3 · web viewa wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu yahaya, yana kira ne mu...

24
3 KALMAR ALLAH (Rhema) – Hurtatcen Kalma (Na ruhamiya) HANYOYI’ DABAM-DABAM DA UBANGIJI KAN MORA WAJEN SADARWA. Ubangiji yana marmari ya bayyana kansa a gare mu ta kowace hanya. Yesu yana so ya zama mana hanya, gaskiya da kuma rai (Yahaya 14:16). Yana nuna mana hanyar da zamu yi tafiya tawurin kalmar sa (Lagos). “Maganar ka (kalma) fitila ce ga sawaye na” (Zabura ta 119:109). Yana kuma jogoran mu, ta wurin shawarar magabatan mu a ikkilisiya (Misalai 11:14). Wani halin da mutum ya tarar da kan sa ciki, kan iya zamar masa jagora a rayuwa (misalin Yunana). Yesu ya zama mana gaskiya ta wurin fayyace mana littafi, yana bishe zuwa mu cikin gaskiya, kuma yana ja mana gora ta wurin bamu salama ko kuma masa mana a cikin ruhun mu. Muna iya samun jagora ta mafarki da ruya ko budi ta ruhu. (Ayy. Manzanni 16:9) BADA MA’ANAR KALMA (Logos) DA KALMA (Rhema) Wata hanyar da Yesu ya zama mana rai, shi ne ta wurin maganar da yake fada mana kai-tsaye, cikin zuciyar mu. Littafi Mai-Tsarki yana maganar yadda zamu ji muryar Ubangiji a cikin zuciyar mu. A cikin wannan babi, za mu dubi wannan al’amarin. A cikin Yahaya 6:63, Yesu ya ce, “kalmomin da na fada muku Ruhu ne da kuma Rai”. Watakila, ko wannen mu, ya dandana nunfashi rai yayin da kalmar Ubangiji ya shigo zuciyar mu, yana jagoran mu da karfafa mu kuma. Akwai kalmomi biyu a helenanci da aka juya su kamar haka “kalma” (Lagos da rhema). Kalma yana iya zama Logos ko rhema, ya danganta ne kan; ko kana son ka nanata wani abu ko ka nuna yadda ka karbi sakon. In ka yi amfani da kalma (Logos) ka nuna kana nanata abinda sakon ya nuna. Amfani da kalma rhema kuma yana nuna yadda kana nanata yadda ka karbi sakon (misali, ta maganar da aka fada maka) takamamme. MISALI DAGA CIKIN LITTAFI MAI-TSARKI A aya ta shida da ta takwas na Yahaya sura goma sha bakwai, Yesu yayi magana akan kalma daya a ayoyin biyu.

Upload: others

Post on 11-Mar-2020

1 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

3KALMAR ALLAH (Rhema) – Hurtatcen Kalma (Na ruhamiya)

HANYOYI’ DABAM-DABAM DA UBANGIJI KAN MORA WAJEN SADARWA.Ubangiji yana marmari ya bayyana kansa a gare mu ta kowace hanya. Yesu yana so ya zama mana hanya, gaskiya da kuma rai (Yahaya 14:16). Yana nuna mana hanyar da zamu yi tafiya tawurin kalmar sa (Lagos).

“Maganar ka (kalma) fitila ce ga sawaye na” (Zabura ta 119:109). Yana kuma jogoran mu, ta wurin shawarar magabatan mu a ikkilisiya (Misalai 11:14). Wani halin da mutum ya tarar da kan sa ciki, kan iya zamar masa jagora a rayuwa (misalin Yunana). Yesu ya zama mana gaskiya ta wurin fayyace mana littafi, yana bishe zuwa mu cikin gaskiya, kuma yana ja mana gora ta wurin bamu salama ko kuma masa mana a cikin ruhun mu. Muna iya samun jagora ta mafarki da ruya ko budi ta ruhu. (Ayy. Manzanni 16:9)

BADA MA’ANAR KALMA (Logos) DA KALMA (Rhema)Wata hanyar da Yesu ya zama mana rai, shi ne ta wurin maganar da yake fada mana kai-tsaye, cikin zuciyar mu. Littafi Mai-Tsarki yana maganar yadda zamu ji muryar Ubangiji a cikin zuciyar mu. A cikin wannan babi, za mu dubi wannan al’amarin. A cikin Yahaya 6:63, Yesu ya ce, “kalmomin da na fada muku Ruhu ne da kuma Rai”. Watakila, ko wannen mu, ya dandana nunfashi rai yayin da kalmar Ubangiji ya shigo zuciyar mu, yana jagoran mu da karfafa mu kuma.

Akwai kalmomi biyu a helenanci da aka juya su kamar haka “kalma” (Lagos da rhema). Kalma yana iya zama Logos ko rhema, ya danganta ne kan; ko kana son ka nanata wani abu ko ka nuna yadda ka karbi sakon. In ka yi amfani da kalma (Logos) ka nuna kana nanata abinda sakon ya nuna. Amfani da kalma rhema kuma yana nuna yadda kana nanata yadda ka karbi sakon (misali, ta maganar da aka fada maka) takamamme.

MISALI DAGA CIKIN LITTAFI MAI-TSARKI A aya ta shida da ta takwas na Yahaya sura goma sha bakwai, Yesu yayi magana akan kalma daya a ayoyin biyu. A aya ta shida, ana nuna abinda sakon ya kunsa, domin haka wannan kalma (Logos) aka mora a Helenanci. A aya ta takwas kuma, domin kana nuna abinda aka fada maka ne, Ubangiji a cikin zuciyar mu. A cikin wannan babi, zamu dubi wanan al’amari sai ya sama kalmar rhema kenan aka mora a Helenanci.

DUKA KALMOMIN, BIYU WATO LOGOS (kalma) DA RHEMA (kalma)Idan aka dauki Littafi Mai-Tsarki kamar wani littafi da ya kunshi maganar, ko kalma Allah a ciki, to ana iya cewa kalma (Logos) ne. Amma idan aka dauka kamar hurarren nassi ta ruya daga Ubangiji Allah, to ana iya cewa, kalma Rhema kenan. Idan Ubangiji ya fada mani wani nassi, ya zo mani a masayin takamamman kalma (rhema) kenan. In kuwa Ubangiji ya nuna mani wani nassi cikin Littafi-Mai-Tsarki, sai in dauke shi a masayin kalma logos. A ainihi, nassi ya zo a masayin kalma rhema ga wadanda suka rubuta, hurarre, takamamme kuma 2 Bitrus 1:21. Amma tundda nassin ya kunshi maganar Ubangiji ne a cikin Littafi, yana iya zama logos ma. Ruhu Mai-Tsarki yana kara mana saurin fahimtar nassosi, cikin Littafi mai-Tsarki, don haka, nassin ya zama kalma (rhema) kamar yadda yake ga ainihi wadanda suka rubuta shi tun ainihi. In muka tsaya

Page 2: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

muna ta tunani wato tsokaci akan kalma (rhema), wato anihi kalmar da Ubangiji ya fada mana kenan, to sai hakan ya mayar da kalma (rhema) ya zama (logos) kalma, tunda an fi bada karfi kan yadda kalman ya zo fiye da abinda ya kunsa. Sai ya zama kalmar rhema kenan aka mora a Helenanci.Duka kalman nan wato Logos da Rhema.

Muna Bukatan Kalma rhema da kalma logos Abinda ke cikin Littafi mai-Tsarki wato kalma (logos), ya wajaba akan mu domin cikin sa muke auna kowace “gaskiya”. Shi ne yake kare mu daga aikata kuskure, muddin rayuwar mu, kuma, shi ne yake bayyana mana yadda za mu yi dukan komai.Kalma (rhema) ma wajibi ne akan mu, domin yana karfafa yadda aka karbi sakon cikin Littafi mai-Tsarki tun farko – ta kowanne mutumin da ya sadu da Allah Ubangiji yana karfafa cewa, gaskiya tun dama Ubangiji yayi magana kuma har wa yau, yana magana da ya’yan sa. Muna bukatan mu ga yadda Littafi mai-Tsarki ya zama mana abin-koyi, don ya nuna mana yadda mutane suke ma’ammala da Ubangiji halitan su. In har Littafi mai-Tsarki ya fada mana wani abu daga farawa zuwa wahayin Yahaya, to, yana fada mana ne cewa, Ubangiji yana da marmari ya rika sadawa da yayan sa, sai mu sa ran jin murya da ganin ruya ko budi ta ruhun sa a cikin rayuwar mu. Dama, ina rayuwa na ne kawai, ba manufa kafin in sadu da Ubangiji. Yanzu da na sadu da Ubangiji, ina rayuwa na bisa fadin kalmar sa da kuma ruya ko budi ta ruhun sa a cikin zuciya ta. Ba mu yin komai bisa ra’ayin kan mu, sai dai abinda muka ji, mu ka kuma ga Uba yana yi (Yahaya 5:19,20,30). Yesu kuma, kyakkyawan misali ne da zamu bi gurbin sa. Domin haka ne muke bukatan wadannan kalmomin duka biyu, wato kalma (Logos) da kalma (rhema). Yana yiwuwa, wannan zaman ya taimaka a fahimci wani abu.Na daya. Kalman da ya kunshi abinda ke cikin Na biyu. Kalma da Littafi mai-Tsarki. Kalma (Logos) Ubangiji ya fada wa

mutum takammae wato Kalma (rhema).

Page 3: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Kwakwalwa ke karatu kuma ana Yayin da nasa zuciya da Samun fahimatar Littafi mai- kwakwalwa ko funani na gaTsarki neman Ubangiji, Ruhun sa yana Magana da ni cikin zuciya na. Yana shaidar tunanin sa da Shiri ko shawarar sa a ciki na.

Karin Bayyani sakanin wadannan kalmomin biyu, wato kalma Logos da kalma rhemaKyakkyawan misali ne da zamu bi gurbin sa.Domin haka ne muke bukatan wadannan kalmomin, wato kalma (Logos) da kalma (rhema) yana yiwuwa, wannan zanen ya taimaka.

Na daya, kalma da ya kunshi abinda ke ciki wato (LOGOS) kalma.

An juya kalma Rhema “Abu” a cikin wadannan nasi uku Luka 1:15; Luka 2:19; Ayukan manzani 5:32

KARI AYOYIMatta 5:11 “suka kuma kaga muku kowace irin mugunta.”

Page 4: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Bazan iya juya da kalma Logos zuwa Rhema ba.

Na yi fadam da ban sani nasara ba, a kokari na domin in bambanta tsakanin kalma (Logos) da kalma (rhema). Na lura cewa a yawanci lokatai, ana amfani da kalma (Logos) kamar maganar da aka fada, wanda daman aka koyar da ni cewa shi din ne kalma (rhema). A karshe dai sai wata rana na lura cewa daga bayyanin ma, ba daidai ba ne, ba a taba amfani da kalma (rhema) kamar rubutatcen kalma ko magana ba”. Na binjiki wurare saba’in da aka yi amfani da kalma (rhema) a cikin sabon alkawari, sai na lura cewa ko sai daya ba a yi amfani da kalma (rhema) kamar rubutatcen kalma ba. Akwai wani abu muhimi game da kalma (rhema) daga baya ne na gane lokacin da nake nazarin Littafin da Dr. Font Shultz ya wallafa lokacin da yake kammala digiri din sa. Ya ce kalma (logos) ya kunshin dukan fannoni na sadarwa, daga lokacin da ake shirin shawaran abin da za a fada, zuwa tunanin yadda za a fada, har zuwa yadda za a yi furci ga wanda ake niyya ya ji. A fannin Rhema kuma, shi masamman “Furci ne” ko kuwa ainihi “bayyana abinda ka yi niyya”. Kana iya duba kowanne wurin da aka yi amfani da kalma (rhema) a sabon alkawari da kan ka, sa’annan ka lura da bambancin, da kan ka.Ga ayoyi: An juya shi “kalma (rhema) zuwa “kalmar da aka fada” a nassasi 54. Sune:

FAHIMTAR IKON KALMA (Rhema): “Magana ko kalmar da aka fada”

Sune:- Matiyu 4:4 Matiyu 12:36Matiyu 18:16 Matiyu 26:75Matiyu 27:14 Markus 14:72Luka 1:38 Luka 2:29

Luka 3:2 Luka 4:4Luka 5:5 Luka 20:26Luka 24:8 Luka 24:11Yahaya 3:34 Yahaya 5:47Yahaya 6:63 Yah. 6:68Yahaya 8:20 Yah. 8:47Yahaya 10:21 Yah. 12:47Yahaya 12:48 Yahaya 14:40Yahaya 15:7 Yahaya 17:8Ayyukan Manzanni 2:4 Ayy. Man 5:20Ayyukan Manzanni 6:11 Ayy. Man 6:13Ayyukan Manzanni 10:22 Ayy. Manz. 10:37Ayy. Man. 10:44 Ayy. Man. 11:14Ayy. Manz. 11:16 Ayy. Manz. 13:42Ayy. Man. 16:38 Ayy. Man. 26:25Ayy. Man. 28:25 Romawa 10:8 (2)Romawa 10:17 Romawa 10:182 Korintiyawa 12:4 2 Korintiyawa 13:1Afisawa 5:26 Afisawa 6:17Ibraniyawa 1:3 Ibraniyawa 6:5Ibraniyawa 11:3 Ibraniyawa 12:19

Page 5: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

1 Bitrus 1:25 (2) 2 Bitrus 3:2Yahuza 17 Wahayi Yahaya 17:17

Haka ma aka juya kalma (Rhema) zuwa “fadi ko ce” a wadannan nassosi guda 8:Markus 9:32 Luka 1:65Luka 2:17 Luka 2:50Luka 2:51 Lukja 9:45 (2)Luka 7:1 Luka 18:34Haka kuma aka juya shi wato kalma (rhema) zuwa “abu” a nasosi uku:Luka 2:15, Luka 2:19, Ayy. Manz. 5:32

Ga karin ayoyi:----- “aka kaga ko fadi kowace irin mugunta (kowacce irin mugunta kalma (rhema) a kanku” - - Matiyu 5:11 da kuma Luka 1:37: Babu wata fadar Ubangiji (wata fadar) da ba zata cika ba”

Juyar da kalma (logos) zuwa (Rhema)Ba zan iya juya kalma (logos) zuwa kalma (rhema) ba. Yana yiwuwa ne ta wurin motsawar ko gushiwar Ruhu mai-Tsarki. Amma, ina iya mayar da hankali na akan magana ko kalma da Ruhu, ta haka ina bawa kaina dama kenan domin in ji abinda Ubangiji zai fada mini. Ina iya karbar ruya ko budi ta ruhu kai-akai yayin da na juya ga kalma ko maganar Allah.Ubangiji yana marmarin yayi magana ta wurin kalma (logos), yana son yayi mana wahayi ko budi ta Ruhun sa, ya bude idanun zuciyan mu (Afisawa 1:17,18), ya sa zuciyar mu ta kuna (Luka 24). Yana marmarin kalma (logos) din, mu juya shi ya zama wani budi a zuciyar mu, ya kuma bamu tabbaci yayin da muke addu’a cikin kalmar, Ruhu kuma ya sa shi ya zauna a cikin zuciyar mu.Ta yaya kalma (logos) zai zama kalma (Rhema) mai iza bangaskiyar mu? Ta yaya kuma zan sa hakan ya faru nan da nan? Da farko dai, in bude, in kuma cika idon zuciya da kunne da tabawa da shinshina da dandano duka na zuciya da kalma (logos). Wannan yana bawa Ubangiji Allah cikakken dama domin ya bayyana ruya ko wahayi a cikin zuciyar mu. Wadannan matakan ne suka sa ni akan hanya domin in iya karbar sako ko ruya daga wurin Ubangiji Allah.

Kunnen zuciya na – Ina mayar da hankali na kacukan akan maganar Ubangiji Allah, yayin da na fara karatun Littafi mai-Tsarki. Sai in sa kunne, domin in ji abinda zai fada mini a cikin kalmar sa da nake karantawa.

Idanun zuciya na sai in tsarkake lissafin zuciya na da nufin Uba ya aka idanun zuciya na da budi ta ruhu akan abinda nake karantawa a cikin Littafi mai-Tsarki.Tunanin zuciya na – sai kullum in sa maganar da Ubangiji ya fada mini da budi ta ruhu da na karba a cikin zuciya na. Ko kadan ba zan bar taraddadin rayuwa ko yawan ayyuka ko shakka ko dai wani abu ya dauke binbinin da nake yi akan maganar Ubangiji a cikin zuciya na ba.Yardar zuciyar ta – Na dauka a zuciya ta cewa ba zan fadi komai ba face kalmomi da budi ko wahayin da na karba a yayin da nake nazarin Littafi na mai-Tsarki. Sosan rai (emotions) a zuciya na – wannan kan auku ne, aukuwar kuwa ya danganta ga irin ababan da suka cike wadancan gabobin zuciya na, na ruhu, sai ya iza ni yin abin. Ina jin salama da tabbaci, yayin da Ruhu yake tabbatar da shaidar sa da karfi a cikin zuciya na.

Page 6: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Yayin da nake cike gabobin jiki na nan biyar cikin addu’a da kalma (logos), na bawa Allah cikakken dama kenan domin Ubangiji ya motsa a cikin zuciya na har yayi mini budi ta Ruhu ko ruya. Zanen da ke gaba yana tabbatar da wannan gaskiyar. Ka rubuta ayoyin da aka bayar akan kowanne layin da aka zana. Ka lura da Romawa 10:17: “Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa (akoe) jawabin da ake ji kuma ta maganar (rhema) Kirisdti”.

Kalman nan Akoe da Helenanci ne, yana nufin “a saurari wani,” ya shiga kunnuwa [daga fihirisar (concordance) Abingdon Strongs Exhaustive]” concordance.Shi ya sa, zaka tarar an rubuta Romawa 10:17 a wata juyin da aka kara bayyani kamar haka.

Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, wato ta wurin sauraro cikin zumunci da Ruhu mai-Tsarki, sa’annan kowace kalmar da yake furtawa na shiga kunnuwa na. Littafin nan “The Masters thesis” “A comparative study of Logos and Rhema” wanda Dr. Font Shultz ya wallafa, ana iya odar sa daga communion with God Ministries. Zai kara bayyani game da wannan darasi.

AIKIN DA KALMA (RHEMA) KE YIKalma (rhema) kalma ne wanda Ubangiji Allah da kansa ya furta, (Mu duba Ishaya 55:11) yana kuma cimma burin sa.

To, haka maganar da na fada take, ba ta kasa cika abinda na shirye mata, za ta yi kowane abinda na aike ta ta yi (Ishaya 55:11).

Littafi mai-Tsarki gaba dayan sa kalma (Logos) ne kalma (rhema) kiwa kalma ne wanda Ubangiji da bakin sa ya furta domin wata bukata a daidai lokaci. Muna bukatan mu fahimta, mu kuma dandana kalma (rhema) haka ma kalma (Logos). An yi amfani da kalma (rhema) ye da san sabain a cikin sabon alkawaari. An yi amfani da su a wadannan ayoyin, ka lura ka kuma rubuta kafin aikin su bisa tunannin ka, a kan kalma (rhema)1. Bada amfani:

Siman Biturus ya amsa yace masa, Ubangiji dukan dare muka yi wahala, bamu sami komai ba: amma bisa majanar (rhema) ka sai in jefa tarori (Luka 5:5).

2. Fa’idar bishara:

Page 7: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Domin wanda Allah ya aiko, zantafukan (rhema) Allah yake fada, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba (Yahaya 3:34)

3. Rai:Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam baya amfani kome, kalmomin (rhema) da nake fada muku rai ne da kuma Ruhu (Yahaya 6:63)

Juyar da kalma (Logos) zuwa kalma (rhema)

4. Dangantaka:Wanda shike na Allah, yana ji maganar (rhema): Allah: abinda ya sa ba ku ji ba kenan domin ku ba na Allah bane (Yahaya 8:47)

Page 8: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Da suka kasa yarda a junan su, kafin su watse sai Bitrus ya yi musa magana daya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu mai-Tsarki daidai ya fada, da ya yi wa kakanniku magana ta bakin Annabi Ishaya cewa,

Je ka wurin jama’an nan, ka ce, za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba ko kadan, za ku gasni kuma, amma ba za ku gane ba ko kadan, don zuciyar jama’an nan ta yi kanta, sun toshe kunnuwan su, sun kuma runtse idannun su, wai don kada su gani da idanun su, sukuma ji da kunnuwan su, su kuma fahimta a zuciyar su, har su juyo gare ni, in warkar da su. To, sai ku sani wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al’ummai, su kam za su saurara. (Ayyukan Manzanni 28:25-28)

5. Koyarwa cikin iko:Wato ba ka gaskata ba, cikin Uba nake, Uba kuma a cikin na? Maganar da nake fada muku, ba domin kaina nake fada ba, Uba na ne da ke zaune cikina yake yin ayyukan sa (Yahaya 14:10)

6. Mu cika da marmari:In kun zauna a cikina, magana kuma ta zauna a cikin ku, za ku roki duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku (Yahaya 15:7).

7. Bangaskiya:Ashe, bangaskiya ta wurin jarabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta maganar (rhema) Almasihu yake. (Romawa 10:17)

Abinda za a iya canza shi da furtatcen muryar Ubangiji Allah – dokokin Allah.A yawancin lokatai, kamar mutane sun fi son jerin dokoki fiye da zummunci cikin kauna. Da shike Allah ya halice mu da wasu halaye, sai ina ganin mutane sun gwammaci rayuwa cikin dokoki domin, suna tsammani zasu fi samun tsaro da kariya fiye da raya zumunci.

Lokacin da Ubangiji yake neman ya sami zumunta da jam’aar Israita, yayi magana da su kai-tsaye daga kan dutse, sai ku ka zaba a tsara musu dokoki. (Maimaitawar Sharia 5:22-31) ka karanta shi yanzu.

Ubangiji ya fada wa mutane Israila, cewa ba zai fasa magana da su ba. Zai ci gaba da zumunta da musa, ta maganan da zai yi da shi, jama’a sami dokokin da zasu bi. An kara doka doka har yayi yawa akan mutanen.

Marubucin Ibraniyawa yayi maganan a Ibraniyawa 12:18-29. Ka karanta shi yanzu. A cikin aya ta so jin karar muryar sa ba. Aya ta 22 da 23 ya ce, mu ma mu zo kan dutse mai tsarki, wato dutsen sihiyona. A aya ta 25 kuma an bamu kashedi, “ku kula fa kada ku ki mai magana nan”Don me? Domin in mun ki, za mu juya wa dangantaka da Ubangiji baya kenan wanda shi ne Kiristanci, sai kuma mu koma karkashi shairia kamar mutane tsohon alkawari. Kamar Musa, sai fasstocin mu, su rika ji daga Ubangiji, sa’annan su bamu dokokin da za su sarrafa rayuwar mu. Da bakin ciki, idan bamu bada kanmu ga Ruhu mai-Tsarki a cikin zuciyan mu, muna zumunta da shi ba. A maimakon haka sai a zabiu rayuwa bisa tsarin sharia na sabon alkawari har mu zama tamkar farisiyawa.

Page 9: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Duk wanda ya taba gwada irin wannan rayuwar kamar ni zai tarar cewa yana da wahala. Karikiyar sai ta yi nauyi, maimakon ya zama da sauki kamar yadda Yesu ya alkawarta. Yayin da mutum yake girma kamar Kirista, dokoki ma sai karuwa har su fi karfin mutum, a karshe dai sai a bar mutum da zabin daina girma, ko kuma fasa kiristancin gaba-daga. A zamanin Yesu, farisiyawa suna da dokoki 613 da suka lankaya wa jama’ar Isra’ila. Yesu kuwa ya sauta musu.Na tarar cewa yayin da wutar Allah na tashi, yana cinye dukan abinda ya kamata, yana kuma girgiza ko’ina, abin da ke karfafa rai sosai a irin wannan lokaci, shine muryar sa a cikin zuciyar mu. Yana tanada mu – wato shi Ubangiji.Domin haka, mu ma kanar jam’ar Isra’ila, muna da zabi ko mu saurari Ubangiji, yana magana da mu, mu kasance cikin zumunci da shi, ko mu kaga wa kanmu dokokin sabon alkawari. Na yi imani, zai fi kyau mu koyi gane muryar Ubangiji, mu rayuwa cikin sa, domin kada zumunci mu da Ubangiji ya koma addini.

Yadda Ake Gane Kalma (Rhema)Watakila babu wata tambayar da ta fi damun Kiristan yamma kamar: “Ta yaya zan iya gane muryar Ubangiji a cikin zuciya na? Zamu yi kokarin bada amsa.A shekaru da dama, hakka ba a cimma ruwa ba a yayin da na ke korin in ji muryar Ubangiji a ckin zuciya na, sai tunani kawai ba iyaka. Ban iya jin wata murya ba. Wannan ita ce takaicin Kirista da yawa. Ta yay zan iya cewa “Ubangiji yace” bayan ban iya gane muryar sa sarai ba? Sai Ubangiji ya fara tsada ni da mutane ni da mutanen da suka dace, sai na tarar cewa ashe deman, an bar a baya domin kwasam sai ga budi ta ruhu da fahimta a rayuwa ta.Kalma (rhema) ko kuwa murya Ubangiji, sadarwa ne na Ruhu zuwa ruhu – Ruhu mai-Tsarki tare da hadin kan ruhun ka, sai ya yi magana da kai a zuciyar ka.

ANA GANE KALMA (RHEMA) KAMAR:TUNANI DA KE TA ZUWA MAKA CIKIN ZUCIYA, KO SHAWAR KO WATA KALMA KO BUDI TA RUHU KO YADDA KAKE JI A JIKIN KA.

Tunani dga zuciya na, suna a lissafe.Tunani daga zuciya na, zuwa kawai suke.Binbinin Littafi mai-Tsarki ya kunshi lissafi da yayi ta zuwa don kansa.

Tunannin da ke ta zuwa zuci – muryar duniyar Ruhu Goyon Bayan Littafi mai-Tsarki.1. Ba dukan tunani ne namu tunanin ba game makaman yakin mu, ba na jiki bane,

amma masu iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu karfi muna ka da masu hujjoji cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna komo da kowane stunani cikin bauta ga biyayya da Kiristi ---- (2 Korintiyawa 10:4-5) an kora bayyani.Don me zamu bautar da wasu tunani ga biyayya? Domin sukan kasance daga shaidan ko aljannu ne? in haka ne, to muna ganin aga ina sauran tunanin ke fitowa? Daga Ruhu mai-Tsarki, deman. To, sai mu ankara da cewar, da yawa daga cikin tunin zuciyan mu, ba na kan mu ba ne. wannan dabarar, da ban mamaki yake! Da ina ganin kamar tunanin zuciya na, kamar ra’ayin kaina ne, amma a gaskiya, Littafi mai-

Page 10: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

tsarki ya nuna a fili cewar, ba haka ba ne. Tunanin, suna zuwa ne daga duniyar ruhu. Don haka, wani ne ke cika ni. Ni kayan aiki ne, reshe kuma da ba a dase ba. Ba na komai don na, wani ne yake aikin sa ta gare ni. Nekan mance har in ga kamar ni ne naka yi, bayan Ubangiji ya nuna a sarari cewar, ba ni nake raye ba amma Kiristi ke raye a cikin na (Gal. 2:20).

Don haka na yarda cewa, tunanin da ke zuwa zuciya na, wadanda ban yi nazarin su ba, ba kuma daga tunaninaba. Su kan zo ne ko daga birnin zuciya na, ko dai wani mugun ruhu ne ke kokarin ba ni shawara. Akwai hanyoyi dayawa da mutum zai gwada ko tunanin da ke zuwa zuciyar sa, ta kansa ce ko ta Ruhu mai-Tsarki da ke hade da nasa a cikin zuciyar sa, ko dai mugun ruhu da ke gaba da shi. Akwai wata babi musamman akan wannan. Amma, a yanzu ga wasu gwaje-gwaje ko ma’auni sauki da na ka amfani da su yanzu. Ka jera jerin tunanin da ke shigowa zuciyar ka, a karkashin suman:- Shaidan da na Ruhu mai-Tsarki. A cikin Littafi mai-Tsarki, sunan mutum kan nuna halin sa

Shaidan Ruhu Mai-TsarkiMai karar yan’uwa Mai gini ko inganta waniMagabci Mai ta’aziyaMakaryaci MallamiMai hallakarwa MahalliciMai kayarwa Mai kaunaBarawo Mai warkarwaMai kisan kai mai bada rai

Kowane tunanin da yake da nasaba da abinda aka jera a hagu, na lakaba wa shaidan. Haka kuma, kowane tunani da yake da nasaba da abin nan da aka jera ta hannun dama, na lakaba shi wa Ruhu mai-Tsarki.

Daidai ne, a kowane lokaci, a gwada ko a auna dukan tunani, da abin da Littafi mai-Tsarki ya ce.Haka kuma kowane abinda ya shiga zuciyar ka har ka rubuta, to, ka mika shi ga jagoran ka domin ya tabbatar da shi, ko daga Allah ne.

A karshe dai, wannan akidar da na gano wato “maganar Allah da ke shigowa cikina ko ilhami, yadda mutum kan ji a jikin sa (insuitive floor), yakan auku ne ta budi ta ruhu ko ruyar da na gani”. Don haka nakan tambayi kai na, ko a lokacin, na kwallafa tunani na da rai na akan Yesu, yayin da wannan ilhamin ke aukura ? in haka ne, nakan tarar cewar kashi 95 na lokacin, daga wurin Ubangiji ne. Dole mu yarda cewar, yana yiwuwa a yi kusuri, hakan daidai ne. Muna iya godiya, har mu yi dariya, sa’annan mu dauki darasi akan kuskurin. (Afisawa 5:20)Mu kara duban goyon baya, daga Littafi mai-Tsarki kan wannan al’amari a wato tunanin da ke zuwa zuciyar mutum, murya ne daga duniyar ruhu.

2. Naba – Annabi kenan da kalmar yahudanci. Naba, ma’anar kalmar da yahudanci shi

ne “ayi annabci” wato kamar wani abinda “ke bulbulowa” Don haka, yayin da annabi zai shiga aiki, kai-tsaye, sai ya mayar da hankalin ga abin nan da ke bulbulowa daga cikin sa, wato zai maida hankali kan tunanin da ke zuwa cikin zuciyar sa wanda ya yi imani, ya kuma gane cewa muryar Ubangiji ne daga cikin sa.

Page 11: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

A yi la’akari da banbancin da ke tsakann annabacin gaskiya da ta karya, a wannan zanan da ka gaba.

3. Paga – dandanon da kan auku ba tare da wata shiri ba. Da yahudanci, mutumin da ya ke tsayawa, yayi addu’a ko roko domin wasu, kalmar shi ne paga, ma’ana, farat daya, “ba tare da shiri ba”, a “shiga roko domin wani ko wasu”. Misalin irin wannan yana samuwa a Farawa 28:1. Ka karanta shi yanzu. Yayin da Yakubu ke cikin tafiya, ba shiri sai ya shiga cikin irin wannan addua” (paga) a wata wuri har ya kwana a wurin.In aka tara ma’anar paga ta zahiri da yin roko domin wani ko wasu, sai a tarar cewar mun zon kan misalin nan na Littafi mai-Tsarki wanda sananne ya kowa wato sadarwa tsanin Ruhu da ruhu. Ko ka tuna, ka taba ji a ranka cewar, kana jin yin addu’a domin wani? Wannan ba tunanin ka ba ne, ya zo ne kawai shi din ne (paga) wato dandanon da kan auku ba shiri ba tsammani. Wannan shi ne ainihin dandano na hurtatcen kalmar (rhema) Allah, muryar Ubangiji da kan shiga zuciyar mu, ba “tsammani ko shiri”, ba domin an yi niyya ba kamar yadda aka sani, amma haka kawai sai ya shiga zuciyar mu. Shiri ne daga Ubangiji, ya tsanya a zuciyar mu, sai tunanin mu ya dauka.

4. Mabulbular – Ruhu mai-Tsarki da ke zuciyar mai bada – gaskiya (Kirista).A ranar karshe ta idan, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya daga murya ya ce, “Duk mai jin kishin ruwa ya zo gare ni ya sha. Duk mai gaskatawa dan:, kamar yadda Nassi ya ce ‘Daga zuciyar sa ne kogunan ruwan rai za su gudana. To, awannan shi ne ya fada game da Ruhu mai-Tsarki, wanda masu gaskatawa da shi za su karba, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba saboda ba a daukaka Yesu ba tukuna. (Yah. 7:37-39)

Yanzu an rigaye an daukaka Yesu, Ruhun kuma an bayar Yesu ya ce zai zama kamar koguna a cikin mu. Don haka, idan mun sa zuciyar kan wannan mabulbular da ke cikin mu, mu na kama tashan Ruhu mai-Tsarki kenan da kae cikin mu. Wannan, ba ilimin tauhidi ba ne. ainihin dandano ne. akwai kogi a cikin, mu na iya kama tashar sa. Wannan bulbulowar da ba da karfin mu ba ne, shi ne Ruhu mai-Tsarki. Yana da sauki ko wajen yaro karami. Na fadi haka ne saboda mu gane, domin Yesu ya ce, sai mun kaskantar da kan mu kamar kenanan yara kafin mu shiga cikin mulkin Allah. Idan Kiristanci yayi wa kanannan yara wuya, to ya yiwu ba daidai ake yin sa ba.

ANNABCI NA GASKIYA DA NA KARYA

Wasu Goyon baya1. Dandana wasu dabaru da kan bugo nan da nan.

Daga ina wadan nan dabarun ke fitowa? Na tabbata mukan sami kan mu cikin wasu matsalolin da hikimar mu kan gaza, sai nantake, ka ji wata dabarar mafita ta bullo. Daga ina kake tsammani ya fito? Daga gwanintar ka? Ko hikimar mahalicin ka da ke raye a cikin ka? Na yi imani wannan hikimar madaukaki Allah

Page 12: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Ne da ke bullowa daga zuciyar mutum. Ba na kara yaba wa kaina kan irin wannan basira mai kaifi. Daukakan ta koma ga Ubangiji, wanda ke raye a cikin na.

2. dana wayo, da kan jawo wahala ko hallaka. Daga ina irin wannan kan. Kunno kai, ba wai kana nazari ko tunanin yadda zaka yi ba, amma kawai, sai ka ji wayo ya kunno kai da karfin gaske? Na tabbata wayon nan daga mugun nan ne mai hallakarwa, wanda yake cucusa mana mugun ra’ayi ko tunani. Don haka, ba na karbar laifi kan irin wannan hali, haka kuma bana yabon kai na kan wata basira da Allah ya bani. Wani ne kawai yake ayyukan sa ta gare ni, yabo, ga Ruhu mai-Tsarki, alhaki kuma na wuyan shaidan.

3. Shaida kan “rayuwa bayan Mutuwa”- yadda aka tarar. A Littafan da aka wallafa akan “rayuwa bayan mutuwa” yadda aka tarar, mun sani wani kwakkwarar shaida, akan abin da sadarwa tsakanin Ruhu da ruhu ya kunsa. Sun fadi yadda, sun ga Yesu ko mala’iku na magana; ko da shike, ba su ji wata murya karara ba, amma, nan da nan sukan ji a ran su abinda aka fada. Cikin ruhun su, suka karbi wannan sako ba tare da wahala ba, sadarwa tsakanin Ruhu da ruhu ko kuma kalma (rhema) ke nan.

4. Misali daga halitta:Sau dayawa ubangiji yajan bayyana mana wasu abubuwa zahiri, na

ruhaniya a dunniyar mu, wanda hakan ya sa duniyar tske cike da daukakar sa. Abin ban-sha’awa ne, idan aka yi la’akari da kogin urdun da ya bi ta kasar isra’ilaa, daga kasa kawai yafara bubbugowa har ya zama wannan babban kogi mai tarhi kamar yadda ruhun mai-tsarki yake bubbugowa daga cikin mu, har ya bayyana al’ajibin ubangiji, haka ma kogin urdun yana bubbugowa daya tumbin kasa har ya zama kogi a ckin dukan kasan.

Wasu halayen da kan nuna Allah ya dauki gurbin tumanin mu, zuwwwa cikin zuwyan mu.

Suna kamar tunanin mu ne ko zulumi, sai dai zaka gane daga birnin zuciyar ka ne a maimakom kwalaralwar ka, ba lissafin yaadda za yi baile kumma nazari.

Su kan zo da dauki kamar yadda ubangiji ke magana ta mutumin farko. A hankali cikin sanaki, kuma abu kadan ke yanke su (misali wani tunani ko son

rai da dai sauran su). Suna dauke da abinda ba a saba ba, ga hilcima gare su, cike da kauna da son

cimma buri fiye da tunanin mutum. Su kan sa mutum ya ji wani iri a jikin sa, kamar sa ka zumudi, da al’ajibi da

bangaskiya ,ya tabbatar maka da wani abu. Idan aka rumgume su, sukan ba wa mutumkarfi ko su iza mutum yin abu, su

kuma sa karfi dadin yin abin. Kana iya horar da tafarkin ruhaniyar ka, da sauki kuma kullum ka dandawa

maganar ubangiji ta wannan hanya. Ka tuna : ubangiji yana magana da kai kullum, kuma ka kanji tunanin da ya ke

tsanyawa a cikin zuciyar sai ka fara bambanta su, don kada kayi kuskurin ganin kamar duka tunanin ka ne. A kokarin koyon rabe muryar sa, kana koyon rabe tunanin sa kai ka ke yi a tunanin ka.

Ga wa zamu yi addu’a ?

Page 13: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

An sha tambaya ta ni kuma na roki ubangiji, ga wa zamu yi addu’a. Ga Allah uba, ko ga Allah Uba, ko ga Allah Da, wato Yesu? Ta wurin aikin Ruhu mai-Tsarki ko bishewar sa, mu ke addu’a ga Uba ta wurin Dan wato Yesu. Don haka, addu’ar mu tas shafi Tirniti wato Allah Uba da Da da Ruhu mai- Tsarki.A wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya shafi hira da shi wanda idan ina neman ruya ko budi ta ruhu, in sadu da Allah Uba ,Yesu ne kamanin da kan bayyana (kol.1:15). Na tarar cewar idan ina addu’a cikin iko, nakan fuskanci uba ne, idan kuma ina kafazumunci ne na kusa, sai in yi da Yesu. A farawa ko sujada, sai in nemin Ruhu mai-Tsarki ya bayyana kasmcewar sa a tsakanin mu.Na roki ubangiiji game da wannan, kuma ya tabbatar mini kyautuwar rokon sa ta bishewarRuhu mai-tsarki a cikin Yesu kuma. Ya kara da cewa, da shike uku cikin daya ne, zai ji,ya kuma amsa idan nayi magana da yesu.Balle ma Yesu yana fadan abinda ya ji uba yake fada ne (Yah.5: 19,20).In zamu yi la’akari da 1Yah. 1:3 da 2 Kol. 13: 14,littafi mai-Tsarki ya ce, mu ns iya zumunci da uban da Dan da kuma Ruhu mai-Tsarki.

Hakika kuwa zumunci ko tarayyar nantamu da uba ne, da kuma dan sa Yesu Almasihu (Yah. 1;3)Bari alherin ubangiji mu Yesu kristi da kaunar Allah Uba, Ya kaasace tare da ku tawurin zumuntan Ruhu mai-Tsarki (2 Kor.13:14, an yi kari daga wata juyi)

Don haka, nayi imani tarayya ko zumuncin mu, yana iya kasance da Uba da Da da Ruhu mai-Tsarki kuma.

YIN ADDU’A DA WATA GUMAKA A CIKIN ZUCIYAWannan sashe akan yin addu’a wata gumaka a cikin zuciya, zai tanada maka wani gagarumin basirra, kan yadda zaka tsabtace kotsarkake daukan rihoton huldr ka da ubangiji. Mabudin, ko kuwa asirin shine ka san inda ka kwallafa ranka a lokacin da kake addu’a . Mu ya la’akari da wannan.

Wanda ya manne wa gumaka, ya sa abin tuntube a gabansa sa’an nan kuma ya zo wurin annabi, ni ubangiji zan saka masa gwaqrgwadon yawan gumakan sa (Ezekiyel 14:4).

Wannan ya kawo mu ga abin ban zarana game da hanyar yin addu’a mara cancanta, abin tsoro,ga shi kuwa mutane da yawa suna yi . Sai in zama hadaya karbabbe, yayin da na 30 gaban ubangiji cikin addu’a. Nufin kwana ya kar, saudai in mika kai ga nufin Allah game da abinda nake addu’a akan sa.In wannan ba shi ne halina ba, sai in roki ubangiji ya canja ni, Ya tsaanya wannan Ruhun a ciki na so’annan in fara yin addu’a game da bukatu na. Idan ina da wata boyayyar dabaka a cikn zuciya ta, sa’annan ina nema fuskan ubangiji cikin addu’a, wannandabara ko hanya” nawan, zai iya kawo rudani har in ga kamar Allah ne ke amsa addu’a ta, ko da ma ba shi bane.Ko kuwa na sa rai akan damuwa ko bukata fiye da dogaro ga Allah, a maimakon Ubangiji ya amsa sai damuwar ta ce ga dabara. In kuwa dogaro ga Allah ya mamaye tunani na fiye da bukatar da nake addu’a akai, amsa kuwa zata zo daga

Page 14: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

wurin Ubangiji kuma zai zama budi ta ruhu ce ta gaskiya, tunani na ba zai gurbace shi ba.

Ka’idar shine, ilhami ko yadda mukan ji a ran mu, yana fitowa ne daga budi ta Ruhu ko ruyar da nake gani da idon zuciya na. Shi ya sa an umurta mu kwallafa rai ko mu sa dogaron mu ga Yesu, shi da yake shugaba da mai kammala bangaskiyar mu. Ta haka, zai kasance ruya ko budi ta ruhu tsantsa.

Ana samun misalin wani mai duba da ya so yayi barna a cikin “Littafi Kidaya 22” mai suna Bal’amu. Balak ya aika wa Bal’amu, ya zo ya la’anta jama’ar Isra’ila. Da Bal’amu ya bidi Allah game da wannan bukatar, Allah ya fada masa a sarari “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa zaka la’anta su ba, gama masu albarka ne su. (Littafi Kidaya 22:12)Balak kuwa ya kara wata aika da kakkaurar murya, da cewar zai arzuka Bal’amu ya bashi duk abin da yake so, muddin zai zo ya la’anta jama’ar Isra’ila. Bisa dukan alamu dai, abinda ke zuciyar Bal’amu dai Ziaariya ne da tarin dukiya, domin ya ce “ko da a ce Balak zai bani gidansa cike da azurfa da Zinariya, ba zan yi wani abu ba kodan ----- (Littafin Kidaya 22:18)” Duk da haka, ya roka su dakata yana cewa “zan koma in tuntubi Allah kuma”. Tunda yana neman girma, zinariya da dukiya ruwa a jallo, ya sake komawa wurin Ubangiji cikin addu’a, a wannan karon da zuciya mara cancanta. Kamar yadda aka sa rai, Ubangiji ya bashi amsa daidai da gumakaar da ke zuciyar sa, ya ce “Hakika! Sai ka tafi” ko da shike, Ubangiji Allah yayi fushi da Bal’amu (Littafi Lissafi 22:22) sai Allah ya aika da mala’ikar sa da takobi ya tare shi akan hanyar sa.Akwai wasu misalai na jama’ar Isra’ila da suke addu’a da gumaka a zuciyar su, kuma sukan sami sakamakon da kan zama wahala a rayuwar su. Isra’ila, sun nema Ubangiji ya basu sarki, Ubangiji ba ya so hakan ba amma domin sun nace, sai ya basu. A jeji ma sun yi kwadayin nama, da suka nace, sai ya basu amma kuma taaare da wata cuta mai lalata neman (Zabura 106:14,15).

A karshe, idan mun yi addu’a da gumaka a zuciyan mu, Ubangiji zai iya amsa mana, amma zai iya ya jawo hallaka. Don haka, mu tabbata mun tsarkake hangan my yayin da muke addu’a, mu ga girma da isan Yesu kan bukatocin da mu ke addua kan su. Ta haka ne zamu sami amsa na kwarai mai bada rai kuma, zanen nan, yana kwatanta hayoyi na yin addu’a

ADDU’A DA WATA GUMAKA A ZUCIYA

Page 15: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

Ga Yadda Za Ka Yi Wannan da Kanka

Ka rubuta awata tambaya, wadda za ka so ka tambayi Ubangiji ko wace iri tambaya muddin ba abinda ke wahalar da kai a rayuwar ka ba. Irin wancan bukatun kan tada hankali; su nema su sha kanka su sha kanka har su hana ka kamewa ka yi shiru a gaban Ubangiji kamar yadda Littafi Mai-Tsarki ya koyar (Zabaru 46:10) – wannan gaskiya ne, ba ma kamar makoyi ba. Kana iya tambayar sa game da kaunr sa zura gareka, ko kan wata matsalar da ta addabe ka, ko ma gaskiyar da yake son ka fahimta a cikin wannan babi. Ka dan dauki lokaci, ka zabi tambayar ka sai ka rubuta shi yanzu.

Bayan ka rubuta tambayar, sai ka roki Ubangiji Yesu Ya bude idanu da kunnuwan zuciyan ka, domin ka karbi abinda yake son ya sanar da kai. Ka sa

Page 16: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya

hoton Yesu a zuciyar ka, ka sa shi a zaune kurkusa da kai a getan ka, ko kamaar kuna tafiya hannu da hannu a bakin kogin Urdun. Sai ka dubi fuskar sa, bayan ka mayar da kanka kamar karamin yaro kana rike da hannun sa. Ka daubi murna ko faaarin cikin sa domin wannan daman da aka samu. Babu wani abinda Yesu ya fi so a ran sa kamr wannan. Dubi doguwar rigar sa, takalmar da ke kaafafun sa. Sai ka shakaaata da dan murmushin a fuskar ka, kana wala kasancewar ku tare, yayin da kake zuba mar ido, sai ka yi maar tambayar da dazu ka ruba. Ka kama tashar abinda ka wakana da kyau, kana zuba maar ido, sai ka fara rubuta abinda yake tsanyawa a cikin zuciyar ka kada ka aunar da abinda ke cikin Littafi Mia-Tsarki yanzu, amma, idan bai zama asiri ba sai ka nuna wa jagoran ka domin a tabbatar da shi.

Page 17: 3 · Web viewA wani fannin kuma, sura ta goma sha biyar a bishara ta hannu Yahaya, Yana kira ne mu zama a cikin Kiristi, ko mu rayu a cikin sa. Na tarar cewarayuwa a cikin Yesu ya