hanyoyin horar da maniyyata aikin hajji

26
Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Bunqasa Basirar Malamai Masu Gabatar Da Bita Ga Maniyyata Na Ahmad Bello Dogarawa Sashin Koyar Da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria [email protected] A Matsayin Qasidar Da Aka Gabatar Wajen Taron Qara Wa Juna Sani, Da Hukumar Kula Da Jin Daxin Alhazai Ta Jahar Neja Ta Shirya Wa Malamai Dake Gabatar Da Bita Ga Maniyyata Aikin Hajji Agusta, 2007

Upload: tarbiyyarmusulunci

Post on 26-Jun-2015

169 views

Category:

Documents


5 download

TRANSCRIPT

Page 1: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Da Bunqasa Basirar Malamai Masu Gabatar

Da Bita Ga Maniyyata

Na

Ahmad Bello Dogarawa Sashin Koyar Da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria

[email protected]

A Matsayin Qasidar Da Aka Gabatar Wajen Taron Qara Wa Juna Sani, Da

Hukumar Kula Da Jin Daxin Alhazai Ta Jahar Neja Ta Shirya Wa

Malamai Dake Gabatar Da Bita Ga Maniyyata Aikin Hajji

Agusta, 2007

Page 2: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 1 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

1.1 GABATARWA

Hajji na xaya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar. Allah ( )

Ya farlanta shi a kan kowane Musulmi, baligi, mai hankali, mai `yanci, da

ke da hali da ikon zuwa, sau xaya a cikin rayuwa. Kuma Ya shar’anta shi

don tabbatar da manufar tauhidi da samar da cikakkiyar `yan’uwantaka, ta

yadda Musulmi daga kowane vangare na duniya ke haxuwa a Makka don

gabatar da ayyukan bauta da samun tarbiyya, da gyaran zuciya da guzurin

duniya da lahira.

Hajji ibada ce da ke da manufofi da hikimomi da falala da alherai masu

yawan gaske. Kuma kamar sauran nau’o’in ibada, wanda zai je aikin Hajji

na buqatar sanin hukunce-hukuncen da suka shafi wannan babban aiki, da

ke wajabta amfani da dukiya da gavuvva, kamar yadda yake buqatar

jagoranci da taimako daga hukuma da malamai da waxanda suka saba

zuwa, don samun nasarar gudanar da wannan muhimmin aiki cikin nasara

a can qasa mai tsarki.

Page 3: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 2 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Kasancewar aikin Hajji na buqatar cikakken shiri da kintsi da tanadi da

tattali daga maniyyata, da kuma kulawa ta musamman da jagoranci da

xaukar xawainiya daga shugabanni, kusan dukan hukumomin jin daxin

Alhazai na jihohin da ke Nijeriya na qoqarin shirya taron bita da horarwa

ga maniyyata tun gabanin lokacin tafiya qasa mai tsarki. Kuma

hukumomin na zavo malamai a kowace qaramar hukuma don gabatar da

wannan aiki, a ilmance.

Da yake malaman da ke gudanar da bitar ga maniyyata na buqatar tuntuvar

juna a kan waxansu mas’aloli, kasancewar matakin ilminsu da qwarewarsu

da fahimtarsu da khibirarsu ya bambanta, hukumomin jin daxin Alhazai

kan shirya wa su kansu malaman taron qara wa juna ilmi tun kafin a fara

horar da maniyyata. Manufofin irin wannan taro sun haxa da qara qulla

zumunci a tsakanin malamai, da daidaita fahimtarsu a kan waxansu

mas’aloli, da bunqasa basirarsu, ta yadda za su gudanar da aikin da

hukumar ta xora masu a cikin nasara.

Wannan qasida ta qunshi tattaunawa ce game da hanyoyin horar da

maniyyata aikin Hajji da bunqasa basirar malamai masu gabatar da bita ga

maniyyata. A matsayin shimfixa, qasidar za ta yi tsokaci a kan hukunci da

falalar Hajji a Musulunci, rukunan aikin Hajji, da kuma yadda ake samun

hajjun mabrur ( ), wato, aikin Hajji nagartacce/karvavve.

An raba bayanan da ke qunshe a cikin qasidar gida biyar: gava ta gaba za

ta yi magana ne a kan hukuncin aikin Hajji, da falalarsa, da sharuxxansa,

da rukunansa, da yadda maniyyaci zai samu gudanar da aikin Hajjinsa

cikin nasara ta yadda zai dace da alherin da ke ciki. Kashi na uku zai yi

magana a kan hanyoyin horar da maniyyata aikin Hajji da bunqasa basirar

malamai masu gudanar da bita. Vangaren qasidar na huxu zai gabatar da

nasihohi da shawarwari ne ga masu yin bita, da maniyyata, da hukumomin

da ke da alhakin tabbatar da nasarar aikin Hajji. Vangare na biyar zai

qunshi godiya da kammalawa.

2.1 HUKUNCIN HAJJI A MUSULUNCI

Hajji na xaya daga rukunan Musulunci guda biyar. Alqur’ani da Sunnah da

Ijma’i duk sun tabbatar da wajibcin yin aikin Hajji sau xaya a cikin

Page 4: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 3 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

rayuwa1 a kan kowane mukallafi (musulmi, baligi, mai hankali), namiji ko

mace, mai `yanci, da ke da iko (istixaa’ah).

Allah ( ) Ya ce:

Kuma Allah Yana da haqqi a kan mutane na yin Hajjin Xaki, ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirce, lallai Allah Mawadaci ne ga barin talikai.2

Manzon Allah ( ) ya ce:

Ya ku mutane, haqiqa Allah Ya farlanta Hajji a kanku, (sabo da haka) ku yi Hajji.3

Haka nan, Manzon Allah ( ) ya ce:

Ku yi gaggawar zuwa Hajji, domin xayanku bai san abin da zai bijiro masa ba (wanda zai iya hana shi zuwa aikin Hajji daga baya).4

Bayan wannan, Ijma’i ya qullu game da wajibcin Hajji a kan kowane

musulmi, baligi mai hankali, mai `yanci, da ke da iko (istixaa’ah), sau xaya

a rayuwarsa.

2.2 FALALAR HAJJI

Hajji na da falala mai yawan gaske. Daga cikin falalar Hajji akwai:

1. Hajji na kankare zunuban da suka gabata, ya rushe su, kuma ya

laqwame su. Manzon Allah ( ) ya ce:

Wanda ya yi (aikin) Hajji, bai yi jima’i (ko wani abu da zai kusantar da shi zuwa ga jima’i) ba, kuma bai yi aikin fasiqanci ba, zai koma kamar ranar da uwarsa ta haife shi (sabo da rashin zunubi)5

1 Ko da yake aikin Hajji wajibi ne sau xaya a cikin rayuwa, duk lokacin da mutum ya yi

bakance (alwashi) cewa zai yi aikin Hajji, Hajji ya wajaba a kansa 2 Aal Imraan 3:97

3 Muslim

4 Ahmad ya ruwaito, kuma al-Albani ya ce Hasan ne a cikin Irwaa’ul Ghaleel

5 Bukhari da Muslim

Page 5: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 4 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Haka nan, Manzon Allah ( ) ya ce wa sahabinsa `Amr

bn al-`Aas ( )

Ba ka san cewa Musulunci na rushe (zunuban da aka yi) kafin (a shige) shi ba, kuma Hijira na rushe abin da aka yi (na zunubai) kafin ita ba, kuma Hajji na rushe abin da aka yi kafin shi ba?6

2. Hajji na daga dalilai na samun `yanci daga wuta. Manzon Allah (

) ya ce:

Ba bu wata rana da Allah Ya fi `yanta bawa daga wuta fiye da ranar Arfah7

3. Hajji da Umrah na kore talauci. Manzon Allah ( ) ya

ce:

Ku bibiyi aikin Hajji da Umrah, domin suna kore talauci da zunubi kamar yadda zugazugi ke kore duddugar qarfe da zinare da azurfa.

8

4. Hajji na xaya daga cikin ayyukan da suka fi falala. An tambayi

Manzon Allah ( ) game da ayyukan da suka fi falala,

sai ya ce:

Imani da Allah Shi kaxai, sa’an nan Jihadi, sa’an nan Hajjun Mabrur (Hajjin da aka yi shi kamar yadda Shari’a ta ce). Tsakanin hajjun mabrur da sauran ayyuka, kamar tsakanin mahudar rana ce da mafaxarta9

5. Hajji shi ne jihadi mafi falala ga mata. A’isha ( ) ta ce wa

Manzon Allah ( ) ‘Ba za mu yi jihadi ba’? sai ya ce:

6 Muslim

7 Muslim

8 Ahmad, Tirmidhi da Ibn Majah

9 Ahmad da Xabaraani. Kuma Bukhari da Muslim su ruwaito da lafazin da bai kai wannan

tsawo ba

Page 6: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 5 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

A’a, kuna da jihadi mafi falala da za ku yi: Hajjun Mabrur.10

6. Hajji da Umrah su ne jihadin tsofaffi da yara da masu rauni. Manzon

Allah ( ) ya ce:

Jihadin tsofaffi da yara da masu rauni da mata shi ne: Hajji da Umrah.11

7. Mahajjata baqin Allah ne da ake ba su abin da suka roqa. Manzon

Allah ( ) ya ce:

Mai yaqi fisabilillah, da mai Hajji, da mai yin Umrah (dukaninsu) baqin Allah ne; Ya kira su, sun amsa kiran, kuma suka roqe Shi (buqatunsu) Ya ba su.

12

8. Aljanna ce sakamakon aikin Hajji. Manzon Allah ( )

ya ce:

Kuma aljanna ce sakamakon Hajjun Mabrur13

2.3 SHARUXXAN WAJIBCIN HAJJI

Hajji na zama wajibi ne idan an cika sharuxxa guda biyar: Musulunci,

hankali, balaga, `yanci, da samun iko.14

Wanda ya rasa xaya daga cikin

10

Bukhari, Nasa’i da Ibn Majah 11

Nasa’i 12

Ibn Majah da Ibn Hibbaan 13

Bukhari da Muslim 14

Da yawa daga malamai na ganin cewa a haqqin mace, samun muharrami (wanda Shari’a ta

haramta aure a tsakaninsu) da za su tafi tare ko mijinta na daga sharuxxan wajibcin Hajji.

Idan ba ta samu muharrami ba, kuma ba tare da mijinta za ta tafi ba, Hajji bai wajaba a kanta

ba. Malikiyyah da Shafi’iyyah sun sharxanta amincin hanya da samun abokan tafiya amintattu

ne kawai, ba wai samun muharrami ko miji ba. Zahiriyyah kuwa na ganin halascin aikin Hajji

ga wadda ba ta da miji ko muharrami ko uban miji. Idan mace ta yi aikin Hajji ba tare da miji

ko muharrami ba, ta sava wa Allah, amma aikin Hajjin ya yi. Wallahu a’alam.

Haka nan, akwai maganganu guda biyu dangane da ko mace mai takaba ko idda za ta iya

zuwa aikin Hajji. Magana mafi qarfi ita ce: macen da ta ke takaba ko idda ba za ta tafi aikin

Hajji ba, domin Shari’a ta umurce ta da lazimtar xakinta idan ba da wata larura ba. Sabo da

haka ba za ta fita ba sai da larurar da Shari’a ta yarda da ita (kamar zuwa asibiti don neman

magani, yin sana’a idan babu wanda ke xaukar nauyinta, makaranta, ko ziyar iyaye da

`yan’uwa). Ya tabbata cewa Sayyidina Umar bn Khaxxab da Uthman bn Affan (Allah Ya

yarda da su) suna mayar da mata waxanda suka yi nufin tafiya aikin Hajji, alhali suna cikin

Page 7: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 6 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

waxannan sharuxxa, Hajji bai wajaba a kansa ba. Ibn Qudamah ya

bayyana cewa babu savani a tsakanin malamai a kan wannan magana.15

Idan kafiri da mahaukaci suka yi aikin Hajji, Hajjinsu bai inganta ba. Idan

kuwa bawa da qaramin yaro suka yi Hajji, ya yi. Sai dai kuma idan bawan

ya samu `yanci ko yaron ya balaga daga baya, wajibcin Hajji na nan a

kansu. Da zarar sun samu iko, dole ne su sake yin aikin Hajji.

Samun ikon zuwa aikin Hajji na tabbata ne idan aka samu abubuwa guda

uku:

1. Lafiyar jiki da kuvuta daga cutar da za ta hana gabatar da ayyukan

Hajji. Idan mutum na da halin yin Hajji, amma ba shi da qoshin

lafiya, zuwa aikin Hajji bai wajaba a kansa ba. A irin wannan hali,

sai ya wakilta wanda zai je ya yi masa, kamar yadda Hadisi ya

tabbatar.16

2. Mallakar abin da zai wadace shi (kuxin kujera da guzuri) har ya

dawo, bayan ya tanadi abin da zai bar wa iyalinsa kuma ya biya

bashin da ke kansa. Babban laifi ne mutum ya bar iyalinsa da sauran

waxanda ciyarwarsu ke kansa cikin yunwa da tsananin buqata sabo

da aikin Hajji. Haka nan, wanda ake binsa bashi ba zai tafi aikin

Hajji ba sai da izinin waxanda ke binsa bashin.

3. Amincin hanya, ta yadda mahajjaci zai samu aminci game da ransa

da dukiyarsa a lokacin da zai fita zuwa aikin Hajji. Idan ana tsoron

halakar rai ko dukiya sabo da rashin aminci a kan hanya, Hajji bai

zama wajibi ba.

takaba, Madina daga wurin da ake kira Baidaa. Wannan ita ce fatawar Sa’idu bn Musayyib

daga cikin tabi’ai.

Dangane da tafiyar da Sayyidatuna A’ishah (Allah Ya yarda da ita) ta yi zuwa aikin Hajji

tare da qanwarta Ummu Kulthum, wadda ke cikin takaba, Ibn Abdil-Barri ya ce ‘mafi

yawancin malaman zamanin A’ishah sun yi mata inkari.’ Ya qara da cewa: ‚Magana mafi

rinjaye ita ce fatawar Umar da Uthman da Sa’idu bn Mussayib (Allah Ya yarda da su), kuma

ita ce muka rinjiyar (a kan maganar da ake dangana wa Sayyidina Aliyu da Ibn Abbas da Jabir

bn Abdullah da A’ishah cewa mai takaba da mai idda za su iya tafiya aikin Hajji). Duba

littafin al-Istizkaar na Ibn Abdul-Barri 18/182-185 15

Al-Mughnee 3/218 16

Bukhari da Nasa’i

Page 8: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 7 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

2.4 RUKUNAN HAJJI

Aikin Hajji na da rukunai guda huxu a wajen mafi yawancin malamai. Idan

aka rasa xaya daga cikin rukunan, aikin Hajji bai yi ba. Kowane rukuni na

da wajibai da sunnoni da mustahabbai ko ladubba da abubuwan da aka

hana yi a cikinsa. Rukunan Hajji su ne:

1. Ihrami, wato niyyar Hajji ko Umrah daga miqatin da Shari’a ta

tabbatar. Ana yin niyyar Hajji ta xaya daga cikin fuskoki guda uku:

Ifradi ga wanda ya samu damar yin Umrah a wannan shekara kafin

shigar watannin Hajji; Qirani ga wanda yake son haxa Hajji da

Umrah a cikin tafiya guda xaya, kuma ya samu damar tafiya da

hadaya; da Tamattu’i ga wanda yake son haxa Hajji da Umrah a

cikin tafiya xaya, kuma bai samu damar tafiya da hadaya ba.

Kafin ya sanya ihrami, an so maniyyaci ya yi wankan tsarki; ya

sanya turare a jikinsa; kuma ya sanya farin harami. An so ya yi nafila

raka’a biyu kafin ya qulla niyyar Hajji, idan akwai masallaci a wurin,

kamar yadda aka so ya yi niyyar aikin Hajjin ko Umrah bayan ya

kammala sallar farilla ko nafila, yana mai fuskantar alqibla. Bayan

wannan, an so mahajjaci ya yawaita yin talbiyya da murya

maxaukakiya, musamman a lokacin hawa da gangara, da hanyar

arfah, da lokacin da ake dawowa daga arfah har mahajjaci ya yi jifar

farko.

Lallai ne maniyyaci ya nisanci jima’i a lokacin da yake aikin Hajji,

kasancewar yana vata aikin gaba xaya. Haka nan, ya nisanci sanya

kewayayyen tufafi; da sanya turare; da aske gashin kai; da yanke

qumba (farce); da neman aure ko xaura aure; da savon Allah; da

husuma da jayayya mara dalili; da duk wani abu da ke iya jawo

jima’i.

Sai dai kuma mahajjaci yana iya yin wankan tsafta; da canza harami

ko wanke shi, idan yana buqata; da taje (gyara) gashin kai; da sosa

kansa ko jikinsa; da yin qaho; da sunsuna turare don gane irinsa ko

ingancinsa; da cire ko yanke qumbar da ta karye; da rufe kai ko

fuska sabo da qura ko zafin rana (da abin da ba xamfare yake da kan

nasa ba); da amfani da lema ko waninta don kare zafin rana; da xaura

maxaurin jaka ko bel; da sanya zobe; da sanya agogo; da sanya

tabarau; da kashe duk wata dabba ko qwaro mai cutarwa. A haqqin

mace kuma, babu laifi ta sanya duk irin tufafin da ta so kuma kowane

Page 9: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 8 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

irin launi; da wando; da huffi; da gwala-gwalai; da yin qunshi; da

sanya tozali idan da buqata.

2. Xawaful Ifaadhah da ake yi daga fitowar alfijir na ranar salla

(kashegarin ranar Arfah). Wanda larura ta hana shi yin xawafi a

wannan rana ko kuma cikin ranakun da ake kwanan Mina, zai iya

gabatar da shi kafin watan shawwal ya wuce.

An so a yi alwala kafin xawafi; da sassarfa a zagaye uku na farko a

haqqin maza; da tava Hajarul Aswad da hannu, sa’an nan a sumbace

shi da baki idan hakan zai yiwu; da yin sujuda a kan Hajaru Aswad;

da tava Ruknul Yamani da hannu; da addu’a a tsakanin Ruknul Yamani guda biyu; da zuwa wajen Maqama Ibrahim bayan kammala

xawafi, sa’an nan a yi nafila raka’a biyu a bayan Maqama Ibrahim;

da shan ruwan zamzam, sa’an nan mahajjaci ya zuba ruwan a kansa.

3. Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa bayan an yi xawafi. An so mahajjaci

ya kasance cikin alwala a lokacin da zai yi sa’ayi; ya fuskanci alqibla

idan ya hau kan safa; ya yi sassarfa a tsakanin korayen lantarki guda

biyu; ya yi addu’a a wajen safa da kuma marwa.

4. Tsayuwa a Arfah daga bayan zawal (lokacin sallar zuhr) zuwa

faxuwar rana. Wanda bai samu tsayuwa da rana ba, amma ya samu

damar tsayuwa cikin dare kafin alfijir xin ranar salla ya fito, Hajjinsa

ya yi.

An so mahajjaci ya tsaya a wajen falalen dutsen da ke qasan Jabalur Rahmah idan zai yiwu (idan bai samu damar haka ba, sai ya tsaya a

kowane wuri a ciki filin arfah); ya fuskanci alqibla; ya xaga

hannuwansa a wajen addu’a; ya riqa yin talbiyya; ya kasance ba ya

yin azumi a wannan rana; ya kama hanyar Muzdalifah a cikin

natsuwa, yana mai yin talbiyya, bayan faxuwar rana.

2.5 YADDA AKE SAMUN HAJJUN MABRUR

Manzon Allah ( ) ya bayyana cewa aljanna ce sakamakon

Hajjun Mabrur. Imam al-Qurxubi ya bayyana ma’anar Hajjin da ake kira

mabrur a cikin tafsirinsa, kuma Ibn Hajar, a cikin Fathul Baari, ya qarfafi

cewa shi ne aikin Hajjin da aka cika hukunce-hukuncensa kuma aka

gabatar da shi yadda Shari’a ta ce, a bisa fuska mafi cika.

Page 10: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 9 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Ke nan mahajjata na buqatar kiyaye qa’idodin Shari’a da hukunce-hukunce

tare da ladubban da suka shafi Hajji domin dacewa da nagartaccen aikin

Hajji da ake saka wa wanda ya yi shi da aljanna.

Al’amuran da ke taimakawa wajen samun nagartaccen aikin Hajji domin

kai wa ga Hajjun Mabrur sun haxa da:

Na xaya

Tsarkake niyya da koyi da Manzon Allah ( ). Wajibi ne

maniyyaci ya tsarkake niyyarsa wajen aikin Hajji, domin Allah ba Ya

karvar duk wata ibada da aka yi ba tare da ikhlasi ba. Ka da maniyyaci ya

biya kuxin aikin Hajji domin alfahari ko taqama ko nuna isa ko gudun ka

da a ce ya gaza ko don kawai a kira shi Alhaji idan ya dawo ko don kawai

ya je yawon buxe ido. Lallai ne maniyyaci ya yi niyyar bautar Allah don

samun yardarSa, da neman dacewa da alherai da lada da falala da ke cikin

aikin Hajji.

Haka nan, lallai ne maniyyaci ya tabbatar da ya gudanar da aikin Hajjinsa,

kamar yadda Manzon Allah ( ) ya koyar. Koyi da Manzon

Allah ( ) a cikin aikin Hajji da sauran ayyukan ibada gaba

xaya, wajibi ne, kuma sharaxi ne na karvar ayyukan bawa. Manzon Allah

( ) ya gudanar da aikin Hajji a aikace, kuma ya yi umurni da

a yi koyi da shi:

Ikhlasi (tsarkake niyya) da Mutaaba’ah (koyi da Manzon Allah –

) sharuxxa ne na karvar kowace ibada da bawa zai yi wa Allah. Idan

aka rasa su, ba maganar ibada. Kuma a aikin Hajji, ikhlasi da mutaaba’ah

mabuxi ne na samun Hajjun Mabrur.

Na biyu

Tattali da tanadi da kintsi ta hanyoyi kamar haka:

1. Maniyyaci ya gyara tsakaninsa da Allah Ubangijinsa ta hanyar tuba

daga zunubansa, tun kafin lokacin tafiya. Hakan zai qara kusantar da

shi ga Allah Mahaliccinsa. Haka nan, maniyyaci ya tabbatar da cewa

hanyar da ya bi wajen biyan kuxin aikin Hajji, hanya ce da Shari’a ta

yarda da ita. Ka da ya kuskura ya yi amfani da kuxin haram domin

yin aikin Hajji

Page 11: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 10 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

2. Neman taimako da dacewa daga Allah, da bayyanar da tsananin

buqata zuwa gare Shi, da tsoron azabarSa da kwaxayin rahamarSa.

Ta haka ne ibadar ta sa za ta zamanto a kan saiti.

3. Kuvuta daga haqqoqin wasu, da mayar da kayan da aka ba shi ajiya,

da biyan bashin da ake binsa. Haka nan, maniyyaci ya sanar da

`yan’uwa da maqwafta da abokan arziqi cewa zai yi tafiya, kuma ya

nemi su yi masa addu’ar dacewa da samun qabuli daga Allah. An so

maniyyaci ya rubuta wasiyya kafin ya tafi idan akwai abin da ya ke

son yin wasiyya da shi.

4. Samun tsarkakakken guzuri, kasancewar guzurin da ya ke na haram

na da mummunan tasiri a kan addu’o’in da mahajjaci zai yi a halin

da ya ke aikin Hajji. Ta’ammuli da abinci ko abin sha ko tufafi na

haram na daga cikin abubuwan da ke hana a amsa wa bawa addu’a,

kamar yadda Hadisi sahihi ya nuna.

5. Maniyyaci ya yi tanadi wadatacce ga iyalinsa da sauran waxanda ke

qarqashinsa gwargwadon ikonsa, kafin ya tafi aikin Hajji. Babban

laifi ne mutum ya tozarta waxanda nauyinsu ke kansa ko ya yi sakaci

game da haqqoqinsu.

6. Zaven abokai na qwarai waxanda za su taimaka wa mahajjaci idan

ya yi rauni, su cincixa shi idan ya gaza, su tunatar da shi idan ya

manta, su ilmantar da shi idan ya jahilta, su umurce shi da

kyakkyawa su hana shi mummuna. Lallai ne mahajjaci ya nisanci

abokan banza da za su kai shi ga varna da savon Allah, da waxanda

ba su da aikin yi a qasa mai tsarki sai yawan buxe idanu da zuwa

kallon abubuwan sha’awa, maimakon su mayar da himma wajen

bautar Allah da neman yardarSa, da waxanda ba su da aikin yi sai

zaman banza da lalaci.

7. Qoqarin fahimtar hukunce-hukuncen aikin Hajji da ladubbansa, da

abubuwan da ke gyara shi da waxanda ke vata shi, da hukunce-

hukuncen da suka shafi tafiya da sallar qasaru, da dai sauransu.

Na uku

Fahimtar manufa da hikimomin aikin Hajji da suka haxa da:

Miqa wuya ga umurnin Allah da sallamawa tare da jawuwa gare Shi

Tabbatar da tauhidi

Page 12: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 11 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Girmama abubuwan da Allah ( ) Ya yi umurni da a girmama

su

Son Manzon Allah ( ) ta hanyar koyi da shi a cikin

ayyukan Hajji gaba xaya

Tunawa da ranar Lahira ta hanyar tuna mutuwa da barin duniya zuwa

lahira a lokacin da maniyyaci ya fito daga gidansa, da tuna likkafani

a lokacin da ya sanya haraminsa, da tuna tsayuwa a gaban Allah a

ranar Qiyama domin yin hisabi a lokacin da ya ga matsatsar mutane,

ya ji xaga muryoyinsu da bambancin yarensu.

Tabbatar da tsoron Allah da taqawa ta hanyar kiyaye dokokin Allah

domin samun guzuri mafi alheri

Samun cikakkiyar tarbiyya da kyawawan xabi’u da suka haxa da

kamun kai, kame fushi da rashin husuma da barin jayayya mara

dalili, tausasawa da natsuwa, qanqan da kai, haquri, kyauta, da

taimakon juna. Dangane da irin wannan tarbiyya da ake son

mahajjaci ya samu a lokacin aikin Hajji, Allah ( ) Ya ce:

Taimakekeniya da `yan’uwantaka da haxin kai a tsakanin Musulmi

Yawaita zikirin Allah

Na huxu

Qoqari wajen xa’a ga Allah da amfani da lokaci yadda ya dace ta hanyar

yawaita karatun Alqur’ani da zikiri da istigfari da sallar nafila da halartar

wuraren da ake yin karatu da wa’azi. Haka nan an so mahajjaci ya zamanto

mai kyauta gwargwadon iko, da taimakon `yan’uwansa, da qoqarin kawo

amfani ga juna, da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, da yawaita

addu’a da roqon Allah buqatu na alheri. Manzon Allah ( )

ya ce:

Na biyar

Nisantar zunubi da savon Allah a wajen aikin Hajji, da dagewa a kan xa’a

tun daga farkon aiki har zuwa qarshe.

3.1 HANYOYIN HORAR DA MANIYYATA

Horar da maniyyata game da aikin Hajji abu ne muhimmi, kasancewar

horarwar ta qunshi karantar da su hukunce-hukuncen aikin Hajji da

ladubban da ya kamata mahajjaci ya kiyaye tun kafin ya bar Nijeriya zuwa

Page 13: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 12 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

qasar Saudiyyah har ya dawo. Wannan ya sa a kowace shekara,

hukumomin jin daxin Alhazai ke qoqarin shirya taron bita don cinma

manufar aikin Hajji. Buqatarsu kowa ita ce maniyyata su dace da

nagartaccen aikin Hajji wanda ya kuvuta daga savon Allah da sauran

abubuwan da ke haifar da cikas ga wannan babbar ibada (Hajjun Mabrur).

A wannan gava, qasidar za ta yi tsokaci a kan hanyoyin da malamai masu

bita da hukumar jin daxin Alhazai za su bi wajen horar da maniyyata aikin

Hajji, ta hanyar amfani da ingantattun hanyoyi da usulubin da ya dace da

zamani da za su taimaka wa maniyyaci fahimtar abubuwan da ake koya

masa cikin sauqi.

Tun da farko, akwai buqatar tunatar da cewa aikin Hajji ya qunshi

hukunce-hukunce masu yawa da ayyuka iri-iri da maniyyaci ya kamata ya

sani. Kasancewar maniyyaci zai gudanar da aikin Hajjinsa ne a cikin wata

qasa dabam da bai saba ba, sau da yawa maniyyata kan koka da cewa abin

da aka sanar da su ko aka kwatanta masu a lokacin bita, ba shi suka gani ba

a can qasar Saudiyya. Wannan yasa ake da buqatar amfani da sabbin

hanyoyi na zamani don cinma wannan manufa.

Horar da maniyyata aikin Hajji na da matakai guda uku: matakin karantar

da hukunce-hukunce da ladubba da tarbiyya, tare da bayani game da yadda

ake gudanar da aikin Hajji; matakin nuna siffar aikin Hajji a majigi ko

na’urar bidiyo ko faifan CD; matakin koyar da aikin Hajji a aikace ta

hanyar amfani da alamomi (kamar ka’aba, wurin safa da marwa, wurin

jifar jamrori, da arfah) irin waxanda maniyyaci zai tarar a can qasar

Saudiya.

Matakin Farko: Karantar Da Hukunce-Hukunce Da Ladubba Da Tarbiyya

A wannan mataki, malamai masu horar da maniyyata na buqatar mayar da

himma wajen ilmantar da maniyyata hukunce-hukuncen da suka shafi aikin

Hajji da ladubbansa. Hukunce-hukuncen sun haxa da ma’anar Hajji,

hukuncinsa, matsayinsa, falalarsa, sharuxxansa, rukunansa, da abubuwan

da ke vata shi. Ladubban aikin Hajji sun haxa da sunnoni da mustahabban

ihrami da xawafi da sa’ayi da tsayuwar arfah da kwanan Mina da jifar

jamrori da hadaya (ga wanda zai yi) da ziyarar Madina. A vangaren

tarbiyya, horarwa a wannan mataki ta qunshi koyar da muhimmancin

taqawa da haquri da zaman lafiya da jurewa wahala da lazimtar abokai na

qwarai da kyautata wa abokan tafiya da tausaya wa waxanda ke cikin

Page 14: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 13 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

matsala da xa’a ga shugabbani da jami’ai da biyayya ga dokokin qasar

Saudiya da kare martaba da mutuncin Nijeriya.

Domin cinma wannan manufa, masu gabatar da bita na buqatar amfani da

sahihan littafai da ke magana a kan aikin Hajji da Umrah. Ban da littafan

fiqihu da Hadisi da ke qunshe da bayanai a kan aikin Hajji, malamai na iya

amfani da littafin al-Qiraa li Qaasidi Ummil Quraa na Imam ax-Xabari; al-Idah fi Manaasikil Hajj na Imam an-Nawawi; Awdhahul Masaalik ilaa Ahkaamil Manaasik na Abdul-Azeez al-Muhammad as-Salmaan; Khaalisul Jumaan na Sa’ood bn Ibrahim Shuraim; al-Mughnee fi Fiqhil Hajj wal Umrah na Sa’eed bn Abdul-Qadir; Sifatu Hajjatin Nabiyyi na Muhammad

Naasiruddeen al-Albani; al-Manhaj li Muridil Umrah wal Hajj da

Manaasikul Hajj na Muhammad bn Saalih al-Uthaymeen; da Ramyul Jamaraat wa maa Yata’allaqu bihi min Ahkaam na Sharaf bn Aliyu as-

Shareef.

A qarqashin wannan mataki, masu bita na buqatar kwatanta wa maniyyata

yadda siffofin waxansu ayyukan suke, kamar sassarfa a wajen xawafi da

sa’ayi, xaura harami, fitar da kafaxa a wajen xawafi, da sauransu.

Malamai masu bita su fahimci cewa a wannan mataki, tsagwaron ilmi ake

buqatar karantar da maniyyata, domin su san hukunce-hukunce, da ladubba

da irin tariyyar da ya kamata a same su da ita. Wannan yasa dole sai an

xauki tsawon makwanni ana gabatar da bayanai a qarqashin wannan

mataki. Sai dai kuma lallai ne karantarwar ta zamanto mataki-mataki, ta

yadda maniyyata za su fahimta a cikin sauqi.

Mataki Na Biyu: Amfani Da Majigi Ko Bidiyo Ko Faifan CD A Wajen

Bita

A wannan mataki, masu gabatar da bita na buqatar taimakon hukumar jin

daxin Alhazai fiye da a matakin farko, kasancewar ana buqatar amfani da

wutar lantarki ko janareto da kaset xin bidiyo ko faifan CD da ya qunshi

hoton yadda ake gudanar da aikin Hajji a aikace da na’urorin da za a yi

amfani da su wajen nuna hoton. Idan da hali, ana iya amfani da na’ura mai

qwaqwalwa (computer) da na’urar da ke nuna abin da ke cikin na’ura mai

qwaqwalwa a kan allon majigi (projector).

Rawar da hukuma za ta taka a wannan mataki ta qunshi samar da

kayayyakin da ake buqata don cinma wannan buri da mutanen da za su iya

Page 15: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 14 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

sarrafa na’urorin. Su kuma malamai, aikinsu shi ne yin qarin bayani a

wajen kowace gava da ke buqatar haka.

Bita a bisa irin wannan tsari ya kamata ta kasance bayan an qosar da

maniyyata da ilmin da ya shafi hukunce-hukunce da ladubba da tarbiyya

kuma ya kamata tsarin ya kasance gab da lokacin tafiya, ta yadda hoton da

za su gani zai tunatar da su abubuwan da suka koya kafin wannan lokaci.

Haka nan, bita a wannan mataki ba ta buqatar xaukan lokaci mai tsawo. A

cikin mako biyu za a iya kammala bitar.

Mataki Na Uku: Koyar Da Aikin Hajji Ta Hanyar Amfani Da Alamomin

Zahiri

A wannan mataki, masu gabatar da bita za su karantar da maniyyata yadda

ake aikin Hajji a aikace, ta hanyar amfani da alamomi na zahiri. Waxannan

alamomi sun haxa da ka’aba da filin xawafi, maqama Ibrahim, wurin

sa’ayi, wurin jifar jamrori, da filin arfa.

Domin gabatar da bita a bisa wannan tsari, hukumar jin daxin Alhazai ta

jiha na iya tara maniyyatan qananan hukumomi biyar zuwa goma a gari

xaya. Daga nan, sai a samu wadataccen fili da za a karkasa shi zuwa wurin

xawafi da sa’ayi da sauransu.

Dangane da wurin xawafi, za a samar da kwatankwacin ka’aba ta katako

ko silin, haka nan ma wurin jifar jamrori. A keve wani wani vangare na

filin da za a yi masa alamomi irin na wurin sa’ayi, da sauransu.

Ta wannan hanya, maniyyaci zai qara fahimtar yadda ake gabatar da aikin

Hajji a aikace kuma mubasharatan, kamar yana can qasar Saudiya. Da

zarar ya isa Saudiya, abubuwan da zai gani za su tunatar da shi waxanda

aka yi masa amfani da su a nan Nijeriya, da kuma yadda zai yi amfani da

su a can.

Wannan hanya, ita ce ya kamata ta zamanto mataki na qarshe a wajen jerin

laccoci ko taron bita da za a shirya wa maniyyata. Kuma babu shakka,

wannan hanyar na da tasiri sosai wajen koyar da maiyyata yadda ake

gudanar da aikin Hajji.

Abu na qarshe da ya kamata a yi tsokaci a kansa a wannan gava shi ne

muhimmancin la’akari da fahimtar maniyyata da zurfin ilminsu. Hakan zai

taimaka wajen sanin yadda ya kamata a yi masu bitar. Qa’idar dai ita ce a

Page 16: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 15 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

yi wa mutane bayani ta yadda za su fahimta, kuma gwargwadon qwaqwalwarsu.

3.2 HANYOYIN BUNQASA BASIRAR MASU YIN BITA

Malamai su ne qashin bayan gudanar da bita sahihiya ga maniyyata aikin

Hajji. Gwargwadon ilminsu da qwarewarsu da sanin hanyoyin isar da

saqo, gwargwadon nasarar bitar da za a gabatar wa maniyyata.

Wannan yasa hukumar jin daxin Alhazai ke da buqatar samar da tsare-

tsaren da za su taimaka wajen bunqasa fahimtar malaman da ke gabatar da

bita don a qara samun nasarar gudanar da aikin.

Bunqasa basirar malamai masu yin bita na da matakai uku:

Matakin Farko: Shirya Taron Qara wa Juna Sani Ga Dukan Malamai

A wannan mataki, hukumar jin daxin Alhazai za ta shirya wa malamai

taron qara wa juna ilmi, kuma ta gayyaci malamai daga vangarori dabam-

daban na qananan hukumomin da ke jahar. A wajen taron za a gabatar da

qasidu a kan mas’alolin da ke da alaqa da aikin Hajji domin ilmi da

fahimta su bunqasa. Zai yi kyau a samu wanda yake da fasahar isar da saqo

ya gabatar da qasida, sa’an nan a samu wani malami daga cikin mahalarta

taron ya yi wa qasidar ta’aliqi. Ta wannan hanya, malamai za su qara sanin

juna, su fahimci juna, su mutunta juna, kuma su san matsayin juna.

Idan da hali, ana iya gayyato waxansu malamai daga wata jahar don su

gabatar da qasidu. Sanannen abu ne cewa baqo na samu qimar da ta fi ta

xan gari a mafi yawancin lokaci ko da kuwa baqon bai kai xan gari ilmi da

qwarewa a cikin harkokin addini ba. Irin wannan haxuwa kan qara danqon

zumunci a tsakanin malamai, a samu shawarwari daga malaman da suka zo

daga wata jahar, bisa abin da ke faruwa da yadda suke gudanar da irin

wannan aiki a garinsu.

A wannan mataki, ana sa ran cewa malamai za su fahimci irin ci gaban da

aka samu a vangaren kimiyya da fasahar isar da saqo, da usulubin zamani

wajen gabatar da bita. Haka nan, ana fatan malamai su fahimci wasu daga

cikin nau’o’in ci gaba da canje-canje da aka samu a qasar Saudiya, domin

su qara sanin yadda za su karantar da maniyyata.

Page 17: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 16 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Mataki Na Biyu: Gayyatar Waxansu Malaman a Keve

Sanannen abu ne cewa Manzon Allah ( ) ya yi aikin Hajji,

kuma ya ce: ‚ ‚ Ku koyi (yadda za ku yi) ayyukan Hajjinku

daga gare ni. Ke nan, kowane Musulmi da zai yi aikin Hajji, na buqatar

sanin yadda Manzon Allah ( ) ya yi, domin koyi da shi.

Sanin yadda Manzon Allah ( ) ya yi aikin Hajji na buqatar

komawa zuwa ga littafan Hadisai da sahihan littafai da aka rubuta dangane

da Haji. Sai dai kuma ana samun bambanci wajen fahimtar waxansu

Hadisai da ke magana a kan siffar Hajjin Manzon Allah ( )

ko ibarorin da ke cikin waxansu littafai. Hakan ya sa ake samun savanin

fahimta a tsakanin masu bita da waxanda ake yi wa bitar wajen gudanar da

ayyukan aikin Hajji.

Dangane da mas’alolin da ake da savani a kansu, kamar Miqati da wurin da za a yi ihrami, da lokacin jifar jamrah, akwai buqatar hukumar Alhazai

ta gayyaci waxansu fitattu kuma kevantattun malamai da za su wakilci

vangarori dabam-daban don tattaunawa bisa ilmi da kyakkyawar fahimta

da bincike mai zurfi, da nufin samar da matsaya guda xaya. Ana iya samun

wani malami ya gabatar da qasida ko maqala, sa’an nan a nemi malamin

da ake ganin yana da ra’ayin da ya sava wa mai qasidar, ya yi ta’aliqi. Ta

wannan hanya, za a iya fito da mas’aloli dabam-daban da aka yi ittifaqi ko

aka yi savani domin samar da matsaya guda xaya.

Daga nan, sai hukuma ta tsayar da abin da aka yi ittifaqi bisa dalilai

tabbatattu a matsayin manhaja. Idan ba a samu ittifaqi ba, sai a tabbatar da

fahimta mafi rinjaye bisa ingantattun dalilai. Daga bisani, malaman da

suka halarci irin wannan kevantaccen taro sai su sanar da sauran malamai

abin da aka tattauna, da matsayar da aka cimma.

Mataki Na Uku: Samar Da Manhajar Bita

Samar da manhajar bai xaya da tsayar da ita a hukumance ta yadda kowace

qaramar hukuma za ta yi amfani da ita a wajen gudanar da bita da horar da

maniyyata, abu ne mai matuqar muhimmanci. Domin kuwa ko da yake ba

za a iya kaucewa bambancin fahimta a kan waxansu mas’alolin furu’a ba,

gwargwadon tsuke da’irar wannan savani a cikin al’umma, gwargwadon

haxin kai da kyakkyawar fahimta da za a samu a tsakanin mutane.

Page 18: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 17 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Hukumar jin daxin Alhazai na sane da cewa matakin ilmi da zurfin

binciken malaman da ke gabatar da bita da horar da maniyyata sun

bambanta. Waxansu manyan malamai ne, a yayin da waxansu matsakaita

ne. Kasancewar akwai nau’o’in savani da ke haifar da rashin jituwa da

kace-nace a tsakanin mahajjata, akwai buqatar samar da tsari na bai xaya

wanda zai taimaka wajen rage waxannan matsaloli ko ma ya magance su

baki xaya.

Idan hukumar jin daxin Alhazai na da littafin da ta qarrara don amfanin

maniyyata da masu gabatar da bita, an samu sauqi. Illa iyaka, za a iya kafa

kwamitin mutane uku zuwa biyar don a qara tace shi da shigar da bayanan

da ya kamata a qara. Idan kuwa babu wani littafi da aka qarrara, zai yi

kyau a samar da kwamitin qwararrun malamai da jami’an hukumar jin

daxin Alhazai da zai yi aiki tuquru don samar da irin wannan littafi da za a

tabbatar da shi a matsayin manhaja. Ana iya fassara littafin zuwa yaren da

aka tabbatar mutanen jihar za su fi amfana sosai.

Samar da manhaja ta bai xaya zai taimaka wajen bunqasa basirar masu

gabatar da bita, musamman waxanda ke da qarancin karatu ko littafan yin

bincike, kasancewar ana sa ran manhajar ta qunshi bayanai ingantattu,

kuma masu sauqi, don amfanin masu horar da maniyyata da su kansu

maniyyatan.

4.1 NASIHOHI DA SHAWARWARI GA MALAMAI DA

MANIYYATA DA HUKUMAR JIN DAXIN ALHAZAI

Wannan vangare na qasida zai gabatar da nasihohi da shawarwari ne ga

malamai masu gabatar da bita, da maniyyata, da hukumar jin daxin

Alhazai. Manufar ita ce faxakar da vangarorin guda uku a kan waxansu

abubuwa muhimmai, kasancewar addini nasiha ne.

4.1.1 NASIHOHI DA SHAWARWARI GA MASU GABATAR DA

BITA

Ya kamata malamai da ke gabatar da bita da horar da maniyyata su kiyaye

waxannan abubuwa:

Malamai su ne magadan Annabawa, kuma yana daga manhajin

Annabawa ba da ilmi yadda ya dace tare da tausasawa da qanqan da kai

da yin bayani ga mutane gwargwadon qwaqwalwarsu. Malamai na da

buqatar tsare mutuncinsu, ba tare da yawon bin ofis-ofis don neman

Page 19: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 18 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

kujerar zuwa aikin Hajji ba. Ya kamata malamai su guji yawon maula

da vatanci ga juna.

Ilmi da karantar da shi amana ce da Allah zai tambaye su a ranar

qiyama. Wajibi ne su zamanto masu faxin gaskiya ba tare da la’akari da

jin daxi ko rashin jin daxin wani ba. Kuma su tabbatar da cewa

abubuwan da suke karantar da mutane ba mujarradin ra’ayinsu ba ne.

Lallai ne su tabbatar da cewa abin da suke karantarwa ya tabbata a cikin

Alqur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na qwarai. Ke nan suna da

buqatar dagewa da qara himma wajen nazari da bincike.

Ka da su mayar da hankali ga `yar fa’idar da ake samu ta duniya wajen

wannan aiki na bita da suke yi. Ko hukuma za ta biya su, ko ba za a biya

ba, su zamanto masu ikhlasi da yin aiki don sauke nauyin da Allah Ya

xora masu.

Bincike da tattaunawa a tsakaninsu, da nufin qara wa juna ilmi da

samun matsayi guda xaya, musamman cikin mas’alolin da ake da

bambancin fahimta.

Ba da muhimmanci ga janibin tarbiyya da ladubban da ya kamata

mahajjata su kiyaye, xoriya a kan sanar da su rukunai da sharuxxan

aikin Hajji da ake yi. Da yawa daga mahajjata na nuna halayen rashin

tarbiyya da rashin qoqarin kiyaye ladubba a can qasa mai tsarki.

Wannan ke nuna cewa, bayan sanar da su hukunce-hukuncen aikin

Hajji, akwai buqatar jaddada muhimmancin vangaren tarbiyya da

suluki.

Malamai da ke gabatar da bita su daina damuwa da wanda aka zava a

cikinsu don jagorantar mahajjata zuwa aikin Hajji. Sau da yawa

waxansu malamai kan janye daga wurin bita, ko su fara qorafi, da zarar

sun fahimci cewar ba da su za a je aikin Hajji ba. Wannan babban

kuskure ne.

Mutunta juna da nisantar xabi’ar nan ta ‚ ‚, wato ‘Sava wa

sauran jama’a don kai ma a sanka’.

Page 20: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 19 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

4.1.2 NASIHOHI DA SHAWARWARI GA MANIYYATA

Lallai ne maniyyata su fahimci cewa aikin Hajji ibada ce da ke buqatar

ikhlasi da koyi da Manzon Allah ( ) wajen gabatar da ita.

Da zarar an rasa xaya daga cikin waxannan abubuwa, aikin Hajji ba zai

zamanto karvavve ba. Akwai buqatar mahajjata su zamanto masu tsantsar

xa’a da haquri da taqawa, kuma su kasance jakadu na qwarai a duk wurin

da suke. Haka nan, wajibi ne su san hukunce-hukuncen Hajji, kuma su

nisanci duk wani abu da zai kawo cikas ga wannan muhimmiyar ibada da

za su yi, ko abin da zai kawo cikas ko abin kunya ga qasarsu a yayin da

suke can qasar Saudiyya.

Bayan wannan, yana da kyau maniyyata su tuna da waxannan bayanai tun

daga farkon aikin Hajji har zuwa qarshe:

Haquri Da Juriya A Cikin Aikin Hajji

Haquri da juriya na daga abubuwan da mai aikin Hajji ke buqata don

samun nasarar yin aikin Hajji nagartacce. Lallai ne mahajjata su zamanto

masu haquri da juriya a tsakaninsu, masu haquri da ba da uzuri ga

hukumarsu, kuma masu dauriya wajen bin umurni da hanin da bai sava wa

Shari’a ba. Maniyyata su sani cewa Allah bai ba wani bawanSa kyauta

mafi yalwa da alheri kamar haquri ba. Sabo da muhimmancin haquri a

cikin dukan al’amura, musamman aikin Hajji, Allah ( ) Ya ambaci

haquri a wurare casa’in (90) a cikin Alqur’ani.

Misali, Allah ( ) Ya yi umurni da yin haquri (16:127, 52:48); kuma

Ya yi hani game da kishiyarsa (46:5, 3:139); Ya rataya samun rabo ga

haquri da juriya (3:200); Ya ba da labari game da rivanya lada da ake yi

wa masu haquri (28:54, 39:10); Ya rataya samun shugabanci a cikin addini

ga haquri da yaqini (32:24); Ya tabbatar da kasancewarSa tare da masu

haquri (2:154); Ya qevance masu haquri da waxansu al’amura guda uku a

lokaci xaya: salati (gafara) daga gare Shi, da rahamarSa da shiriyarSa gare

su (2:155-157); Ya sanya haquri a matsayin dalili na samun taimako

(2:45); Ya rataya samun nasara ga haquri da taqawa (3:125); Ya sanya

haquri da taqawa a matsayin babbar garkuwa daga makirci da kaidin

maqiya (3:120); Ya ba da labarin cewa mala’iku za su yi masu sallama a

cikin aljanna sabo da haqurinsu (13:23-24); Ya rattaba samun gafara da

lada mai girma a kan haquri da kyakkyawan aiki (16:126); Ya yi wa

muminai masu haquri alqawarin samun nasara da xaukaka (7:137); Ya

Page 21: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 20 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

bayyana soyayyarSa ga masu haquri (3:146); Ya bayyana cewa xabi’o’in

alheri ba bu mai samunsu sai masu haquri (28:80, 4:35); Ya ba da labarin

cewa ba bu waxanda ke amfana da ayoyinSa kuma su wa’azantu sai masu

haquri (14:5, 31:31, 34:19, 42:33); Ya hukunta hasara ta dindindin ga duk

wanda bai yi imani, ya kasance daga cikin masu gaskiya da haquri ba

(103:1-3); kuma Ya gwama haquri da rukunan Musulunci (2:45, 11:11).

Ke nan, ba bu wanda zai wadatu daga haquri a kowane hali ya samu kansa,

musamman kuma a lokacin aikin Hajji. Sabo da haka, mahajjata su

zamanto

Masu haquri cikin xa’a ga Allah da barin sava masa, da haquri wajen

rabuwa da iyali a lokacin barin gida, da haquri a kan wahalhalun da ke

cikin ayyukan Hajji, da sauransu.

Masu haquri da junansu da jami’an da ke kula da al’amarinsu.

Masu xa’a, musamman lokacin shiga mota zuwa Makka daga Jeddah ko

Mina ko Arafa, da lokacin zuwa masauki, da lokacin tafiya Madina daga

Makka, da lokacin komawa Jedda don dawowa Nijeriya. Haka nan, su

zamanto masu xa’a a wajen awon kaya, da karvar jaka da guzuri.

Masu dauriya da haquri, musamman lokacin da aka samu`yar tangarxa a

wajen gudanarwa, imma sabo da jinkirin zuwan jirgi ko mota ko ba da

jaka ko guzuri. Su kasance masu yin haquri da ba da uzuri ga hukumar

jin daxin Alhazai da sauran jami’ai.

Wannan zai tabbatar wa maniyyata tarbiyyar zuciya ta vangaren haquri da

juriya da ake son a samu a qarshen aikin Hajji.

Taqawa Da Lazimtar Umurni Da Hani Na Allah

Taqawa ita ce mafi alherin guzuri da maniyyaci zai riqe tun daga lokacin

da ya bar gida domin tafiya qasa mai tsarki har ya dawo. Taqawa ta qunshi

aikata abin da Allah Ya farlanta da barin abin da Ya haramta, da tsarkake

ibada gare Shi. Don haka, dole ne maniyyaci ya nisanci dukan abubuwan

da aka haramta, ya aikata abubuwan da aka umurce shi, ya tsarkake

zuciyarsa da tabbatar da xa’a ga Allah a cikin aikin Hajjinsa, tare da

kaucewa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga karvuwar aikinsa.

Page 22: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 21 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Allah ( ) Ya girmama masu taqawa: Ya tanadar masu matsayi

babba da martaba maxaukakiya (2:212); Ya tabbatar masu da rabauta da

aljanna da ke da qoramu masu gudana da mata tsarkaka, sa’an nan kuma

ga yardar Allah a gare su (3:15); Ya bayyana cewa Yana tare da su kuma

Yana sonsu (3:76 2:192); Ya tabbatar masu da nasara (5:100); da rashin

tsoro da baqin ciki, tare da rabauta da bushara da alheri a duniya (7:35,

10:72-74); Ya yi alqawarin buxe masu albarkatu da ni’imomi daga sama

da qasa (7:96); Ya ba su ma’aunin gane bambanci tsakanin gaskiya da

qarya (8:29); Ya tabbatar da cewa Shi ne Majivincinsu (45:19); Ya yi

masu alqawarin kuvuta daga wuta a ranar qiyama (19:71-72); da tashi tare

da baqin Allah a ranar qiyama (19:85); da kyakkyawar makoma (20:132);

da babban rabo tare da gafarar zunubi (24:52, 33:70-71); da rahama da

shiriya (57:28); da matsayi amintacce (44:51); da mazauni na gaskiya

(54:54-55); da kuvuta daga mahassada da maqetata (3:120); da samun

sauqi a cikin dukan al’amura, da fita daga qunci (65:2-3, 65:4-5); da

samun karvar ayyuka (5:30); da kyakkyawar tariya daga mala’iku a ranar

qiyama (39:73).

Sanin amfanin taqawa da falalarta za su sanya maniyyaci ya kasance mai

kulawa sosai, musamman a vangaren haquri, da dogara ga Allah, da

girmama abubuwan da Allah Ya ce a girmama, da kamewa daga fushi, da

yafewa, da rashin tayar da hankali ko rashin biyayya a tsakanin shi da

sauran mahajjata ko hukuma.

Lazimtar Sunnah Da Nisantar Bidi’ah

Lallai ne maniyyaci ya quduri aniyar lazimtar Sunnah da nisantar bidi’a

tun daga farkon aikin Hajjinsa har zuwa qarshe. Ya tabbatar cewa ya yi

koyi da Manzon Allah ( ) a wajen gabatar da wannan

babbar ibada. Ya tuna cewa Manzon Allah ( ) ya yi umurni

da a koyi aikin Hajji daga gare shi.

Yana daga vangarorin da ya kamata a yi wa maniyyaci tanbihi a kai:

1. Qoqarin ganin bai wuce miqati, ba tare da ihrami ba. Idan an samu

wucewa Madina kai tsaye daga Jeddah, zai yi ihraminsa daga Zul Hulaifah. Idan kuwa ba za a samu damar wucewa ba sabo da

qurewar lokaci, maniyyaci ya yi ihrami a jirgi ko kafin ya shiga jirgi

ya fi zama daidai fiye da ya yi a Jeddah.

Page 23: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 22 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

2. Tabbatar da cewa ya jinkirta jifar jamrori zuwa bayan zawali a

ranakun kwanan Mina, ba wai ya riqa zuwa yin jifa da safe ba.

Manzon Allah ( ) bai yi jifa kafin zawali ba ko sau

xaya a cikin ranakun kwanan Mina.

3. Nisantar xabi’ar yawon kashe qwarqwatar ido, ta yadda za a tafi

wuri mai nisa a dawo a gajiye, hakan ya haifar da sakaci da salla a

cikin jam’i, a harami sabo da wannan gajiya.

4. Nisantar kurakuren da ake yi a Madina bayan ziyarar masallacin

Manzon Allah ( ) da masallacin Quba don yin salla,

da maqabartar Baqi’ah da shuhada’u Uhud don yi wa Sahabbai

addu’a. Da yawa daga mutane kan je waxansu wurare da sunan

ziyara ta ibada bayan waxannan wurare guda huxu da aka lissafa a

sama, waxanda Shari’a ta tabbatar. Wuraren da ake zuwa sun haxa

da: masjidul qiblataini, waxansu masallatai da ake cewa na sayyidina

Abubakar da Umar da Uthman da Aliyu ne, waxansu masallatai guda

bakwai da ake yin raka’a biyu a cikin kowanensu, wata rijiya da ake

cewa wai zoben Manzon Allah ( ) ya faxa ciki don su

sha ruwan rijiyar, wani kogo da ke dutsen Uhudu, da sauransu. Zuwa

waxannan wurare da sunan ibada ba shi da asali a cikin Sunnah.

5. Nisantar kurakuren da ake yi wajen xawafi da suka haxa da shiga

cikin hijru Isma’eel da tsayawa wajen indararo da sunan yin addu’a,

kasancewar hakan bai dace da Sunnah ba. Haka nan ma, yin karatu

ko addu’a cikin jam’i a wajen xawafi ko mutum xaya na faxi sauran

jama’a na amsawa bai dace da Sunnah ba. Bayan wannan, mahajjaci

ya guji matse mutane da tutture su a wajen xawafi da sa’ayi da jifar

jamrori.

6. Nisantar irin munanan xabi’un nan na biye wa mata tikari a yi ta

sakarci a ranakun kwanan Mina. Akwai bayanan da ke nuna cewa

waxansu mahajjata kan sheqe ayarsu a waxannan ranaku. Haka nan,

akwai bayanan da ke nuna cewa wasu daga cikin irin waxannan mata

har alfahari suke yi game adadin mutanen da suka vata wa aikin

Hajji.

7. Yawan husuma da savani da jayayya mara dalili da xabi’ar rashin

son bin doka da oda daga hukumar jin daxin Alhazai ko waxanda

aka ba shugabanci a cikinsu.

Page 24: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 23 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

4.1.3 NASIHOHI DA SHAWARWARI GA HUKUMA

Ko da yake manufar wannan qasida ita ce gabatar da bayani ga malamai

masu horar da maniyyata aikin Hajji, akwai buqatar gabatar da shawarwari

da nasihohi ga hukumar jin daxin Alhazai, kamar yadda aka gabatar ga

malamai da sauran maniyyata. Hasali ma, hukuma ta fi su buqatar

nasihohin da shawarwarin, kasancewar mas’uliyar a kanta yake.

Nasihohi da shawarwarin sun haxa da:

Ya kamata hukumar Alhazai ta riqa ba da gamsasshen ilmi ga mahajjata

tun daga nan gida Nijeriya har zuwa qasar Saudiya a kan karantarwar

Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah ( ) bisa fahimtar

magabata na qwarai. Wannan ne zai ba kowane Alhaji damar yin akin

Hajji cikin ilmi da basira. Hakan kuwa ba zai yiwu ba, sai an samu

malamai masu ilmi da tsoron Allah, waxanda suka san yadda ake aikin

Hajji.

Jami’an Alhazai su kasance masu matuqar haquri da Alhazai, domin

suna matsayin likitoci ne masu ba da magani ga waxanda ba su da

lafiya. Su tuna cewa su ne shugabanni kuma za su yi mu’amala ce da

mutane iri-iri, masu tarbiyya da halayya dabam-daban. Saurin fushi da

yawan faxa ko qyale, bai dace da jami’ai ba. Kuma jami’ai su kasance

masu mutunta Alhazai, kamar yadda ake son Alhazai su yi masu xa’a.

Ka da jami’ai su nuna rashin goyon bayansu qarara ga wanda ya yi

qoqarin kiyayewa da kuma aiki da abin da ya fahimta, matuqar hakan

ba zai jawo savani na usulu ba, ko ya kawo barazana ga zaman lafiya da

kwanciyar hankali ko kuma kyakkyawan jagoranci. Misali, wanda ya

fahimci cewar ya fi dacewa a yi ihrami a cikin jirgi ko kafin ma a shiga

cikin jirgi, maimakon sai an je Jeddah (kasancewar Jeddah ba miqati ba

ne), a qyale shi, ba tare da tsangwama ko takurawa ba. Sauran Alhazai

da ke ganin sai a Jeddah za su yi harama, idan an je sai su yi. Haka nan,

wanda ke ganin rashin halascin yin jifa a ranakun kwanan Mina kafin

zawal (kasancewar Manzon Allah – bai yi jifa ba sai bayan zawal a

cikin kwanaki uku na Mina), shi ma ka da a tsangwame shi.

Ya kamata hukumar Alhazai ta samar da wadatattun amsa kuwa

(na’urar xaga sauti) a Mina, ta yadda za a xaura su a qusurwoyin

tantunan Alhazai na wannan jiha. Hakan zai taimaka wajen samar da

tsarin wa’azi na bai xaya da kuma isar da saqo ga dukan mahajjata.

Page 25: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 24 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

Ya kamata jami’an Alhazai na qananan hukumomi su tanadar wa

malamai masu wa’azi qananan lasifika na hannu domin samun sauqin

isar da saqo a gidajen da suka sauka ko kuma wajen waxansu ayyukan

ibada a Makka ko Madina.

Ya kamata hukumar Alhazai ta qarfafa gwiwar waxanda za su buqaci

yin kwana uku a Mina, ta hanyar tanadar masu dukan abubuwan da suka

dace.

5.1 GODIYA DA KAMMALAWA

Kafin in kammala, ina son jawo hankalin mahalarta wannan taro da

waxanda ma ba su a nan cewa aikin Hajji ibada ce babba da ke kawo alheri

ga wanda ya yi ta, ko kuma ya taimaka wajen samun nasarar gabatar da ita

yadda ya dace. Don haka, waxanda ba su samu zuwa aikin Hajji ba daga

cikin malamai masu bita, da waxanda za su riqa faxakar da maniyyata

kafin su bar Nijeriya, da ma’aikatan hukumar jin daxin Alhazai, na ba da

gudummuwa ce gagaruma wajen samun nasarar wannan aiki. Qoqarin da

suke yi da gudummuwar da suke ba da wa, ibada ce da za ta kawo masu

lada mai yawa matuqar sun yi don Allah kuma bisa karantarwar Alqur’ani

da Sunnah. Sabo da haka, su ci gaba da ba da gudummuwarsu ba tare da

la’akari da cewa za a ba su kujerar Hajji ko ba za a ba su ba.

Su kuma maniyyata, akwai buqatar su lazimci dalilai na karvar kyawawan

aiki don gudun ka da su kasa cin moriyar wannan gagarumin aiki da suke

fuskanta. Su kasance masu qanqan da kai da rashin taqama ko ruxuwa da

yawan aikin da za su yi ko kyawun aikin a idanunsu; su kasance masu

tsoron a dawo masu da ayyukansu ba tare da an karva ba, sabo da rashin

ikhlasi ko rashin dacewa da bin Sunnah; kuma su kasance masu tsananin

kwaxayin rahama da falalar Allah da yawaita istigfari da kyawawan

ayyuka.

Daga qarshe, ina godiya ga hukumar jin daxin Alhazai ta jihar Niger da ta

ba ni damar gabatar da wannan qasida a matsayin ta wa gudummuwar, duk

da rashin cancanta ta, idan aka yi la’akari da qarancin ilmi da shekaru.

Ina roqon Allah Ya amsa mana wannan xan qoqari, kuma Ya sanya shi a

cikin mizanin kyawawan ayyukanmu. Abin da yake daidai, daga Allah ne,

kuma ina roqon Ya ba mu lada, kuma Ya ba mu ikon aiki da shi. Kuskuren

da ke ciki, daga gare ni ne, kuma daga shaixan; Allah da

Page 26: Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji

Shafi na 25 a cikin 21

Hanyoyin Horar Da Maniyyata Aikin Hajji Da Buqasa Basirar Malamai – Ahmad Bello Dogarawa

ManzonSa sun barranta daga gare shi. Ina roqon Allah

Ya yafe mani, kuma Ya ba ni ikon fahimtarsa, don in gyara.