gudummuwar malamai da jami'ai wajen aikin hajji

22
Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai Masu Gabatar Da Bita Wajen Gudanar Da Aikin Hajji Cikin Sauqi Na Ahmad Bello Dogarawa Sashin Koyar Da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria [email protected] A Matsayin Takarda Da Aka Gabatar Wajen Taron Qara Wa Juna Sani, Da Hukumar Kula Da Jin Daxin Alhazai Ta Jahar Neja Ta Shirya Wa Jami'anta Da Malamai Dake Gabatar Da Bita Ga Maniyyata Aikin Hajji Asabar, Sha'abaan 8, 1429 (Saturday, August 9, 2008)

Upload: tarbiyyarmusulunci

Post on 26-Jun-2015

55 views

Category:

Documents


8 download

TRANSCRIPT

Page 1: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai

da Malamai Masu Gabatar Da Bita Wajen

Gudanar Da Aikin Hajji Cikin Sauqi

Na

Ahmad Bello Dogarawa Sashin Koyar Da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria

[email protected]

A Matsayin Takarda Da Aka Gabatar Wajen Taron Qara Wa Juna Sani, Da

Hukumar Kula Da Jin Daxin Alhazai Ta Jahar Neja Ta Shirya Wa

Jami'anta Da Malamai Dake Gabatar Da Bita Ga Maniyyata Aikin Hajji

Asabar, Sha'abaan 8, 1429 (Saturday, August 9, 2008)

Page 2: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 1 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

1. GABATARWA

Akwai kusan ayoyin Alqur'ani guda talatin da tara (39) da suka yi magana

a kan Hajji.1 Waxansu ayoyin sun bayyanar da Hajji a matsayin xaya daga

cikin rukunan Musulunci, waxansu kuma suka bayyana ayyukan Hajji, da

manufofi, da hikimomi, da falala, da alheran da aikin ya qunsa.

Allah ( ) Ya shar’anta Hajji don tabbatar da manufar tauhidi da

samar da cikakkiyar `yan’uwantaka, ta yadda Musulmi daga kowane

vangare na duniya ke haxuwa a Makka don gabatar da ayyukan bauta da

samun tarbiyya, da gyaran zuciya da guzurin duniya da lahira.

Wannan takarda ta qunshi tattaunawa ce game da Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malaman da ke Gabatar da Bita wajen Gudanar da Aikin Hajji cikin sauqi. A matsayin shimfixa, takardar za ta yi tsokaci a

kan matsayi da falalar Hajji a Musulunci, da kuma yadda ake samun hajjun

mabrur ( ), wato, aikin Hajji nagartacce/karvavve.

1 Baqara (2:125-128; 158; 189; 196; 197-203); Aal Imraan (3:96-97); Maa'idah (5:1-2; 95-

97); Taubah (9:3; 19; 28); Hajj (22:27-37).

Page 3: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 2 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

An raba sauran bayanan da ke qunshe a cikin takardar gida uku: gava ta

gaba za ta yi magana ne a kan matsayi da falalar Hajji a Musulunci, da

kuma yadda ake samun hajjun mabrur. Kashi na biyu zai yi magana a kan

gudummuwar da jami'an hukumar Alhazai da malaman da ke gabatar da

bita za su ba da wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. Vangare na uku

zai qunshi godiya da kammalawa.

2. HAJJI A MUSULUNCI

Hajji na xaya daga rukunan Musulunci guda biyar. Alqur’ani da Sunnah da

Ijma’i duk sun tabbatar da wajibcin yin aikin Hajji sau xaya a cikin

rayuwa2 a kan kowane mukallafi (musulmi, baligi, mai hankali), namiji ko

mace, mai `yanci, da ke da iko (istixaa’ah).

Allah ( ) Ya ce:

Kuma Allah Yana da haqqi a kan mutane na yin Hajjin Xaki, ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirce, lallai Allah Mawadaci ne ga barin talikai.3

Manzon Allah ( ) ya ce:

Ya ku mutane, haqiqa Allah Ya farlanta Hajji a kanku, (sabo da haka) ku yi Hajji.4

Haka nan, Manzon Allah ( ) ya ce:

Ku yi gaggawar zuwa Hajji, domin xayanku bai san abin da zai bijiro masa ba (wanda zai iya hana shi zuwa aikin Hajji daga baya).5

A magana mafi qarfi da inganci, an farlanta Hajji ne a shekara ta tara da

Hijra ( ); wato shekarar da Manzon Allah ( ) ya naxa

babban sahabinsa, Abubakar ( ) a matsayin shugaban Alhazai. A

shekara ta goma, Manzon Allah ( ) ya jagoranci dubban

2 Ko da yake aikin Hajji wajibi ne sau xaya a cikin rayuwa, duk lokacin da mutum ya yi

bakance (alwashi) cewa zai yi aikin Hajji, Hajji ya wajaba a kansa 3 Aal Imraan 3:97

4 Muslim

5 Ahmad ya ruwaito, kuma al-Albani ya ce Hasan ne a cikin Irwaa’ul Ghaleel

Page 4: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 3 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Sahabbai zuwa aikin Hajjin ban kwana ( ). Ke nan, Manzon Allah

( ) sau xaya ya samu damar yin aikin Hajji a rayuwarsa, ko

da yake ya yi aikin Umrah kafin wannan lokaci.

Hajji na da falala mai yawan gaske. Daga cikin falalar Hajji akwai:

1. Hajji na kankare zunuban da suka gabata, ya rushe su, kuma ya

laqwame su. Manzon Allah ( ) ya ce:

Wanda ya yi (aikin) Hajji, bai yi jima’i (ko wani abu da zai kusantar da shi zuwa ga jima’i) ba, kuma bai yi aikin fasiqanci ba, zai koma kamar ranar da uwarsa ta haife shi (sabo da rashin zunubi)6

Haka nan, Manzon Allah ( ) ya ce wa sahabinsa `Amr

bn al-`Aas ( )

Ba ka san cewa Musulunci na rushe (zunuban da aka yi) kafin (a shige) shi ba, kuma Hijira na rushe abin da aka yi (na zunubai) kafin ita ba, kuma Hajji na rushe abin da aka yi kafin shi ba?7

2. Hajji na daga dalilai na samun `yanci daga wuta. Manzon Allah (

) ya ce:

Ba bu wata rana da Allah Ya fi `yanta bawa daga wuta fiye da ranar Arfah8

3. Hajji da Umrah na kore talauci. Manzon Allah ( ) ya

ce:

Ku bibiyi aikin Hajji da Umrah, domin suna kore talauci da zunubi kamar yadda zugazugi ke kore duddugar qarfe da zinare da azurfa.

9

6 Bukhari da Muslim

7 Muslim

8 Muslim

9 Ahmad, Tirmidhi da Ibn Majah

Page 5: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 4 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

4. Hajji na xaya daga cikin ayyukan da suka fi falala. An tambayi

Manzon Allah ( ) game da ayyukan da suka fi falala,

sai ya ce:

Imani da Allah Shi kaxai, sa’an nan Jihadi, sa’an nan Hajjun Mabrur (Hajjin da aka yi shi kamar yadda Shari’a ta ce). Tsakanin hajjun mabrur da sauran ayyuka, kamar tsakanin mahudar rana ce da mafaxarta10

5. Hajji shi ne jihadi mafi falala ga mata. A’isha ( ) ta ce wa

Manzon Allah ( ) ‘Ba za mu yi jihadi ba’? sai ya ce:

A’a, kuna da jihadi mafi falala da za ku yi: Hajjun Mabrur.11

6. Hajji da Umrah su ne jihadin tsofaffi da yara da masu rauni. Manzon

Allah ( ) ya ce:

Jihadin tsofaffi da yara da masu rauni da mata shi ne: Hajji da Umrah.12

7. Mahajjata baqin Allah ne da ake ba su abin da suka roqa. Manzon

Allah ( ) ya ce:

Mai yaqi fisabilillah, da mai Hajji, da mai yin Umrah (dukaninsu) baqin Allah ne; Ya kira su, sun amsa kiran, kuma suka roqe Shi (buqatunsu) Ya ba su.

13

8. Aljanna ce sakamakon aikin Hajji. Manzon Allah ( )

ya ce:

Kuma aljanna ce sakamakon Hajjun Mabrur14

10

Ahmad da Xabaraani. Kuma Bukhari da Muslim su ruwaito da lafazin da bai kai wannan

tsawo ba 11

Bukhari, Nasa’i da Ibn Majah 12

Nasa’i 13

Ibn Majah da Ibn Hibbaan 14

Bukhari da Muslim

Page 6: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 5 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Daga abin da ya gabata, Manzon Allah ( ) ya bayyana cewa

aljanna ce sakamakon Hajjun Mabrur. Imam al-Qurxubi ya bayyana

ma’anar Hajjin da ake kira mabrur a cikin tafsirinsa, kuma Ibn Hajar, a

cikin Fathul Baari, ya qarfafi cewa shi ne aikin Hajjin da aka cika

hukunce-hukuncensa kuma aka gabatar da shi yadda Shari’a ta ce, a bisa

fuska mafi cika.

Al’amuran da ke taimaka wa maniyyaci samun nagartaccen aikin Hajji

domin kai wa ga Hajjun Mabrur sun haxa da:

1. Tsarkake niyya (ikhlasi) da koyi da Manzon Allah (

) a cikin dukan ayyukan Hajji (mutaaba'ah).

2. Tattali da tanadi da kintsi ta hanyar tuba daga zunubansa, tun

kafin lokacin tafiya; neman taimako da dacewa daga Allah, da

bayyanar da tsananin buqata zuwa gare Shi, da tsoron azabarSa da

kwaxayin rahamarSa; kuvuta daga haqqoqin wasu, da mayar da

kayan da aka ba shi ajiya, da biyan bashin da ake binsa, da sanar

da `yan’uwa da maqwafta da abokan arziqi cewa zai yi tafiya,

kuma ya nemi su yi masa addu’ar dacewa da samun qabuli daga

Allah; samun tsarkakakken guzuri, kasancewar guzurin da ya ke

na haram na da mummunan tasiri a kan addu’o’in da mahajjaci zai

yi a halin da ya ke aikin Hajji; tanadi wadatacce ga iyalinsa da

sauran waxanda ke qarqashinsa gwargwadon ikonsa, kafin ya tafi

aikin Hajji; zaven abokai na qwarai waxanda za su taimaka wa

mahajjaci idan ya yi rauni, su cincixa shi idan ya gaza, su tunatar

da shi idan ya manta, su ilmantar da shi idan ya jahilta, su umurce

shi da kyakkyawa su hana shi mummuna; qoqarin fahimtar

hukunce-hukuncen aikin Hajji da ladubbansa, da abubuwan da ke

gyara shi da waxanda ke vata shi, da hukunce-hukuncen da suka

shafi tafiya da sallar qasaru, da dai sauransu.

3. Fahimtar manufa da hikimomin aikin Hajji da suka haxa da: miqa

wuya ga umurnin Allah da sallamawa tare da jawuwa gare Shi;

tabbatar da tauhidi; girmama abubuwan da Allah ( ) Ya yi

umurni da a girmama su; son Manzon Allah ( ) ta

hanyar koyi da shi a cikin ayyukan Hajji gaba xaya; tunawa da

ranar Lahira ta hanyar tuna mutuwa da barin duniya zuwa lahira a

lokacin da maniyyaci ya fito daga gidansa, da tuna likkafani a

lokacin da ya sanya haraminsa, da tuna tsayuwa a gaban Allah a

Page 7: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 6 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

ranar Qiyama domin yin hisabi a lokacin da ya ga matsatsar

mutane, ya ji xaga muryoyinsu da bambancin yarensu; tabbatar da

tsoron Allah da taqawa ta hanyar kiyaye dokokin Allah domin

samun guzuri mafi alheri; samun cikakkiyar tarbiyya da

kyawawan xabi’u da suka haxa da kamun kai, kame fushi da

rashin husuma da barin jayayya mara dalili, tausasawa da

natsuwa, qanqan da kai, haquri, kyauta, da taimakon juna;

taimakekeniya da `yan’uwantaka da haxin kai a tsakanin

Musulmi; da yawaita zikirin Allah.

4. Qoqari wajen xa’a ga Allah da amfani da lokaci yadda ya dace ta

hanyar yawaita karatun Alqur’ani da zikiri da istigfari da sallar

nafila da halartar wuraren da ake yin karatu da wa’azi. Haka nan

an so mahajjaci ya zamanto mai kyauta gwargwadon iko, da

taimakon `yan’uwansa, da qoqarin kawo amfani ga juna, da

umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, da yawaita addu’a

da roqon Allah buqatu na alheri.

5. Nisantar zunubi da savon Allah a wajen aikin Hajji, da dagewa a

kan xa’a tun daga farkon aiki har zuwa qarshe.

3. GUDUMMUWAR MALAMAI DA JAMI'AN HUKUMAR

ALHAZAI WAJEN GUDANAR DA HAJJI A CIKIN SAUQI

Hajji ibada ce da ke buqatar cikakken shiri da kintsi da tanadi da tattali

daga maniyyata, da kuma kulawa ta musamman da jagoranci da xaukar

xawainiya daga shugabanni, tare da ilmantarwa daga malamai (tun daga

matakin bita har zuwa faxakarwa da ba da fatawa a lokacin aikin Hajji).

A wannan gava, takardar za ta yi tsokaci a kan irin gudummuwar da

jami'an hukumar Alhazai da malaman da ke gabatar da bita ga maniyyata

za su ba da wajen gudanar da ayyukan Hajji cikin sauqi.

3.1 GUDUMMUWAR MALAMAI

Ilmantar da maniyyata game da aikin Hajji abu ne muhimmi, kasancewar

ya qunshi karantar da su hukunce-hukuncen aikin Hajji da ladubban da ya

kamata mahajjaci ya kiyaye tun kafin ya bar Nijeriya zuwa qasar

Saudiyyah har ya dawo. Wannan kuma aikin malamai ne. Kenan, malamai

Page 8: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 7 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

na da babbar gudummuwa da za su ba da wajen gudanar da aikin Hajji

cikin sauqi da nasara.

Akwai vangarori guda huxu da malamai za su taimaka don cinma wannan

manufa:

3.1.1 Fahimtar da Maniyyata Manufofin Hajji ( )

Hajji na da manufofi. Aikin malamai ne da ke gabatar da bita su fahimtar

da maniyyata manufofin Hajji a Musulunci. Alqur'ani da Sunnah sun

bayyana manufofi guda uku na Hajji:

1. Gyaran zuciya ( ) da samun cikakkiyar tarbiyya da za ta zama

guzuri ga mutum a cikin dukan al'amura [Baqara, 197]. Dama duk

rukunan Musulunci irin wannan tazkiyya da tarbiyyar suke samar wa

wanda ya gudanar da su kamar yadda Shari'ah ta tabbatar [Baqara,

183; Taubah, 103; Ankabut, 45].

2. Ambaton Allah ( ) ta hanyar talbiyya da kabbarbari da addu'o'i

da sauran nau'o'in zikirin da ake yi a cikin ayyukan Hajji [Hajji, 37].

An ruwaito daga A'ishah ( ) cewa an shar'anta xawafi da

sa'ayi da tsayuwan Arfa da jifar jamrori ne domin a ambaci Allah.15

3. Shaida abubuwan amfani [ ] na duniya da lahira [Hajji,

28]. Imam Xabari ya ruwaito daga Mujahid cewa amfanin da ake

nufi ya haxa da kasuwanci da abubuwan da Allah Ya yarda da su

daga cikin albarkatun duniya da lahira.

Idan maniyyaci bai fahimci waxannan manufofi ba, zai iya tafka kura-

kurai. Idan kuma ya fahimta amma bai bi hanyoyin tabbatar da su ba, zai

rasa samun amfani da alherai masu tarin yawa, kamar yadda ba zai amfana

da tasirin da Hajji ke yi a cikin rayuwar Musulmi ba.

An ya kuwa, mutumin da ya fahimci waxannan manufofi zai qi tuba daga

zunubansa kafin ya bar Nijeriya, ko ya tozartar da haqqin iyalinsa don wai

zai je aikin Hajji, ko ya riqa kutsawa cikin mutane ba tare da la'akari da

waxanda ya ture ko ya taka ba, ko ya riqa yin gaggawar da ta wuce buqata

a cikin tafiya da gudanar da ayyukan Hajji, ko turereniya wajen shiga da

15

Daarimi (1780)

Page 9: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 8 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

sauka daga mota, ko zaven xaki a masauki, ko rashin natsuwa wajen

dawowa daga Arfa, ko rashin la'akari da sauran mutane a wajen jifa da

xawafi?

Don haka, gudummuwar malamai ta farko ita ce fahimtar da maniyyata

manufar aikin Hajji da kuma xaukar matakan tarbiyyantar da su a kan

haka.

3.1.2 Karantar da Hukunce-hukuncen Aikin Hajji

Karantar da maniyyata na da matakai guda uku: matakin karantar da

matsayi da falala da hukunce-hukunce da ladubba da tarbiyya, tare da

bayani game da yadda ake gudanar da aikin Hajji; matakin nuna siffar

aikin Hajji a majigi ko na’urar bidiyo ko faifan CD; matakin koyar da aikin

Hajji a aikace ta hanyar amfani da alamomi (kamar ka’aba, wurin safa da

marwa, wurin jifar jamrori, da arfah) irin waxanda maniyyaci zai tarar a

can qasar Saudiya.16

3.1.3 Ba da Muhimmanci ga Janibin Tarbiyya

A vangaren tarbiyya, gudummuwar malamai ta qunshi koyar da

muhimmancin taqawa da haquri da tsantsar bin Sunnah wajen gudanar da

ayyukan Hajji da zaman lafiya da jurewa wahala da lazimtar abokai na

qwarai da kyautata wa abokan tafiya da tausaya wa waxanda ke cikin

matsala da xa’a ga shugabanni da jami’ai da biyayya ga dokokin qasar

Saudiya da kare martaba da mutuncin Nijeriya.

Nazari da bin diddigin salon gudanar da bitar aikin Hajji a Nijeriya sun

tabbatar da cewa an fi ba da qarfi ga janabin ilmantar da maniyyata

hukunce-hukunce maimakon cusa masu tarbiyya da xabi'u masu kyau da

16

Takardar da na gabatar a wajen taron qarawa juna ilmi a shekarar da ta gabata (2007) mai

taken 'Hanyoyin Horar da Maniyyata Aikin Hajji da Bunqasa Basirar Malamai masu Gabatar da Bita ga Maniyyata' ta tattauna a kan matakai guda uku na horar da maniyyata da karantar

da su vangarorin tarbiyya.Domin cinma wannan manufa, masu gabatar da bita na buqatar

amfani da sahihan littafai da ke magana a kan aikin Hajji da Umrah. Ban da littafan fiqihu da

Hadisi da ke qunshe da bayanai a kan aikin Hajji, malamai na iya amfani da littafin al-Qiraa li Qaasidi Ummil Quraa na Imam ax-Xabari; al-Idah fi Manaasikil Hajj na Imam an-Nawawi;

Awdhahul Masaalik ilaa Ahkaamil Manaasik na Abdul-Azeez al-Muhammad as-Salmaan;

Khaalisul Jumaan na Sa’ood bn Ibrahim Shuraim; al-Mughnee fi Fiqhil Hajj wal Umrah na

Sa’eed bn Abdul-Qadir; Sifatu Hajjatin Nabiyyi na Muhammad Naasiruddeen al-Albani; al-Manhaj li Muridil Umrah wal Hajj da Manaasikul Hajj na Muhammad bn Saalih al-

Uthaymeen; da Ramyul Jamaraat wa maa Yata’allaqu bihi min Ahkaam na Sharaf bn Aliyu

as-Shareef.

Page 10: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 9 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

za su taimaka masu wajen gudanar da aikin Hajji cikin nasara. Wajibin

malamai shi ne bin usulubin magabata na qwarai ( ) wajen

karantarwa. Magabata sun kasance suna gabatar da janibin tarbiyya da

suluk a kan janibin koyar da ilmi.

Ban da wajibcin haquri, da taqawa, da lazimtar Sunnah, da yin xa'a da

biyyaya ga hukuma, da nisantar bidi'a da duk wani abin assha na zahiri, da

ya kamata a ilmantar da maniyyata, akwai buqatar malamai su tarbiyyantar

da maniyyata a kan waxannan vangarori guda uku:

Vangare na Farko: Matsalar Maimaita Aikin Hajji

Babu shakka, yin aikin Hajji fi ye da sau xaya abu ne mai kyau ga wanda

Allah Ya ba iko. Hasali ma, yawaita aikin Hajji da Umrah na kore talauci

kamar yadda Hadisi ingantacce ya nuna.

To sai dai kuma rashin maimaita aikin Hajji shi ya fi amfani da zama mafi

alheri ga Musulmi idan maimaitawar za ta haifar da xaya daga cikin

abubuwa guda uku:

1. Tozarta haqqin iyali da watsi da wajibinsu don kawai ana son

komawa aikin Hajji. Hakan zai kasance idan aka tafi ba tare da an

tanadar masu abin da zai wadace su ba har a dawo (wanda ya haxa

da abinci, kula da ilmi da lafiya, da muhalli), ko kuma idan ya

zamanto barinsu a gida zai jefa su cikin wani hali mai tsanani ko

mara kyau.

2. Cutarwa da quntatawa ga waxanda ba su tava zuwa ba. Hakan zai

kasance ne idan kujerun da hukuma ta tanada ba su kai yawan

mutanen da ke buqatar zuwa ba a wannan shekara, ko kuma zuwan

na shi zai haifar da qarin cunkoso mai cutarwa ga maniyyata ko

hukuma.

3. Yanke zumunta ta hanyar qin tallafa wa `yan'uwa da dangi a cikin

wani muhimmin abu da ya addabe su, kuma su ba su da halin

magance matsalar, amma shi zai iya taimakawa in ba domin ya yi

amfani da kuxin wajen biyan Hajji ba. Wannan ya sa Imam Ahmad

ibn Hanbal, da Abu Miskin, da Ibrahim an-Nakha'iy, da Ibn

Taimiyyah, da waxansu malamai masu yawa suke ganin fifiko da

Page 11: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 10 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

rinjayen taimaka wa `yan'uwa mabuqata a kan maimaita aikin

Hajji.17

Sabo da irin waxannan matsaloli da aka gabatar a sama, musamman ma na

biyu, da kuma fatawoyin da manyan malamai suka ba da, ya sa qasar

Saudiya ta sanya dokar hana duk wani xan qasar Saudiya gudanar da aikin

Hajji fi ye da sau xaya a cikin kowace shekara biyar.18

Ko da yake ba lalle

ne mutanen Nijeriya su kalli matsala ta biyun ta wannan fuskar ba,

sanannen abu ne cewa matsala ta xaya da ta uku sun zama kamar ruwan

dare a Nijeriya.

Sai dai kuma wannan hukunci bai haxa da jami'an hukumar Alhazai ko

jami'an gwabnati da sauran mutanen da ake tafiya da su don taimaka wa

Alhazai wajen gudanar da aikin Hajji yadda ya kamata ba.19

Vangare na Biyu: Cutar da Alhazai wajen Gudanar da Ayyukan Hajji

Da yawa daga Alhazai na tafka varna yayin gudanar da ayyukan Hajji ta

hanyar cutar da sauran mutane, da nuna qarfi ko wauta ga jama'a, da

tattake masu rauni, da rashin tausayi da tsoron Allah, da cuxanya da

mata/maza ba tare da larura ba. Waxannan matsaloli sun fi aukuwa a wajen

xawafi da sa'ayi da jifar jamrori.

Ya kamata masu gudanar da bita su sanar da maniyyata waxannan

ingantattun bayanai:

1. Manzon Allah ( ) ya umurci Umar ibn Khattab (

) da ya yi xawafinsa daga gefe kuma ya bi a hankali wajen jifar

jamra don gudun ka da ya cutar da mutane, sabo da qarfinsa.20

2. Ibn Abbas ( ) ya hana yin turereniya a wajen xawafi,

kuma ya ce: "Idan ka tarar da mutane da yawa a wajen ruknul yamani, ka da ka tsaya don wai ka tava shi, ka ci gaba da tafiya."

21

17

Duba littafin Al-Furu' na Ibn Muflih, da Kitaabuz Zuhd na Imam Ahmad, da Al-Fataawal Kubraa na Ibn Taimiyyah don qarin bayani 18

Sanin ilmin da da da abin da ake kira za su taimaka

wa mutane fahimtar dalilan irin waxannan hukunce-hukunce. 19

Irin waxannan mutane sun haxa da malamai da jami'an kula da lafiya ko jami'an tsaro 20

Ahmad da Abdur-Razzaaq 21

Musnad As-Shaafi'i da Abdur-Razzaaq

Page 12: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 11 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

3. A'ishah ( ) ta yi addu'ar rashin samun lada ga wani mutum

da ya shaida mata cewa ya tava rukn har sau biyu (2) ko uku (3) a

cikin xawafinsa. Ta ce: "Da ka ce 'Allahu Akbar' ka ci gaba da

tafiya (a cikin xawafinka) ya fi ka yi turereniya da matsatsa da

mutune wai don ka tava dutsen."22

4. Sa'ad ibn Abi Waqqas ( ) ya ce: "Idan ka samu sarari, je ka

tava. Idan kuwa ba ka samu ba, ka ce 'Allahu Akbar', ka ci gaba (da

xawafinka)23

5. Ibn Abbas ( ) ya kasance yana jin haushin wanda ke

turereniya (a wajen xawafi ko sa'ayi ko jifa) sabo da ko dai ya ji

rauni ne ko kuma ya ji wa waninsa.24

Lallai kam da maniyyatanmu za su fahimci waxannan bayanai kuma su yi

azamar aiki da su, za a samu ci gaba sosai, kuma za a daina yi wa `yan

Nijeriya kallon-biyu-ahu sabo da rashin tsari da xa'a a wajen aikin Hajji.

Vangare na Uku: Tsananta wa Kai

Waxansu Alhazanmu kan tsananta wa kansu wajen yin abubuwan da ba

dole ba ne. A wani lokacin, sukan takura kansu wajen aikata abin da babu

lada kwata-kwata. Tarbiyyantar da su a kan waxannan abubuwa tun

gabanin su bar Nijeriya zai tamaka in sha Allah wajen rage waxannan

matsaloli. Yana daga quntata da tsanantawar da Alhaji zai yi wa kansa ba

tare da dalili na Shar'iah ba:

1. Dagewa da nacewa a kan sai ya dafa multazim ko sai ya tava rukn ko ya sumbaci hajrul aswad, ko da kuwa irin wannan dagewar da

nacewar za su jawo a tattake shi ko ma a yi masa rauni. Wannan ya

sha faruwa! Duk da cewa aikata waxannan abubuwa na da falala,

maslaha da bayanan da suka gabata na hukunta cewa wani lokaci ya

fi kyau a haqura.

2. Shiga cikin hijr Isma'il da qoqarin yin addu'a a cikinsa. Ban da ma

turereniya da hakan kan jawo, babu dalili a kan falalar shiga wurin.

Hasali ma, hijr Isma'il vangare ne na Ka'aba.

22

Baihaqi 23

Baihaqi 24

Ibn Abi Shaybah

Page 13: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 12 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

3. Zuwa wajen indararo (da mutane ke cewa wai nan ne saitin

Madina) domin yin addu'a, alhali hakan na jawo matsanancin

turereniya da matsatsa. Akwai wadda aka tava tattake ta har ta

suma a qoqarin yin addu'a a wurin! Maganar da Al-Qadhi Iyaad ya

yi a cikin littafin As-Shifaa cewa an so mutum ya je wurin

indararon don yin addu'a ba ta inganta ba.

4. Tsananta wa kai wajen maqama Ibrahim da zimmar yin salla a

wurin duk da irin matsatsi da turereniyar da ake samu wani lokaci.

Ko da yake an so a yi raka'a biyu a wurin, bayan an kammala

xawafi, idan hakan zai sa a tutture mutane ko a cutar da su, sai a yi

sallar a wani wurin.

5. Hawa kan jabalur-rahmah a filin Arfa ko hawa kan dutsen Uhud a

Madina. Hakan ya kan jawo haxari ga mutane da dama. Mun sha

jin labarin waxansu dun faxo daga kan dutsen, tare da cewa babu

wani dalili ko falala da ya/ta tabbata a kan hawa dutsen. Haka nan

ma, yin amfani da kuxin guzuri mai yawa wajen ziyarar buxe ido a

masaajidus sab'ah, masjidul qiblatain, rijiyar da aka ce wai zoben

Manzon Allah ( ) ya faxa ciki, da sauransu. Irin

wannan kashe kuxi mara dalili kan haifar wa Alhazai da dama

matsala, musamman idan an samu jinkiri wajen dawowa Nijeriya

bayan aikin Hajji.

3.1.4 Nema wa Maniyyata Sauqi a cikin Fatawa da Karantarwa

Malamai su ne magadan Annabawa, kuma yana daga manhajin Annabawa

bayar da ilmi yadda ya dace tare da tausasawa, da qanqan da kai, da yin

bayani ga mutane gwargwadon qwaqwalwarsu. Ilmi da karantar da shi

amana ce da Allah zai tambaye su a ranar qiyama. Wajibi ne su zamanto

masu faxin gaskiya ba tare da la’akari da jin daxi ko rashin jin daxin wani

ba. Kuma su tabbatar da cewa abubuwan da suke karantar da mutane ba

mujarradin ra’ayinsu ba ne. Lallai ne su tabbatar da cewa abin da suke

karantarwa ya tabbata a cikin Alqur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata

na qwarai.

Yana daga abin takaici, ka ga waxansu malamai na karantar da abubuwan

da ba su tabbata ba a cikin ingantacciyar Sunnah, ko ka ji suna zafafawa a

wurin da ya dace a sauqaqa, ko tsanani a muhallin sauqi. Babu shakka,

waxannan kura-kurai ne a haqqin mai karantarwa da bayar da fatawa.

Page 14: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 13 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

A wajen aikin Hajji, malamai na da buqatar amfani da (qa'idodi) na

sassauci da sauqaqawa a cikin dukan al'amura, matuqar hakan bai sava wa

wani tabbataccen nassi ko wata sananniyar qa'ida ba. Hakan ya samu asali

a cikin Hadisin Jabir ibn Abdillah ( ) dangane da sauqin da

Manzon Allah ( ) ya yi wajen fatawa da karantarwa a

lokacin . Waxansu mutane sun yi tambaya game da gabatar da

waxansu ayyukan ranar goma ga wata (ranar jifar farko) maimakon jinkirta

su, amma Manzon Allah ( ) ya ce: 'Aikata wanda

ka jinkirta xin, kuma babu kome a kanka'.

Haka nan, akwai (abubuwan lura da la'akari) da (qa'idodi) da ake

buqatar malamai su yi amfani da su wajen ba da fatawa da karantarwa, ba

kawai a lokacin aikin Hajji ba, har ma da sauran lokuta. Waxannan

abubuwa sun haxa da:

1. La'akari da halin da ake ciki, da (bi'ar) da mutane suka taso a ciki, da

kuma savanin malamai in mas'ala ce da aka yi savani a kanta

2. Amfani da abin da ake cewa

3. La'akari da manufar Shari'ar Musulunci ( )

4. La'akari da matakin fahimtar waxanda ake karantarwa (

)

5. Bi sannu-sannu, kuma mataki-mataki ( ) a wajen karantarwa

6. Tabbatar da haxin kai da maslaha, ko da zai sa a bar wajibi (

)25

25

Irin wannan ya faru a zamanin halifancin Uthman ibn Affaan ( ) a lokacin da ya

cika sallar Zuhr da Asr a Mina, maimakon Qasru. Abdullah ibn Mas'ud ( ) ya yi masa

inkari a kan hakan, kasancewar Manzon Allah ( ) da Abubakar ( ) da

Umar ( ) qasaru suka yi, ba cikawa ba. Duk da haka, ya bi Uthman ( ) sallar.

Da aka tambaye shi dalili, sai ya ce: (savani sharri ne).

Page 15: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 14 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Akwai buqatar malamai su yi amfani da waxannan qa'idodi a lokacin aikin

Hajji domin samar da sauqi ga Alhazai, matuqar hakan bai yi karo da

tabbataccen nassi ba. Daga cikin wuraren da ya kamata a xabbaqa wasu

daga cikin qa'idodin, akwai:

Na Xaya: Filin Arfa

Akwai malaman da ke ganin cewa barin filin Arfa kafin faxuwar rana laifi

ne babba. Waxansu ma sun kai ga cewa wanda ya bar filin Arfa kafin

faxuwar rana, ya yi laifin da dole ya yanka dabba (a matsayin fidya).

Tabbatacciyar magana dai ita ce, tsayawa a filin Arfa har faxuwar rana

mustahabbi ne ko Sunna. Idan mutum bai tsaya har wannan lokaci ba,

matuqar dai ya tsaya a filin Arfa a cikin wani yanki na yinin ko dare,

Arfarsa ta yi.26

Kenan dai kuskure ne malamai su bayyana cewa wanda duk

ya bar filin Arfa kafin faxuwar rana, ya yi laifi.

Sai dai kuma, idan hukuma ta nemi a tsaya har zuwa faxuwar rana, sabo da

wata maslaha, lallai ne kowa da kowa ya tsaya. Waxanda ba a yi wani tsari

na xaukarsu zuwa muzdalifa ba, suna da damar barin filin kafin rana ta

faxi, idan sun so.

Na Biyu: Xawaful Ifadha da Sa'ayi a tsakanin Safa da Marwa

Dangane da xawaful ifadha, akwai mas'aloli guda biyar da ke buqatar

kulawa ta musamman:

Ba dole ne mutum ya yi xawaful ifadha a ranar goma ga wata ko a

tsakanin kwanakin Mina ba. Mafi yawancin malamai na ganin halascin

jinkirta wannan xawafi har zuwa kafin qarshen watan Zul Hijjah,

musamman idan ana tsoron cinkoso ko akwai rashin lafiya, ko wata

larura dabam.

Mutumin da bai yi xawaful ifadha ba sabo da mantuwa, kuma bai tuna

ba sai bayan ya yi xawaful wada'i (xawafin ban kwana), Hajjinsa ya

inganta, kasancewar wannan xawafin ya xauke wa wancan, kamar

yadda Imam Nawawi ya tabbatar a cikin littafin sharhin Sahih

Muslim [8/193].

26

Dalili a kan haka, na qunshe cikin wani Hadisi sahihi da Abu Dawud (1950); Tirmizi (891);

Nasa'i (3041); da Ibn Majah (3016) suka ruwaito.

Page 16: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 15 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Akwai savani dangane da yin xawafi ba tare da alwalla ba. Mafi

yawancin malamai sun sharxanta alwalla ga wanda zai yi xawafi.

Waxansu na ganin idan ma alwallar mutum ta karye alhali yana cikin

yin xawafi, zai yanke, ya sake alwalla, ya fara xawafin daga farko;

waxansu na ganin zai yi gini ne a kan adadin da ya yi kafin warwarewar

alwallar; waxansu kuma suka ce zai iya qarasawa ba tare da alwallar ba.

Amma, Imam Abu Hanifah na ganin halascin yin xawafi ba tare da

alwalla ba, tun daga farkonsa har qarshe. An ruwaito irin wannan

magana daga Imam Ahmad ibn Hanbal. Ibn Taimiyyah da Ibn Qayyim

da Al-Uthaymin sun qarfafi wannan fahimta, kuma sun rinjayar da ita a

kan ta jumhur. Kuma tabbas wannan fahimta ta fi inganci, musamman

idan aka yi la'akari da cewa babu wani dalili sahihi a kan wajibcin

alwalla kafin a yi xawafi.27

Bayan wannan, dagewa a kan wajibcin

alwalla a lokacin xawafi abu ne da ke zamantowa tsanani ga masu

larurori dabam-daban, kuma yana haifar da tsananin cunkoso a wajen

alwalla.

Duk da cewa wannan fahimtar ta fi kawo sauqi a cikin ayyukan Hajji,

lallai ne Alhazai su yi qoqarin yin alwalla kafin su fara xawafi, matuqar

babu wata larura babba da za ta hana su. Idan alwallarsu ta lalace kafin

su kammala xawafin, za su ci gaba, ba tare da jaddada alwalla ba.

Mai jinin al'ada (ko jinin haihuwa) za ta yi ayyukan Hajji gaba xaya, in

ban da xawafi, kamar yadda Hadisi ya tabbatar. A haqqinta, za ta

jinkirta xawafi har sai ta samu tsarki. To amma idan lokacin dawowarta

gida daga Makka ya yi kafin ta samu tsarki, kuma babu wani tanadi da

aka yi na dawowarta daga baya, tana da damar ta yi qunzugu (wato,

kamar ta sanya audugar mata), ta gabatar da xawafinta a hakan, kamar

yadda Ibn Taimiyyah da Ibn Qayyim suka haqqaqa. Sun bayyana cewa

yin hakan shi ne iyakar qoqarinta, tun da ya zama larura. Hakan ya dace

da abin da aka ruwaito daga Abu Hanifa da Ahmad ibn Hanbal. Kuma

qa'idar za ta yi aiki a nan.

Yana daga sauqaqawa a cikin ayyukan Hajji, fatawar da waxansu

malamai su ka ba da cewa idan akwai tsananin cinkoso a wajen xawafi,

za a iya gabatar da sa'ayi a tsakanin safa da marwa, sa'an nan, daga baya

a yi xawafin. Irin waxannan malamai na ganin cewa babu wani dalili

27

Babu hujjar wajibcin yin alwalla a cikin Hadisin da ya zo da hukuncin yin xawafi ga mai

jinin al'ada. Shi kuma Hadisin da ya zo da maganar wajibcin yin alwalla qarara, bai inganta

ba.

Page 17: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 16 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

tabbatacce da ya sharxanta yin xawafi kafin sa'ayi. Sabo da haka, suke

xaukar gabatar da xawafi a kan sa'ayi a matsayin Sunnah, kasancewar

hakan ne Manzon Allah ( ) ya yi. Ke nan, idan akwai

larura, za a iya akkasawa, kamar yadda ya zo qarara a cikin Hadisin da

aka yi wa Manzon Allah ( ) tambaya dangane da gabatar

da sa'ayi a kan xawafi, kuma ya ce, 'je ka yi (xawafin), babu laifi'.28

Kasancewar ya halasta a jinkirta xawaful ifadha, da zarar mutum ya jefi

jamratul aqabah, ya yi aski, shi kenan, ya samu tahallulin farko (

), wato cire harami da samun damar yin amfani da duk abubuwan da

aka haramta masa a lokacin aikin Hajji, in ban da saduwa da mace.29

Ba

ya buqatar ya sake sanya haraminsa a lokacin da zai yi xawafin. Shaikh

Muhammad Nasiruddeen Al-Albani na ganin cewa za a mayar da

harami matuqar ba a yi xawaful ifadha a ranar goma ga wata ba, sabo

da wani Hadisi ingantacce. Amma Shaikh Muhammad Salih Al-

Uthaymin ya yi raddin wannan ra'ayi, kasancewar al'umma gaba

xayanta ta sava wa wannan Hadisi. Ya bayyana cewa mutum xaya ne

daga cikin tabi'ai ya tafi a kan ma'anar Hadisin. Don haka, ya kamata

malamai su yi amfani da wannan sauqi.

Na Uku: Jifar Jamratul Aqabah da Jamrori uku a ranakun Mina30

A qarqashin wannan gavar, akwai mas'aloli guda biyar: lokacin fara jifar

jamratul aqabah a ranar goma ga wata (kashegarin Arfa); lokacin jifa a

ranakun Mina; haxa jifar kwana biyu ko kwana uku a rana xaya; wakilci a

wajen jifa; da rashin kwana a Mina a ranakun jifa. 28

Shaikh Muhammad ibn Salih Al-Uthaymin ya yi magana mai kyau dangane da wannan

qa'ida ta (je ka yi babu laifi). Ya ce:

.

29

Waxansu malaman na ganin cewa Alhaji na samun tahallulin farko da zarar ya yi jefi

jamratul aqabah, ko da bai yi aski ko yanka ba. 30

Ranakun da ake gabatar da ayyukan Hajji na da sunayensu. Ranar takwas ga wata, wato

ranar da ake fita Mina, ana kiranta ; ranar tara ga wata ; ranar goma ga wata, wato

ranar jifar jamratul aqabah ; ranar sha xaya ga wata ; ranar sha biyu ;

ranar sha uku ga wata

Page 18: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 17 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Wajibi ne Alhaji ya kwana a Muzdalifa, matuqar ba larura ce ta hana

hakan ba. Idan mutum bai kwana ba, zai ba da jini, ta hanyar yanka

dabbar fidyah. Idan kuwa bai samu isowa Muzdalifa ba sai bayan

fitowar alfijir, sabo da cunkoso ko gajiyar tafiya daga filin Arfa, ko wata

larura, wajibinsa shi ne ya tsaya a filin Muzdalifa na xan wani lokaci,

sa'an nan ya wuce zuwa wurin jifar jamratul aqabah. A irin wannan hali,

babu kome a kansa na fidyah. A taqaice dai, ba a jifar jamratul aqabah

sai bayan sallar alfijir. Yana daga Sunna a xan jinkirta jifar har sai

bayan fitowar rana, kamar yadda Manzon Allah ( ) ya yi.

Amma, waxanda ke da rauni, kamar mata da yara da tsofaffi da

marasa lafiya, ba su shiga cikin wannan hukunci ba. A haqqinsu, ya

halasta su bar Muzdalifa a qarshen dare, ta yadda za su isa wurin jifar

jamratul aqabah kafin fitowar alfijir, ko kuma da zarar ya fito. Manufar

ita ce su samu damar yin jifa kafin sauran mutane su iso. A magana mafi

qarfi, duk lokacin da suka isa wurin jamrar, za su gabatar da jifa, ko da

kuwa alfijir bai fito ba.

Asali dangane da lokacin yin jifa a ranakun Mina, shi ne daga bayan

zawal, wato wucewar rana daga tsakiyar sama zuwa faxuwar rana. A

wannan lokacin ne Manzon Allah ( ) da Sahabbansa (

) suka jefi jamrori. Ya tabbata a cikin Hadisi cewa Manzon Allah

( ) ya ba waxansu damar yin jifa cikin dare har zuwa

kafin fitowar alfijir.31

Hanafiyya da waxansu malaman malikiyya da

shafi'iyya duk sun bayar da fatawa da wannan. Haka nan ma,

ta tabbatar da wannan.

To sai dai kuma an ruwaito daga Ibn Abbas ( ) da Xawus, da

Muhammad Baqir, da Abu Hanifa, da Ibn Aqil, da Ibnul Jauzi32

, da Ar-

Rafi'í33

cewa za a iya yin jifa kafin zawal, tun daga lokacin walha. A

wannan zamanin kuma, an samu irin wannan fatawa daga Abdullah ibn

Mahmud, da Musxafa Zarqa, da Salih Al-Bulaihi. Haka nan, an ce

Abdur-Rahman As-Sa'adi ma yana ganin halascin haka.

31

Bukhari da Abu Dawud 32

Ibn Aqil da Ibnul Jauzi `yan hanbaliyya ne 33

Ar-Rafi'i xan shafi'iyya ne

Page 19: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 18 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Bin diddigin abin da aka ruwaito daga Ibn Abbas ya tabbatar da cewa

isnadin mai rauni ne. Ban da wannan ma, abin da aka ruwaito daga Ibn

Umar ( ) na goyon baya ga maganar Ibn Abbas ( ) bai

inganta ba, ballantana ma Hadisin da Daru Qutni ya ruwaito cewa wai

Manzon Allah ( ) ya halasta yin jifa a kowane lokaci.

Dangane da ra'ayin Abu Hanifa kuwa, manyan xalibansa, Abu Ishaq da

Abul Hasan, sun bayar da fatawa savanin wannan, kuma mazhabar

hanafiyya ta yi watsi da ra'ayin Abu Hanifa a kan wannan. Al-Uthaymin

kuma ya yi wa sauran malaman raddi, ya bayyana cewa ka da Alhazai

su yi jifa sai bayan zawal.

Duk da cewa babu hujja mai qarfi dangane da gabatar da jifa kafin

zawal, idan maslaha ta hukunta yin jifar kafin zawal xin, zai shiga cikin

babin sauqaqawa. Wataqila la'akari da irin matsalolin da ake yawan

samu a ranakun jifa, sabo da yawan jama'a, yasa hukumar Saudiya ta

tsara wa kowace qasa lokacin da za ta yi jifa, ba tare da la'akari da

bayan zawal ne ko kafinsa ba. Qa'idar za ta yi amfani a

nan.

Yana daga sauqin da malamai za su yi, ba da fatawa a kan halascin haxa

jifar kwana biyu ga jami'an da ya zamanto dole su yi hakan ko masu

tsananin larura. Ko da yake qa'idar ita ce, a yi jifa a kowace rana, ya

tabbata cewar Manzon Allah ( ) ya yi rangwame ga

makiyaya da su haxa jifar kwana biyu a rana xaya.34

Wannan ne

fahimtar Imam Shafi'i da Ahmad ibn Hanbal.

Kenan, waxanda suka samu kansu a irin halin da waxancan makiyaya

suka kasance, kamar masu ayyukan kula da lafiya, ko marasa lafiya, ko

jami'an hukuma da ya zama dole su kasance a Makka ko Madina, za a

iya ba su fatawar yin haka. Shaikh Muhammad Salih Al-Uthaymin

yana ganin halascin yin jifar yini ukun gaba xaya a rana xaya, matuqar

da larurar haka.35

Ko da yake wajibi ne kwana a Mina a ranakun jifar jamrori, waxanda ke

da sahihiyar larurar da za ta hana su kwana a Mina, na da damar kwana

a Makka ko wani wuri dabam. In ya so, kowace rana, sai su tafi Mina

domin yin jifa. Dalili a kan haka na cikin Hadisin da Ibn Abbas (

34

Muwaxxa (815); Abu Dawud (1975); Tirmizi (955) 35

Duba littafin As-Sharhul Mumti' Ala Zaadil Mustaqni

Page 20: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 19 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

) ya ruwaito cewa Manzon Allah ( ) ya ba Abbas

( ) damar ya kwana a Makka a ranakun Mina domin taimakawa

wajen shayar da Alhazai.36

Haka nan, Hadisi ya tabbata cewa Manzon

Allah ( ) ya ba makiyaya damar kwana a wajen Mina.37

3.2 GUDUMMUWAR JAMI'AN HUKUMAR ALHAZAI

Hukumar jin daxin Alhazai ce ke da alhakin tabbatar da cewa an gudanar

da aikin Hajji cikin sauqi, kuma yadda ya kamata. A matakin jiha da

tarayya, ana sa ran jami'an su kai su kawo wajen tabbatar da samun nasarar

ayyukan Hajji baki xaya.

Gudummuwar jami'an hukumar Alhazai na da yawan gaske, musamman da

yake rashin ba da ta su gudummuwar na iya durqusar da aikin Hajji ko ma

ya hana gudunarsa baki xaya. Yana daga vangarorin da ya kamata jami'an

su kula:

Fahimtar cewa wata dama ce Allah Ya ba su, ta su yi wa baqinSa,

Alhazai, xawainiya da hidima, don gudanar da aikin Hajji cikin

walwala. Abin da Allah Yake girmamawa, wajibi ne kowane musulmi

ya girmama, kuma ya ba shi muhimmanci. Tun da Alhazai baqin Allah

ne, kuma aikin Hajji ibada ce da Allah Yake matuqar so, lalle ne

ma'aikacin hukumar Alhazai ya ba wannan aiki muhimmanci.

Ya kamata su tuna cewa akwai mutane da yawan gaske da ke matuqar

buqatar zuwa aikin Hajji, amma ba su samu dama ba. Wasu daga

cikin jami'an hukumar Alhazai sun tafi aikin Hajji ya fi sau goma.

Gwabnati ke xaukar nauyin tafiyarsu da guzurinsu da sauransu.

Wannan ya nuna abubuwa guda biyu: wajibcin gode wa Allah a kan

ni'imar zuwa aikin Hajji shekara da shekaru, tun da lallai Allah zai

tambaye su a kan wannan ni'ima; da wajibcin gudanar da ayyukan da

hukumar Alhazai ta xora masu, ba tare da son rai ko kasala ba,

kasancewar ta hakan ne kawai za su tabbatar da cancantar kashe kuxin

da gwabnati ta yi a kansu. Ke nan, barci, ko yawon buxe idanuwa, ko

zaman hira, ko tafiyar ganin gari, bai dace da su ba, musamman a

Makka da Madina.

36

Bukhari da Muslim 37

Muwaxxa (815); Abu Dawud (1975); Tirmizi (955)

Page 21: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 20 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

Wajibi ne su ji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukan amana da aka ba

su, a madadin Alhazai. An daxe ana kuka da jami'an hukumar Alhazai

na mafi yawancin jihohi game da sama-da-faxi da suke yi da kuxin

hadaya.

Xabi'ar nuna wariya ko bambanci a tsakanin Alhazai ba ta dace ba. Lalle

ne jami'an hukumar Alhazai su guji yin haka.

Ya kamata jami'ai su taimaka wa hukumar Alhazai wajen bayar da

gamsasshen ilmi ga mahajjata tun daga nan gida Nijeriya har zuwa

qasar Saudiya a kan karantarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah

( ) bisa fahimtar magabata na qwarai. Wannan ne zai ba

kowane Alhaji ya samu damar yin akin Hajji cikin ilmi da basira.

Hakan kuwa ba zai yiwu ba, sai an samu malamai masu ilmi da tsoron

Allah, waxanda suka san yadda ake aikin Hajji.

Jami’an Alhazai su kasance masu matuqar haquri da Alhazai, domin

suna matsayin likitoci ne masu bayar da magani ga waxanda ba su da

lafiya. Su tuna cewa su ne shugabanni, kuma za su yi mu’amala ce da

mutane iri-iri, masu tarbiyya da halayya dabam-daban. Saurin fushi da

yawan faxa, ko qyale, bai dace da jami’ai ba. Kuma jami’ai su kasance

masu mutunta Alhazai, kamar yadda ake son Alhazai su yi masu xa’a.

Ka da jami’ai su nuna rashin goyon bayansu qarara ga wanda ya yi

qoqarin kiyayewa da kuma aiki da abin da ya fahimta, matuqar hakan

ba zai jawo savani na usulu ba, ko ya kawo barazana ga zaman lafiya da

kwanciyar hankali ko kuma kyakkyawan jagoranci. Misali, wanda ya

fahimci cewar ya fi dacewa a yi ihrami a cikin jirgi ko kafin ma a shiga

cikin jirgi, maimakon sai an je Jeddah (kasancewar Jeddah ba miqati ba

ne), a qyale shi, ba tare da tsangwama ko takurawa ba. Sauran Alhazai

da ke ganin sai a Jeddah za su yi harama, idan an je, sai su yi.

Ya kamata jami'ai su ba hukumar Alhazai shawarar samar da wadatattun

amsa kuwa (na’urar xaga sauti) a Mina, ta yadda za a xaura su a

qusurwoyin tantunan Alhazai na wannan jiha. Hakan zai taimaka wajen

samar da tsarin wa’azi na bai xaya da kuma isar da saqo ga dukan

mahajjata.

Ya kamata jami’an Alhazai na qananan hukumomi su tanadar wa

malamai masu wa’azi qananan lasifika na hannu domin samun sauqin

Page 22: Gudummuwar Malamai Da Jami'ai Wajen Aikin Hajji

Shafi na 21 a cikin 19

Gudummuwar Jami'an Hukumar Alhazai da Malamai wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. – Ahmad Bello Dogarawa

isar da saqo a gidajen da suka sauka ko kuma wajen waxansu ayyukan

ibada a Makka ko Madina.

Ya kamata jami'an hukumar Alhazai su qarfafa gwiwar waxanda za su

buqaci yin kwana uku a Mina, ta hanyar tanadar masu dukan abubuwan

da suka dace.

4. GODIYA DA KAMMALAWA

Daga qarshe, ina son jawo hankalin mahalarta wannan taro da waxanda ma

ba su a nan, cewa aikin Hajji ibada ce babba da ke kawo alheri ga wanda

ya yi ta, ko kuma ya taimaka wajen samun nasarar gabatar da shi yadda ya

dace. Don haka, waxanda ba su samu zuwa aikin Hajji ba daga cikin

malamai masu bita, da waxanda za su riqa faxakar da maniyyata kafin su

bar Nijeriya, da jami'an hukumar jin daxin Alhazai, na bayar da

gudummuwa ce gagaruma wajen samun nasarar wannan aiki. Qoqarin da

suke yi da gudummuwar da suke bayarwa, ibada ce da za ta kawo masu

lada mai yawa matuqar sun yi don Allah kuma a kan karantarwar

Alqur’ani da Sunnah. Sabo da haka, su ci gaba da bayar da

gudummuwarsu ba tare da la’akari da cewa za a ba su kujerar Hajji ko ba

za a ba su ba.

Su kuma maniyyata, akwai buqatar su lazimci dalilai na karvar kyawawan

aiki don gudun ka da su kasa cin moriyar wannan gagarumin aiki da suke

fuskanta. Su kasance masu qanqan da kai da rashin taqama ko ruxuwa da

yawan aikin da za su yi ko kyawun aikin a idanunsu; su kasance masu

tsoron a dawo masu da ayyukansu ba tare da an karva ba, sabo da rashin

ikhlasi ko rashin dacewa da bin Sunnah; kuma su kasance masu tsananin

kwaxayin rahama da falalar Allah da yawaita istigfari da kyawawan

ayyuka.

Daga qarshe, ina godiya ga hukumar jin daxin Alhazai ta jihar Neja da ta

ba ni damar gabatar da wannan takarda a matsayin ta wa gudummuwar

wajen gudanar da aikin Hajji cikin sauqi. Ina roqon Allah Ya amsa mana.