binciken littafi mai tsarki domin mata - cdmissions.org · domin ya diba masu bin sa. 2. dawowarsa...

8
BINCIKEN LITTAFI MAI TSARKI DOMIN MATA (A CIKIN ZUMUNTA KO A GIDA) Daga Hanun Christ’s Disciples’ Missionary Foundation Inc

Upload: lamminh

Post on 30-Mar-2019

214 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

BINCIKEN LITTAFI MAI TSARKI

DOMIN MATA (A CIKIN ZUMUNTA KO A GIDA)

Daga Hanun

Christ’s Disciples’ Missionary Foundation Inc

BINCIKE 1

Kan Bincike

Wa zai shiga mulkin Allah? (A)

Wurin karatu: Yahaya 3:3-7; Ezekiel 36:26-27.

KOYASWA

1. Wanda ya yarda cewa shi mai zunubi ne, ya kuma ba da gaskiya cewa jinin Yesu zai wanke Zunuban sa.2. Wanda ya zo wurin Yesu domin a sake haife shi ta ruhu.3. Wanda ya mika kai ga Allah domin ya sabonta zuciyarsa.

HADDACEWA:

Yahaya 3:3 - Yesu ya amsa masa ya ce, “lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sake haifar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba”.

BINCIKE 2

Kan Bincike

Wa zai shiga mulkin Allah? (B)

Wurin karatu: Zabura 15:1-5 Luka 3:7-9.

KOYASWA1. Wanda ya yi tuba, ya kuma ba da baya ga zunubi; ya ki kowane irin zunubi.2. Ya na jin tsoron Allah; ya na aikata gaskiya da nagarta a rayuwansa.3. Ya na kame bakin sa, da ransa daga kowane mumunar hali.4. A lissafta halaye na cikin zabura 15.

HADDACEWA

Zabura 15:2: Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, ya na kuwa aikata abin da yake daidai, wanda yake fadar gaskiya da zuciya daya.

2

BINCIKE 3

Kan Bincike

Lidiya

Wurin karatu: Ayukan Manzanni 16:10,13-15,40.

KOYASWA1. Mace nan Lidiya, ta yarda ta bude zuciyarta ga wa'azin bishara.2. Lidiya ta mai da hankali ga koyaswar Bulus.3. Ta karbi Yesu ya zama mai ceton ta da Ubangijin ta.4. Ta karbi masu bishara zuwa cikin gindan ta. Ta yi taimako ga masu bishara.5. Lidiya ta ba da gidan ta domin sujadan ikklisiya.6. Za mu iya koyi iri halayen Lidiya?

HADDACEWA: Ayukan Manzanni 16:15b: Ta roke mu ta ce, “Da yake kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gida na ku sauka.” Sai ta rinjaye mu.

BINCIKE 4

Kan Bincike

Matar Lutu

Wurin karatu: Farawa 19:15-26; Luka 17:32-33.

KOYASWA

1. Lutu da iyalinsa sun sami jinkai da alherin Allah da aka fitarda su daga birnin Saduma, domin ka da su hallaka tare da mutanen birnin.2. An ceci matan Lutu tare da iyalinta da hannu mai karfi.3. Allah ya dokace su cewa, kada su waiwaya baya (ayar 17).4. Matan Lutu ta waiwaya baya, sai ta zama surin gishiri.5. Me ya sa ta waiwaya baya?6. Wane koyaswa ne labari nan yake a gare masu bin Yesu Almasihu a yau?

HADDACEWA: Luka 17:32 - Ku tuna fa da matar Lutu.

3

BINCIKE 5

Kan Bincike

Dawowar Yesu: Tabbaci ne

Wurin karatu: Yahaya 14:1-3; Luka 17:23-37.

KOYASWA1. Ubangiji Yesu Almasihu ya shaida ma almajiransa cewa zai sake dawo domin ya diba masu bin sa.2. Dawowarsa za ya zama a bayane ga kowa. Domin haka, kada mu yarda a rude mu cewa yana nan ko yana can.3. Mu zama a fadake da shiri domin mu iya tafi tare da shi.4. Za a bari wadansu a baya domin rashin shiri da rashin zama a fadake.5. Rayuwa zai ci gaba yadda take ranar da Yesu zai diba masu bi.6. Mu zama da shiri. Kada mu yi zaman tsakaci.

HADDACEWA: Matta 24:31: Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa kaho mai tsananin kara, su kuma tattaro zababbunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.

BINCIKE 6Kan Bincike

Tsarkakewa

Wurin karatu: 2 Timoti 2:19-24; 1 Peter 1:14-16.

KOYASWA1. Ubangiji yana bukatar mutanensa su zama kayan aiki a gidansa. Yana nema ma aikaci.2. Ko da yake yana nema masu aiki, Allah ba zai yi aiki mai daraja da kazamtattun kayan aiki ba.3. Ya na bukatar kowanenmu shi tsarkake kansa daga kazamtattun ayyuka.4. Ubangiji zai more mutum mai aikin adalci, mai bangaskiya, mai kauna, mai salama da zuciyar tsarkakakkiya.

HADDACEWA: 1 Bitrus 1:15 - Amma da yake wanda ya kira ku mai tsarki ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka a cikin dukan al'amuranku.

4

BINCIKE 7

Kan Bincike

Hannatu: Ta bude kofar albarka da addu'a

Wurin karatu: 1Samila 1:1-20.

KOYASWA1. Hannatu ta daidai da damuwan ta na rashin haifuwa. Ta cika zama da bakin ciki akan damuwan, ta har ta na ki cin abinci.2. Bayan shekaru dayawa, Hannatu ta kai kukanta wurin Ubangiji. Ta yi addu'a. Ta roki yaro daga wurin Allah da bangaskiya.3. Hannatu ta hadda rokon ta da wa'adi(alkawari), cewa za ta ba yaron ma Ubangiji domin ya zama maikacin Allah..4. Kula fa, bayan da ta gama yin addu'a tare da albarkan Eli, fristi na Allah, Hannatu ta ci abinci, bata kara yin bakin ciki ba (aya 17-18).5. Za mu iya maganta damuwoyi rayuwar mu da iri addu'ar bangaskiya kamar hannatu ta yi.

HADDACEWA1Samaila 1:10: Hannatu tana fama da bakin ciki kwarai, sai ta yi addi'a, tana kuka da karfi ga Ubangiji.

BINCIKE 8

Kan Bincike

Hannatu ta cika alkawarin ta da Allah.

Wurin karatu: 1Samaila 1:20-28; 2:18-21.

KOYASWA

1. Ubangiji Allah ya ji rokon Hannatu: Ya ba ta da namiji bisa ga addu'anta.2. Hannatu ta mika yaron (Samaila) ga Ubangiji muddin ransa bisa ga alkawarin da ta yi da Allah a cikin rokon ta (aya 11).3. Hannatu ta koma gidanta bayan da ta mika yaron ta Samaila ga Allah a Shiloh.4. Domin amincin Hannatu, Ubangiji ya kara sa mata albarka. Ta haifi 'ya'ya maza uku (3) da mata biyu (2), banda Samaila wanda ta riga ta mika ga Ubangiji.

5

5. Mu koyi halin Hannatu: yin addu'a da cikar wa'adin da mu ka yi a cikin addu'a. Mu zama masu aminci da Allah a kowane hali.

HADDACEWAMai Hadishi 5:4: Sa'ada ka yi wa'adi ga Allah, yi hanzari ka cika, gama wawa bashi da wani amfani a gare shi, Sai ka cika wa'adin da ka yi.

BINCIKE 9

Kan Bincike

Menene Kauna

Wurin karatu: 1 Korintiyawa 13:1-13

KOYASWA

1. Kauna wani abu ne wanda yana maida halin mutum shi kasance haka: (A tattauna a kan wadanan halaye) - Hankuri, da kirki, farin ciki da gaskiya, daurewa a cikin kowane hali, bangaskiya, bege, da jimiri a cikin kowane hali.2. Kauna har yanzu ta na mai da halin maishi shi kasance haka: - Ba ta da kishi, ba ta yin kumbura ko daga kai, ko rashin hankali. - Ba ta jin tsokana, ba ta rikon wani a zuciya, ba ta farin ciki da mugunta.3. Kauna ta fi kowane iri baye baye na ruhaniya babba. Idan babu kauna a rayuwarmu, duk aikin mu da ibada mu zai zama a banza. Domin Allah kauna ne.

HADDACEWA1 Yahaya 4:7: Ya ku kaunatattu na sai mu kaunaci juna, domin kauna ta Allah ce. Duk me kauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.

6

BINCIKE 10

Kan Bincike

Mu Kaunaci juna

Wurin karatu: Yahaya 13:34-35; 1 Yahaya 3:1; 1 Yahaya 4:7-12.

KOYASWA

1. Allah ya kaunace mu har ya bamu Dan sa domin ya mutu domin mu. Kaunar Allah ne ya sa ya maishe mu 'ya'yan sa.2. Allah ya dokance mu cewa mu kaunaci juna domin shi ya kaunaci mu.3. Wanda bashi da kauna ga 'yan'uwa bai san Ubangiji ba.4. Mu lissafta wadansu hanyoyi na nuna kauna ga junan mu.5. Kauna ne alama cewa mu masu bin Yesu ne..

HADDACEWA: 1 Yahaya 4:8 Wanda ba ya kauna, bai san Allah ba sam domin Allah shi ne kauna.

BINCIKE 11

Kan Bincike

MISALAI NA MATAYE DA SUKA YI HIDIMA GA UBANGIJI

Wurin karatu: Ayukan Manzanai 2:12,18, Zab. 68:11

GABATARWA

Ubangiji yayi amfani da mataye dayawa cikin hidimarsa, tun daga lokacin tsoho alkawari har zuwa ga yau, hakika ma azamanin nan muna da kyakkyawar alkawari na zubawar Ikon Ruhu Mai Tsarki domin cikita muradin Ubangiji game da mata cikin hidima. A cikin wannnan bincike za mu duba wadannan mataye da suka mika kansu domin Ubangiji ya mori su ta fannoni daban-daban daga lokacin tsoho alkawari da kuma sabon alkawari

7

Deborah: -- Deborah ita macece wanda ta yi hidiman shugabanci(alkali) ta kuma yi yaki na Ubangiji. Littafi Mahukunta 4:4-10; 5:6-8. - Haka nan kuma ita Maryamu yar'uwar Musa ta yi hidima ta cece ran Musa-Fit. 2:3,7 ta yi shugabanci na kasa tare da Musa da Haruna, Mika 6:4.

HADDACEWA: Littafin Mahukunta 5:7

Esta: -- Esta sarauniya ce wadda Ubangiji ya mori matsayinta ya cece dukan kasar Israila daga hallakaswa. Ta yi addu'a kuma ta mika ranta domin ceton mutaninta, Ubangiji kuma ya bisheta, ya bayana ikonsa yayi ceto,- Esta 4:15-17, 8:11. Mu ma zamu iya kawo yantaswa/ceton Ubangiji ta wurin addu'a , HADDACEWA: Ayukan Manzanai 1:14a

Bilkisu: - A cikin sabon alkawari Bilkisu ta yi aikin bishara tare da mijinta da kuma manzo Bulus, har suka yi kasai da ransu. Ikklisiya ma na taruwa a gidansu. Rom. 16:3-5a. Tare da maigidanta kuma suka koyar da maganar Allah A/M 18:26 Afolos wanda suka koyar da shi kuma ya san Litattafi kwarai da gaske-kada mu ji kunya, ko tsoro dominmu mata ko kuwa domin muna gani kamar an fi mu sani.

Fibi:-- Fibi ta yi shugabanci a cikin Ikklisiya ta kuma yi taimako ga mutane dayawa, har da masu bishara A/M 16:1-2 - Ba ita kadai ba da wadansu mataye kamar Tarafina da Tarafusa Rom. 16:12 sun yi aikin Ubangiji da kuma masu hidiman taimako kamar su Dokas(Tabitha) A/M 9:36-42; Rom 16:6; Filib. 4:3

Kamalawa: Misalan da muka duba, sun nuna mana da cewa hidimomi kamar, annabci, shugabantar kasa/Ikklisiya, kai bishara, koyaswa, taimako, mika gidanmu don Ikklisiya ta yi sujada, bayaswa, addu'a da sarauransu. Dukkan hidima ne wanda Ubangiji na neman mata su yi masa

Ayar hadacewa: Ayukan Manzanni 2:18

8