magama - photos.state.gov · shirin na yali na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun...

24
CROSSROADS | 2012 December/2013 January Special 1 A Kan Hanya Zuwa Shekarar 2015: Batutuwan Sun Wuce Na Za~u~~uka Yadda Ake Mi}a Mulki A Dimokura]iyya Sa}o Na Musamman Daga Jakadan Amirka Game Da Za~u~~uka Sifili Lamba Na 5 Mujallar Ofishin Jakadancin Amirka A Nijeriya Kyauta Jumadal Ula/Jumadal Akhir, Hijra 1435 Fitowa Ta Musamman

Upload: leminh

Post on 29-May-2019

269 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

CROSSROADS | 2012 December/2013 January Special 1

A Kan Hanya Zuwa Shekarar 2015: Batutuwan Sun Wuce Na Za~u~~uka

Yadda Ake Mi}a Mulki A Dimokura]iyyaSa}o Na Musamman Daga Jakadan Amirka Game Da Za~u~~uka

••

MAGAMASifiliLambaNa5

Mujallar Ofishin Jakadancin Amirka A Nijeriya Kyauta

JumadalUla/JumadalAkhir,Hijra1435FitowaTaMusamman

Page 2: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 2

A watan Maris ’yan Nijeriya suka amsa kiran Gwamnatin

Amirka, inda suka yi tururuwa daga garuruwan Abuja da Kaduna da Jos da Legas da Fatakwal da Ibadan domin ganawa da jami’an ofishin Jakadancin Amirka saboda tsinto wa]anda suka cancanta zuwa }asar Amirka don wakiltar }asarsu, cikin mutane 500 da za a za~a a nahiyar Afirka, domin shirin nan na shugabannin matasa masu haza}a.’Yan Nijeriya 15,000 suka nemi shiga shirin na matasan shugabannin Afirka na Shugaba Obama, da ake kira “YALI.” Tun farkon

watan nan an za~o ’yan Nijeriya 50 da ma’aikatar }asashen wajen Amirka ta yi domin ba su horo kan shugabanci da karatu da kuma shawarwari. Ina taya wa]anda suka samu shiga murna.

Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin arzi}insu da kuma }arfafa dimokura]iyya. Wa]anda suka gudanar da ganawar da ’yan Nijeriya su 600 wa]anda shekarunsu ya kama daga 25 zuwa 35,

zan fa]a muku ka]an kan yadda ganawar ta kasance.

Mun gamsu }warai da irin haza}ar matasan Nijeriya da muka gana dasu, kuma muna cike da kyawawan hange, cewar gaba za ta yi kyau ga matasan Nijeriya a bisa canji mai kyau da za a samu. Mun ha]u da matasa masu }wazo da za su iya kawo canjin da ake bu}ata na kasuwanci da mulkin dimokura]iyya.

Wa]annan matasa suna da tambayoyi da dama ga kansu da ’yan Nijeriya da kuma shugabannni. Sun kuma }uduri aniyar amsa wa]annan tambayoyi a

YALI: Jakadan Amirka Ya Gode Wa Matasan Nijeriya

Jami’ar ya]a labarai, Rhonda Ferguson-Augustus daga dama da Jami’in diflomasiyya, Ellen Peterson (hagu) suke ganawa da masu sha’awar shiga shirin YALI a Kaduna. Sani Mohammed ya ]auko hoton.

Duba shafi na 18

Page 3: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 3

YALI: Jakadan Amirka Ya Gode Wa Matasan Nijeriya

Gaisuwa ga makaranta

Mujallar Magama. Ina

mai farin cikin amfani da

wannan mujalla don sake magana da

ku. Kafin gudanar da za~u~~ukan

shekarar 2015, zan yi amfani da

wannan damar domin isar da wasu

muhimman batutuwa game da

dangantakar Amirka da Nijeriya.

[aya daga cikin wannan

batutuwa, shi ne damar ka]a }uri’a.

Ko shakka babu za~u~~uka na canja

tarihin kowace }asa. A }asata muna

sane da wahalar dake tattare da kaiwa

ga mulki na dimokura]iyya. Tarihin

}asar mu na cike da gwagwarmayar

baiwa ’yan }asa ’yancin kai. Mun yi

ho~~asa wajen }arfafa al’ummar mu

a }arni da dama da suka wuce, kuma

har yanzu muna ci gaba.

A lokacin da nake matashi a

garinmu na Alabama, na taso a

tsakiyar gwagwarmayar neman

’yanci da }ungiyoyin farar hula ke

yi. Ina iya tunawa da tafiyar da ]an

gwagwarmaya Martin Luther King

ya yi daga Selma zuwa Montgomery

a shekarar 1965.

Ina iya tuna gwagwarmayar da

ba}a}en fata ’yan Amirka suka yi

don neman ’yancin yin za~e. Tun

daga wancan lokaci ne na fahimci

muhimmancin yin za~e. A don haka

nake kira ga ’yan Nijeriya da su fito

su yi za~e don karrama wa]anda

suka mutu wajen gwagwarmayar

neman yin za~e. Ku fita ku ka]a }

uri’a a ranar za~e.

Daga }arshe, ina son kowa ya

]auki al}awarin gudanar da za~e

ba tare da tashin hankali ba, kuma

ina fatan masu karatu za su janyo

hankalin za~a~~unsu da masu neman

matsayi da su guji tashin hankali

na ko a mutu ko a rayu don neman

kujerar mulki.

Ana bugawa duk bayan wata uku daga ofishin hul]a da Jama’a na Jakadancin

Amirka da ke Nijeriya. A rubuto duk wata wasi}a zuwa ga; Edita, sashin

hul]a da Jama’a, Ofishin Jakadancin Amirka a Nijeriya, Gida Mai Lamba 1075, Titin Harkokin

Jakadanci,Yankin Tsakiyar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nigeria.

Lambar tarho: (09) 461-4000. Fax: 09-461 4305

OFISHINMU NA LEGAS {aramin Ofishin Jakadancin Amirka, Sashen Hul]a da Jama’a, Lamba 2, Walter Carington

Crescent, Akwatin Gidan Waya, P.O. Box 554, Legas, Nijeriya. Wayar Tarho, +234-703-150-4867/2444. Yanar-Gizo, [email protected]

ko a shiga http://Nijeriya.usembassy.gov.

MA’AIKATAN WALLAFA MUJALLAVICTORIA SLOAN

(Babban Jami’ar Hul]a da Jama’a), DEHAB GHEBREAB (Jami’ar Hul]a Da Jama’a),

RHONDA FERGUSON-AUGUSTUS (Jami’ar ya]a labarai)

SANI MOHAMMED (Edita)ISHAKA ALIYU (Mai Ba Da Shawara

Game Da Wallafawa)

Sa}on Jakada 3

Fiye Da Za~e 4

Jakadiya Rice Ta Tattauna Kan Tsaro Da za~e 7

[aukar Al}awari Kan Zaman Lafiya 8

Aikin Da Amurka Ta Baiwa Matasan Nijeriya 10

Jakada Ya Yi Gargaliyar Turanci A Gidan Rediyo 11

BNC: Goyon Bayan Za~e Bisa Gaskiya 13

Amirka Ta Hana Ta~a Haramtattun Ku]in

Janar Abacha Dala Miliyan 458 13

{arfafa Dangantakar Ciniki Da Saka Jari

Tsakanin Amirka Da Nijeriya 14

YALI: Jakadan Amirka Ya Gode Wa

Matasan Nijeriya 18

An Haskaka ]akunan Karatu A Arewacin Nijeriya 19

Abubuwan Da Ke Ciki

James F. EntwistleJakadan Amirka A Nijeriya

Ambasada James F. EntwistleA

Sa

}o

n J

ak

ad

a

Page 4: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 4CROSSROADS | 2014 March-April Special Edition 4

More Than Elections

BABBAN LABARI

Akasari an amince mulkin dimokura]iyya ya fi kasancewa

halastaccen gwamnati. A mulkin dimokura]iyya an baiwa al’umma damar tattauna batutuwan dake

damun su da damar za~en wanda zai magance musu damuwar tasu.

Baiwa al’umma damar za~en irin yanayin da za a mulke su, shi ne matakin farko

na dukkan cibiyoyin dimokura]iyya da gudanar da su. Dimokura]iyya na gaskiya na bu}atar fiye da haka. Baya ga za~e, dimokura]iyya na bu}atar }a’idojin tsarin

Yadda ake mi}a mulkin dimokura]iyya lauya ne kuma }wararre na fiye da shekara 20. Eric Bjornlund na ]aya daga cikin wa]anda suka kafa }ungiyar dimokura]iyya na }asa da }asa, wanda yake shugabanta. Ya yi bayanin cewar a dimokura]iyya, ba kasafai shugabanni ke amincewa da ’yancin ]an Adam ba: dalilin da ya sa suke gudanar da gwamnati. Ga bayanansa.

Yadda Ake Mika Mulki A Mulkin Farar Hula

Daga Eric Bjornlund

Wannan hoton masu jefa }uri’a ne a za~en shugaban }asa na shekarawr 2011 – Idika Onyukwu ya ]auki hoton.

Fiye Da Za~e

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 4

Page 5: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 5CROSSROADS | 2014 March-April Special Edition 5

mulki kan }arfin gwamnati da tabbatar da ’yancin al’umma da ha}uri game da addini ko tsirarun }abila da gabatar da ra’ayoyi daban-daban da sauransu. Domin kafa dimokura]iyya mai ]orewa, dole ne a saba da al’adar sa da kuma tabbatar da bin doka, wanda hakan ne zai bambanta tsakanin za~u~~uka da kuma duk wani tarna}i game da hanyoyin gudanar da za~e.

Kamar yadda tsohuwar ministar harkokin }asashen wajen Amirka, Hilary Clington ta fa]a a Jami’ar Georgtown a 2009, “Dimokura]iyya ba wai za~en shugabanni kawai ba ne, amma ana bu}atar al’umma masu walwala da ’yan jarida, masu fa]in albarkacin baki ba tare da tsangwama ba da ~angaren shari’a mai cin gashin kai da kuma samar da hukumomin gwamnati masu tsage gaskiya ga al’ummarsu da kuma kare musu ’yancin su ba tare da nuna bambanci ba, a mulkin dimokura]iyya ba za~i ba ne ga shugabanni su kare ’yancin al’ummar su, wajibi su yi hakan, dalilin da ya sa suke karagar mulki ke nan.”

Mi}a mulki cikin kwanciyar hankali bayan za~e na da muhimmanci. A mulkin dimokura]iyya

na gaskiya, duk ]an takarar da ya fa]i za~e alhali shi ne akan karagar mulki, ya kan mi}a mulkin ne salun-alun ba tare da tashin hankali ba. Yin haka na sanya wa]anda suka fa]i za~e su tsira da mutuncin su, kuma abin koyi don inganta mulkin dimokura]iyya a }asarsu. Har ila yau, a bisa dalilin rungumar wanda ya yi kaye ko aka kayar, wa]anda suka yi nasara na cike duk

wani gi~i na nuna bambanci da rage duk wani cikas da zai haddasa ci gaban dimokura]iyya. A mulkin dimokura]iyya na gaskiya, yin doka da kasancewa cibiyoyin siyasa da }ungiyoyin fararen hula masu cin gashin kai na taimakawa wajen tabbatar da sakamakon za~e na gaskiya. Ayyukan

wa]annan }ungiyoyi na baiwa mutane }warin gwiwa a gwamnati da kuma ba su }arfin amincewa da bayar da goyon baya kan harkokin siyasa.

Tsarin Bin DokaDimokura]iyya na

bu}atar bin doka sau da }afa wanda hakan ne zai tabbatar da ]orewarsa duk yadda sakamakon za~e zai kasance. Kwamitin tsaro na majalisar ]inkin duniya ya bayyana tsarin bin doka da cewar “dukkan mutane da cibiyoyi ko }ungiyoyi na gwamnati da na al’umma da }asa sun dogara da bin doka da aka kafa, aka gabatar sannan aka shari’antar, kuma ya dace da amintar }asa da }asa na ’yancin ]an Adam.” Bin doka ya }unshi halasci da gaskiya da inganci da kuma tabbatar da daidaito.

Halasci na bu}atar amincewar kowa ga dukkan al’amura a bisa bin tafarkin dimokura]iyyar gaskiya, kuma ya }unshi tabbatar da hukunci a kan kowa, kare ’yanci da kuma samar da adalci. Inganci kuma shi ne bin tafarkin gaskiya a kowane lokaci. Bin tafarkin gaskiya na kare dukkan al’umma wajen tabbatar da dimokura]iyya a }asa, saboda irin wa]annan dokoki a mulkin dimokura]iyya yana wanzar da yarda da biyayya,

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 5

Page 6: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 6

al’umma na amincewa da za~e a yadda sakamakon sa ya kasance.

Duk }asar da ake bin doka sau da }afa, kuma ana sasantawa bisa shari’ar adalci, ba a cika samun matsala ba. A kan samu akasin haka idan ya kasance babu adalci a bin doka wajen yanke hukunci, kuma jama’a basa mutunta irin wannan mulki. Idan aka samu tsanantar rashin adalci ya kai ga tayar da zaune-tsaye tsakanin al’umma, musamman danniya da magu]in za~e da kuma rashin adalci a ~angaren shari’a.

A don haka ne, tsohon shugaban Amirka Dwight D. Eisehower ya ce, “Domin a bayyana abin da ake nufi da tsarin bin doka a dukkan rayuwar ]an Adam, shi ne a tuna abin da zai faru idan babu doka a }asa.”

Bin doka na nufin mutunta ’yanci da duk wani abu yardajje ga al’umma. Sannan yana bu}atar duk wani abu da zai kasance bayan kowane irin za~e. A mulkin dimokura]iyya, sakamakon za~e ba ya shafar kariyar ’yancin fa]in albarkacin baki da na ’yancin aikin jarida ko ~angaren shari’a mai cin gashin kai. Duk wani shugaba bai kamata ya nuna shakka game da wa]annan

yardaddun al’adu ba, ko nuna barazana game da ’yancin al’umma tare da wa]anda suka goyi bayan wanda ya fa]i za~e ko ’yan adawa. A don haka mutunta tsarin bin doka na taimakawa wajen mi}a mulki cikin kwanciyar hankali. Duk ]an takarar da ya sha kaye ya }i rungumar }addara a kan wannan tsari, yana iya rasa goyon baya, mutane na iya ]aukar sa mai sa~a doka, wanda zai iya kawo ru]ani. Har ila yau, irin wa]annan mutane ba za su samu goyon baya don aikata bore a }asar da suka amince da bin doka ba.

Hukumomin Siyasa

Idan ana da cibiyoyi ko hukumomin siyasa masu inganci, akwai yiwuwar za a sami mi}a mulki lami lafiya. Hukumomin za~e ko }ungiyoyi na da rawar takawa wajen da dimokura]iyya ke bu}ata domin magance duk wata ~araka da za ta taso dalilin za~e. A maimakon yin bore, duk wanda bai gamsu da sakamakon za~e ba na iya kai }ara kotu don bin ha}}insa. Akwai zaton cewar hukumomin za su iya tabbatar da gaskiyar da zai samar da sakamakon za~en da zai kwantar wa da kowa hankali, musamman a inda aka samu zargin magu]i. Samun hukumar

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 6

Hoton Jakadan Amirka, James Entwistle da Attahiru Jega a lokacin da Jakadan ya kai ziyara zuwa hukumar za~e ta }asa a Abuja ranar 20 ga Janairu, 2014. Idika Onyukwu ya ]auko hoton.

Page 7: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 7

za~e mai inganci na baiwa harkokin siyasa daraja da amintar al’umma a bisa sakamakon za~e da kowa zai mutunta. Haka kuma irin wannan hukuma na bayar da }warin gwiwa ga duk wanda ya fa]i za~e, cewar akwai damar sake tsayawa takara bayan kammala wa’adi.

Hukumomin da ke sanya ido kan ikon gwamnati na iya taimakawa wajen baiwa sakamakon za~e halasci da mutunci. Hakan na da muhimmanci, musamman a }asashen da ke koyon mulkin dimokura]iyya, inda ake samun kokwanton sakamakon za~e da ka iya haifar da tashin hankali. Idan shugaba ya }i yarda da sakamakon halastaccen za~e, ana

bu}atar kotu mai adalci da za ta yi tsayin daka don tabbatar da gaskiyar lamari. Akwai ha]ari }warai idan ma’aikatan gwamnati suka dogara kan za~a~~un shugabanni wajen samun

na goro don gudun agaza mishi ta wata hanyar magu]i idan ya fa]i za~e. Hukumomin za~e tsayayyu na baiwa shugabanni da ’yan majalisa da ma’aikatan gwamnati isasshen ku]i domin gudanar da mulki bisa dimokura]iyya.

Ingantacciyar gwamnati, wadda ta ha]a da tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da ha}}in al’umma na taimakawa wajen gudanar da dimokura]iyya mai inganci. Kamar yadda Barack Obama ya shaida wa ’yan majalisun Ghana. “A cikin wannan }arni na 21, samun nasara mai inganci wajen gudanar da }asa, na bu}atar hukumomin gwamnati masu ri}on gaskiya da

Mutunta doka da hukumomin gudanar da harkokin siyasa da karfafa ayyukan kungiyoyiin farar hula da kuma kyautata zaton mika mulkin siyasa lami lafiya

A ranar 19 ga watan Matris, 2014 ne mai baiwa gwamnatin Amirka shawara ta fannin

tsaro, Susan E. Rice, ta yi marhabin ga gwamnoni 12 daga Nijeriya zuwa fadar White House, inda suka tattauna batutuwan ci gaba tsakanin }asashen biyu.

Jakadiya Rice ta kawo batun kawo }arshen tashin hankalin da ke aukuwa a jihohin arewacin Nijeriya da samo hanyoyin inganta tattalin arzi}in yankin da Nijeriya gaba ]aya da kare martabar ’yancin ]an Adam da }arfafa gwamnatin dimokura]iyya da kuma tabbatar da cewa an gudanar da za~en 2015 cikin gaskiya da kwanciyar hankali.

Taron, babbar dama ce ta inganta dam}on zumunci tsakanin gwamnatin

Amirka da ta Nijeriya, wanda ya ha]a da tarayya da jihohi da kuma al’ummar Nijeriya.

Jami’an gwamnatocin sun fito ne daga arewaci da kuma tsakiyar Nijeriya dake fama da }alubalen tsaro da na tattalin arzi}i.

Shugabannin sun nuna damuwa game da tashin hankali na ’yan Boko Haram dake haddasa salwantar rayukan ]aruruwan mutane a wannan shekara.

Jakadiya Rice tare da gwamnonin sun amince da ]aukar gagarumin matakai don magance tashin hankali da ta addabi yankin da kuma ha~aka tattalin arzi}in yankin da Nijeriya.

Ta kuma jaddada muhimmancin za~en shekarar 2015 da rawar da gwamnonin za su taka don magance cin hanci da rashawa da kuma yadda }asar Amirka ta dage wajen }awance da Nijeriya don tunkarar }alubalan da suka addabi }asar. Gwamnonin sun ziyarci Washington ne don halartar taro na hukumar wanzar da zaman lafiya na Amirka.

Jakadiya Rice Ta Tattauna Batutuwa Kan Tsaro Da Gwamnonin Arewa

Mai bayar da shawara kan Tsaro Susan E. Rice.

Duba shafi na 20

Page 8: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 8

A daidai lokacin da ake tunkarar za~en 2015 na }asa,

Jakadan Amirka, James Entwistle ya }alubalanci ’yan siyasar Nijeriya da su ]auki al}awarin cewar ba

za su tayar da hankali ba, kafin za~e da lokacin za~en da kuma bayan za~en. Jakada Entwistle ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai ziyara zuwa gidan gwamnatin Jihar Zamfara, Gusau, ranar 9 ga watan Fabrairu.

A lokacin da gwamnan tare da ’yan majalisar dokokin jihar suka kar~e shi, Jakadan ya ce “A daidai lokacin da muke tunkarar shekarar za~u~~uka a

}asar, ina son ganin ’yan siyasa sun ]auki al}awarin gudanar da za~en ba tare da tashin hankali ba.” Ya ci gaba da cewa, za~e na ]aya daga cikin abu mafi muhimmanci a mulkin dimokura]iyya.

A cewar Jakadan, }asar

Amirka a shirye take ta ci gaba da baiwa Nijeriya

Game Da Za~en 2015:

Jakadan Amirka Entwistle Ya Yi Kira Ga ’Yan Siyasa Da Su Yi Al}awarin Tabbatar Da Zaman Lafiya

goyon baya, kuma tana son ganin an gudanar da za~en cikin gaskiya da kwanciyar hankali da ’yan }asar ke bu}ata.

Jakada Entwistle ya fa]a wa gwamnan da jama’ar sa cewa, ofishin Jakadancin Amirka ta

himmatu a Jihar Zamfara na gudanar da ayyukan

raya }asa ta hukumar ci gaban }asashe da kuma cibiyar ya}i da cututtuka (CDC), wajen ya}i da annobar gubar dalma da kuma ya}i da cutar }anjamau.

Kafin ya je Zamfara, sai da Jakadan ya kai ziyara Jihar Kaduna inda ya sadu da mataimakin gwamnan Jihar, Nuhu Audu Bajoga. Ya tabbatar

Jakadan Amirka James Entwistle ne (tsakiya), sai a dama, gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari daga hagu sai kuma Mataimakinsa, Malam Ibrahim Wakkala a Gusau. Ayodele Durodola ya ]auko hoton.

Daga Idika U. Onyukwu Editan Magama

Ambasada Entwistle ne suke musayar kyauta da mataimakin gwamnan Jihar Kaduna Nuhu Audu Bajoga. Idika U. Onyukwu ya ]auko hoton.

Page 9: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 9

Matar Jakada, Dr. Pam Schmoll sai Jakada Entwistle (tsakiya) take gaisawa da Shugaba Shehu Shagari. Idika U. Onyukwu ya ]auko hoton.

Hoton tsakiya daga hagu: Darakta a USAID, Mike Harvey da Jakada Entwistle suke duba wani aiki da USAID ta ]auki nauyi a Sakkwato. Hoton dama: Jakada Entwistle yake gwada famfon tu}a-tu}a wanda USAID ta ha}a a wani ]akin shan magani. Hoto na }asa: Jakada Entwistle tare da Mai Alfarma Sultan Sa’ad Abubakar na uku. Idika U. Onyukwu ya ]auki hoton.

wa gwamnatin Jihar Kaduna cewar, }asar Amirka da Jihar na aiki tare wajen inganta al’amuran ilimi da tsaro da kiwon lafiya da saka jari da kuma al’adu. “Amirka ba ta zo ba ne don ta yi wa Nijeriya abubuwa, sai dai su yi abubuwa tare da Nijeriya, saboda mu hu]u, mu inganta rayuwa a duniya.”

Da yake ci gaba da bayani, Jakadan ya ce zuwan sa Kaduna shi ne na farko a Duba shafi na 21

Page 10: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 10

Jakadan Amirka da kuma mai bayar da shawara, Thomas

Shannon sun shawarci matasan Nijeriya da su yi ayyukan da zai inganta }asar su a idon duniya. Jakada Shannon wanda shi ne ya wakilci tawagar Amirka a lokacin taron cika shekaru 100 na kasancewa Nijeriya }asa ]aya a watan Maris, ya yi bayani a lokacin yaye ]aliban makarantar Carrington ta matasa (CYFI), wanda ofishin }aramar Jakada da ke Legas ya ]auki nauyi. Matasa 15 suka shiga shirin a shekarar 2013.

“A matsayin ku na matasa wanda Allah ya yi wa baiwa, kuna da ]imbin }warewa da za ku taimaka wa unguwannin ku, musamman a wannan lokaci

da ake neman ci gaban ha~aka tattalin arzi}in }asa da na siyasa” in ji Jakadan.

Ya }ara da cewa, “Ina fata sana’ar da ku ka koya a wannan makaranta, zai taimaka wajen inganta rayuwar ku, saboda matasan

yanzu su ne shugabannin gobe.”

Shi ma da yake jawabi, }aramin Jakadan Amirka, Jeffrey Hawkins ya bayyana makarantar ta CYFI da cewar, “babban abin alfahari ne kafa ta

tare da ha]in gwiwa tsakanin matasa masu baiwa daga Nijeriya da kuma Jami’an diflomasiyya na Amirka.”

Makarantar ta CYFI tana taimakawa da ku]i don gudanar da ayyuka, kuma “muna bayar da isasshen lokacin da ya dace domin inganta ci gaban masu koyon sana’ar, a cewar Jeffrey Hawkins.

Shirin na CYFI an sa ne da sunan tsohon J akadan Amirka a Nijeriya, Walter Carrington, kuma cibiya ce aka }ir}iro na horar da matasa wanda aka }addamar a shekarar

Jami’in sashin harkokin }asashen wajen Amirka, Thomas Shannon yake mi}a wa ]alibin da ya kammala karatu a cibiyar Walter Carrington da ke Legas. Ayodele Durudola ya ]auki hoton.

Mambobin shirin CYFI ke zaune.

Amirka Ta Shawarci Matasan Nijeriya Da Su Yi Ayyukan Da Zai Inganta {asa

Duba shafi na 21

Page 11: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 11

A daidai lokacin da Oga jakada ya samu sukunin halartar

gidan Rediyo don saduwa da Oga Madam na gidan Rediyon da ake gabatar da shirye-shirye cikin harshen gur~ataccen turanci ko gargaliyyar turanci, masu sauraron gidan Rediyon sun kasa kunne domin sauraron yadda jakadan na Amirka zai kwa~a turanci irin na gargaliyya, kasancewa ya saba da turancinsa na ainihi.

Babban ba}on, wato Jakada James Entwistle na Amirka a Nijeriya yana jin turanci da Faransanci da Siamese.

Mai gabatarwa ita ce Omotunde David, wanda ake kira da la}anin Omotunde Lolo, Oga Madam ta Rediyon Wazobiya FM da ke Legas, ba ta magana sai da harshen gur~ataccen turanci. Yaya za a yi ke nan? Sai dai, Jakada Entwistle wanda ya ta~a aiki a }asashen

Nijar da Kamaru da Afirka ta tsakiya, kafin ya zo Nijeriya, a shirye yake tsaf don fuskantar }alubalen da aka yi ranar 30 ga watan Janairu, 2014.

How you dey? “I dey kampe,” da irin wannan gur~ataccen turancin aka marabci jakadan a gidan rediyon. Daga nan aka ta maganganu na ban dariya wanda masu gabatarwa kamar Yaw Yaw da Nedu da Diplomatic OPJ da Igos suka taya Lolo gabatar da

“Ga Jakada da ya }ware a Turanci da Faransanci da harshen Siamese, zai yi kyau ya ta~a turancin gargaliya ko da harshen sa ya ma}ale wajen }aranta” labari daga Bam, hoton Mutum-mutumi daga Mujallar TELL.

Jakadan Amirka Ya Buga Turancin Gargaliyya A Gidan Rediyo

Page 12: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 12MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 12

shirin. Bayan an kammala gaisuwa ne sai aka fara tambayar Jakadan, kan batun auren jinsi, wanda gwamnatin Amirka ta yi barazanar ]aukar matakin duba dangantakar }asashen biyu, saboda Nijeriya ta yi dokar hana auren jinsi ]aya.

Daga nan ne sai Jakadan ya ce, shi bai ce Amirka za ta ]auki matakin ladabtarwa kan Nijeriya ba, ya kuma ce zai maimata abin da ya fa]i cewar, Amirka ba ta ce za ta ladabtar da Nijeriya game da batun auren jinsi ba.

Ko shakka babu, Jakadan bai ji da]in yadda

ake ta maganganu game da yadda Amirka ta yi tanka kan auren jinsin ba, wanda shugaban N ijeriya ya sanyawa hannu don haramtawa.

Wani batu da aka ta~o, shi ne za~en 2015, inda

aka tambayi jakadan ko wane taimako Amirka za ta baiwa Nijeriya

don tabbatar da an samu za~e na gaskiya, da zai samar da shugabannin da za su tafiyar da }asar bisa amana.

Sai jakada ya ce, “Da farko ina so in shaida miki cewar, Amirka ba ta da ]an takara nata.

Ya ci gaba da cewa, su dai abin da suke son gani, shi ne an gudanar da za~en gaskiya wanda mutanen Nijeriya za su amince da shi.

Ya kuma amsa tambayoyi game da ta’addancin tsagerun Neja-Delta da tsaron teku da kuma shirin Shugaban Amirka na Shugabancin Matasa a Afirka, (YALI).

Wani tambaya da ake zaton zai taso, shi ne na samun izinin shiga }asar Amirka, wato biza, inda mai gabatarwar ta tambaya, cewar wai shin me

Ambasada Entwistle a ]akin gabatar da shirye-shirye na gidan rediyon Wazobiya da suke ya]a shirinsu da turancin gargaliya.

Dama zuwa hagu – Pamella Schmoll, sai matar Jakada, sai Omotunde Lolo ta Rediyon Wazobiya, sai Jakada Entwistle.

A gidan rediyon Wazobiya, hagu zuwa dama, Entwistle, biyu daga hagu da tawagar sa, da matar sa Pamela da Jeffrey Hawkins }aramin Jakada (su ne na biyu da na farko), tare da tawagar Rediyo Wazobiya, Omotunde Lolo ta uku daga hagu da Igos da kuma Ago.

Duba shafi na 23

Page 13: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 13

Amirka Ta Haramta Ta~a Ku]in Sata Na

Janar Abacha Har Dala Miliyan 458.

Ma’aikatar Shari’a ta Amirka ta haramta ta~a

ku]in da marigayi Janar Sani Abacha ya mallaka ta hanyar cin hanci da r ashawa da kuma sata.

A wani }ara kan dokar }wace kadara ko ku]in da ba a samu ta hanyar doka ba, da aka shigar ranar 5 ga watan

Maris, a wata kotu da ke jihar Colombia ta }asar Amirka, ta nemi a kar~e fiye da dalar Amirka miliyan 550 da ked a ala}a da mummunan halin sata da aka ta~a kawowa a tarihin ma’aikatar shari’ar.

Hana ta~a ku]in ya kama daga a}alla dala miliyan 313 a bankuna biyu dake Bailiwick da ke jihar New Jersey da

113

Duba shafi na 14

Mataimakiyar Sakataren }asashen waje mai kula da Afirka, Linda Thomas-Greenfield ta jagoranci tawagar Amirka zuwa taro game da gwamnati, gaskiya da kuma masu son ganin tsafta a dukkan mu’amala, na hukumar }asashen Amirka da Nijeriya (BNC) wanda aka gudanar a Abuja ranar 17 zuwa 18 na watan Fabrairu.

Tawagar Amirka sun ha]u da ma’aikatar }asashen waje na Nijeriya da na ma’aikatar shari’a da hukumar za~e ta }asa (INEC), da hukumar ya}i da tu’annatin ku]i (EFCC), da hukuma mai zaman kanta wajen ya}i da cin hanci da rashawa (ICPC). Ma’aikatar harkokin }asashen waje ne ta ]auki nauyin taron, wanda babban sakatare a ma’aikatar, Dr. Martin I. Uhomoibhi ya gabatar.

Ga kuma jawabin bayan taron na ha]in gwiwa;

{asashen Nijeriya da na Amirka sun fahimci cewar, wajibi ne a sami kar~a~~en za~e wanda aka gudanar cikin lumana don samun }asa ]aya dun}ulalla. {asashen biyu sun amince da cewa, muddin ana son samun za~e nagari dole ne a yi kyakkyawan shiri don gudanar da za~u~~ukan.

{asashen biyu har wa yau, sun yarda da ci gaba da kawo ci gaba domin gyara harkar za~e a }asar kamar yadda hukumar za~e ta zayyana. Haka kuma sun fahimci lahani da tashin hankali ake haddasawa a lokacin kamfe da takara. Nijeriya ta nuna }udurinta na kawo }arshen ta’addanci da duk wani nau’in tashin

BNC: Tana Goyon Bayan Za~e Na Gaskiya

Mataimakiyar Sakataren harkokin wajen Amirka mai lura da Afirka, Linda Thomas-Greenfield da Babban Sakatare a ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya Uhomoibhi, a bu]e taron BNC. Idika Onyukwu ya ]auko hoton.

Duba shafi na 22

Page 14: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 14

dala miliyan 145 a bankuna biyu da ke }asar Faransa. Da]in da]awa, akwai kadarori a }asar Birtaniya da darajar su ya kai dala miliyan 100 da su ma aka hana ta~awa, duk da haka ana sa ran tabbatar da ha}i}anin ku]in nan gaba.

Mu}addashin babban mai shari’a na ma’aikatar shari’ar, Mythili Raman wanda kuma yake ~angaren sashin masu aikata manyan laifuka da kuma mataimakin darakta, Valerie Parlake ta ma’aikatar tsaro ta FBI da ke ofishin Washington ce ta bayar da sanarwar. Ta ce, “ba za mu yarda a mayar da bankunan mu inda shugabanni masu kama- karya za su ri}a ~oye ku]in da suka sace ba, wannan }o}ari na FBI ya tabbatar da ho~~asan da suke yi na hana tu’annati da ku]in sata da zamba cikin aminci da wasu ke yi.”

“Ina matu}ar godiya ga jami’an tsaro da }wararru a fannin ku]i da sauran wa]anda suka agaza wajen gano wannan bada}ala a aikin da suka yi na shekaru goma da suka gabata.”

14

jagoranci tattaunawar a yayin da ministan ciniki da kasuwanci na Nijeriya Olusegun Aganga ya jagoranci Nijeriya.

“Nijeriya da Amirka na da da]a]]en tarihi game da kasuwanci da saka jari,” a

cewar wakilin Amirka. A matsayin ta na babbar kasuwa a Afirka ta Yamma, kuma wadda tattalin arzi}inta na da girma a nahiyar Afirka, Nijeriya na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzi}in nahiyar.”

“Jimillar kasuwancin da ke tsakanin Amirka da Nijeriya (tsakanin kayayyakin da ake shigowa da su da wa]anda ake fitarwa) ya kai dala biliyan 18 da miliyan 2 a shekarar 2013, in ji USTR. {asar Amirka ta fitar da kaya daga Nijeriya da yawan su ya kai dala biliyan 11 da miliyan 6 kuma duka ]anyen man fetur ne. Kayayyakin da ba na man fetur ba, daga Nijeriya zuwa Amirka sun ha]a da fata da wake da koko da rogo.

Kayayyakin da ke

{arfafa Harkar Kasuwanci Da JariAmirka Da Nijeriya Sun

A ranar 11 ga watan Maris, 2014, gwamnatin Amirka

ta ]auki nauyin taro karo na takwas kan yarjejeniyar kasuwanci da saka jari (TIFA) inda ake ha~aka yanayi da kuma }arfafa dangantakar da ke tsakanin }asashen biyu.

Tattaunawar ta ta’ala}a ne kan manufofi da dama, da suka ha]a da hanyoyin ha~aka kasuwanci da amfani da dokar samun damar ha~aka ci gaban Afirka (AGOA), da kare ayyukan fasaha, da gudanar da sabon yarjejeniyar }ungiyar kasuwanci da inganta yanayin saka jari tsakanin }asashen biyu, kamar yadda aka bayar da labarai daga ofishin wakilin kasuwanci na Amirka.

Mista Michael Froman, wakilin }asar Amirka ne ya

Olusegun O. Aganga

For more, visit http://www.justice.gov/Duba shafi na 23

Page 15: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 15

A ranar Juma’a, 7 ga watan Maris, a Birnin Abuja, hukumar ci

gaban }asashe na Amirka, (USAID) da ha]in gwiwar hukumar kula da cinikayyar kayayyaki daga Nijeriya zuwa }asar waje (NEPC), suka kar~i ba}uncin mata ’yan kasuwa su takwas a wani

biki na baje kolin kayayyaki da kuma wakilci daga Le look da Sheacoco da Oluchi da Gems da Gurara, wa]anda suka halarci bikin baje kolin kayayyakin.

An yi bikin baje kolin ne don karrama ranar mata ta duniya na shekarar 2014 a Nijeriya. An samu halartar

wa]anda suka baje kolin da suka fito daga jihohin Legas da Kano da Minna da Nasarawa, da kuma wa]anda suka fito daga Birnin tarayya, Abuja.

“Sana’ata shi ne yin jakunkunan hannu, da rigar sanya na’urar Ipad da kuma jakar ’yan makaranta, kuma

An Shirya Kayayyaki Don Kaiwa {asar Waje

Mataimakiyar Darakta a hukumar USAID, Julie Kolnen take sunsuna man shafawa na kamfanin Shea Coco. Idika U. Onyukwu ya ]auko hoton.

Page 16: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 16

daga dagwalon bola nake ha]a wa]annan kayan,” inji Chinwe Ezenwe, babbar shugabar kamfanin Le Look, ta ci gaba da cewa hukumar kasuwancin kayayyakin Nijeriya zuwa }asar waje ta taimaka mini don inganta sana’ar ta yadda zan iya sayar da kayan sana’ata zuwa }asar waje. Yanzu haka ina da shaguna a Legas da Abuja.

Hukumar ta NEPC tare da ha]in gwiwar USAID suna da shirin da ke taimakawa ana sayar da kayayyakin gona da na sana’ar hannu zuwa }asashen waje.

Hukumomin USAID da na NEPC sun }ulla yarjejeniyar fahimta a watan Fabrairu, 2014 don }arkafa wa ’yan kasuwa inganta sana’ar su ta yadda kayan su zai kar~u a

Hoto na sama: Chinwe Ezenwa (na biyu daga dama sai babban Jami’I, Le Look ke ri}e da jaka a bikin baje koli da USAID ta shirya.

Daga tsakiya, Mataimakiyar Darata ta USAID, Julie Kolnen (a dama) sai Kodinata ta shiyya, na shirin kai kaya waje na mata, Obidike Ifeyinwa take duba kayan fata da aka yi.

Hoto na }asa: Tsakiya na masu kaya ne daga kamfanin Oluchi James, an baje kolin su. Hotuna daga Idika Onyukwu.

Duba shafi na 22

Page 17: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

CROSSROADS | 2014 March-April Special Edition 17CROSSROADS | 2012 U.S. Election Special 17MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowar Musamman 17

makarantun firamare da ke Nijeriya. Ta ci gaba

A gaba ]ayan cibiyoyin, ku na koyon ilimin

kwamfuta, da taimakon africoder Dojo karon farko, kuna taimakawa wajen inganta ilimin matasa domin gobe.” Da wa]annan bayanai ne Jami’ar sashin hul]a da Jama’a ta ofishin Jakadancin Amirka, Dehab Ghabreab ta taya gidauniyar Oando murnar }addamar da cibiyar africoderDojo/ICT wanda ya samu taimakon sashin hul]a da }asashen waje na Amirka da aka gudanar a makarantar firamare ta tunawa da Acibishop Taylor da ke Legas. Ta ci gaba da cewa, “wannan ya nuna }arara irin azamar inganta sana’ar ilimin kwamfuta a tsakanin matasan Nijeriya.”

{addamar da cibiyar koyon aikin kwamfutar ya zo daidai da }addamar da na africoderDojo a Nijeriya (a ziyarci http://coderdojo.com/tags/africoderdojo). A cewar daraktar gidauniyar Oando, Tokunbo Durosaro, gidauniyar ta }ir}iro cibiyar koyon ilimin kwamfutar ne saboda cike gurbi da ake da shi na ilimin na’urar a

da cewa, a halin yanzu gidauniyar ta kai irin wannan ilimi zuwa makarantu 47 a jihohi 19 da ke Nijeriya, inda ake koyar da malamai da ]alibai ilimin, da kuma baiwa wa]anda suka cancanta gurbin }aro ilimi.

Africoder Dojo wani yun}uri ne

da aka yi na musamman wa matasan Afirka domin koyon yadda ake sarrafa ko }ir}iro wasu dabaru na amfani a kwamfuta, kamar yadda ake yin adireshin na’urar kwamfuta ko }ir}iro yanar-gizo ko

{arfafa Wa Matasan Nijeriya Samun

Ilimin Kwamfuta

Hoton ]alibai lokacin }addamar da cibiyar kwamfutar.

Hoton mahalarta taron }addamar da na’urar kwamfutoci da africoder Dojo, a Legas.

Duba shafi na 23

Page 18: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 18

cibiyoyin matasa inda za su ri}a aikin sa kai, kamar bayar da shawarwari game da dogaro da kai da taimaka wa marasa galihu da marayu da ziyartar gidan yari da asibiti da gidajen kangararru.

Ba kawai matasa na tambayar dalilin da ya sanya abubuwa ba sa kyau ba ne, har ma sukar ce, “me zan yi don inganta shi? Muna jinjina masu }warai da gaske. Ofishin Jakadancin Amirka da mutanen YALI da suka gana da matasan daga Washington na mi}a godiyarsu a bisa damar da suka samu na tarihi da ake kan kafawa. Duk da cewar ba mu gayyaci matasa da dama ba a wannan shekara, mun yi aiki tu}uru wajen ganawa da matasan Nijeriya daga ~angarori da dama don shiga shirin na YALI, 2014.

Har ila yau, muna }o}arin ganin mun sama wa sauran ]aruruwan matasan da muka gana dasu wani abin yi, da kuma sauran da suka rubuto don neman shiga wannan shirin. Dukkan ku kun kasance wa]anda za a iya dogaro dasu wajen kawo canji na ci gaba a Nijeriya. Muna mi}a fatar alheri ga wa]anda suka samu nasarar shiga shirin YALI 2014 da kuma wa]anda suka nemi shiga shirin. Ambasada James F. EntwistleJakadan Amirka A Nijeriya

A cikin watan Agusta na 2010, kuma a lokacin bikin cika shekaru 50 da samun ’yancin kai na }asashen Afirka, Shugaba Obama ya gayyaci shugabannin matasa fiye da 115 daga }asashen Afirka fiye da 40 zuwa fadar sa ta White House. Shugabannin matasan sun kwashe fiye da kwanaki uku suna musayar ra’ayi kan tafiyar da gwamnati mai kyau da hanyoyin tattalin arzi}i da kuma }awance tsakanin Afirka da Amirka.

A watan Yuni, 2011 – Matar Shugaba Obama ta jagoranci taron shugabanni mata na kwanaki biyu a Johannesburg da Soweto a Afirka ta Kudu kuma matasa mata fiye da 75 ne suka halarta. Taron ya ta’alla}a ne kan }ara wa mata }warin gwiwa da ayyukan ci gaba na unguwanni da kuma fahimtar cewa, mata ne ke ri}e da makullan gina nahiyar Afirka.

Taron bayar da shawarwari na game da shugabancin matasa da kuma kawo canji.

A watan Yuni na 2012 – Gwamnatin Amirka ta tara fiye da mutane 60 daga }asashen Afirka 35 don gudanar da taro kan kawo canje-canje, da aka yi a Washington DC. Haka kuma an samu mako biyu inda ake aikin abubuwan da aka koya don a samu }warewa a }asar ta Amirka, inda aka sadu tsakanin ’yan kasuwar Amirka da shugabannin }ungiyoyin farar hula da kuma matasan ’yan kasuwa da suka fito daga Afirka.

Shirin YALI A Cikin Shekaru

Zauren Shugaba Obama tare da shugabanni matasa daga Afirka.

Zauren matar Obama tare da shugabanni matasa daga Afirka.

Daga shafi na 2

YALI: Jakadan Amirka Ya Gode Wa Matasan Nijeriya

Page 19: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 19

Haske Ya Bayyana A [akunan Karatu Na Nijeriya

A ranar 19 ga watan Maris, gwamnatin Amirka a shirinta na

taimaka wa harkar ilimi a Nijeriya, ta kai wasu kayayyaki ]akunan karatu a wasu jihohi na arewa. Jihohin sun ha]a da Binuwai da Nasarawa da

Kaduna da Neja da Kogi da kuma Birnin Tarayya Abuja. Kayayyakin sun ha]a da fitila }irar HD8.9 4GLTE da na’urorin WIFI da kuma bayar da hanyoyin aiki da yanar-gizo kyauta na tsawon wata shida.”

Jami’an cibiyoyin karatun su shida da aka za~o, sun sami horo na kwana ]aya game da yadda ake amfani da na’urar hasken, wadda cibiyar samun labarai ta Abuja ta bayar. Jami’a Malore Brown ce ta gudanar da horon. Na’urar hasken wani siriri ne mara

nauyi da ke haskakawa don karatu, kuma ana iya

kwashe bayanai a na’urar don }arin ilimi. Kamfanin Amazon.com na Amirka mai }ir}iro kayayyakin amfani da hasken wuta ne suka yi na’urar, kuma shi ne kamfani mafi girma dake sayar da kaya ta hanyar yanar-gizo.

Wannan na’ura na da }arfin ajiye bayanai na littattafai da mujallu da wa}o}i da bidiyo.

Za a ajiye na’urorin ne a ]akunan karatu shida da aka ke~e don gwaji, wanda wani sashi ne na kula da harkokin Afirka da ke }ar}ashin ma’aikatar

Jami’ar cibiyar ya]a karatu ta ofishin Jakada Malore Brown (ta biyu daga dama a jerin farko) take mi}a na’urar hasken kyandir ga cibiyoyin karatu da ke Abuja, ranar 20, ga Maris 2014. Idika Onyukwu ya ]auko hoton.

Daraktar cibiyar ya]a karatu, Elizabeth Akinbulumo (ta biyu daga hagu), take bayanin yadda ake amfani da na’urar kyandir wa gami’an cibiyar karatu. Idika Onyukwu ya ]auki hoton.

Duba shafi na 21

Page 20: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 20

amana da jami’an tsaro masu gaskiya da ’yan majalisu na }warai da al}alai da ’yan jarida da }ungiyoyi masu zaman kansu.

Kamar yadda ake bu}atar hukumomin siyasa masu }arfi da inganci, haka ake bu}atr bin doka da }ungiyoyin farar hula wa]anda za su samu goyon bayan ’yan jarida masu tsage gaskiya, don samar da harkar dimokura]iyya wanda zai baiwa duk wanda ya ci za~e da wanda ya fa]i }warin gwiwar amincewa da sakamakon za~en. {ungiyoyin farar hula ka iya sanya ido kan ’yan siyasa da suka fa]i za~e don gudun kar su dagula al’amura.

{ungiyoyi da ba na gwamnati ba, na iya taimakawa wajen ganin ’yan siyasa wa]anda ke neman }uri’a da za~a~~u sun mutunta sakamakon za~e da hanyoyin gudanar da za~en.

Suna iya shirya wani taron tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma da kuma samar da bayanan da za~a~~u da jami’an gwamnati ke bu}ata. Suna iya matsa wa gwamnatin da aka za~a ta cika al}awarin

da ta ]auka. {ungiyoyin farar hula na iya kawo canji ta sanya gwamnati ta yi abin da al’umma ke bu}ata.

Yanar-gizo da sauran kafofin ya]a labarai na zamani suna taimaka wa }ungiyoyi wajen samun bayanai da za su yi amfani da su don musayar bayanai don sanya gwamnati ta ri}a aikata gaskiya a harkokinta. Irin wa]annan sababbin kafofin samun labarai na zamani na taimaka wa }ungiyoyin fa]a]a abokan hul]ar su da kuma }arin mambobinta.

Misali a nan shi ne, a lokacin bayan za~e a }asar Iran, al’umma sun yi amfani da kafofin ya]a labarai na zamani don tambayar halascin za~en da kuma shaida wa duniya halin da ake ciki game da yadda aka gudanar da za~en.

Tsohuwar ministar }asashen waje ta Amirka, Hilary Clinton ta danganta irin wa]annan }ungiyoyi a matsayin masu mahummanci wajen tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati. Ta ce, “{ungiyoyin farar hula sun kasance a tsaye wajen tursasa wa gwamnatoci su bauta wa al’ummarsu yadda ya kamata. Ta ci gaba da cewa, }ungiyoyin suna wayar da kan al’umma wajen fahimtar da su hanyoyin da za su bi don tsawata wa gwamnati ta bi tafarkin

gaskiya wajen mulkarsu.

A mutunta lokacin bayan za~eMulkin dimokura]iyya

na samar da wasu hanyoyi da al’umma za su ri}a zato da kuma fahimta, wanda ya ha]a da mutunta bin doka sau da }afa da kuma kar~ar sakamakon za~e a duk yadda ya zo. A lokacin da yake jawabi a }asar Kairo a 2009. Shugaba Obama ya jaddada gaskiyar irin wa]annan batutuwa, inda ya ce, “A duk yadda aka ka]a aka raya, gwamnati ta jama’a wadda jama’a suka za~a tana gaba wajen yin abin koyi don wasu su yi koyi.

Wajibi ne ka somo mulkin ka bisa yarda, ba da }arfi ba, dole ne a martaba ’yancin marasa rinjaye, a kasance ana da jimirin ha}uri da fahimta, kuma wajibi ne a kula da abin da al’umma ke bu}ata da kuma bin tafarkin gaskiya a harkar siyasa fiye da jam’iyyar ka, idan babu wa]annan muhimman abubuwa, za~e kawai baya tabbatar da dimokura]iyyar gaskiya.

Mutunta bin doka da ingantattun hukumomin siyasa da kuma }ungiyoyin farar hula masu }arfi. Wa]annan na iya tabbatar da mi}a ragamar mulkin

Fiye Da Za~eDaga shafi na 7

Duba shafi na 22

Page 21: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 21

shiyyar arewa, kuma sai ya dangana da Jihar Sakkwato ya isa Kaduna ne ranar 8 ga watan Fabrairu.

Ya ce a matsayinsa na Jakadan Amirka a Nijeriya, zai ci gaba da tabbatar da ingantuwar dam}on zumunci tsakanin }asashen biyu.

Tawagar Jakadan da suka kai ziyara Kaduna da Zamfara sun ha]a da, Mike Harvey, darakta a

hukumar taimakon }asashe na Amirka (USAID), da Dr. Pam Schmoll, matar Jakadan da Laura Harvey, matar daraktan.

Har ila yau, tawagar Jakadan ta isa jihar Sakkwato a ci gaba da ziyarar tasa.

A Jihar ta Sakkwato, tawagar ta ha]u da gwamnan Jihar, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko a gidan gwamnatin Jihar, kuma

ya ziyarci tsohon shugaban }asa, Alhaji Shehu Shagari a gidansa.

Tawagar ta ziyarci wasu ayyukan ci gaba da USAID ke yi, da suka ha]a da makarantar koyon sana’a da kuma ]akin shan magani a }aramar hukumar Wamakko.

Kafin su koma Abuja, Jakada Entwistle sun kai wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ziyara a fadar sa.

2011 da ofishin jakadanci da ke Legas ya yi.

Cibiyar ta CYFI ta ha]a kawunan matasa masu baiwa da haza}a da zurfin tunani da }warewa domin su }ir}iri hanyoyin da za su kawo abubuwan ci gaban }asarsu. Jakada Walter Carrington ya kasance ]an gwagwarmayar }ungiyar farar hula da dimokura]iyya, kuma ya kusantar da dangantaka tsakanin Nijeriya da Amirka.

Cibiyar ta CYFI da mahalartanta sun ]auki }udurin tabbatar da ganin sun yi koyi da irin tunanin Jakada Carrington, sun kuma yi amfani da shi. Shugabannin Cibiyar CYFI da ha]in gwiwar sashen hul]a da jama’a da ke ofishin jakadanci na Amirka a Legas, sun za~i mahalarta cibiyar da suka yi fice, aka ke~e su gida-gida bisa sha’awarsu ko }warewar su. Kowane gida suka }ir}iri wani aiki na musamman game da abin da suka

koya ne tsawon shekara ]aya da suka yi. Baya ga aikin da suka yi na kowane gida, mahalartan na CYFI na da damar shiga duk wani taro ko harka da ofishin jakadancin Amirka dake Legas ya shirya a kan batutuwa na zamantakewa.

Daga }arshe an }arrama wa]anda suka yi fice kuma aka }addamar dasu a matsayin ’yan }ungiyar tsofaffin ]alibai.

}asashen waje ta Amirka da ke Washington DC. Ita dai wannan na’ura za ta bayar da zarafin samun bayanai kyauta ga masu amfani da cibiyoyin karatu.

Su dai cibiyoyin karatu

sun kasance wuraren da al’umma ke samun bayanai da ake bu}ata. Kuma suna samar wa makaranta komai shekarun su littattafan da suke bu}ata da na bincike da littattafai na labaran

gizo da }o}i.A lokacin da ake bayar

da kayayyakin, Brown ta ce, “muna fata wannan babbar kyauta da muka bayar, za ta baiwa ’yan Nijeriya }warin gwiwar kasancewa sun la}anci al’adar yin karatu.”

Jakadan Amirka Entwistle Ya Yi Kira Ga ’yan Siyasa...Daga shafi na 9

Daga shafi na 10

Daga shafi na 19

Amirka Ta Shawarci Matasan Nijeriya...

Haske Ya Bayyana A [akunan Karatu Na Nijeriya

Page 22: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 22

kasuwannin duniya.Kayayyakin sun ha]a

da yazawa da fata da tufafi da abinci da koko da ‘ya’yan itatuwa da abincin ruwa da sauran su wanda ake samu daga Afirka ta yamma da kasuwannin Amirka, }ar}ashin shirin fa]a]a harkokin kasuwanci da na sufuri (NEXTT), }ar}ashin jagorancin USAID.

Kayayyakin da aka baje kolin su, sun ha]a da wa]anda aka yi da fata kamar jakar mata da takalma da kushin da timtim da ]an kunne da yari da sauran kayayyaki. Har ila yau, akwai wasu kayayyakin da aka baje kolin su kamar

man shafawa da man gashi da maganin amosanin kai, wa]anda aka yi su daga man kwakwa da wasu itatuwa, kuma duk sun samu shiga a kasuwar baje kolin.

A jawabin da ta yi lokacin bikin, mataimakiyar darakta a ofishin jakadancin Amirka, Julie Koenen, ta gode wa matan su takwas da suka baje kolin inda ta }ara da cewa babu shakka sun haskaka ranar bikin mata ta duniya da kayayyakinsu masu ban sha’awa. Ta ce hukumar USAID da ha]in gwiwar NEPC sun shirya bikin ne don nuna ci gaban

da mata ke samu a Nijeriya.A }ar}ashin shirin nan

na dokar da ta bayar da damar ha~aka nahiyar Afirka (AGOA), an ]auke wa Nijeriya biyan ku]in fito wajen fitar da wasu kayayyaki zuwa }asar Amirka, kamar ‘ya’yan itatuwa da jus da ci kwi da jaka da kifi busasshe da takalma da tufafi da sauransu. Sai dai duk da haka }asar ba ta samun amfani da ya dace daga hukumar ta AGOA. Tun da an kammala bikin taron baje kolin wanda USAID ta shirya, akwai wasu damar da wa]annan mata za su samu don ci gabansu.

siyasa cikin lumana, muddin an yi aiki kafa]a da kafa]a.

{asashen da hukumomin siyasa ke wakiltar al’ummomi da dama, kuma suna tunawa da bu}atun al’umma, su kuma samar da yanayin tattaunawa a siyasance, a kuma gudanar da bin

doka yadda ya dace ba tare da nuna bambanci ba, to, irin wa]annan }asashe na da mutunci matu}a a idon al’umma.

A wannan }asa, tabbatar da samar da canji ta hanyar lumana yana karya gwiwar amfani da tsarin mulki ta hanyar da bai dace ba game da sakamakon za~e, ya kuma taimaka wajen ganin cewar za~e ne hanyar farko na

fa]a]a mulkin dimokura]iyya.“Mutunta bin doka da

ingantattun hukumomin siyasa da kuma }ungiyoyin farar hula masu }arfi, wa]annan na iya tabbatar da mi}a ragamar mulkin siyasa cikin }ima, muddin sun yi aiki kafa]a da kafa]a.”

hankali lokacin za~e.{asar Amirka ta shirya

domin bayar da taimako wajen gudanar da shirye-shirye.

Duk }asashen, sun

auna muhimmancin gudunmawar da majalisun dokoki, ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da }ungiyoyin fararen hula da ’yan jaridu

ya kamata su bayar don ci gaban }asa da tabbatar da al’adar mulkin dimokura]iyya. Akwai }arin karatu a: http://nigeria.usembassy.gov/ae02191412.htm/.

Daga shafi na 20

Fiye Da Za~e

Daga shafi na 16

Daga shafi na 13

An Shirya Kayayyaki Don Kaiwa {asar Waje

BNC: Tana Goyon Bayan Za~e Na Gaskiya

Sakon edita- dukkan ra'ayin da aka bayyana a wannan kasida ,

ba manufa ko ra'ayin gwamnatin tarayya bane.

Page 23: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

MAGAMA | Maris zuwa Afrilu, 2014 Fitowa Ta Musamman 23

shigowa Nijeriya daga Amirka sun tasar ma dala biliyan 6 da miliyan 5 a shekarar 2013. Manyan kayayyakin Amirka da suka shigo Nijeriya sun ha]a da motoci da kayayyakin gyaran motoci da alkama da robobi. Jarin da Amirka ta sanya a Nijeriya, ya kai dala biliyan 8 da miliyan ]aya a shekarar 2012, }ari ne da ya kai kashi 53 cikin

100 daga shekarar 2011.Hukumar TIFA,

~angare ne na samar da }wa}}waran yanayi na gudanar da dokokin cinikayya da kawo masu saka jari a Nijeriya da kuma tabbatar da ]orewar ci gaban al’amuran kasuwanci. Hukumar ta TIFA har way au na aiki don ha~aka ha]in kai tsakanin Amirka da Nijeriya don fa]a]a hanyoyin ma’aikata da

manoma da kasuwanci da masu saye na }asashen biyu.

{asashen biyu sun sanya hannun yarjejeniyar ce na TIFA a shekarar 2000. Hukumar na aiki ne don tabbatar da ana samun damar tattaunawa game da dangantakar }asashen Amirka da Nijeriya ta fuskar kasuwanci da saka jari. A bara ne aka gudanar da taron TIFA a Abuja, Nijeriya.

wasanni da sauran shirye shirye. A bisa la}anin CoderDojo na duniya (http://coderdojo.com/), africoderDojo ya dogara ne kan abokai ko }awaye da masu sa kai su koya wa matasa }arancin ilimin na’urar a ko’ina da ake da kwamfuta da na’urar gizo.

An }ir}iro africoder Dojo ne sakamakon ha]in gwiwa da aka yi tsakanin CoderDojo da sashin harkokin }asashen waje na Amirka.

Jami’ar ya]a labarai Ghebreab ta ce an tsara

africoder Dojo da gudanar da kuma koyar da shi ne wanda }wararru na duniya a kan ci gaban makarantun karkara da jami’o’i da kamfanoni a fa]in Afirka suka yi.

“Ta irin wa]annan hanyoyin nuna haza}a ne matasa suka ci gaba, sannan }aunar fasaha ta shigesu, kuma za mu ci gaba a wannan turba.”

Jami’ar ta lura da cewa a cibiyoyin na kwamfuta yara ke samun damar ha]uwa da ’yan uwansu masu tunani iri

]aya. “Kuma suna ha]uwa da }wararru da ke ba su }warin gwiwar samun wasu hanyoyin da ke da ala}a da amfani da kwamfuta.”

Wa]anda suka halarci }addamarwar, sun ha]a da kwamishinan ilimi na jihar Legas, Olayinka Oladunjoye da Dr. Odein H. Ajumogobia, shugaban amintattu na gidauniyar Oando da sauran jama’a da kuma wakilan gidauniyar Ford da Lego, da Jami’an }aramar hukuma.

’yan Nijeriya suka yi wa }asar Amirka ne da basa son basu biza. Sai ya amsa da cewa;

“Na yi mamakin jin haka.” Inda ya ce yanzu haka akwai

mutane da dama da za a baiwa takardar izinin shiga }asar Amirka, bayan sun nema. Ya }ara da cewa, a yanzu haka ma, mutane ba sa da]ewa wajen kar~ar biza.

Mai gabatarwa, wato Omotunde Lolo wadda ta yi karatun lauya a jami’ar Legas ta yi maganganu da dama na ban dariya tare da Jakadan.

Daga shafi na 14

Daga shafi na 17

Daga shafi na 12

Amirka Da Nijeriya Sun {arfafa Harkar Kasuwanci Da Jari

{arfafa Wa Matasan Nijeriya Samun Ilimin Kwamfuta

Jakadan Amirka Ya Buga Turancin Gargaliyya A Gidan Rediyo

Page 24: MAGAMA - photos.state.gov · Shirin na YALI na taimaka wa wa]anda suka shiga shirin wajen samun damar aikata abubuwan da suka koyo a ziyarar tasu Amirka, musamman don ha~aka tattalin

Maganar Kerry Kan Hare-Haren Boko Haram A Nijeriya Tashin hankali da bala’in da ’yan Boko Haram suka aikata a arewacin Nijeriya satin da ya gabata, suna da muni kuma ba daidai ba ne, ba su da gurbi a wannan duniyar tamu. An kai mummunan hari ranar Asabar da ta gabata a }auyen Izge da ke Nijeriya kusa da iyakar }asar Kamaru inda aka rasa rayukan

wa]anda ba su ji ba kuma bas u gani ba, su ]ari. {asa da mako ]aya bayan ’yan Boko Haram sun kai farmaki a garin Bama inda suka }ona gidaje 1,500 da kuma mutane da dama da suka samu raunuka. Akwai }arin bayani a: http://goo.gl/IsYVCd.

Ilimi Daga Amirka / Cibiyoyin Samun labaraiAbuja – Legas

Watan Tarihin Mata, 2014 – Bayanan shugabaA tsawon rayuwar tarihin mu, matan }asar Amirka

sun jagoranci gwagwarmayar neman ’yanci kan tattalin arzi}i da kuma adalci da kuma yin abin tarihi kan kimiyya. Matan har wa yau, sun

inganta martabar al’adunmu da fasaha da kuma yin abin a zo a gani a bisa manufofin mu na harkokin }asar waje. Sun bauta wa }asarmu ta fuskokin ya}i, tun daga Hamadar filin daga na Ira}i zuwa manyan tsaunukan Afghanistan.A lokacin bikin tunawa da watan mata, mun karrama nasarori da gwagwarmaya da tarihin matan da suka agaza wajen mayar da }asarmu yadda take a yau. A kara karatu a: http://goo.gl/SeYzeJ.

Bayanan da aka bayar a }asa, ana iya samun su a cibiyar samar da labarai da ke Abuja da Legas. Domin zama mamba sai a yi rajista a – http://tinyrl.com/ircregistration, domin }arin bayani, sai a rubuta zuwa ga: [email protected](north) da kuma [email protected](south).

Wa]annan cibiyoyi da aka yi bayaninsu a }asa, ana iya samunsu a cibiyoyin samun labarai da ke Abuja da Legas. Idan kana sha’awar zama mamba, sai ka ziyarci: http://tinyurl.com/ircregistration, domin duk wani }arin bayani, a rubuta zuwa: [email protected] (Arewa) da kuma [email protected] (Kudu).

Ilimi daga Amirka yana baiwa cibiyoyi shawara a Abuja da Legas ingantacce, kuma sahihan labarai wadanda babu son kai kuma a kan lokaci game da makarantun da aka amince da darajarsu ga duk mai sha’awar karatu a Amirka. Ga duk mai sha’awar son karatun, sai ya ziyarci adireshin nan: http://www.educationusa.state.gov. Cibiyoyin bayar da shawarwari kan ilimi:Abuja: Ofishin Jakadancin Amirka da ke Plot 1075Diplomatic Drive, Central District Area, Abuja.Tarho: 234 – 09 – 4614251/4241/4257;Fax: 234 – 09 -4614334/4010; e-mail: [email protected]. Facebook:http??www.facebook.com/educationusa.abuja.

Legas:US Consulate General, Public Affairs Section,2 Walter Carrington Crescent; Victoria Island, Lagos.Tarho: 01-460-3400/2724/2725/3801/3802 e-mail: [email protected]

Matasan Nijeriya na tattauna makomar ci gaban Legas A ci gaba da aniyarsu ta ganin Legas ta zama }asaitacciyar birni a nan gaba, matasan Nijeriya na ganin cewa ya dace gwamnatin jihar

Legas ta mayar da hankalinta kan ha~aka ilimi da yin tunanin magance al’amura na tsawon lokaci maimakon yin abubuwa cikin gaggawa. Akwai }arin bayani a: http://nigeria.usembassy. Gov/pc – 09152012.html.

Kana bu}atar karatu a }asar Amirka?

Whitney M. Young. Information Resource Centre

Sashin hul]a da Jama'a, {aramin ofishinJakada, Lamba 2 Walter Carrington Crescent,

Victoria Island, Legas, Najeriya.Tarho: 01-460-3400Fax: 01-1-261-2218

e-mail: [email protected] bu]ewa ranar Litinin zuwa Alhamis

Daga }arfe 9.00 a.m. zuwa 12.00 p.m. ranar Juma’a.A aika da duk e-mail zuwa ga [email protected] (Arewa), [email protected] (Kudu) ko [email protected].

Rosa Parks CenterSashen hul]a da Jama'a na Ofishin Jakadancin AmirkaPlot 1075 Diplomatic Drive, Central District Area,Abuja, Najeriya.Tarho: 09-461-400 Fax: 0-9-461-4011e-mail: Ircabuja elstate.govAna bu]ewa daga }arfe 9.00 a.m. - 4.00 p.m.Litinin zuwa Alhamis.9.00 a.m – 12 noon Friday

Ga Adireshen mu kamar haka: