a new way - text hausa - joyce meyer ministries · 2017. 7. 21. · babi na biyu. 10 sabuwar hanyar...

46

Upload: others

Post on 21-Feb-2021

6 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)
Page 2: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

SABUWAR HANYAR RAYUWA

Fahimtar Me Ake Nufi da Karban Kristi

P.O. Box 5, Cape Town, 8000

Page 3: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

Unless otherwise indicated, all Scripture quotations are taken from THE AMPLIFIED BIBLE: Old Testament. Copyright © 1962,

1964 by Zondervan Publishing House (used by permission); THE KING JAMES VERSION; and from THE AMPLIFIED NEW TESTAMENT

Copyright © 1958 by the Lockman Foundation (used by permission).

Copyright © 2013 by Joyce Meyer Ministries – South Africa

All rights reserved. No part of this publication may be reproduced, distributed, or transmitted in any form or by any

means, or stored in a database or retrieval system, without the prior written permission of Joyce Meyer Ministries – South Africa.

Joyce Meyer Ministries – South AfricaPO Box 5, Cape Town, 8000

Phone: +27 (0) 21 701 1056Website: www.joycemeyer.org

A New Way of Living – HausaNot For Resale

Page 4: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

3

1. Ingantacciyrar Zabi A Rayuwa 5

2. Dukan Mu Mun Yi Zunubi 9

3. Yanzu Ne Lokacin Mika Kai 13

4. Sabuwar Hanyan Rayuwa 17

5. Tsarin Sabuwar Tunani 21

6. Sabuwar Hanyar Yin Magana 27

7. Sabuwar Hanyan Kallon Rayuwan Ka 31

8. Maye Gurbin Tsoro Da Bangaskiya 35

9. More Rayuwar Ka 39

Addu’arSamunCeto 42

ABIN DA KE CIKI

Page 5: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)
Page 6: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

5

Babi na Daya

INGANTACCIYRAR ZABI A RAYUWA

Ko kana da rashin gamsuwa da rayuwar da kake ciki? In haka ne, mutane da yawa suna cikin wanan hali, Jama`a da yawa suna cikin damuwa, bakin ciki da rashin gamsuwa. Wasu sun dogara ga addini da tsammanin cewa za su sami biyan bukata a halin da suke ciki,maimakonhaka,sukasamikansucikinhalinƙakanakayidadokokin da ba za su iya kiyayewa ba. Domin kana bin addini bai nunacewakadaukiAllahamatsayinwandazaifishekadagacikindukan damuwa da matsaloli ba.

In kana da bukatar kaji ana kaunar ka, in kana bukatar aboki, in kana son a yafe maka zunubanka, da kuma in kana son rayuwa mai kyau a gaba… Yesu Kristi kadai shine amsa. Yana nan a kofar zuciyar ka yana jira ka bude ya sabunta rayuwar ka ya kuma baka hutawa. In baka gamsu da rayuwar da kake ciki ba, to sai ka/ki canja rayuwar ka/ki. Idan mun ci gaba da rayuwar da muke ciki, za mu ci gaba da samun damuwowi da matsaloli. Sai ka/ki dauki mataki kumabamafiingantacciyarshawaradazakadaukaba.

Wananshawarwarinsunadamuhimmancifiyedashawarwarinhidimomin duniya game da rayuwa wurin tsai da shawara game da makaranta, aure, aiki, wurin zuba jari, da kuma wurin zama. Wannan shawara ce game da rayuwa na har abada. Rayuwa na har abada rayuwa ce wanda babu iyaka, kuma ko wanenmu ya kamata ya san indazaiƙarasa.Akwairayuwabayanmutuwa,idanka/kinmutu,ba

Page 7: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

6

SABUWAR HANYAR RAYUWA

wai ka/kin daina rayuwa bane, za ka/ki soma wata rayuwa a wani wurinadabam,anfadacewa,mutuwatanakamadawucewataƙofamai juyawa, za ka/ki bar wani wuri ne ka/ki bayyana a wani wuri dabam.

Ko kana so ka yi Dangantaka da Ubangiji a nan duniya ka kuma kasance tare da shi a aljanna? In haka ne, sai ka karbi yesu ya zama maicetonka,dukanmumunyizunubikumamunabuƘatanceto,AllahyaaikoƊansadominyashafezunubanmu.Akagicciyeshi,ya zub da jininsa mai tamani domin ya biya zunuban mu. Ya mutu, aka bisne shi, ya tashi a rana ta uku daga mutuwa, yanzu yana zaune a hanun dama na Allah uba shi ne kadai hanyar samun salama, da daidaituwa a wurin Allah.

Dominsamunkuɓutadagazunubanmu,littafimaitsarkiyanakoyar da mu da cewa dole sai mun furta, kuma mu shaida cewa yesu shine mai ceto kuma sai mun bada gaskiya a zuciyar mu cewa Allah ya tada shi daga matattu.

Gama idan ka shaida da bakin ka Yesu Ubangiji ne, ka kuma bada gaskiya cikin zuciyar ka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka tsira. -ROMAWA 10:9

Domin in ka amince ka kuma furta da bakin ka, cewa yesu shine maiceto,kabadagaskiyadazuciyarka(ɗafewa,badagaskiya,dakuma ka dangana ga gaskiya) a kan cewa Allah ne ya tada shi daga matattu, za ka samu tsira.

Irin wannan bangaskiya ya wuce sanin mutum, sahihiya ce, kwarai daga zuciya. Mutane dayawa sun bada gaskiya akwai Allah, amma basu sadaukar da rayuwan su zuwa gareshi ba. Allah shi ne mawallafin rayuwa, kuma yana so ka sadaukar masa rayuwarkahannu sake. Allah ya hallaceka ka zabi duk abin da kake so, ba zai tilasta maka ka zabe shiba. Amma ko ka bi tsarin sa ko ba ka bi ba, zai nuna a tsarin salon rayuwar da ka yi a nan duniya, kuma shine yake nuna alkiblar inda mutum zai je ya dawwama bayan ya bar duniya.

Ko ka yi kyakkyawar tanadi da gudanar da rayuwar ka? In ba haka ba, to me yasa ba za ka mika rayuwar ka zuwa ga mahallicin ka

Page 8: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

7

Ingantacciyrar Zabi A Rayuwa

ba, wanda ya yi ka kuma ya san komai game da rayuwar ka. Idan na sayi mota kuma ina ta samun damuwa da ita, sai in

komar da ita ga wadanda suka kera ta, domin su gyara ta. Haka yake ga Ubangiji, ya halice ka kuma yana kaunar ka matuka, idan ba ka gamsu da yadda ka ke gudanar da rayuwar ka ba, saboda rayuwar ka ta karkace, sai ka kai masa (Ubangiji) don ya gyaro ta. Kamar yadda na fada a baya, babu abin da zai canza in ba ka dauki mataki ba, kana so ka zama krista? Kana shirye domin ka mika kanka ga ubangiji ba wai zunuban ka kadai ba amma har da rayuwarka? Kana shirye domin ka bar irin rayuwar ka ta zunubi ka rungumi sabon tsarin rayuwa ta sadaukarwa da dangana ga Allah? In haka ne, ka cigabadakaratu;akwairayuwamaikyaudaingancifiyedayaddakake tsammani da ke jiran ka a gaba, wanan dama tana ga kowa, ba wanda aka bari. Wanan shine abin da Allah ya tanada wa rayuwar ka a nan gaba.

Gama na san irin tunanin da ni ke tunaninku da su, in ji Ubangiji,tunaninalafiya,banamasifaba,domininbakubege mai-kyau a karshe. -IRMIYA 29:11

Babu wanda zai yi maka zabi, zabi yana gare ka kuma kai kadai ke yin ta. Wanne irin rayuwa mai inganci kake so ka samu? Ko lallai ne kana so ka bi tsarin rayuwa irin da muke gani a cikin al`ummar mu a yau. Ubangiji Allah yace bamu zo duniya da komai ba, kuma bazamutafidakomaiba,(1Timatawus6:7)Allahshinefarkoshinekuma karshe, da farko akwai Allah, a karshe kuma zai kasance akwai Allah.KowazaitsayaagabanAllahyabadalisafinkansa.(Romawa14:12) yanzu ne lokacin yin shiri, a kullum na kan cewa, ko a shirye ko ba a shirye ba yesu zai dawo. Ka shirya yanzu, ka dau mataki yanzu, domin gobe ba naka ba.

Page 9: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)
Page 10: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

9

ZunubirashinbiyayyanegasanannennufinAllah.Dukanmumun yi zunubi. Babu wanda bai taba zunubi a duniya ba. (Romawa 3:23,MaiWa’azi7:20).Labarimaradadinkenan,ammaakwailabarimai dadi. Za a iya yafe mana kuma mu daidaita da Allah.

Tunda dukan mu mun yi zunubi kuma mun kasa ga daukaka da darajan da Allah yakan sa mana ya kuma karba.

(Dukanmu) ya nuna mana adalci kuma ya shirye mu tsayayyu da Allah, kyauta kuma tukwici ta wurin alherin sa. (Tagomashi da jinkan sa) ta wurin kubutarwa wanda ake samu a Isah Almasihu. -ROMAWA 3:23-24

Yesu ya rigaya ya biya zunuban ka; abin da ya kamata ka yi shi ne ka bada gaskiya ka kuma karbe shi. Idan zaka amince da zunuban ka, ka gane kuskuren ka, ka yarda ka juyo gaban Sa gaba daya, Allah Zai gafarce ka ya mai da kai sabon mutum.

Idanmun yarda da cewamun yi zunubi sa’an nanmunfurta zunuban mu, Shi mai aninci ne, mai gaskiya (gaskiya daga halitan sa kuma mai cika alkawallai) kuma zai yafe dukanzunubanmu.(fitaddahargitsaiarayuwanmu)yakuma (cigaba da) wanke mu daga dukan rashin adalci,

DUKAN MU MUN YI ZUNUBI

Babi na Biyu

Page 11: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

10

SABUWAR HANYAR RAYUWA

(Dukanabubuwandabasuamincedanufinsaba,tawurintunani da aikatawa.) -1 YOHANNA 1:9

Ba sai ka jira Allah yayi wani abu ba. Ya rigaya ya yi abin da ya kamata ya yi. Ya bada Ɗansa makaidaci ya mutu domin mu,dominsaidaihadayamaraaibinezaiiyabiyanlaifuffukandamukayi. Adalci ya biya bukata, za mu iya rayuwan yanci ta wurin bada gaskiya ga Yesu Kristi kuma ta wurin hulda da Ubangiji ta wurin Sa. Ba za mu iya zuwa wurin Allah da kan mu ba- muna neman lauya. Muna neman wanda zai tsaya a-tsakanin, kuma wannan mutum shine Yesu. Yesu ya tsaya a tsakanin mu da Allah, babban ramin da zunuban mu ya tona tsakanin mu da Allah, Yesu ya rufe ya kuma kawo mu ga Allah.

Kamar yadda yaro yana da yanayin baban a cikin sa (Jinin sa, kwayar hallita da sauran su) haka nan Allah yake cikin Yesu, yana kuma sulhunta duniya zuwa gareshi. Allah yana kaunar mutanen da ya hallita, ba zai so ya gan su su hallaka cikin bautar zunubi ba tare da nuna masu hanyar kubuta ba. Yesu shine hanya!

Zunubi Ya Kan Kawo La’ana

Kalmar Ubangiji tace zunubin mu zai tone mu (Kidaya 32:23). Zunubi ya kan kawo la’ana sa’anan biyayya yana kawo albarka.(Kubawar sharia 28) Za ya iya kasancewa mutum na jin dadin zunubi a rayuwan sa na dan lokaci. Rayuwan sa ta kasance da kyau Kamar kowa, amma a karshe dole a samu sakamakon shawaran da ya dauka a rayuwan sa.

Idan muka zabe rayuwan zunubi maimakon rayuwan biyayya gaAllah,zamusadudabala’iazukatanmu.Mutumyafijikindaaka yi da nama da kasussuwa. Shi ruhu ne kuma yana da kurwa wanda yana hade da tunani da tausayi. Yanayin mutum kenan. Masu zunubi sukan sha wuya a tunani, suna cike da tsananin wuya a tunani, yawan arziki da mallakan da suke da shi ba zai iya basu salama ba. Suna da bakin ciki kwarai da gaskiya. Tun da sun zaba su yi jagorancin rayuwan su da kansu, sai suka sami kansu a cikin mawuyacinhali,idanabubuwabasatafiyayaddasukeso.Basusan

Page 12: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

11

Dukan Mu Mun Yi Zunubi

hanyanbangaskiyaba.YardadaAllahmafigirmaabunemaiwuyagaresu. Basu da kwanciyar hankali ko kadan, domin samun kwanciyar hankali sai ta wurin bada gaskiya ga Allah kadai. (Ibraniyawa 4:3).

Haka nan, rayuwa cikin zunubi rayuwa ne wadda ke cike da la’anoni,babuabumaikyaudakefitowadagacikinta.GaabindaUbangiji ya ce game da wanda ke son yayi rayuwa ba tare da shi ba.

ZanjawowamutaneazabaharsaisunrudeKamarmakafidomin sun yi wa Ubangiji zunubi, za a zubas da jininsu kamar kura, naman su kuma kamar najasa. -ZAFANIYA 1:17-18

Wadan nan ayoyi suna da ban tsoro, amma bai kamata ya sa tsoro a zuciyar mai bin Isah Almasihu na kwarai ba. Wadan da sukabadagaskiyagaYesubazasufuskancishari’akohukunciba(Yohanna 3:18).

Tsoron Hukunci

Mai zunubi yana tare da tsoro kullayomi, za ya iya yin abubuwa dayawa, yayi Kamar bai san menene ke faruwa ba, amma a cikin zuciyar sa ya san rayuwan sa akwai damuwa. Yesu ya ce, masu zunubi baza su iya tsere wa alhaki ba. (Yohanna 9:41)

Littafimai tsarki an raba shi kashi biyu, TsohonAlkawali daSabon Alkawali. Tsohon Alkawali tana dauke da tsoffin alkawalaiwanda Allah yayi amfani da su don shafe zunuban mutane kamin Zuwan Isah Almasihu da sabon alkawali. Ta wurin ayyukan hadaya don shafe zunubai, zunuban mutane yakan sami rufuwa amma ba yakan kau da shi ba, tsoro da shakku yana nan har yanzu. Ko dayake, a cikin sabon Alkawali muna da tsayayyen hadaya wanda ba yakan rufe zunubi amma yakan cire shi gabaki daya. Ya kan wanke zunubi ya kuma cire tsoron da zunubi ke kawowa.

Ka karanta ayoyin nan a hankali ka kuma yin tunani akan abubuwan da suke cewa. Dukan su daga Ibraniyawa 10.

Bisagawannannufian tsarkakemu tawurinmika jinin

Page 13: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

12

SABUWAR HANYAR RAYUWA

Yesu Kristi so daya dungum. -IBRA. 10:10

Amma shi, sa’an daya mika hadaya guda daya dominzunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah. -IBRA. 10:12

Wannan shine alkawarin da zanyi dasu bayan wadannan kwanaki in ji Ubangiji in sa dokokina a bisa zuciyar su, a bisa hankalin su kuma in rubuta su, kana yace. -IBRA.10:16-17

Bari mu guso da zuciya mai gaskiya da sakankancewar bangaskiya, zukatanmu yayaffu ne dagamugun lamiri,jikunanmu wankakku ne da tsatsabtan ruwa. -IBRAN. 10:22

Wadan nan ayoyi suna ilimantar da mu akan abubuwa masu kyau da amfani kwarai. Na fari shine, Yesu ya zama mana hadaya na har abada, kuma babu wata hadaya da za a kara yi bayan sa. A tsohon alkawali akan yi hadaya akai akai, duk da haka basu iya cire tsoron da zunuban mutane ke kawowa ba. Yesu ya zama mana hadaya mai kyau na har abada kuma yakan cire/yafe zunubai da tsoron da yake biye da zunubi.

Tsoron an cire shi tabbas, amma mutum sai ya koya inda zai yi rayuwa ba tare da tunanin abubuwan da sun wuce ba. Sabon rayuwa cikin Yesu yana neman mu koya yadda zamu yi rayuwa dabam da na da. Baza ku bar tunani ya bi da rayuwar ku kuma ba. Dole ku koya daga Kalmar Ubangiji kuma ku yi biyyaya gare shi, koma yaya kuke ji. Wannan sabon hanyan rayuwa yakan kawo albarku wanda yafigabanmisali.

Page 14: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

13

MaiyiwuwanekarigayakakarbiyesuKristikumakabuƙaciwanan litafi domin ya yi maka jagora wajen tafiyar da sabuwarrayuwar ka a cikin Kristi, ko kuma ka rigaya ka yi shiri domin daukar wanan mataki a yanzu haka.

Yohana3:16gamaAllahyayikaunarduniyaharyabadaƊansahaifaffeshikadaidomindukanwandayabadagaskiyagareshikadaya lalace amma ya sami rai na har abada.

Bari in ba ka wani labarin da zai taimake ka ka gane hikimar da ke cikin wanan aya,

A cikin birnin Chicago, a wani dare mai tsananin sanyi, da bakin duhu,ansomaiskamaikarfi,waniɗanyaroyanasayardajaridaa bakin titi, sauran mutane suna ta kai da kawowa a cikin wanan sanyin,ammaɗanyaronnanyanajintsananinsanyiharbaidamudayasayardajaridannankokadanba,saiyanufiwurinwanidansandayace,malamkokasanindawaniɗanyaromaragalihuzaiiya samun wuri mai dumi da zai kare shi daga wanan tsananin sanyi har ya yi barci? Ka gani, na saba kwanciya ne a cikin wata yar kwali a wata yar lungu a can gefen hanya, amma yanzu ina jin sanyi sosai, kumazaiyikyaumutumyasamiwurimaiɗumidonyasamisa`ida.Saiɗansandannanyakalliyaronnanyacemasa,todai,zangayamaka inda za ka iya zuwa ka sami biyan bukata, ka je can kasa ta wannan layi, ka ga wancan farin gidan can, ka je ka kwankwasa

YANZU NE LOKACIN MIKA KAI

Babi na Uku

Page 15: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

14

SABUWAR HANYAR RAYUWA

masuƙofa,dazaransunfitokacemasuYohana3:16zasucekashigo.

Sai yaron nan ya yi yadda aka gaya masa, ya haura bisa matakalar dayakaishiharƙofargidan,yakumakwankwasaƙofargidan,saimatargidantafito,saiyakallisama,yacemataYoahana3:16,saitace masa ya shigo ciki.

Sai, ta sa shi ciki, ta bashi wurin zama mai lilo ya zauna, sai ta yitafiyarta,yanazaunenannadanwanilokaci,yacearansa,nidaikomeakenufidaYohana3:16ban gane ba amma na san yana iya maidaɗanyaromaijintsananinsanyiyasamidumi.

Bayan an jima kadan sai ta zo ta tambaye shi, kana jin yunwa ne? sai ya ce, ko da yake ina dan jin yunwa don na yi yan kwanaki bansamiabincinaciba,innasamiɗanabincizaitaimaka,saitakaishidakinabincitazaunardashi,tazubomasaabincimasudaɗida inganci iri-iri, ya yi ta ci har ya ishe shi yadda ba zai iya ci kuma ba. Sai ya ce a ran sa, Yohana 3:16, ni dai ban gane ta ba amma tana iya kosar da mai jin yunwa.

Sai matar ta haura da shi daki na bisa, inda ruwa mai dumi ke cike a cikin kwanon wanka da aka tanada mai yawa, ya shige ya yi wanka, ya shakata, sai ya ce a ran sa, Yohana 3:16 ni dai ban san ma`anar ta ba,amma tana mai da yaro mai datti ya zamo wankakke.

Sai ta zo ta dauke shi ta kai shi daki ta kwantar da shi a kan wani irin shimfida da aka kera shi da tsofaffin gashin tsuntsaye,ta lullubeshidamayafiharwuya, tasumbaceshi tayimasabankwana,takashefitilardakecikindakin,dayakekwancecikinduhu,sai ya hango waje ta cikin taga sai ya ga dusar kankara na zubowa daga sama a cikin wanan duhun dare mai tsananin sanyi, sai ya ce a ran sa, Yohana 3:16, ni dai ban san ma`anar ta ba amma tana iya mai da gajiyayye ya sami hutu.

Washe gari, ta sake kai shi dakin abincin nan mai abinci masu inganci iri-iri, ya ci ya koshi, ta kuma kai shi wurin kujeran nan mai lilo wanda ke kusa da hurarriyar wuta mai dumama daki, sai ta daukolitafimaitsarki,tazauna,saitacemasa,kokasanmeneneakenufidaYohana3:16?

Ya amsa ya ce a`a uwargida ban sani ba. Jiya ma na fara jin

Page 16: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

15

Yanzu Ne Lokacin Mika Kai

ta a wurin wani dan sanda da na nemi taimako a wurinsa kuma ya umarcenidainyiamfanidaita.Nantakesaitabudelittafindakehanun ta, ta yi mashi karatu daga Yohana 3:16, ta yi mashi wa`azi da fassara tana bashi bayanin Yesu, nan take a gaban hurarriyar wutan nan mai ba da dumi, ya bada zuciyar sa da rayuwar sa ga yesu, yana zaune wurin nan sai ya ce a ran sa, Yohana 3:16 ni dai ban san ma`anar ta ba amma tana mai da battacen da ya sami kwanciyar rai.(baasanmawallafinwananlabarinnanba).

Yanzu in kana shirye ka mika rayuwar ka ga Allah ta wurin karbandansayesuamatsayinshinehadayamafikarbabbedazaishafe zunuban ka ina karfafa ka ka yi wanan adu`a tare da ni, ka furtakalmominwananadu`adakarfiyafitosaraidayabayandayakana jin ta domin ka dauke ta da muhimmanci.

Allah uba, ina kaunar ka, na zo gare ka a yau cikin imani da bangaskiya, ina rokon ka, ka gafarta mani zunubaina, na gaskanta cewa na sami ceto, an sake haifuwa ta, ta biyu, kuma in na mutu zan shigaal-janna.Allahuba,zanjidadintafiyatakumazanyiAllahuba, ina kaunar ka, na zo gare ka yau a cikin bangaskiya, ina rokon ka, ka gafarta mani zunubai na, yesu na yi imani da kai, na yarda cewa ka mutu a kan giciye domina, ka zub da jinin ka mai tamani domina, ka dauke mani duk tsanani da azabar da zan sha sabili da zunubai na. na gaskanta ka mutu, an bisne ka, kuma ka tashi daga matattu a rana ta uku, mutuwa ta kasa rike ka, ka yi nasara a kan shaidan kuma ka kwace makulin jahannama da na mutuwa daga gare shi. Na bada gaskiya kayi haka ne saboda kauna ta kake yi, ina so in zama kirista, ina so in bauta maka har iyakar rayuwa ta. Ina so in koyi yadda zan gudanar da sabuwar rayuwar da ka alkawarta ma ni. Na karbe ka yanzu ya yesu, kuma na sallamar da kai na gareka, ka karbe ni a yadda na ke, ka kuma maishe ni yadda ka so in kasance.

Na gode maka da ka cece ni, ka cika ni da ruhun ka mai tsarki, ka koya mani duk abinda ya kamata in sani, yanzu, ga rayuwa ta bisa ga tsarin ka.

Idan har ka yi wanan adu`a da cikakkiyar imani da bangaskiya, tokatsaidashawaramafimuhimmancigarayuwarka,kodayayaka ke ji, Allah ya ji kumaya karbi adu`ar ka, kana iya jin farin ciki ko

Page 17: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

16

SABUWAR HANYAR RAYUWA

salama, yanci ko walwala, kana iya kasancewa ba ka jin komai, kada ka bar yadda kake ji ya zama maka mizani ko kadan nan gaba, ka tsaya a kan maganar Allah, gama shi mai tsayawa a kan alkawarin sa ne. ya ce Dukan abin da uba na yaba ni zai zo gare ni, wanda ya zo gare ni kuwa bani korin sa ba ko kadan. Yohana 6:37

Ubangiji ya yi alkawari zai kasance tare da kai kullayaumi har iyakar rayuwar ka, yana yiwuwa ba ka iya jin motsin sa kullum, amma yana nan ko ina a ko yaushe. Ya sa idanun sa a kan ka, kuma yanakuladakaisosai.Yadamudadukanal`amurandasukashafirayuwar ka, kuma yayi alkawari ya daidaita su, ubangiji ya soma kyakkyawar aiki a rayuwar ka, kuma zai karasa shi. (Farawa 15:27. Zabura 138:8. Filibiyawa 1:6)

Albishirin ka! Kana da aboki na kwarai-yesu- babban amini wanda ba za ka iya taba samu ba, kana iya gaya mashi komai a kan kowanne abu, saboda ya fahimci komai game da rayuwar ka a kullum. (Ibraniyawa 4:15) babu abin da ya yi mashi girma, haka kuma babu abin da ya yi mashi kankanta, ubangiji yana so ka saka shicikindukanal`amaridayashafirayuwarka,

Kazamosabuwarhalitta,dukantsofaffinal`amurasunshude,(2 Korintiyawa 5:17) za ka soma komai sabuwa.

Yana yiwuwa ne ka yi kuskure, dukan mu muna yin kuskure, kanatayinkoyikumakafaratafiyaakanturbamaikyauhartsawonrayuwar ka, ka dinga tunawa cewa kullum in ka yi kuskure ko ka kasa, gafara da tsarkakewa na ubangiji yana nan domin nema da kuma samuwa, a duk lokacin da ka kasa ka yi sauri ka tuba, kuma kada ka boye komai ga Allah domin yana sane da komai a ko yaushe.

Page 18: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

17

Sa’andakafarayinsabonrayuwacikinKristi,zakaganecewatana da bambanci sosai da rayuwa cikin jiki. A gaskiya, rayuwa cikin jiki ta na da matsaloli da dama amma rayuwa cikn Kristi tana tsaye ne daram. Mutane ba su saba da rayuwa cikin Kristi ba sabo da haka tana masu wuyan ganewa da fari.

Baftisma

Abu na fari da ya kamata ka yi a matsayin ka na mai bin Isa Almasihu shine ka sami yin baftisma mai tsarki. Baftisma alama ce wanda ke nuna wa da cewa ka karbi Yesu kristi ya zama mai ceton ka. Idan mutum ya sami yin baftisma mai tsarki yana nuna cewa mutumin nanyabinnetsohonrayuwandayayi.Ayayindakafitocikinruwantana nuna cewa rayuwar ka ta sami sakewa. Ana yin haka domin mu bi umurnin ubangiji. Ba a yin baftisma domin a cire datti na jiki ba, amma domin mutum ya sami sakewa ta wurin maimaitawar zumuncin mu da Allah. Baftisma na nuna cewa ka yarda da mutuwa da kuma tashin Isah Almasihu.

(Dai dai kuwa, bisa ga wannan misali, baftisma ke ceton ku yanzu ba zancenj kawas da kazamta ta jiki ba, amma addu’arkyakkyawan lamirizuwagaAllah, tawurin tashi

SABUWAR HANYAN RAYUWA

Babi na Hudu

Page 19: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

18

SABUWAR HANYAR RAYUWA

Yesu Kristi. -BITRUS 1 3:21

Sai Biturus ya ce musu, ku tuba, ayi wa kowanne daya daga cikin ku baftisma cikin sunan Yesu kristi zuwa gafarar zunuban ku; za ku karbi ruhu Mai tsarki kyauta kuma. -AYYUKAN MANZANNI 2:38

Zuwa Ekklisiya

Waniabumafimuhimmancishinezuwanmajami’a.Zuwamajami’akuwa bai nuna cewa mutum Krista ne ba amma idan mun kira kan mu Kristayakamatamuyisujadadayan’uwanmukristociamajami’a,domintawurinzuwanmajami’amutumyakankoyimaganarAllah.Ba dukan Ekklisiyoyi bane na kwarai, wasu kame kame ne, a waje su na nan fari fat amma a ciki suna nan baki kirin. Idan ka na sujada a majami’andabatakoyamakamaganarAllah,kasakelallai.

Yadda jebun likitoci sunyi yawa haka kuma masu kyau su na da yawa. Dole ne ka nemi masujada da za kayi girmar da bangaskiyar ka. Zuwan Ekklisiya yana da muhinmanci sossai domin kana iya samin Abokai da za ku karfafa bangaskiyar juna. Ka tabbata cewa a majami’andakakekanagirmacikinruhu,idanbahakaba,kanemimajami’andazakarikagirmacikinruhukullumyomi.Yanadamuhinmanci sabon mai bi ya koyi abubuwa da dama game da yadda bangaskiyarsa zata rika girma, idan ba haka ba, yana iya bijirewa ya kumakomaga tsohuwar hanyar da ya bari. Binciken littafidatambayoyi kan iya taimaka wa sabon mai bi. Binciken kuwa na iya kasancewa a gida, makaranta, wurin aiki ko kuma a cikin Ekklisiya.

Kuntatawa

Kuntatawa yana da muhimmanci sossai, ba abin da mu ka yi a baya bane ya samu a halin da muke ciki amma abubuwan da muke yi kullumyomi ne, rayuwan fadi tashi ba zai taimake mu ba. Dole ne mu yi abin da ya kamata ko a yayin da jikin mu ba ya so. Gama Allah baya ba mu ruhun tsoro ba amma ruhu na iko da na kauna

Page 20: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

19

Sabuwar Hanyan Rayuwa

da na horo. Timotawus 2 1:7, ka dauki lokaci domin ka duba daga maganan Allah kayi binbini cikin Kalmar Sa ka kuma dinga sayan takardu da kasetin da zaya karfafa bangaskiyar ka. Ka dauki lokaci dominyinaddu’akakumatunacewaAllahyanasonkasosaikumaaddu’aMagananeda ubangiji. Idan kayi addu’a zaka ji kana yinmagana da Allah. Kuma hakan kan sa rayuwar ka ta sami sakewa ta wurin Sa.

Sabuwar Hanyar Rayuwa

Wata hanya mai inganci game da kuntatawa shine bayaswa, Allah ya ba mu abubuwa da dama ya kuma zama dole ne mu ma mu bashi domin aikin sa ya sami yaduwa a cikin duniya. Idan wani ya taimake ka kai ma za kaji marmari ka taimaki wani. Kana iya taimaka wa aikin Allahtawurinbayaswaamajami’arkadakumawasukungiyoyindake shallar bishara ta Allah. Dukan wanda ya bayar domin aikin Allah, Allah kuwa zaya yi masa albarka kwarai da gaskiya. Gama Kalmar Allah ta ce abin da ka shuka shi za ka girba. Babu wuya kamin ka ba da ranka ga Allah bayaswa yana yi maka wuya amma ka so mutane suyi maka kyauta amma da ka sami ceto sai ka sami sakewa kwarai da gake.

Baftisma Cikin Ruhu Mai Tsarki

Baftismananufindulmuyawacikinruwa,dukanabindaakadulmuyacikin ruwa zaya sami cika idan baya da huji, a yayin da ka karbi Yesu ya zama mai ceton ka ka na cike ne da Ruhu mai tsarki amma kila ba’ashiryekakekabudezuciyarkaba.Ayayindakabudezuciyarka, Allah zai cika ka da Ruhu mai tsarki. Ubangiji yana so yayi amfani da kai wurin shelar bisharar sa kuma ka na bukatar iko da taimako dagawurinsaidankanasokacigaba.Ubangijiyakanbamukarfidaga samaniya dominmu sami karfin yin rayuwa a duniya. Allahkumayakanbamubaiwairiiriammanawasuyafiwasu.IdanAllahya bani baiwa na koyaswa wani baiwan sa na waka ne wani kuma na taimaka wa mutane. Akwai baye baye guda tara da aka lisafta a cikin litafin (Korintiyawa 1, 12:7-10) da ya kamata muna sane da

Page 21: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

20

SABUWAR HANYAR RAYUWA

su. (Amma ga kowane daya an bada bayanuwar Ruhu garin amfani. Gama an bada maganar hikima ga wani ta wurin Ruhu; ga wani kuma maganar ilimi, bisa ga wannan Ruhu daya: Ga wani kuma bangaskiya, cikin wannan Ruhu daya, ga wani kuma baye baye na warkaswa cikin wannan Ruhu daya; Ga wani ayyuka masu iko; ga wani annabci; ga wani rarrabewar Ruhohi: Ga wani harsuna iri iri; ga wani fasarar harsuna.)

Ko da ba za ka fahimci wannan baiwa (Kyauta) ba, ina karfafa ka ka roki Allah domin ya ba ka kuma ya koyar da kai a kan su da kuma amfanin su a rayuwar ka. Mun kalli bayanai da dama a cikin Kalmar Ubangiji, yadda mutane suka yi ta magana a wata harshe dabam(yaretaRuhaniya).Idanmunyiaddu’acikinharsuna,munafurta abubuwan da ke a boye (Asiri) kuma wan da ya gagare mutum yafahimtagaAllahsa’annanmunakarfafakanmune.AnnabiBulusya ce, ya so kowa yayi magana cikin harsuna (Korintiyawa 1 14:2, 4-5).

Baiwan Magana cikin harsuna ya zama abin rarrabuwa tsakanin Krista tun shekaru da dama da suka wuce. Wadansu sun ba da gaskiya cewa wannan baiwa don yau ne, wadansu kuma sun ce ba haka ba. Ni na karbi wannan baiwa a rayuwa ta kuma nayi Magana cikinwasuharsunafiyedashekarutalatinyanzu,sabodahakanasan da cewa tana da muhimmanci cikin rayuwan Krista a yau. Muna neman dukan abin da zai taimake mu.

So da dama mutane sukan ki abubuwan da ba su daba ba ko kuwa ba su gani ba. Wannan kuskure ne. Yana da kyau mu karanta littafimaitsarkimukumayardadaabindayakefadi.

Ina maku gargadi ku sa hankalin ku ga Ruhu mai tsarki da Kansa, amma ba a kyaututtukan Sa ba. Kyautan za su zo. Mutane dayawa sukannacewaMaganacikinharsunakokuwawayensukyautaifiyeda yadda ya kamata. Idan mu ka je mu sayi takalmi, baza mu je shagon sai mu tambayi harsuna ba amma sai mu tambayi takalmi domin takalmin yakan zo tare da harsuna. Hakan nan ne yake da Ruhu mai tsarki, ko wace rana ka neme shi don ya zo cikin rayuwar kasa’nnanMaganacikinharsunadawasukyautaidagaRuhumaitsarki za su zo a lokacin da ya kamata.

Page 22: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

21

TSARIN SABUWAR TUNANI

Yin koyi da sabuwar tasrin tunani,yana da muhimmanci, Allah yanadakyakyawarshirigamedarauyuwarka,ammasaikayitafiyaa kan tsari irin nashi. Haka kuma shaidan yana da nashi shiri game da rayuwar ka wanda ba shi da kyau sam-sam. Barawo (shaidan) ya zo ne domin ya yi, sata, kisa, kuma ya lalata dukan abubuwa masu kyau, (Yohana 10:10) Shaidan yana shuka mugayen tunani a zukatan mu, da fatan cewa za mu yi na`am da shi, mu karbe shi, ta haka yake rudin mutane ya kuma sami shiga rayuwar su.

Kada ku sake da tsarin rayuwa irin ta duniya, (zamani), wanda an tsara shine, a kan shagulgula da al`amura ko al`adu irin na duniya. sai dai ku dukufa ga tsarin rayuwa irin ta sabon salo wanda ake samuwa daga sabunta zuciyar ku gaba daya, domin ku tabbatar (wa kanku) da kuma tantance abin da kemai kyau kuma karɓabbe ga Allah.-ROMAWA 12:2

Wanan hadisi da ke bisa, yana tabbatar mana da cewa ba za mu iya canza rayuwar mu zuwa ga tafarki mai kyau ba sai mun canza tsarin tunanin mu. Idan kana son sabuwar rayuwa, to sai ka canza salon tunanin ka; tukuna. Allah yana da kyakkyawan shiri domin mu, amma za mu iya gane ya tabbata ne in mun fahimci fa`idan tsarin

Babi na Biyar

Page 23: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

22

SABUWAR HANYAR RAYUWA

tunani mai kyau.

Kana Iya Tsare Tunanin Ka

Watakila kana nan kamar yadda na ke a da, ka na tsammani ba za ka iya yin komai ba a kan yadda ka ke tunani, amma ba haka ya ke ba, kana iya zaban abin da za ka yi tunani a kai da kuma abin da ba za ka yi tunani a kai ba. Kuma sai ka sa hankali, duk inda zuciya ta bi nan mutum yake bi, dukan mu muna da sani a kan soma tunani a kan abin da za mu ci, watakila madara mai kankara, gurasa, ko kuma wasu naukin abinci masu sa kwadayi, da zaran mun kwal-lafa rai ga cin su, jarabar mu na samun cin su zata karu, har ta kai dole sai mun ci su, idan mu ka ci gaba da tunanin su, sai mun kai gashigamotamuyi tafiyarmildayawadominmusamesu.Candaga baya sai mu koma muna ta nadama a kan me yasa mu ka bata lokacin mu da kudin mu a kan wanan abu. In wani ya bata mana rai, kuma mu ka ci gaba da tunani a kan abin da ya yi mana da ya bata mana rai din, sai mu ji mun kai ga bacin rai da damuwa sosai, tu-nanin mu yana shafar lamirin mu har ya zama kalmomin da za mu furta da bakin mu.

A duk lokacin da kana cikin bacin rai ko damuwa, ka tambayi kan ka, ko a kan menene nake ta tunani ko bata rai? Za ka fahimci cewar tunanin ka yana da dangantaka da abin da ka ke ji.

Zuciyarmushinefilindagadamuke fafatayakidashaidan.(2 Korintiywa 10:4-5). yana koya mana cewa, dole ne mu kawar da mugayen tunanin mu, mu kuma danka su ga yesu Kristi. Hakan yana nufincewa tunaninmuya yi tafiyadaidaidamaganarAllah.Dukwani abinda ya ci karo da koyarwar yesu sai mu kawar da shi daga zuciyar mu, mu kuma ki, mu dauke shi a matsayin karya ne daga shaidan. Idan magabcin ka (Shaidan) yana iya iko da tunanin ka, to zai iya iko da rayuwar ka da kuma makomar ka.

Misali, idan kana tunanin ka kashe kan ka, ba ubangiji ne ya saka maka wanan tunani a zuciyar ka ba. Ubangiji yana so ka rayu, ka ji dadi ka kuma more rayuwar ka. Idan kana jin kai ba wani abu ba ne ko kuma babu wanda yake kaunar ka, to irin wadanan tunanin ba dagaubangijiyakeba,sabodabaitafidaidaidamaganarsaba.

Page 24: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

23

Tsarin Sabuwar Tunani

Tunani Mara Amfani

Ka yi hankali a kan ko wanne irin tunani mara amfani, babu wani abu mai rashin amfani game da kyakkyawar shiri da tanadi da Allahyayiwarayuwarka,zaifikyaukatarardagorarabicikedakatarar da ita rabi babu komai! Kasancewa mai sa rai cewa abubuwa za su yi kyau ba ya yin illa ga kowa, ko da yaya rayuwar ka ta kasance ya kamata ka kwallafa rai da hangen nesa da fatan cewa abubuwa game da rayuwar ka za su yi kyau nan gaba. Ka yi yarjejeniya da ubangiji ka kuma gasganta cewa abubuwa game da rayuwar ka za su yi kyau. Idan kai mutum ne mai tunani mara fa`ida kamar yadda na ke a da, yin tunani mai fa`ida zai dauke ka wani lokaci kamin ka iya yin ta. Na taso ne a wani yanayi da muhalli mara kyau wanda a kullum ina cikin tsananin masifa da bala`i. Amma na zo na gane cewa damuwoyin mu sukan zo ne saboda muna yin tunani mara fa`ida.

Dukan kwanakin masu shan wuya da cuta suke: amma mai farin zuciya yana da buki tuttur. -MISALAI 15:15

A lokacin da ruhu mai tsarki ya jawo ni ga karanta wanan aya, dafarkobansanmeneneakenufidaKalmar‘‘zullumi”ba,ammana gane cewa kalma ce wadda take nufin yanayi mai tsoratarwakuma mara kyau mai nuni da cewa abubuwa marasa kyau za su faru, kuma na kasance dukan abin da ke faruwa da ni masifa ce da bala’I,dominsunenaketsammani.Nayitabegenincanzarayuwata amma ban san don menene Allah ya ki canza mani rayuwata ba, saidagabayanaganecewakafinAllahyacanzarayuwata,sainasauya tunani na

Kada ka taba kau da fatan abubuwa za su yi kyau a kan ko wacce al’amuragamedarayuwarkananangabakomanada,rayuwarkada ta wuce ma tana iya ta daidaita da kyakyawar tanadi da ubangiji ya shirya game da kai idan ka yi imani da ubangiji, dukan kuskure da kasawa da kayi a baya tana iya sa ka ka zama ingantacen mutum maibasira,dominzakadaukidarasidala’akariakankuskurenkana baya ka kuma san yadda za ka kauce ma aikata su anan gaba.

Kadakayitunanimarama’anaakandukiyrka,koabokinka,

Page 25: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

24

SABUWAR HANYAR RAYUWA

iyalin ka, yadda ka ke, aikin da ka ke yi ko ba ka aiki, inda kake zama, motar da ka ke hawa, ko wani abu makamancin haka, ka kasance mai kwallafa rai ga hali mai kyau da fatan cewa komai zai yi kyau a rayuwar ka. Wanan shi ne abinda zai sa ka kafu ka kuma karfafa a rayuwa.

Kada Ka Yi Gaggawa Ko Damuwa

Damuwa da Gaggawa wasu nauyin tuinani ne guda biyu marasa kyau,damuwabayahaifardawaniabumaifa’ida,ammayanahaifarda abin da ke cutar da mutum, ka maye gurbin dukan damuwar ka da sa rai ga ubangiji domin ya biya maka bukata. Damuwa tana mai dakaikatsufafiyedashekarunka,damuwayakansakakayitaciwon kai, da ciwon ciki, har ma ya sa ka kasa yin kuzari, wanan ba abin da Allah ya tanada maka a rayuwa bane.

Kasancewa babu yin damuwa ba abu ne mai sauki ba, da farko dai,kasabayiwakankatanadidakumasamarwakankamafitaaduk yanayin da ka sami kanka, amma ka tuna, yanzu kana koyan sabuwar hanyar rayuwa.

Mutanen da ba su da hulda mai kyau da ubangiji dole ne su yi damuwa, amma banda kai, saboda ubangiji yana tare da kai, kuma ya ce, ka kawo mashi dukan damuwarka shi kuma zai biya maka bukatar su. (1 Bitrus 5:7).

Gaggawa tana nuna rayuwa a yau amma ana damuwa da gobe, Yesu ya ce kada mu yi haka,saboda gobe yana da nashi damuwa, (Matiyu 6:34), za ka san abin da za ka yi in lokacin yin shi ya yi, kuma ba za ka iya sani ba sai lokacin ya yi, Ubangiji yana so ka koyi yadda za ka dogara gare shi, shi ba ya yin gaggawa kuma ba ya yin jinkiri, ga sabon mai ba da gaskiya wanan jiran yana da wuya saboda ba ka saba da shi ba, amma bayan wani lokaci kadan, za ka fara jin dadin shi, zuciyar ka za ta sami salama kuma za ka kasance kana rayuwar ka kullum ba tare da damuwa da me zai faru gobe ba.

Duk lokacin da ka ji damuwa a ran ka, ka tunatar wa shaidan cewa kai da ne ga ubangiji kuma ya yi alkawari zai kula da kai.

Hanyar sabunta tunanin ka yana samuwa ne a cikin bincike da nazarin maganar Allah. Hanya ce kuma na fahimtar bambamcin

Page 26: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

25

da ke tsakanin tunani mai kyau da tunani mara kyau. Alal misali, mutumzaiyitunanincewazaikasancematalaucinesabodayafitodaga zuriyar da ba su da arziki, amma za ka gane a cikin maganar ubangiji, ba haka ya ke ba, da taimakon Allah, da kuma biyayya da umarnin sa ake samun arziki, za ka iya karya kangin talauci a kowace sashi na rayuwar ka har ka zama mai arziki da yalwa. Gama maganarubabangijitace,yanasokabunkasa,kasamilafiyarjiki,kamar yadda ran ka yake bunkasa. (3 Yohana 2) Kamar yadda kake girmaacikinruhu,kumakanatafiyacikinyinbiyayyadaubangiji,zai ba ka komai da ka ke bukata kuma ya tsare ka da dukiyar ka.

Allah zai biya maka dukan bukata, kuma ba za ka yi rayuwa cikin tsorokumaba, in aiki ka kenema, ka yi adu’a zai taimakamaka ka sami aiki, zai yi maka alfarma, zai albarkaci hannayen ka, duk abin da hanun ka ya taba zai bunkasa,

Yesu yana so ka ji dadin rayuwa, yana so ka mori rayuwan da ya mutu domin ka samu, ka sami ilimi, ka sami fahimta, ka sami basira da hikima, gama saboda rashin ilimi mutane kan lalace, ka neme ta, Yesu Kristi shine hikimar mu daga wurin Allah, (1 Korintiyawa 1:30) ka roke shi ya sa hikimar da ke cikin ka ya taso, ya bude maka hankali,dominkayitafiyaakantafarkinsa,“Gamahikimatafilu’ulu’aikyau:kumadukanabindaakemuradibasugamuwadaitaba(Misalai 8:11).

Litafinadanawallafawaddatafiyinkasuwaitace,“Filin daga nazuciya” zan so in sanar da kai da ka karanta nan ba da dadewa ba. Ka tuna, sabunta tunanin ka zai kasance kamar yaki ne zuwa wani lokaci, amma kada ka yi kasa a gwiwa, domin dukan wadanda suka nemi Ubangiji da gaske za su sami babban lada.

Tsarin Sabuwar Tunani

Page 27: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)
Page 28: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

27

Kalmomi jakunkuna ne wanda suke dauke da iko, suna duke ne daikomasumuhimmancikokumamarasamuhimmanci,sa’andaubangiji yayi Magana da farko, ya hallice abubuwa masu kyau, haka mu ma ya kamata mu yi koyi dashi.

Cikin mutum za ya koshi da amfanin bakin sa: Ran sa kuma za ya kwanta da gallar lebunansa. Mutuwa da rai suna cikin ikon harshe: Masu kaunan sa kuma za su ci amfanin sa. -MISALAI 18:20-21

Kyakkyawan nazari a kan wanan nassi yana bayyana mana da cewa furucin mu yana da sakamako. Wasu kalamun mu sukan jawo abu mai kyau, wasu kuma suna jawo abubuwa mara kyau. A duk lokacin da muka bude bakin mu don mu furta wani abu, ya kamata mu yi la’akari da karfin ikon da ke cikin kalmomin mu. Wananshine daya daga cikin manyan dalilan da shaidan yake shuka mana mugayen tunani a zuciyar mu.

Yana sane da cewa da zaran mun dauke su cikin tunanin mu, zasu zama furucin mu. Wanan shi zai bude masa kofar da ya ke bukata ya shigo domin ya yi ayyukan da zai gurbata rayuwar mu.

Wanda ya tsare bakin sa da harshen sa, ya na kiyaye ran sa daga wahala. -MISALAI 21:23

SABUWAR HANYAR YIN MAGANA

Babi na Shida

Page 29: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

28

SABUWAR HANYAR RAYUWA

Jarabamafigirmaaduniyashine,muyiMaganaakanabindamuke gani muke kuma ji, amma Allah yana so ne mu yi Magana a kan abin da maganar sa ya ce mu mallaka. Ba wai ina ba ka shawara ka yi watsi da matsalolin ka bane, amma ina gaya ma ka cewa za ka iya cin galaba a kan su. Kuma yadda ka ke yin Magana a lokacin da ka ke fuskantar matsalolin ka yana da dangantaka da su.

Isra’ilawasunyishekaruarba’insunatafiyandayakamatasuyi a cikinkwanagomashadaya, suna ta tafiyaawuridaya sunata kewaye tsaunuka, basu ci gaba ba. Suna da matsaloli da yawa kuma daya daga cikin manyan matsalolin su shine, gunaguni. Sun yitayintsegumidagunaguniakowanelokacindaabubuwabaitafiyadda su ke so ba. Ubangiji yana so mu yabe shi mu kuma gode masa a lokacin da muna cikin kuncin rayuwa, da kuma lokacin da muna cikin jin dadi, abubuwan da muke fadi a lokacin da muna cikin matsala yana dagewa da tasowon lokacin da za mu kasance a cikin matsalan.

Hakan zai zama abin mamaki a gare ka, amma furcin ka na dauke da iko a cikin ta. (Kamar yadda an rubuta ni na sanya ka Uba gaal’ummaimasuyawa)agabanwandayabadagaskiyagareshi,wato Allah kenan, wan da yake rayar da matattu, yana kira abubuwan da ba su da kasancewa sai ka ce akwai su. Romawa 4:17. Ya ce: muna bauta wa ubangijin da ya ke kiran abubuwan da kwata-kwata babu su kamar suna nan tun da. Allah yana ganin abin da zai faru nan gaba kuma ya yi Magana a kan shi kamar ya riga ya faru. Yin haka sai ka yi kallo da idon bangaskiya.

Bangaskiya yana ji da kuma ganin abin da a zahiri ba a gani ko ji. Bangaskiya yana daukan alkawaran Allah ya kuma maishe su kamar zahiri!

Idan muna da matsala kuma lallai muna son ubangiji ya cece mu daga wanan matsala, sai mu yi murna yanzu. Ba wai sai mun jira mun ga abin ya tabbata bane, domin mu na da tabbaci ta wurin bangaskiya. Mun sani kuma mun tabbatar Allah yana aiki a madadin mu.

Lokacin da anabi Ezekiel ya duba ko ina, ba abin da yake gani sai busassun mattatun kasussuwa, sai Allah ya tambaye shi, ko wadanan busassun matattun kasussuwan za su sake rayuwa? Ezekiel ya amsa

Page 30: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

29

Sabuwar Hanyar Yin Magana

ya ce, “yaubangiji, kai kadai ne ka sanwanan”, sabodahaka saiubangiji ya ce masa, ka yi Magana (anabci) da wadanan kasussuwa ka ce masu, su ji muryar ubangiji, sai Ezekiel ya soma Magana yana anabci kamar yadda aka umarce shi. sai kasussuwan nan suka fara tattaruwa wuri daya suna haduwa, tsoka da jijiyoyi suka hade, har sukatashisukatsayaakankafafunsujama’adayawa.(Ezekiel37)kajibabbanabinal’ajibinaikonAllah.

Furta Maganan Allah Ya Fito Da Karfi

Akoinanake,inakoyawamutanesufurtamagananAllahyafitoda karfi, kuma su yi hakan ne da tsayayyen nufi, ya kuma zamamasu abin yi kullum domin gina ruhaniyar su. Wannan yana cikin daya daga cikin manyan abubuwan da ubangiji ya koya ma ni, kuma zan fade shi kai tsaye cewa haka ya taimake ni sosai wajen sabunta zuciya ta da canza rayuwa ta.

MaganarAllahshinetakobinruhu,shinemakamimafigirmada za ka yaki shaidan da shi, shaidan yana jin tsoro da rawan jiki ga maganar Ubangiji. A cikin Luka 4. mun ga yadda shaidan ya jarabce Yesu, yana cikin Hamada, kuma yana jin yunwa domin bai ci komai ba na tsawon lokaci, sai shaidan ya fara shuka ma sa miyagun tunani a zuciya. Ko yaushe shaidan ya so ya yaudare Yesu, sai Yesu ya ce masa“arubucetake”saiyajamasaayadagamaganarAllahyafurtamaganandakarfidominyakaryatashaidan.InmunyikoyidaYesuto mu na kan hanyar samun nasara.

Kana da niya ka fara nazari a kan furcin ka? In kana da niya, za ka tarar, kamar sauran mu, kana furta wasu abubuwa wanda ba za ka so su faru da kai ba, na tabbata, za mu iya kara ko rage yawan kwanciyar rai da salama da muke da shi ta wurin yadda mu ke Magana. Idan hakan gaskiya ne, me zai hana ka ka dinga furta abin da zai sa ka farin ciki maimakon bakin ciki.

Yin Magana cikin bangaskiya ya shiga sabuwar tsarin rayuwar ka yanzu, saboda haka, sai ka fara.

Kana iya fadin wani abu kamar haka,Allah yana kauna ta, kuma yana da kyakkyawar shiri game da

rayuwa ta.

Page 31: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

30

SABUWAR HANYAR RAYUWA

Sabuwar Tsarin Rayuwa

Ina mai samun tagomashi a duk inda na je.Komai na sa hannaye na a kai zai bunkasa. Ubangiji ya kulle kofa ga duk abinda ba shi da kyau, kuma ya baude kofa ga duk abu mai kyau a rayuwa ta.Inatafiyaacikinhikima.Ina cike da salama.Ina da farin ciki. Inatafiyaacikinkauna.Wani abu mai kyau zai faru da ni yau. Yara na duka suna kaunar Allah kuma suna bauta masa.Zaman aure na yana dada yin kyau kullum.Ina da albarka duk inda na je.

Yawan irin wadanan kalamu masu dadi ba su da iyaka, kai dai ka tabbata abin da ka ke furtawa shine abin da maganar Allah ya ce. Daidaituwa da tasarin ubangiji zai bude wani babban babi a rayuwar ka. Zai sa kyakkyawar shirin da ubangiji yake da shi game da rayuwar ka ya tabbata.

Page 32: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

31

Yaya kake ganin kan ka? Yadda ka ke daukan kan ka ya na nan kama da hoto wan da ka ke dauke dashi ka na ta yawo da shi a birnin zuciyar ka. Ta wurin shekaru da yawa na yin aiklin Ubangiji da kuma wa’azigamutane,naganocewamutanedadamabasasonkansusossai. Na yi rayuwa rashin son kai na na shekaru da dama, kuma ya zama mani Kaman guba a dukan abubuwan da nake yi a rayuwa. Allah na kaunar ka kuma yana bukatanka ka kaunace kan ka, ba ta wurinn son kai ba amma ta tsabtacecciyar hanya. Ba za ka iya bayar da abinda ba ka da shi ba, Allah na kaunar mu kuma yana so mu ba wakaunarnanhanyadomintawarkasdamudafarkonfarisa’annanta bi ta taba sauran mutane. Idan ka ki karban Kauna wanda Ubangiji ya ke da shi domin ka ta wurin kaunan kan ka yadda ya kamata, ba za ka iya kaunan wasu ba.

Ra’ayinkayanakankayanananbisagaabubuwandakakeyine?Yawancinmu,wannanneyanayin,kuma ra’ayinmubazaiiya yin kyau ba domin abubuwan da mu ke yi ba kullum bane su na nan daidai. Mu yan tara ne kuma mu kan yi kuskure. Muna son yin abubuwa daidai amma kullumyomi sai mu dagula abubuwa, wannan netakamammendalilindayasamunanemanYesu.Yanunakarfinsa cikin kasawan mu.

Kai ba abin mamaki ba ne ga Ubangiji. Ya san kai wanene ne da ya gayyace ka kayi hulda da shi, ya kuma san dukan kuskuren da za

SABUWAR HANYAN KALLON RAYUWAN KA

Babi na Bakwai

Page 33: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

32

SABUWAR HANYAR RAYUWA

ka taba yi a rayuwa kuma yana kaunar mu da bukatan mu duk da haka. Kar ka takura wa kan ka, ka yi koyi da karban jinkan Ubangiji ko wacce rana. Ka tashi ko wace rana ka yi abin da ya kamata da dukankarfinkadomindaukakansunanUbangiji.Kayiabindakedaidai domin kana kaunar Allah amma ba domin kana neman ya kaunace ka ba, Ya rigaya ya kaunace ka da kauna mara matuka kuma kaunar sa zuwa gareka yana da kyau.

A karshen kowacce rana, ka nemi gafaran zunuban ka da kuskuren ka daga wurin Ubangiji, ka sami barci mai kyau ka kuma fara washe gari da salama.

Shaidan na gaba da kai, amma Allah na tare da kai. Ya kamata kanataredaAllah,dominwandaketaredaAllahyanadakarfisossai.Ka na da muhimmanci a gaban Ubangiji kuma kana da baiwa dayawa wayenda ke da amfani ga Ubangiji. Kar kana duban abubuwan da kake tsammanin cewa ba daidai bane a gareka. Kar ka duba yawan nisanindazaka-ammakadubayawannisantafiyandakayi.Kaimai ban gaskiya ne cikin Yesu Kristi yanzu kuma wannan ne mafarin dukan kyawawan abubuwa a rayuwa.

Fahimtar Adalci

Adalci (Kyakkyawan tsayuwa da Ubangiji) yana zuwa ne ta wurin bangaskiya a cikin Yesu ba ta wurin ayukan mu ba. Kyauta ne na Allah kuma ana samun ta a lokacin da ka karbi Yesu ya zama mai ceton ka. Akwai ayoyi da yawa da suka goyi bayan wannan, zan lisafta kadan domin in karfafa ku.

2 KORINTIYAWA 5:21. Shi wanda baya san kowane zunubi ba, ya maishe shi ya zama zunubi sabili da mu: domin mu mu zama adalcin Allah a cikinsa)

Waiyo! Kyakkyawan aya! Kristi mara zunubi ne, duk da haka domin kaunar sa zuwa garemu ya dauke zunuban mu domin mu sami zumunta da Uba wato Allah. Allah, yanzu yana ganin mu karbabbu kuma tsayayyu gare shi domin mun karbi Yesu ya zama mai ceton mu. Zan sake in fada kuma….waiyo!

Page 34: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

33

Sabuwar Hanyan Kallon Rayuwan Ka

Maimakon mu ji tsoro don cewa Ubangiji bai ji dadi ba, za mu iyatsayawagabansa‘’cikinKristi’’mukumasanicewamukarbabbune.

ROMAWA3:20.Gamatawurinayukanshari’abamai-raidazashibarataagabansaba:gamatawurinshari’anake sanin zunubi.

ROMAWA 3:22. Watau adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kristi ke nan zuwa ga dukan masu-bada gaskiya; gama ba marar-ba.

GALATIYAWA 2:16. Amma mun sani mutum ba za shi baratabisagaayyukanshari’aba,saitawurinbangaskiyacikin Yesu Kristi, mu da kanmu muka bada gaskiyan ga Kristi Yesu, domin mu barata ta wurin bangaskiya cikin Kristi,babisagaayyukanshari’aba,gamabisagaayyukanshari’abamai-raidazashibarata.

Yana da muhinmanci ga girman ruhaniyan ka ka ga kan ka kana nan tsayeyye gaban Allah ta wurin bangaskiya ga Yesun Kristi. Kyau-ta ne da ga Allah. Idan kullumyomi ba mu sami gamsuwa da kanmu, muna kuwa tunani ko Allah na fushi da mu, zamu yi nasara da iko daAllahyakesomuyitafiyacikinta.Munadaikoakanshaidanamatsayin mu na masu bangaskiya ga Yesu, amma dole mu tsaya a gaban Ubangiji cikin adalci ba tsoro da kuma rashin bangaskiya ba.

Afisawasurashiddatanacewa,muyafaadalciyazamamatarinkirjin mu kamar yadda ake yi a yaki. A wurin sojan yaki, wannan matarin ne ke tsaron zuciya ko kuwa kirji. Menene asalin abin da ka ke ba da gaskiya a kai a kan ka? Za ka iya yarda ta wurin bangaskiya cewa ka na tsayayya da Allah? Za ka iya idan ka sa idanun ka ka na bin Yesu ya yi ma ka amma ba a kan kuskuren da ka yi ba. Za ka iya yin kuskure amma idan ka yi, nan da nan sai ka tuba ka kuma nemi gafara daga wurin Ubangiji. Wannan ne hanya kadai da zamu iya tafiyacikingaskiyadaadalci.Baadalcinmunemuketafiyacikiba,dominadalcinmunanankamartsummamaiƙazanta,ammasaimu

Page 35: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

34

SABUWAR HANYAR RAYUWA

yitafiyacikinadalcinAllahtawurinbangaskiyacikinYesuKristi.Wannan kyakkyawar sabuwar hali da za ka iya samu wa kan ka,

kashi ne na sabuwar rayuwar ka a matsayin ka na mai bangaskiya ga Yesu.

Jin Dadin Ka

Kanadayancikajidadinrayuwankayanzu,kumanufinAllahnehakan ta faru. Kar ka yarda da abubuwan da mutane suka fada domin kimanta darajan ka ya zama in da ka ke ganin kan ka, ko kuwa, yadda mutane suka bashe ka ko abubuwan da ka yi a rayuwa. Allah Ubangiji ya san ka na da daraja a gaban sa har ya aiko da Ɗansayamutudominka,wannandalilinenayinmurna.

Littafimai tsarki yanunamanaafili da cewaAllah yana somu ji dadin rayuwa amma wannan ba zai faru ba idan baka ji dadin rayuwankabatukuna.Kaimutumnedabazakaiyatafiyakabarkan ka ba ko na dan lokaci. Idan ba ka ji dadin kan ka ba, to, kana cikin tsananin rayuwa. Kamar ni, kila kana nan dabam da sauran mutane da ka sani, haka babu damuwa. Abu ne wanda Allah ya yi da son sa. Ya hallace mu dabam dabam, ya na son abubuwa dabam dabam. Kai ba safai ba ne, babu kamar ka kuma ka na da daraja a gaban Allah sossai.

Kada ka gwada kan ka da wadansu, kada ka yi ta rayuwan gasa dukan kwanakin ka. (2 Korintiyawa 10:12). Kar ka yi koyi da wani amma ka ji dadin kan ka yadda Allah ya yi ka. Ya na da kyau ka canzaawasuwurarekamarkowannedayanmusa’annanruhumaitsarki zai yi ta aiki dukan kwanakin ran ka ya kuma canza ka domin ka zama mutumin kirki. Labari mai kyau shine, kana da yanci ka ji dadin rayuwan ka yayin da kana ayuka ci gaba.

Page 36: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

35

Dukan mu mun san yadda tsoro yake, tsoro yakan rikita mu, yakan kuma hana mu cin gaba. Tsoro kan sa mu rawan jiki, zufa, kasala da fargaba, yakan kuma sa mu mu gudu daga abubuwan da ya kamata mu fuskanta. Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da kauna da na horo (2 Timatawus 1-17).

Ubangiji yana so muyi rayuwa cikin bangaskiya. Bangaskiya shine sa dukan yarda da kuma tunanin ka ga iko, hikima da kuma kaunar Allah. Bangaskiya, ita ce ainihin abin da mu ke bege, tabbacin alamuran da ba a gani ba tukunna. Bangaskiya abu ne na ruhu. Ba wuya ka saba da ba da gaskiya ga abin da ka na iya gani ko tabawa. A matsayin ka na da ga Allah, ya kamata ka na da kwanciyar hankali da yin rayuwa a in da ba ka gani amma ka bada gaskiya (wato rayuwa cikin ruhu). Ba za mu iya ganin Allah ba domin Allah ruhu ne amma munba da gaskiya gare shi. Bamu saba da ganinmala’iku ba,amma Kalmar Allah ta ce su na tare da mu kullayaumi. Ta wurin bada gaskiya ga Ubangiji da kuma Kalmar Sa, zamu iya karban abin dakenamuacikinruhu,kodaidobayaganinsuafili.

Shaidan ya na farin ciki da jawo hankulan mu cikin damuwoyi, domin ya sa mana tsoro game da rayuwa na gaba. Ubangiji kuma ya na so mu ba da gaskiya gare shi mu kuma yarda da cewa ikon sa ya fikowacceirindamuwadamatsalolindashaidankekawomana.

Littafimaitsarkiyanacikedakwatancenmazadamatadayawa

MAYE GURBIN TSORO DA BANGASKIYA

Babi na Takwas

Page 37: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

36

SABUWAR HANYAR RAYUWA

wadanda suka sami kansu cikin mawuyacin hali. Tsoro kuwa ya ratsa su ya kuma cika zukatan su, amma duk da haka sai su ka bada gaskiya ga Ubangiji, rayuwan su kuwa ya sami sakewa daga cikin tarkon shaidan. Dole ne mutum ya zabi daya daga cikin biyun nan; ‘’Rayuwan bangaskiya ko Rayuwan tsoro domin rashin bangaskiya’’KodayakekaiKristaneyanzu,kanaiyayinrayuwacikintsoro da shakka idan ba ka da cikakken bangaskiya ga Ubangiji. Tunda ka karbi Yesu Kristi ya zama mai ceton ka, sai ka yi rayuwa da bangaskiyagaUbangiji,dominbisharataceacikinlittafinROMAWA1:17, Gama a cikin ta an bayyana adalci na Allah daga bangaskiya zuwa bangaskiya: yadda an rubuta, amma mai -adalci da bangaskiya zai rayu.

Tunda mun gane da kaunar Allah, mun kuma gane cewa muna da bangaskiya ta wurin mutuwa da tashiwan Yesu Kristi, ya zama mana da saukimu yi tafiya cikin bangaskiya. Dukanwanda yanacikin Yesu ba shi da fargaba ko kadan. Idan Allah yace mana kada mu ji tsoro, ba doka bane kawai yake bamu amma mu ba da gaskiya gare shi mu kuma bi umurnin sa cikin ko wanne hali.

Allah ya sani cewa rayuwa cikin tsoro na iya hana mu cin gaba da kuma zumunci da shi, dalilin da ya sa kenan yana gaya mana a kullumyomi cewa yana tare da mu, domin haka ne babu amfanin mu yi ta rayuwa cikin tsoro.

Eheanar Roosevelt yace; kwazo, kuzari da bangaskiya na samuwa idan mutum ya daina bauta wa tsoro. Dole ne mu dinga yin abubuwan da mun ba da gaskiya gare su.

KUBAWARSHARIYA31:6.Kayikarfikayigabagadi,kadakajitsoro,kadakafirgitadominsu:GamaUbangijiAllahnka,shineyaketafiyataredakai;bazayabarkaba,bakuwa za ya yashe ka ba.

Ta wurin ban gaskiya ne kadai mutum ke iya faranta wa Allah rai, kuma ta wurin bangaskiya ne mu kan iya ji daga wurin Allah, sabo da haka, dukan wanda ya ba da ransa ga Allah yakuma maye haifuwar sa ya koyi rayuwar cikin bangaskiya da tsoron Allah. Girman bangaskiya na kama da yadda jikin mutum na girma ko kuwa kamar

Page 38: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

37

Maye Gurbin Tsoro Da Bangaskiya

yadda dan kwallo na gudu domin ya motsa jinin sa. Idan muka yi kokari domin bangaskiyar mu ta girma kamar yadda dan kwallo ke motsa jinin sa, bangaskiyar mu zata samu karfafuwa sossai.

(Matiyu 17:20. Y ace masu, saboda karamtar bangaskiyar ku: Gama ina ce maku, hakika, idan kuna da bangaskiya kwantancin kwayar mustad, sai ku ce wa wannan dutse, ka kawu daga nan ka koma can; sai shi kawu kuma babu abinda baza shi yiwu gare ku ba).

Babu mamaki ka dade ka na kokarin neman biyan bukata ta wurinkarfinka, ammabaka samuba. Idanhakane,kanakusada samun biyan bukata, idan ka bada gaskiya ba abin da zai zama maka da wahala a rayuwa, gama abinda ke da wuya ga mutane abu ne mai sauki ga Allah. (Matiyu9:29.Sa’annanyatabaidanunsu,yace,gwalgwadon bangaskiyar ku shi zama maku).

Babu mamaki ka yi ta tsoro dukan rayuwarka, yau ne lokacin da za ka maye gurbin tsoro da bangaskiya. Girman bangaskiya kan dauki lokaci amma kada ka karaya domin komai a rayuwa takan dau lokacikafintagirma.IdanmunyardadaAllah,munyiabubuwandaUbangijiyafadaacikinlittafimaitsarki,bangaskiyarmuzaisamukarfafuwa.

Page 39: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)
Page 40: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

39

MORE RAYUWAR KA

Babi na Tara

Ɓarawobayakanzobasaidominsata,dakisadahallaka:ni na zo domin su sami rai, su same shi a yalwace kuma. -YOHANA 10:10 Yesuyamutudominkamorerayuwarka,hakanbayananufin

cewa za ka sami komai da ka ke bukata ba, ba tare da shan wani wahalaba.Yananufincewa,tawurinhuldankadaUbangiji,zakaci galaba a kan matsalolin duniyan nan, ka kuma yi rayuwan tashin matattu wadda ake yi, tare da, kuma domin, Ubangiji ta wurin ruhu mai tsarki.

Allah shine rayuwar mu na gaskiya, a cikin sa muke rayuwa, muke tafiya,mukekumakasancewa.YinkoyidamoranUbangijizai ba ka daman more rayuwar ka a kowacce rana. Ci gaba da more rayuwarkanahuldataredashi,Allahyadamudadukanal’amurandasukashafirayuwarka,kumalittafimaitsarkiyatabbatarmanadacewa, Ubangiji zai daidaita komai game da rayuwar ka. Ya na aiki a cikin mu ko yaushe, ya na jayo mu zuwa gare shi gaba daya.

Kada ka ji tsoron Ubangiji ta hanyar da bai dace ba, ya kamata munadadacacciyar tsoronAllah.Wanda yakenufinmuyimasabiyayya,taredasanincewashimaiikonemaigirma,mainufinabinda ya fada. Amma kada mu taba jin tsoron cewa Ubangiji zai bata rai a kan kowanne kuskuren da mu ka yi, ko kuma zai Hore mu a

Page 41: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

40

SABUWAR HANYAR RAYUWA

duk lokacin da muka kasa. Allah mai tausayi ne, kuma mai jinkirin fushi ne, mai jimriya ne, kuma ya san mu, ya kuma san kasawar mu, da rashin tsarkin mu.Idan kai ma kana kamar sauran mu ne, mu na da abubuwa ma su Yawa a rayuwar mu da suna neman canji, kuma Allah zai canza su, amma labari mai kyau shi ne, ka na iya moran Ubangiji ka kuma more rayuwar ka a lokacin da ya ke yi.

Rayuwar da ka ke da ita yanzu ya na iya kasancewa ba shi ne rayuwar da ka ke son ka karasa da shi ba, amma shi ne ka ke da shi a yanzu, saboda haka sai ka fara morewa yanzu. Ka nemi abubuwan dakedakyauaciki,kajaddadamasuma’ana,kakumaiyatantanceabubuwa masu kyau a cikin kowanne abu, ka ji dadin iyalan ka da abokanen ka, kada ka rarraba su ka na faman canza su. Ka yi masu adu’akabarwaUbangijiyayicanjidakansa.

Ka ji dadin ka, ka more gidan ka, ka more rayuwar ka na yau da kullum, wanan mai yiwuwa ne in za ka yi imani da Allah kuma ka yi halin kirki, ka sa idon ka ga Ubangiji, ba a kan kowanne abin da ya dame ka ba, rayuwar ka, iyalin ka, ko duniya ba. Allah yana da kyakkyawar shiri a kan ka kuma tuni ya soma aiki a kai. Ka yi murnatunlokacibaiyiba,kanahangenlokacindaal’amurazasuyi kyau.

Mutane da yawa suna yin rayuwar su kamar ba su amince za su iya jin dadin rayuwar su ba saboda wasu matsaloli da su ke da shi. Amma wanan wautar tunani ne, kada ka yi ta jimami a kan kuskure da ka yi a baya, ka ci gaba da tuna babban albishir da ka ke da shi cikin Yesu kriti.

Za ka mori duk abin da ka ke so ka mora. Ka tuna cewa ina koya ma ka yadda za ka yi sabon rayuwa ne, kuma halayan ka na rayuwa yana da babban muhimmanci game da haka.

A karshe dai na koyi yadda zan mori inda na ke, tun ina kan hanyar zuwa inda zan je. Kuma ina mai kiran ka da kai ma ka yi haka.

Da sauran abubuwa da yawa da Ubangiji zai yi a rayuwar ka, kuma ba ya son ka kasance mai shan wuya a lokacin da ya ke ,maganin matsalolin ka, kamar yadda jarirai su kan girma su zama manya, haka kiristoci suke girma. Wannan wani yanayi ne wanda ya kedaukanlokacifiyedayaddamukeso,ammababuhikimaacikin

Page 42: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

41

More Rayuwar Ka

rashinmoretafiyannan.Allahba ya zaton za ka kasancemara laifi a yau, saboda ya

rigaya ya sani cewa ba za ka iya kasancewa cikakke ba a duk tsawon rayuwarkaaduniyaba,ammayanasaraidukanmuzamudukƙufaga yin haka, mu farka a kowacce rana mu iya kokarin mu na bauta wa Allah. Mu amince da kasawar mu kuma mu nemi gafaran zunuban mu,mudukƙufawajenbarinsu, idanzamuyihaka,Ubangijizaikarasa sauran. Zai ci gaba da aiki tare da mu cikin ruhun sa mai tsarki. Zai koyar da mu, ya canza mu, ya kuma yi amfani da mu. Ka shigo cikin tsarin sabuwar rayuwa, kuma na tabbata ba ka taba yin nadama ba, ka mori Ubangiji, ka mori rayuwar ka, ka kuma mori rai din da Yesu ya mutu don ya ba ka.

Page 43: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

42

Allah uba, ina kaunar ka, na zo gare ka yau a cikin bangaskiya, ina rokon ka, ka gafarta mani zunubai na, Yesu na yi imani da kai, na yarda cewa ka mutu a kan giciye domina, ka zub da jinin ka mai tamani sabili da ni, ka dauke ma ni dukan tsanani da azabar da ya dace in sha saboda zunubai na, na gaskanta cewa, ka mutu, an binne ka, ka kuma tashi daga matattu bayan kwana uku. Mutuwa ta kasa rike ka, ka yi nasara a kan shaidan har ka kwace makullin jahannama da na mutuwa daga gare shi. Na ba da gaskiya cewa ka yi haka ne saboda matukar kauna ta da ka ke yi. Ina so in zama kirista, in kuma bauta maka har iyakar rayuwa ta. Ina so in koyi yadda zan gudanar da sabuwar rayuwar da ka alkawarta ma ni, na karbe ka yanzu ya Yesu, kuma na mika kai na a gare ka, ka dauke ni yadda nake, ka kuma mai da ni yadda ka ke so in zama.

Na gode Yesu domin ka cece ni, ka cika ni da ruhun ka mai tsarki, ka kuma koya ma ni duk abin da ya kamata in sani. Yanzu na tabbata na samu ceto, an sake haifuwa ta, kuma na ba da gaskiya in na mutu zan shiga aljanna. Allah uba,zanjidadintafiyaakantsarinka,rayuwatakumazaidaukaka ka.

ADDU’AR SAMUN CETO

Page 44: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

43

BAYANI AKAN MAWALLAFI

JOYCE MEYER tanadayadaga cikinfitattunmalamainakoyar da Littafi mai tsarki a duniya. Tana kuma na dayadaga shahararrun mawallafa da suka yi fice na New YorkTimes. Ta rubuta takardu kusan casa’in masu iza tunani,a cikin su har da Living Beyond Your Feelings (Rayuwa fiyeda yadda kake ji), Power Thought (Tunani mai karfafawa) da kuma dukan dangin takardun The Battle field of TheMind (Filin yaki na zuciya) da Two Motels (Masauki guda biyu) da kuma The Penny (Anini) da kuma Any Minute (Ko wane minti). Ta kuma sake duban kaset-kaset na ji, har ma da gidan ajiya na bidiyo gaba daya. Joyce tana gudanar da shirye-shirye a kan rayuwa a ko wace rana a rediyo da talabijin wanda ake watsawa zuwa sassan duniya. Tana yawan tafiye-tafiye sossai da gudanar da tarurruka nawayar da kai da samun cin gaba. Joyce da mijinta iyaye ne na yara guda hudu wanda dukan su sun girma, suna kuma zama a gidan su da ke St. Louis a Missouri a kasar Amurka.

Page 45: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)

ADU’A DOMIN CETO

Allah Yana kaunan ka kuma Yana so ya kulla kyakkyawr dangantaka da kai. Idan ba ka karbi Yesu Kristi ya Zama mai ceton ka ba, zaka iya yin haka yanzun nan. Bude mashi zuciyan ka Kayi wannan adu’a.

“Uba, na san nayi maka zunubi, ka yafe ni. Ka wanke ni. Nayi alkawari zan amince da Yesu, ‘dan ka. Na bada gaskiya ya mutu domina- ya dauke zunubaina a kansa sa’anda ya mutu a kan giciye. Na bada gaskiya an tashe shi daga mattatu. Na mika rayuwa na ga Yesu yanzun nan. Na gode, Uba, saboda kyautan ka na gafara da rai na har abada. Ka sa in yi rayuwa domin Ka. A cikin sunan Yesu, Amin”.

Kamar yadda kayi adu’a daga zuciyar ka, Allah ya rigaya ya karbe ka, ya wanke ka, ya kuma yantad da kai daga kangin mutuwa na ruhaniya. Samu lokaci kayi karatu da nazarin wadannan nasosi. Ka roki Allah yayi magana da kai ayayin da kake yin tafiya da shi cikin wannan tafiyar ka na sabon rayuwa.

Yohanna 3:16. 1 Korintiyawa 15:3-4Afisawa 1:4 Afisawa 2:8-9 Yohanna 1:9 1 Yohanna 4:14-15 1 Yohanna 5:1 1 Yohanna 5:12-13

Yi adu’a ka roke shi ya taimake ka Ka sami ingantacciyar Majami’ad da ta amince da Littafi Mai Tsarki domin ka karfafu ka kuma girma cikin dangantakan ka da Kristi. Allah Yana tare da kai kullum. Zai bi da kai kowane rana da sa’a ya kuma nuna maka yadda zaka rayu cikin yalwataccen rayuwa da ya tanada domin ka!

Page 46: A New Way - Text Hausa - Joyce Meyer Ministries · 2017. 7. 21. · Babi na Biyu. 10 SABUWAR HANYAR RAYUWA (Dukan abubuwan da basu amince da nufinsa ba, ta wurin tunani da aikatawa.)