin Bobby da Kareena.A cikin shekara ta 2000 sunsanya hannu kanyarjejeniyar shirya wani fimmai suna Ajnabee wandafurodusa Vijay Galani yashiga, kuma Abbas Mustanke wa darakta. Bobby daKareena sun ci wa fim ]inburi ganin yadda aka ware]imbin ku]i domin Ajnabeeya yi kyau kuma ya kar~u.Sauran taurarin fim ]in su neAkshay Kumar da BipashaBasu.

To, tun ba su fara zama�yan gari a }asar Siwizelanba (inda can aka fara shiyafim ]in), sai rikici ya ~arke.Bobby Deol ya je }asar netare da matarsa Tanya. Bibitakuma, da }aramar ]iyarta taje. Su kuma Akshay daBipasha kowa shi ka]ai yatafi, tsinken raginsa.

Kareena ta je tare da maiyi mata ado da kwallya maisuna Vikram Phadnis.Kwatsan, wata rana saiBapisha ta sami matsala dakayan kwalliyar. Ganin cewadole sai ta nemi taimakonwanda zai ha]a matalaunukan zabibin da takeshafawa, sai ]an kwalliyarKareena ya kama fuskarta yaranga]a mata kwalliyar,fuskarta kuwa ta yi ra]au.Wannan shi neummulhaba�isin tashinharkalin.

Wata majiya ta ce,�Lokacin da Kareena ta jicewa Vikram ya taimakiBapisha ya yi mata kwalliya,sai ta harzu}a matu}a.�

�Yaya za ka taimaki wata candaban bayan kuwa ka san nina ]auko ka don yi minaiki?� Abin da Kareena tafurtawa Vikram kenan.

Kareena ta ]auki gaba daBobby, domin ita a ganintaita ya kamata Bobby ya goyawa baya, ba Vikram ba.

Da ma masu magana nacewa wai zomo ba ya fushida makashinsa, sai daimaratayi. To haka aka ci gabada irin zaman nan da ake cewa zaman mazurun Addani.

Ganin cewa fasalin adonBipasha ya fara dagulewa,dama ita sabon shiga ce, fim ]inAjnabee shi ne nata na farkokuma ba ta saba da yinsamfurin adon }walisarzamani na matan fim irin suKareena ba, sai matar BobbyTanya ta ri}a shiga waAkshay. Shi kuwa Bobby inaruwansa? Da Tanya fa ya tafi.

Wannan sa~ani nasu dai ya}ara munana bayan sun dawogida domin }arasa fim ]in akan wani }aramin jirginruwa. A wurin dai an ceKareena ba ta yarda sungaisa da Bobby ba, ko dayake shi ma ya }ara harzu}aa lokacin da ya nuna cewa�ai yarinta ce ke ]ibarta, dukabin da ta yi daidanta ne�.

Tabbas wannan rikici yashafi Ajnabee da kuma shikansa mai fim ]in, furodusaVigay Galani. Fim ]in ya zo}arshe, saura wa}a ]aya takita ta rage � wadda Bobbytare da Kareena za su yi. Bisadukkan alamu za a sokewannan wa}a daga cikin fim

Labarin shirin fim a Indiya

D A N { O Nzumunci kon a

abokantaka (}awance)kan ]auki shekarumasu yawa tsakaninma�abota biyu. Amma

To a waccan ranadai sai ita Kareena taumarci Vikram da yafita daga ]akin otal]in da ta kama masa,kuma ya koma

}asarsu Indiya. Ganinhaka sai Bobby daAkshay suka taimakamasa ya kwashe kayansa,suka }ara masa wani ]anihsani domin biyanku]in jirgi. Daga nan

Kareena

Page 54: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

I.S.I. FilmsSabon Titi, Dandago, Kano

presents

Produced by: ZILKIFILU MUHAMMAD

Directed by: ISHAQ SIDI ISHAQ

Coming Soon!!

... A movie you shouldn’t miss

61

No. 17, Dala Special Primary School, kusa da CDS, Dala, KanoTel.: 064-632081

General Printing and Contractors

for the best in:

* Stickers* Calendars

* Identity Cards* Invitation Cards

* Memos* Customised Clocks

* PostersEtc., etc.

Bobby Deol: Shi ya jawo rikicin?

]in, domin Bobby daKareena duk sun nuna wadarakta rashin bu}atarsu dayin aiki da junansu.

Sai dai kuma abin da masukallon al�amurranBollywood ke hange shi neKareena ta fara tafasa ruwanda idan ba ta yi taka-tsantsanba, da shi za a dafa ta kumata dafa kanta da shi. Dalili,rigimarta da Bobby ta sa ta}ara yawan abokan gabarta.Ta yi fa]a da Sanjay LeelaBhansali, ta yi da VashuBhagnani, ta maida sabuwar�yar wasa Bipasha abokiyargaba, ita da Preity Zinta basu yi wa juna kallonmutunci. Ga shi kuma yanzuba su shan inuwa ]aya daBobby.

Shawara ga Kareena da ire-irenta ita ce: Idan ta yi sake(ko da yake ta fara), yawanabokan gabarta suka kai gamasoyanta ko finafinanta, tosai dai wata ba ita ba. Da mayanzu Bollywood ya-ya-da-}anen-wani ake yi. Kuma su

�yan matan fim ]in sun komatamkar tukunyar

madambaci. Ma�ana, dole saitukunya ]aya ta hau kan]aya sa�annan dambu zaidafu.

Ga abin da wani mai

nazarin al�amarin ya ce:�Kareeena a yi hattara! Idanwata jaruma ta hau kanki saidai ta yi girkin, kina ji kinagani a cinye ba tare da ke ba.�

Page 55: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 200162

MUSBAHU M. Ahmadshahararren mawa}i ne kumamarubucin wa}a. Wa]anda

suka fara ganinsa sun fara ne a cikinfim ]in Sangaya na 2. A ciki ne ya fitoda sunan Ibrahim [an Malam, saurayinNusaiba (Fati Mohammed wadda ta cikaro da shi har ya cire mata layar asirinda aka yi mata na kurciya. Sai dai dukwannan bai isa jama�a su gane wannanyaro ba. Abin tambaya shi ne waneneMusbahu M. Ahmed? Hausawa na cewain ba ka san gari ba, saurari daka. ToFim ta yi nata daka kan Musbahu, harma da }ul}ule.

Da baiwar da Allah Ya ba shi ta wa}ane ya fara taka rawa cikin finafinanHausa. Wa}ar da ya fara rubutawa kumaya rera har ta game }asashe da yawa ba}asar Hausa ka]ai ba, ita ce �Ayye LaleMaraba Sangaya� ta cikin fim ]inSangaya na 1. Yadda wa}ar �Sangaya�ta yi tashe ko�ina daga sauran wa}o}i,haka shi ma Musbahu ya yi tashinGwauron zabo daga cikin harkar

kuma ya zama furodusa da fim ]inAmalala. Sannan tudu na biyar shi nesayar da kaset, domin a kwanan baya,bayan ya rabu da kamfanin �Sarauniya�a cikin ~acin rai, Allah Ya taimake shiya bu]e ofis mai suna �Usmaniyya Pro-duction� inda yake saida kaset. Duk mainemansa ya je can ofishin da ke kanhanyar �Aminu Kano,� hanyar GoronDutse, zai same shi. Ya ce dillalin kasetma yake son ya zama nan gaba. Gaalama, a nan gaba zai iya cin tudu nashida, wato idan ya zama darakta kenan.Abin ai ba wuya, ki]an ganga da lauje.

Da wannan mujallar ta tambaye shiyadda aka yi har ya }ir}iro wa}ar�Sangaya,� sai Musbahu ya bayyanacewa: �Tun ina yaro }arami na sha jinwata wa}a ana cewa:

Dokin mai doki,Sangaya!Da ya zaburi doki,Sangaya!Bai kwana gida ba,Sangaya!Sai a }ofar fada,Sangaya!Aka aiko ya mutu,Sangaya!Allah Ya ji}ansa,Sangaya!To wa]annan baituka ne da ya

haddace tun yana }arami ya jirkita yayi wa}ar �Ayye Lale Maraba Sangaya.�

Ya kuma bayyana wa Fim cewa bashi ya kai kansa cikin harkar fim ba.�Aminu Mohammed Sabo, daraktankamfanin �Sarauya Films,� ya fara gwadani bayan ya gwada wa}ata.� Musbahuya ce shi ya kai kansa wurin Aminu, bakai shi aka yi ba.

Yadda duniyar finainan Hausa ke}ara bun}asa da yaran jarumai masu jinia j ika, lallai ko ba a tambaya ba abinzai zama mizanin auna }arkon jarumanda ke duniyar su a yanzu. Su ne irin suGalin Money, sabon Zik, SulaimanTupac, Ali Rabi�u (Daddy), da daisauransu, da dama. Idan ka fa]i sunansuko ba a kalli fim ]insu ba, an san sunkusan zama a-kori-su-wane-da wane.Amma wanda ba zai yi fargabar yingogayya da irin wa]annan yara ba shine Musbahu ba, wanda shi da su duk}warya ta bi }warya ne. Musbahu da

]in kasuwa ba, watau wa}ar �AmalalaMai Fitsarin Kwance,� ta cikin fim ]inAmalala. Kuma shi ya yi wa}ar�Tantabara� ta cikin Adali, inda har mayau ya fito yana rera wa}ar.

Wani abin lura a wurin Musbahushi ne yadda tauraronsa ya fara haske,to zai yi wuya a ce ya dusashe cikin]an }an}anen lokaci. Irin salon da yaketakawa ne idan mutum ya duba zai iyayarda da wannan magana. Salon kuwashi ne, duk finafinan da ya fioto amatsayin jarumi, to za ka ga shi newanda ya rubuta wa}o}in cikin fim ]in,shi kuma ke rera su.

Musbahu kenan. Ba ga wa}a ka]aiya tsaya ba. Shi ne jarumin wa]ansufinafinai kamar su Samodara, Amalala,Alfijir, Dawayya da kuma Qazaf. Akwaikuma wa]ansu finafinan da ya fito jefi-jefi a ciki, irin su Sangaya, Linzami DaWuta, Adalci, da kuma Laila.

Idan an lura kenan, Musbahu fasihine mai cin tudu biyar: yana rubutawa}a, yana rera wa}a, yana wasa a fim,

Jarumi Mai Cin Tudu Biyarfinafinani.

A fim ]in Allura Da Zarene aka ne aka fara jinmuryarsa inda shi ne ya rerawa}ar Ga Mu Cikin Harka,�amma ba shi ya rubuta taba. Haka ita ma wa}ar �NaGangaro� da ke cikin fim]in, duk shi ya rera su. Shine kuma ya rubuta kuma yarera wa}ar �Iya Duba Duba�ta cikin Samodara. Wandaduk ya ga wa}ar da AliRabi�u Ali ya yi ta �LililoDa Dariya Danya� ta fim]in Haya}i, to sautin muryarMusbahu ne ya ji.

A cikin Sangaya na 2kuwa, Musbahau ne yarubuta wa}ar �Ban DaKomai.� Shi ne har ila yauya rubuta wa}ar �{wan{wan Nai Sallama {ofar[aki,� ta cikin fim ]inZarge.

Ba wa]annan ba ne ka]aiwa}o}in da ya rera kuma yarubuta. Shi ya rera wa}ar daa yanzu take tashe duk dacewa ba a tashi fito da fim

Page 56: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 63

No. 21, Zaria Road, Gyadi-Gyadi, Kano, kusada Fly-over, gefen ofishin mujallar FIM

Tel.: 064-665482, 666419

Alh. Adamu A. UmarJanar Manaja

In dai ]inki mutum yake so nagargajiya ko na zamani, to ya zoshagonADAMU TAILORING/FASHION SERVICES

domin mun }ware a kan kowaneirin ]inki na maza ko na mata,yara da manya

{wararrun telolinmu sun da]eana damawa da su a sana�ar]inki, don haka mutane da damasukan kawo aikin ]inkinsuwurinmu.Me zai hana kai ma ka jaraba?Aikinmu akwai rahusa da biyanbu}ata.

[inki na gani na fa]a, sai

ADAMU TAILORING &FASHION SERVICES

Sai kun zo.

Musbahu a matsayin dan sarki a cikin shirin Laila

ya tashi yi wa kansa gayauna daga cikin gandunfinafinan Hausa, sai ya fara noma da fartanya mai kaifiniya wasa. Koda yake dai sai da ya fara �School of LegalStudies� ta Kano, ya daina ya shiga harkar fim a cikin1998.

Musbahu bai yi dogon karatu mai zurfi ba. Sai daiinda ya tsere wa sa�o�insa, shi ne ta yadda yake da zurfin}ir}iro wa}a, kuma ya ri}a zuba ta yana rerawa kama data Alfazazi. Da ma Hausawa sun ce dokin mai baki ya figudu.

Tarihin Musbahu ta}aitacce ne. Ko kuma a ceta}aitacce ya ba mujallar Fim. An haife shi a cikin 1974(watau shekarar da aka daina amfani da kwabo maihuda). Da karatun Firamare da na sakandare duk aunguwar Gwammaja ya yi a inda aka haife shi. A Masa}aPrimary School na yi. Bayan nan kuma sai na tafi G.S.SGwammaja II.�

Kada mai karatu ya ]auka ko Musbahu kifin rijiyane don ya yi firamare da sakandare a gida. Bayan yagama sakandare sai ya garzaya garin Bauchi. A can yayi karatun haddace Al}ur�ani Mai Tsarki a MakarantarHoron Haddace Al}ur�ani, watau School of IslamicTahfizul Qur�an. Can Allah Ya ba shi sa�a ya haddaceAl}ur�ani tun daga Baqara har Nasi.

�A gidanmu ba ni ka ]ai ba ne ya haddace Al}ur�ani,za mu kai mutum hu]u. Ka ga ba ni ka]ai Allah Ya bawannan baiwa ba,� inji Musbahu. �Ni da sauran �yanuwana.�

Wannan sardidin matashi dai ba shi da aure. Sai daiyana neman wadda ta dace da shi da kuma halinsa. Kocikin �yan matan da ke fim? E, }warai kuwa. Ai ya ta~aneman auren zabiyar nan Jamila Mohammed Sabo.Sauran }iris, to amma Allah bai yi da shi ba. Hausawasun ce komai yana da lokacinsa.

Page 57: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001 65

Daga IRO MAMMANda ALIYU A. GORA II

SUNAN �Wasila� ba ~oyayye ba nea harkar finafinan Hausa. Sunanya yi fice ne sakamakon fim ]in

Wasila, wanda shi ne fim na farko nabidiyo da ke ]auke da sunan jarumarda ke cikinsa. To, rikicin Wasila yajanyo aka sa Fatima Ibrahim a madadinWasila Isma�il a cikin Wasila 3. Donhaka sai ta taki sawun Wasila ta farko,ta fito da sunan Wasila ita kanta.

To amma ba muna nufin cewa ba}o}arin Fati ba ne ya sa aka ba tamatsayin. Da ma can ta ]an ta~a wasan,duk da yake ba da]ewa ta yi a fagenba. Ma�abuta kallon finafinan Hausasun ga irin rawar da sabuwar jarumar tataka a cikin fim ]in Adali wandakamfanin Lerawa da ke Kaduna yashirya. Ta ]auke hankalin duk wandaya kalli fim ]in musamman inda takecashewa tare da Musbahu Ahmed(wanda ya fito a matsayin saurayinta)lokacin da suke wa}ar �Ni Sai Ka BaNi Tantabarata.� Burgewar da Fati ta yia fim ]in ta sa �yan kallo da yawatunani tare da tambayar kansu cewawacece wannan? Ga ta dai sabuwaamma tamkar da ita aka fara fim aNijeriya!

A Kaduna, inda take da zama, harwasu sun fara yi mata la}abi da �A koriWasila.� A lokacin da wakilinmu AliyuAbdullahi Gora II ya yi tattaki zuwagidan su Fatima Ibrahim don ya ganada ita, tambayar farko da ya yi mata itace yana son ya san asalinta. Shin itaBahausa ce cikakka ko tana da surki?Nan da nan Fatima ta amsa: �A�a banda surki, ni Bahausa ce.�

Fatima dai }anwa ce ga shahararriyar�yar wasan nan A�isha Ibrahim (Salaha).Ciki ]aya suka fito.

Asalin su Fatima �yan Gusau ne taJihar Zamfara, amma ita a Kaduna akahaife ta. Da farko, ta }i fa]in ko a waceshekara aka haife ta, waoi don kada ayi mata dariya a ce ashe ma }aramaryarinya ce. Duk da haka, da ya matsamata sai ta yi dariya ta ce shekarunta19.

Fatima ta yi makarantun firamare dayawa. Da farko, ta fara da �Jamon Nurs-

�Wasila ta 2� ta tsinci dami a kala, sannan ta yi wa shirin fim�shiga sojan Badakkare�

Fatima Ibrahim

ery and Primary School� a Kaduna, takoma Unguwar Rimi Primary School.�A nan ta gama. Sai ta je makarasntarsakandaren da ke Giwa a Jihae Kaduna,ta bari ta ]an yi a sakandare ta �TafawaBalewa,� a Kaduna, ta yi �J.S.S.,� daganan kuma sai ta koma Illela a JiharSokoto. To daga an aka yi masu canjigaba ]aya, aka ce makarantar ta yi nisada gari, sai aka dawo da su Bo]inga anan Jihar Sokoto dai. To a nan ta gamaa cikin 1998.

A yanzu, �yar wasan ]aliba ce aJami�ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna(wato Federal University of Technol-

ogy).Shin me ya jawo ra�ayinta zuwa harkar

fim ganin cewa tana karatun jami�a ]inne ta shigo harkar, wato ba ta shiga dafarko ba ko kuma ba ta bari sai ta }areba?

Fatima ta ce, �To gaskiya dai da farkoina gani ina cewa wannan (harkar fim)duk shirme ne, ni ban so dai. Sabodalokacin ba a fara }ayatar da fim kamaryanzu ba. To da na fara ganin an zo anairin wa}e-wa}en nan abin na bansha�awa kuma irin ga shi A�isha sister]ina na yi, sai na ga in ta zo ta zaunairin in tana kallon abin da take yi, sai

Page 58: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

ni kuma�. Sai na samu ra�ayin ai nima ina son in ga ni ma ina yi dai kawai,irin� in zama dai ina entertaining(nisha]antar da) mutane dai haka... adai ce, �Kai, wannan she is very funny!�Ka gane ai (dariya). Kawai that�s it, saina samu interest.

Fatima ta fara yin wasa ne a fim ]inAdali. In ka ji lasbarin yadda ta shigafim ]in, sai ka ce lallai ta tsinci dami akala ganin yadda �yan wasa mata dadama suke wahalar yin wasa a ]imbinfinafinai kafin a ba su wani babbanmatsayi a fim, misali su fito a jarumai.

Mun bu}aci Fatima ta ba mu labarinyadda furodusan fim ]in, Yakubu Lere,ya jawo ta ya sa ta a fim ]in. Sai ta amsa:�Gaskiya wannan ban sani ba. Don ni�ya ma muka yi? Ban san yanda ma mukayi ba! So, abin da ma ya faru dai naAdali, shi ne Fati Mohammed yakamata ta ]auki role ]in da na yi; shine sai muna tare a location a ranar, dani da A�isha; mun fita dai haka za muwani wuri sai ta ce mu je za ta biya lo-cation. Sai (Yakubu Lere) yake ta kukan�Fati ba ta zo ba.� To ni ban ma ta~amaganar fim da shi ba. Sai na ce, �Meya sa ba ta zo ba?� Sai ya ce wallahi baisani ba. Haka ya yi ta waya (gun Fati aKano). Sai na ce, �Ayya! shi kenan!�Sai a cikin wasa sai na ce, �Zan yi.� Saiya ce, �Da gaske?� Sai na ce, �E.� Sai yace in ya ba ni yanzu zan yi? Sai na ce ezan yi. To sai ya ba ni, kawai sa na yi.�

Kun ji fa, abin ba wuya � kamar ki]anganga da lauje! Yawanci akan yi zarginidan irin haka ta faru, to kila akwai watadangantaka ta musamman a tsakaninfurodusa ko darakta da �yar wasa.Jarumar dai ta ce babu wani abu saimutunci. A fahimtanmu, da]a]]enmutuncin da ke tsakanin Lere da A�ishashi ne ya }ara dan}on zumuncitsakaninsa da }anwarta da suke uwa]aya uba ]aya.

To, ga wata sabuwa kuma. Fatima daiha]a]]iyar yarinya ce. Ga shi tanakamfatar ruwan ilimi a jami�a, kuma gaharkar fim ta rsunduma a ciki. Don hakawane mataki za ta ]auka a kan zarginda ake yi wa �yan wasa mata cewa ba suson aure?

Fatima ta ce: �To gaskiya� ba waimun }i yin aure ba ne. Komai dalokacinsa, ko ba gaskiya ba? In za kayi abu ya kamata ka yi tunani; mu daitun farko iyayenmu sun sa mu a boko,sun gwada mana dai in mun je� sunkai mu Islamiyya sun kai mu boko...Duk abin da za ka yi ya kamata a cekana da ilimi, ko ba gaskiya ba? Sabodahaka ni ina da ra�ayin yin aure ammasai na kammala makaranta.�

Shin akwai wani lokaci da ta ]ibacewa in ya cika za ta daina fim, ko kuwadai ta shiga kenan sai hali? �Ni daigaskiya game da harkar fim na shigo

kenan, sai abin da Allah Ya yi,� inji ta.Fim: Wato shiga sojan Badakkare

kenan?Fatima: �E, ko da na daina fim ina da

bu}atar in zama furodusa amma ba zaniya daina harkar fim ba.�

Fim: A cikin �yan fim kina da saurayi?Fatima: �Gaskiya babu, ni wa ma na

sani? Ban san kowa ba!(dariya) Babu.Ni ina da wanda nake so da aure.�

Fim: Wane ne?Fatima: Wannan dai sirri ne (dariya).

Wannan tsakanina da shi ne da Allahkawai.�

Fim: Shi ma ]an wasa ne?Fatima: �A�a.�Fim: Ma�akacin gwamnati ne kenan?Fatima: �Wannan na ce ma sirri ne

(dariya) da na san�� (dariya) ka fiyeson jin magana!�

A cewar Fatima, ita dai ba ta san ana

yi mata lakabi da sunan �a kori Wasila�ba. Ta ce, �Ban ta~a ji ba ma.�

To yaya za ta gwada basirarta da taWasila Isma�il a fim?

Fatima ta amsa: �Haba, ya za ka ha]ani da Wasila! Ita na zo na same ta ne;mutum ya da]e yana yin abu sannankai da ka zo daga baya ka ce za kakwatanta kanka da shi?�

An tambaye ta a tsakanin Adali daWasila 3 wanne ya fi burge ta? Ta ceduk da yake dai ba ta kalli Wasila 3 ba(domin a lokacin hirarmu da ita fim ]inbai fito ba) amma Adali ya fi burge ta.

A }arshe, da Fim ta tambaye ta ta fa]adaga cikin furodusoshin Hausa wanefurodusa ya fi burge ta, sai FatimaIbrahim ta yi dariya, ta ba mu amsar damuke tsammanin za ta ba mu. �E, to zaa ce na yi son kai, duk suna burge ni,amma ba kamar Yakubu Lere,� inji ta.

Fati tare da Ahmed Nuhu ... lokacin daukar shirin Wasila 3 a Kaduna

66

Page 59: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA

LA{ANIN Sulaiman GamboAwaisu �Tupac.� Yaro ne matashi.Idan za a bayyana sigar Tupac,

wanda ya ce shi ]an wasan }wallon }afane, to za a yi masa adalci in aka ce agaskiya bai yi kama da ]an wasankwaikwaiyo ba, koda yake �yan wasaba wata kama suka tara ba. Baya gawannan, la}abinsa (watau Tupac) yanuna cewa yaron ya shafi masu sha�awarhalayyar �yan rawar �hip hop� naAmerika. Duk da cewa Sulaiman ya fito a cikinwa]ansu finafinai kamar Mujadala,[an Halak, Duniya, Laila da Karamci,haka bai sanya jama�a sun san shi ba.Ko da an san Sulaiman ma, to a bisadukkan alamu sanin shanu aka yi masa.Amma fim ]in da ya fito da yaron asarari shi ne Alaqa, wanda kamfanin�Sarari Ventures� da ke Kano ya shirya.Wani abin burgewa shi ne, ko kafin asaki fim ]in a kasuwa jarumin ya somacin kasuwarsa. Ma�ana ya yi suna, ansan shi. To bare da fim ]in ya fito. Lokacin da aka je birnin Dikko(Katsina) domin nuna Alaqa, Sulaimanya shaida wa mujallar Fim cewa a gidansinima na Rex dole sai da aka kulle shicikin wani ]aki saboda yawan jama�arda ke son ganinsa. Sulaiman ya gama karatun sakandarene a �G.S.S. Gwammaja II� cikin birninKano a cikin 1998, koda yake da masai da ya yi karatunsa na firamare a�Masa}a Primary School�. Bayankaratun zamani, ya ta~o na addini a�Qulumiddin Islamiyya� da ke {o}i. Bai da]e da shiga harkar fim ba,domin shekaru biyu kacal ya yi a ciki.Kafin ya shiga finafinai kuwa, Tupactu}in mota ya yi, watau �]an Hayis ne�.Tu}in mota sana�a ce, haka nan harkarfim ita ma sana�a ce. Bisa dukkan alamu,Sulaiman ya yi amfani da karin maganarda Hausawa ke cewa, da mai bara damai tashe duk tsaba suke nema. Sai yabar tu}i ya koma shirin fim. Kila kumadubawa ya yi sai ya bi shawarar masucewa inda fata ta fi taushi can ake maida

Ko rawar da ya taka a shirin Alaqa za ta sa yadage don yin zarrar da ake zaton zai iya har

ya shiga sahun gwanayen wasa? jima. Sulaiman ba shigar-sharo ya yi waharkar fim ba. Sai da ya koma tamkar}wai, inda }ungiyar wasan kwaikwayota �Dabo Films� ta yi kwancinsa, kumata }yan}yashe shi, kafin ya fara harkarfim. [an wasan ya shaida wa Fim cewasai da ya shwarci iyayensa, kuma sukaamince. Matashin dai tun bai yi nisa cikinharkar ba har ya fara waiwaye. Ganincewa ya fara samun masoya, Tupac yayi kira ga masoyansa su fahimci cewaabin da aka ba ]an wasa ya yi a cikinfim ba gaske ba ne, shiri ne. Sabodahaka su daina ]aukar ba}in jini ko}iyayya suna ]ora wa ]an wasa idan yayi abin da bai kwanta masu a rai ba acikin fim. Sulaiman Tupac yaro ne, bai farasoyayya ba. Haka dai ya fa]a. Sai daikuma a cikin Alaqa ya karantar damatasa yadda ake soyayya tare dayarinya Zulai Iliyasu. Shin ko za su ]orekamar su Ali da su Fati ko Abida? Kozai iya kutsawa cikin sahun su AminuAsid? Sai an gwada ake gane gwani!

Sulaiman Gambo Awaisu tare da Zulai Iliyasu a cikin shirin Alaqa

Sulaiman Gambo Awaisu

67

Page 60: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

K WARANKWATSAidanun wani furodusasun yi ja jawur kwanan

nan. Furodusan yana ganin yaisa ya isa ya sa a yi ko a bari afagen shirya finafinai na Hausa,kuma �yan fim suna ]aukarsa da}ima saboda suna zaton ya fikowa sani a fagen.

Rannan yana zaune a gidansaa birni mai duwatsu, yana kallonlabaran NTA na }asa da }arfe 9na dare. Matarsa ta yi tafiya.Kwatsam, abin kamar wal}iya,sai ya ga an nuno matarsa cikinagogon gayu. Ankwa! An ha]ahannunta da na wani abokinaikinta an kulle, ga kuma jami�antsaro nan na biye da su.

Wata}ila da ya ]auka fim neyake kallo duk cewa kafin ta tafiAbuja inda aka kama ta akagar}ame, ta sanar da shi cewa zata je kashe wata wuta wadda wani

ya kunno masu a lokacin da ya yi}ararsu ga kwamitin hana cinhanci da rashawa na gwamnatintarayya saboda sun tauye masaha}}insa a ma�aikatar da sukeaiki tare. Ita wannan mata daibabbar akanta ce a ma�aikatar; saida sa hannunta ma ku]i ke fita.Da]in da]awa ma, ita wannanmatar �yar wasa ce domin ta yiwani fim wanda yake gab dafitowa.

�Oga� bai tabbatar wa da kansafim yake kallo ba ko kuma dagaske ne, sai da aka nuno ofishinda suka shiga suka nemi bai wamai kar~ar takardun }arar cinhancin naira ]ai-]ai-]ai harN350,000.00 domin su janyetakardar }arar. Ita wannan �yarwasa cif-akanta, an nuno ta tareda abokan aikinta tana ]auke dairin ]irkekiyar jakar nan da akekira �Ghana must go,� ta zazzage

ku]in a kan teburin mai kar~ar}ara. Taf]ijam!

Da ma can tun kafin su kawoku]in sun zo an yi ciniki. Bayansun tafi sun gaya masa ranar daza su kawo ku]in, sai shi kumaya sanar da jami�an tsaro daogansa da kuma NTA, aka zo akadaddasa kyamarorin talbijin acikin ofishin. Ya}i ]an zambakenan! Ba su sani ba, suka zo damasu-gida-rana ]in, ana]aukarsu a ~oye. Sai da aka gamakomai sannan aka nuna musukyamarorin. [aya daga cikinsuya sa hannu a ka ya ruga}ar}ashin tebur, wai kadamutanen cocinsu su gan shi ya jikunya. An ce wani ma sai dafitsari ya kucce masa. Da ma ance akwai ranar }in dillanci, randa rigar maigari ta ~ata a hannundillali!

Shi ko oga furodusa, cikinsa

Assha, ranar }in dillanci ta zo!ya ka]a. A daren bai yi barci ba.Ban da u}ubar da madam tashiga, wani abu da ya dame shishi ne an ce yawancin ku]in dayake samu ta hanyarta ne. Waiidan za a ba da kwangila ama�aikatar, sai ta ba da sunankamfanin da ita da �oga� sukejagoranta. Ribar tasu ce.

A yanzu kam, sakamakon abinda ya faru a Abuja, komai yatsaya. Hukuma ta sa an jema�aikatar da mai walda an yiwaldar }ofofin shiga har sai angama bincike. Ya zuwa lokacinda nake yin wannan rubutun,mai]akin oga furodusa tana cana gar}ame a hannun hukuma, cikina ta }ugi. Shi kuma oga, ni aganina gaba ta kai shi � gobararTiti; domin ya sami abin rubutawaya shirya fim da shi, wato irin�true life story� ]in nan.

Allah ya kiyashe mu!

Ashe nazari na sa a fasa da~e da }eya?

WATA{ILA hangennasarar da yake samune a gidajen sinima da

nazarin nawa zai ci gaba da samua sauran sinimu (tunda duksinimar da aka nuna fim ]in nasasai an nemi a sake nunawa), dakuma nazarin yawan kwalayenda yake tunanin zai sayar, gamida nasarar da aka samu a fim ]inNazari nan gaba ko ba za a samuba; ya kamata ya dun}ulema}udan ku]a]e ya zuba a cikinfim ]insa na gaba ko kuma yasake nazari... ya sa ya shafa�a.Yana cikin wa]annan tunane-tunane ne ya shiga ]akin cinabinci da shi da abokansa.

Ina yi muku maganarfurodusan fim ]in Nazari ne,Yusuf Khalid. Bai ankara ba a]akin cin abincin, bayan ya zaunaa wata kujera yana jiran abincinda ya yi oda, sai kwatsam kujerar

da yake zaune a kai ta lan}washe,ya tintsere ya fa]i da }eya; an cesai da ginin gidan ya girgiza,sannan kuma }eyarsa sai da takusa farfasa da~en simintingidan. Amma wata}ila nauyi yayi wa kujerar, tunda a gaskiyashi yake ba ba}on ri}e ku]i ba

ne. Kwanakin nan Nazari ya samasu kallon finafinai a sinimasuna nazarin aljihunsu domin yafara zama fankam-fayam.

Furodusa Yusuf Khalid, a yinazarin abin da za a kashe wafim na gaba kuma a samu}wa}}waran fim, ba don komai

ba ma illa saboda sunan da ka sawa fim ]in � Dafa�i � wandafassararsa ta yi kama da�

Kada kuma a zo ana hawa kankujera ana fa]uwa da }eya.Saboda gigita wannan karon ankashe ku]i ba su dawo ba. Mazaa yi nazari!

68

Dillalan kaset sarakan ya}i!BABU shakka, masu shirya

finafinan Hausa suna}amfar labarai a yanzu. Ina nufin}wa}walwarsu ta fara toshewa,da }yar suke iya }ago labari sabogal; shi ya sa a kullum na kallifim sai in ga ya yi kama da wanida na kalla jiya. Abin ban haushinma shi ne sai ka ga labarin ma nawani fim ]in Indiya ko Amerikako Canis ne kawai aka kwafo,

aka mai da shi na Hausa. Donhaka ne duk dabarar da aka yi saika ga wani abu wanda ya sa~awa al�adun Hausa.

To ina furodusoshi? Ga labarizan ba ku. Ina so waninku yashirya fim a kan ta}addamar data faru a tsakaninku da dillalankaset na Kano. A nuna yaddafurodusoshi suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da

}in }arin ku]in jaket ]in kaset,har suka tursasa wa wasu dillalansuka rattaba hannu a takardaryarjejeniya. Mu �yan kallo za muso mu ga yadda a }arshe dillalanne suka yi nasara a kan ku, dominduk bayan zare idon da kuka yi,ku]in kwali ya tsaya a kan N45kacal, maimakon N50. Idan kuka}i yin fim ]in, to wani dillali yayi, tunda su ma furodusoshi ne.

Page 61: Mujallar FIM - July 2001

FIM, YULI 2001

A cikin wannan watan...

ZA A YI ABIN TARIHI

sabuwar mujallar

ZA TA FITO!

Mujalla ce mai ba da bayanai a kan finafinai tsagwaronsu. Ta }unshi abubuwa kamar:

* yadda ake shirya fim* yadda aka shirya wani fim wanda kuka sani* yadda aka yi wani abin mamaki a cikin fim

* yadda wani al�amari ya faru a wurin shirya wani fim* bayanai a kan finafinan da ba su fito ba

* sharhi a kan finafinan da suka fito* yin jagora ga mai kallo zuwa ga irin finafinan da suka dace ya kalla

kai, da dai sauran abubuwa da suka shafi harkar fim na Hausa ko na wani yare daban.

Wa]anda suka shirya wannan mujallar ba �sabon yanka rake� ba ne. Sun san aikin. Sun san harkar.Sun san masu harkar. Sun kuma san yadda ake yin mujalla, domin sun karanto yadda ake yin ta,

sannan sun sha yin ta.

DON HAKA KADA KA YARDA A BA KA LABARI

Mujallar BIDIYO ... za ta fito nan da �yan kwanaki ka]an!