sunnah news nigeria · 2018-01-26 · kungiyar jni, dakta khalid aliyu, ya maida martani ga wani...

7
SUNNAH NEWS NIGERIA Labaran Sunnah A Tafin Hannun ku MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI DATE: Friday 26, January, 2018 Sheikh Balalu Ya Zama Shugaban Ahlussunnah Na Tarayyar Turai Kungiyar Izala ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa kungiyar ba kungiya ce ta siyasa ba, kuma bata da wata alaka da wata kungiyar siyasa hasalima an kafa kungiyar domin kira izuwa ga hanyar Allah ba domin yiwa wani bangaren siyasa aiki ba, Dr. Pakistan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da Sunnah News Nigeria tayi dashi jim kadan bayan da wani dan siyasa a jihar ya bayyana sunayen wasu daga maluman addini na bangarorin darika da kuma Izalar da cewa sunyi musu addu’o’I dangane da wasu shirye-shirye da suke yi na siyasarsu, hakan kuma yana zuwa ne a dai-dai lokacin da masu adawa da gwamnatin jihar Kano ke zargin cewa an kasha ma’udan kudade wajen yiwa shugaban kasa addu’a a lokacin zuwansa Kano. Allah ya kyauta Sunnah News Nigeria 26/01/2018 Sabuwar Tashar Sunnah News TV Tana Kan Hanya A yanzu zaku iya samun shirye-shiryen mu a dandalin Youtube a Sunnah News Nigeria, Idan kunje kawai kuyi subscribing Izala Ba Kungiyar Siyasa Bace - Dr. Abdallah Saleh Pakistan SUNNAH NEWS NIGERIA DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253,08066989773, 08149332007, 08168015170 Shugaban kungiyar Izalar Naijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya zama Shugaban Ahlus Sunnah na Europe baki- daya, bayan karba gayyatar kungiyar Sautus Sunnah Europe ta kasar Turai. Haka Zalika kungiyar Sautus Sunnah Europe ta gina wa kungiyar Izala Ofishi, a Cibiyar Ahlus Sunnah ta Turai baki- daya. "Mun yi nazarin kungiyoyi- kungiyoyi na Musulunci da Ahlus Sunnah a duniya, sama da kungiyoyi sittin (60), a kasashe daban-daban. Amma ba mu ga kungiyar da Allah Ya ba nasara cikin takaitaccen lokaci irin wadda Ya ba kungiyar Izala ba". — Inji Jagororin Kungiyar Sautus Sunnah Europe ta kasar Turai. Allah Ka kara wa kungiyar Izala albarka da daukaka. Ameen. Rahoto: Abdurrahman Abubakar Sada Darulfirk.com Takuce Domin Yada Sunnah Cibiya guda daya tilo wadda take kawo muku karatuttukan maluman Sunnah daga wurare daban- daban a kowane lokaci, aciki da wajen kasarmu Nigeria. http://facebook.com/darulfikrng

Upload: others

Post on 25-Jan-2020

0 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

SUNNAH NEWS NIGERIA

Labaran Sunnah A Tafin Hannun ku

MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI DATE: Friday 26, January, 2018

Sheikh Balalu Ya Zama Shugaban Ahlussunnah Na

Tarayyar Turai

Kungiyar Izala ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa kungiyar ba kungiya ce ta siyasa ba, kuma bata da wata alaka da wata kungiyar siyasa hasalima an kafa kungiyar domin kira izuwa ga hanyar Allah ba domin yiwa wani bangaren siyasa aiki ba, Dr. Pakistan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da Sunnah News Nigeria tayi dashi jim kadan bayan da wani dan siyasa a jihar ya bayyana sunayen wasu daga maluman addini na bangarorin darika da kuma Izalar da cewa sunyi musu addu’o’I dangane da wasu shirye-shirye da suke yi na siyasarsu, hakan kuma yana zuwa ne a dai-dai lokacin da masu adawa da gwamnatin jihar Kano ke zargin cewa an kasha ma’udan kudade wajen yiwa shugaban kasa addu’a a lokacin zuwansa Kano. Allah ya kyauta Sunnah News Nigeria 26/01/2018

Sabuwar Tashar Sunnah News TV Tana Kan Hanya A yanzu zaku iya samun shirye-shiryen mu a dandalin Youtube a Sunnah News Nigeria, Idan kunje kawai kuyi subscribing

Izala Ba Kungiyar Siyasa Bace

- Dr. Abdallah Saleh Pakistan

SUNNAH NEWS NIGERIA DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253,08066989773, 08149332007, 08168015170

Shugaban kungiyar Izalar Naijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya zama Shugaban Ahlus Sunnah na Europe baki-daya, bayan karba gayyatar kungiyar Sautus Sunnah Europe ta kasar Turai. Haka Zalika kungiyar Sautus Sunnah Europe ta gina wa kungiyar Izala Ofishi, a Cibiyar Ahlus Sunnah ta Turai baki-daya. "Mun yi nazarin kungiyoyi-kungiyoyi na Musulunci da Ahlus Sunnah a duniya, sama da kungiyoyi sittin (60), a kasashe daban-daban. Amma ba mu ga kungiyar da Allah Ya ba nasara cikin takaitaccen lokaci irin wadda Ya ba kungiyar Izala ba". — Inji Jagororin Kungiyar Sautus Sunnah Europe ta kasar Turai. Allah Ka kara wa kungiyar Izala albarka da daukaka. Ameen. Rahoto: Abdurrahman Abubakar Sada

Darulfirk.com Takuce Domin Yada Sunnah Cibiya guda daya tilo wadda take kawo muku karatuttukan maluman Sunnah daga wurare daban-daban a kowane lokaci, aciki da wajen kasarmu Nigeria.

http://facebook.com/darulfikrng

Page 2: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

2

Kungiyar Musulman Najeriya, Jamatul Nasir Islam (JNI) ta zargi kungiyar Kristoci Najeriya CAN da kirkiran rikicin makiyaya. Da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna , sakataren kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da yi wa Kiristocin Najeriya kisan ‘kare dangi. Khalid Aliyu yace karya kungiyar CAN ta ke yi kuma dole a bayyana gaskiya, ba don kare gwamnati ba sai dai don kare Musulmai daga sharrin da ake yi masu. JNI tace ba ta manta da lokacin da wani Fasto (Johnson Suleman)yayi kira da a kashe Fulani a kasar nan ba. Bayan haka Dr.Khalid yace akwai lokutan da aka rika kama Kiritoci a lokacin da suke kokarin kona coci da sunan Musulmai a Najeriya amma CAN tayi shiru ba ta ce komai ba. A Jihar Benuwe an kama masu ta’adanci kuma babu musulmi ko makiyayi guda daya a cikin su. An kashe musulmai da yawa a jihar Taraba, Kaduna, Zamfara, da Katsina amma Kristoci sun yi shiru basu ce komai ba.

Rahoto: Hassan Auwalu Ya’u

Nasril Islam Ta Zargi Kungiyar Can Da Hannu Cikin Rikicin Makiyaya

Kotun daukaka kara a Najeriya ta fara sauraron karar da gwamnatin tarayya ta daukaka, a kan hukuncin da wata babbar kotun kasar ta bayar da umurnin a saki shugaban kungiyar ‘yan uwa musulmi ta ‘yan shi’a na kasar. Gwamnatin na ci gaba da tsare El Zakzaky ne, duk da umarnin babbar kotun kasar da ta ce a sake shi a watan disamban shekarar 2016. Alakalan kotun uku ne suka saurari karar a ranar Litinin wadda gwamnatin Najeriya da wasu hukumin tsaro da suka hada da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da rundunar ‘yan sandan kasar da kuma ministan shari’a Abubakar Malami suka daukaka. A yayin zaman kotun, Lauyan gwamnatin Najeriya, Oyi Kolishon ya bukaci kotun ta ba su damar gyara wasu takardu da suka shafi karar da suka daukaka. Sai dai lauya mai kare jagoran ‘yan shi’a Femi Falana ya mayar da martanin cewa, kotun ba za ta saurari gwamnatin Tarayya ba idan ba a saki wanda yake karewa ba. Falana ya ce ba zai yiwu gwamnati ta zo da wata bukata a wata kotu ba, bayan kin mutunta umurnin babbar kotu. Mai shari’a Mojeed Owoade wanda ya jagoranci zaman kotun da kuma mai shari’a Chidiebere Uwa sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnati ta ki mutunta hukuncin kotun kasar, abin da suka ce bai da ce ba. Alkalan kotun sun bayyana cewa sakin El Zakzaki ba zai hana gwamnati ta daukaka karar ba. Lauyan da ke kare gwamnati, Mista Koloshon ya bukaci kotun ta ba su damar mayar da martani. Amma Femi Launa ya shaida wa kotun cewa,” Ministan shari’a na kasar, Abubakar Malami ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta bi umarnin daukaka karar ba. A shari’ar da aka fara saurare dai, Jagoran kungiyar ‘yan Shi’ar Ibrahim El Zakzaki bai samu halartar zaman kotun ba. Rahoto: Hussain Auwalu Ya’u

Shiri ne dake kawo muku jigon sakonnin hudubobin jumu’a da aka gabatar a masallatan jumu’a daban-daban a ciki da wajen kasarnan, shiri ne da Ammar Isah Nuhu Batagarawa ke shugabanta tare da taimakawar Basheer Journalist Sharfadi, Shiri ne da yake da dimbin masu sauraro sannan zaku dinga jin halin da duniyar musulunci ke ciki a kowane mako ta cikin shirin, zaku iya samun wannan shiri da ma wadanda suka gabata a kowane lokaci a www.darulfikr.com Domin daukar nauyi ko tallata hajar ku ta cikin shirin, ko kuma aiko da taku hudubar sai a tuntubi: 08035830253, 08066989773, 08149332007, [email protected] http://facebook.com/masallatanmu.ng http://twitter.com/dagamasallatai

DAGA MASALLATAN JUMU’AR MU

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

An Fara Sauraren Karar Da Gwamnatin Tarayya Ta

Daukaka Kan Sakin Zakzaky

Page 3: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

3

Dole A Cire Nikabi A Ofishin Mu Inji Kwansul Janar Na Saudiyya

Hukumomin tsaro na Najeriya da suka hada da rundunar tsaro ta farin kaya sun bayyana cewa, kungiyar Daular Musulunci ta Arewacin Afirka ce ke da alhakin kai hare-hare tare da kashe mutane a jihar Benue ta Najeriya. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa, wannan batu na kunshe a cikin wani rahoto da hukumomin tsaron yankin suka mika wa shugaban kasar Muhammadu Buhari. Rahoton ya bayyana cewa, ‘yan ta’addar masu rajin kafa Daular Islama a Yammacin Afirka na shiga yankunan kudu maso-kudu da arewa ta tsakiyar Najeriya daga kasashen waje inda suke kai wa kabilun yankunan hare-hare tare da kashe mutane. Rahoton ya kuma ce, Kungiyar na amfani da mayakan kasashen waje tare da diban matasa a Najeriya don kashe mutane babu gaira babu dadlili. Wata majiyar fadar shugaban Najeriya ta ce, an gano hakan ne bayan an kama mambobin kungiyar da dama da suka hada da Fulani makiyaya, ‘yan ta’adda da gwamnati ta dauki nauyi da sauran bata gari a jihar Benue. Majiyar ta ce, daga cikin wadanda aka kama akwai wadanda ba sa magana da yarukan Najeriya sai Faransanci kawai. Rahoto: Ammar Isah Nuhu Batagarawa

Bangarorin kungiyar Izala biyu sun hadu a garin Maiduguri inda suka shirya wa’azuzzuka na hadin gwiwa a garin wanda ya samu halartar dukkan bangarorin, Wa’azin dai ya samu tagomashi sosai domin kuwa an haska wannan wa’azi kai tsaye har a gidan talabijin na garin Maidugurin muna addu’ar Allah ya kara hada kan Ahlussunah baki daya amin. Rahoto: Abdullahi Suraj Nagegime

‘Yan Ta’addar Daesh Ne Ke Kashe Mutane A Jihar Benue

SUNNAH NEWS NIGERIA DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253,08066989773, 08149332007, 08168015170

Wani babban Malami ya kira Jakadun Najeriya a Jeddah na kasar Saudiyya Dr Ahmad Gumi ya nemi a sake dokar hana mata sa nikabi a ofishin Jakadancin kasar – Babban Malamin ya nemi hukuma su ji tsoron Allah a ba kowa hakkin sa Sunnah News Nigeria ta samu labari na musaman cewa babban Malamin Addinin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya soki tsarin haramtawa Mata daga Najeriya Nikabi a ofishin Jakadancin Najeriya a Kasar Saudiyya Idan ba a manta ba kwanan nan ofishin bada biza da sauran takardun shiga Kasar Saudiyya ta haramtawa Mata shiga neman biza da fuskar su a rufe. Sheikh Ahmad Mamud Gumi ya kira Ambasada Muhammad Sani Yunus a wayar tarho. Rahoto: Muhd Habib Adam

Mun wayi gari da labarin wata doka da Consulate General namu da ke Jedda ya yi akan mata yan Najeriya masu sa Niqab wadanda suke zuwa neman Passport a ofis dinsa tare kuma da wani clip na tattaunawarsa da Sheikh Dr. Ahmad Gummi a kan wannan batu. Alhamdu lillahi wasu yan uwa masu lura da abinda wannan doka za ta iya haifarwa sun nemi Consule General sun tattauna da shi a cikin natsuwa a kan wannan doka kuma ya fahimta ya amince da janye ta. Bisa ga haka muna rokon jama’a su daina watsa wannan magana daga yau. Masu bukatar samun karin bayani suna iya tuntunbar ofishin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). Allah ya yi mana muwafaqa.

Dokar Dage Niqab A Nigerian Consulate, Jedda

-Dr. Mansur Sokoto

Izala Ta Hadu A Maiduguri

TANA NAN TAFE

Page 4: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

4

1. Ba a kafa Kungiyar Izalah a kan mazhabar Malikiyyah ko wanin Malikiyyah ba daga cikin Mazhabobin da ke cikin fage, a'a an kafa ta ne a kan yin aiki da Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i. 2. A inda duk mazhabar Malikiyyah ko waninta suka dace da Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i, to lalle kungiyar Izalah na tare da su a nan, a inda kuma mazhabar Malikiyyah ko waninta suka saba wa Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i to lalle kungiyar Izalah ba ta tare da su a nan. 3. Lalle abin takaici ne har kullum 'yan bidi'ar da ba sa jin kunyar yi wa Duniya karya su rika cewa: an kafa kungiyar Izalah ne a kan Alkur'ani da Hadithi da kuma Mazhabar Malikiyya! 4. Tabbas babu inda lafazin ambaton mazhabar Malikiyyah ya zo koda sau daya ne a cikin constitution din Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah. Babu inda za a sami lafazin Mazhabar Malikiyyah a rubuce tun daga shafin farko na Constitution din Kungiyar har zuwa shafinsa na karshe. 5. Lalle abin da yake rubuce cikin constitution din Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah shi ne: Ita kungiya ce ta addinin Musulunci tsantsa kamar yadda Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah ya taho ta shi, wacce take dogara da Alkur'ani da Hadithan Manzon Allah da kuma Ijma'i. 6. Wannan shi ne hakikanin Kungiyar Izalah da constitution dinta, ba wai karairayin da wasu yan bidi'ah ke yadawa ba game da ita. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Tambaya: Assalamu alaikum,Allah gafarta malam shin zan iya yawo acikim gida ba dan kwali? Amsa: Mace zata iya yawo babu Dan kwali idan tana tsakanin ‘yan uwanta mata musulmai saboda al’aurar mace ga ‘yar uwarta mace musulma tana kasancewa ne tsakanin guiwa zuwa cibiya, mutukar akwai mazan da ba muharramai ba to bai halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al’ura ce in ban da fuska da tafukan hannu. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Yuauf Zarewa 24/1/2016

Ya Halatta Na Karbi Kyauta Daga Wajen Karuwa?

Tambaya: assalam,malam akwai hujjar da ta kore kar6ar kyauta daga karuwa ? Amsa: Tabbas Annabi s.aw. ya haramta cin kudin karuwa, wanda ta samu ta hanyar karuwanci, kamar yadda hakan ya zo a hadisi mai lamba : 1567, wanda Muslim ya rawaito Saidai malamai suna cewa : Duk wanda ya zama a cikin dukiyarsa akwai halal da haram, to idan ya maka kyauta za ka iya amsa, mutukar ba ka tabbatar daga haram ya dauko ya baka ba, saboda Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal da haram, har ma ya mutu silkensa na yaki yana jingene a wajansu. Don neman Karin bayan duba Al-muhallah na Ibnu Hazm 6/184. Allah ne mafi sani Dr. Jameel Zarewa 26/1/2015

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

Ba A Kafa Kungiyar Izalah A Kan Mazhabar Malikiyyah Ba Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Shin Ya Halatta Mace Tayi Yawo Babu Dankwali A Gidanta?

Ya Halatta Na Karbi Kyauta A Wajen Karuwa?

–Dr. Jamilu Zarewa

Page 5: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

5

Dakta Isa Ali Pantami ya jagoranci ma'aikatar cigaban ilimin zamani taron baja kolin ilimin zamani a kasar Indiya.

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

Labarai Cikin Hotuna

Hotuna Daga Masallachin Gwallaga Dake Bauchi, Ranar Asabar Din Wannan Makon Yayin Daurin Auren Dr. Sani Umar Rojiyar Lemo.

Mal. Sani Yahaya Jingir Ya Ziyarci Inda Izala NHQ Jos Take Ginin Makaranta Bangaren NCE Dake Jos, Shugaban Bangaren NCE Din Mal. Ahmad Garba Yayi Bayani Akan Yadda Aikin Yake Gudana, Mal. Sani Yahaya Ya Yaba Da Yadda Aikin Yake Gudana

SUNNAH NEWS NIGERIA -LABARAN SUNNAH A TAFIN HANNUNKU

Page 6: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

6

DAGA KASASHEN WAJE

Wani Babban Dan Siyasa A Jamus Ya Karbi Musulunci

Mataimakin shugaban jam’iyyar AfD ta ‘yan mazan jiya na jihar Brandenburg ta kasar Jamus Arthur Wagner ya rungumi Addinin Musulunci. Jaridar Tagesspiegel ta bayar da labarin cewa, ba da jima wa ba Wagner ya Musulunta. A labaran da aka fitar an sanar da cewa, Wagner ya ki ya yi dogon jawabi game da karbar Addinin Musulunci da ya yi inda ya ce, batu ne da ya shafe shi. Shugaban Majalisar Shura ta jam’iyyar AfD Andreas Kalbitz ya ce, tabbas da gaske ne Wagner ya Musulunta. Kalbitz ya kuma ce, a ranar 11 ga watan Janairu ne Wagner ya sanar da ficewar sa daga majalisar gudanarwar jam’iyyar AfD a jihar Brandenburg. Kakakin jam’iyyar na jihar daniel Friese ya ce, zabin mutane ne su shiga Addinin da suke so.

Amurka Ta Tsayar Da Ranar Mayar Da Ofishinta

Birnin Kudus

Amurka ta sanar da cewa nan da karshen shekarar 2019, za ta kammala matsar da ofishin jakadancinta na Isra’ilu zuwa birnin Kudus daga Tel aviv. Mataimakin Shugaban kasar Mike Pence a ziyarar da yanzu haka ya ke ci gaba yi a yankin Larabawa, ya ce zuwa yanzu za su fara matsar da wasu ayyukansu zuwa birnin na Kudus gabanin kammala komawa a 2019. Mista Pence da ke sanar da haka cikin jawaban da ya gabatar a gaban majalisar dokokin isra’ila a ziyara da ya kai kasar ya bukaci Falasdinuwa da Isra’ila su koma teburin tattaunawa don samar da sulhu kan takkadama da ke tsakaninsu. Rahotanni sun ce an tursasa ‘yan majalisun Isra’ila Larabawa ficewa daga zaman majalisar lokacin da suka nuna adawa da jawaban mataimakin shugaban na Amurka. Sanarawar Amurkan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban Falasdinuwa Mahmud Abbas ya bukaci Kungiyar Tarayar Turai ta amince da yankin Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Mahmud Abbas wanda ke sanar da hakan yayin wata ganawarsa da ministocin kasashen kungiyar a Brussels ya ce yana fatan amincewar ta zamo martini ga Amurka wadda ta yi kunnen kashi da matakin majalisar dinkin duniya da ta bukaci yin watsi da yunkurin na ta na ayyana Qudus din a matsayin babban birnin Isra’ila. Kusan ilahirin kasashe mambobin majalisar dinkin duniya sun ki amincewa da matakin na Amurka kan mayar da Qudus babban birnin Isra’ila, batun da ya haddasa tashe-tashen hankula a galibin kasashen Musulmai, yayinda a bangare guda ya haddasa asarar rayuka a yankin Falasdinu ta yadda jami’an tsaron Isra’ila suka rika harbe Falasdinawa.

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

Page 7: SUNNAH NEWS NIGERIA · 2018-01-26 · kungiyar JNI, Dakta Khalid Aliyu, ya maida martani ga wani jawabi da sakataren Kungiyar CAN Dr. Musa Asake yayi kwanakin baya inda ya zargi Gwamnatin

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

7

Isra’ila Ta Kame Shugaban Kungiyar Musulman Falasdinu

‘Yan sanadar kasar Isra’ila sun kame Shugaban Kungiyar Musulman Falasdinu Sheik Kemal Hatib Kamar yadda lauyan shehin malamin Halid Zabarka ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu, ‘yan sandar Isra’ila sun kame sheik Hatib a gidansa a garin Kefr Kanna dake arewacin Isra’ila ba tare da wa ta dalili ba. Lauya Zabarka ya bayyana cewar ya zargaya zuwa ofishin ‘yan sandar dake garin Nasıra domin jin dalilin kama shehin malamin. A shekarar 2015 an nada Sheik Kemal Hatib a matsayin shugaban kungiyar ‘yancin Falasdinawa bayan da aka bayyana Kungiyar Musulman Falasdinawan a matsayar kungiyar ta’addanci dalilin kalubalantar yunkurin Isra’ila na mamayar gabashin Qudus.

‘Yan Ta’addar PKK Sun Kai Hari A Masallatai A Jamus

Kungiyar ta’addar PYD/PKK ta kai hari a wani Masallaci dake garin Hannover a kasar Jamus. Masallacin mallakar kungiyar haddin kan Musulmi dake karkashin ma’aikatar addinin Turkiyya mai suna Stade-Bützfleth Ulu ,’yan ta’addar sun tarwatsa gilasan kofofin da tagogin kudancin sa. A yayinda kuma su ka rubuta kalaman batanci da nuna kalubale ga bangon masallacin. Hukumar kula da masallacin takai karar wannan lamarin ga hukuman ‘yan sandar kasa. Wannan dai ba shi ne karon farko da aka soma kai irin wannan harin ba. A wasu masallatan kungiyar hadin kan musulmi watau DITIB dake garin Minden, Frankfurt, Saksonya ma an kai irin wadannan hare-hare a cikin ranakun 20 zuwa 21 ga watan janairu.

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman da gwamnatin Myanmar ta haramtawa shiga kasar Yanghee Lee, ta ce akwai yiwuwar zabtarewar kasa a sansanin ‘yan gudun hijira na Cox’s Bazar lamarin kuma da zai iya shafar daruruwan ‘Yan kabilar ta Rohingya la’akari da galibinsu suna sansanin. A watan nan ne dai jakadun majalisar dinkin duniya za su isa kasar ta Myanmar don gudanar da bincike kan zargin cin zarafin bil’adaman da aka yiwa musulmi ‘yan kabilar Rohingya, da ya tilasta musu ficewa daga kasar don tsira da rayukansu. Jami’an majalisar za kuma su tattauna kan batun Fyade da kisan gillar da ake zargin jami’an tsaron kasar da aikatawa, wanda majalisar ta bayyana a matsayin yunkurin shafe wata kabila. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta yi magana kan sharuddan da ‘yan Rohingyar suka gindaya dangane da batun komawarsu gida, duk da cewa yawan Musulmi ‘yan Rohingyar da ke gudun hijira a kasashen waje ya tasamma miliyan guda.

Sansanin ‘Yan Gudun Hijirar Rohingya Na Cikin Hadari

Sojojin Isra'ila Sun Sake Kama Falasdinawa 14

Sojojin Isra'ila sun kama Falasdinawa 14 a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye. Sanarwar da Rundunar Sojin Isra'ila suka fitar ta ce, a farmakan da suka kai a yankuna daban-daban na Yammacin Gabar Kogin Jordan sun kama mutane 14 da aka zarga da yunkurin kai hari. Sojojin Isra'ila na yawan kai hare-hare a Yammacin gabar Kogin Jordan da gabashin Kudus inda suke kama Falasdinawa da dama tare da daure su. Akwai kusan Falasdinawa dubu 7 da suka hada da sama da yara kanana 300 a gidajen kurkukun Isra'ila.

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

SUNNAH NEWS NIGERIA –LABARAN SUNNAH A TAFIN HANNUNKU