mujallar sunnah domin sanin halin da sunnah ke ciki · akwai yan uwa guda 4 da suka taimaka har...

4
SUNNAH NEWS NIGERIA Labaran Sunnah A Tafin Hannun ku MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI DATE: Friday 29, December, 2017 Kungiyar Daliban Jihar Gombe Dake Karatu A Jami’ar Bayero Ta Karrama Sheikh Kabiru Gombe Civilian Institute of Democratic Administration (CIDA) tare da hadin gwiwar kasar Ghana sun karrama daya daga cikin maluman sunnah na wannan kasa Sheikh Dr. Dahir Inuwa Ibrahim, babban limamin masallacin jumu’a na jami’ar jihar Gombe (GSU), wanda aka gabatar ranar asabar ta wannan makon 23/12/2017 a Birnin ikko na jihar Lagos. Rahoto: Abdulmalik Abuya Gombe Sabuwar Tashar Sunnah News TV Tana Kan Hanya A yanzu dai tuni dandalin Sunnah News yayi nisa wajen samar muku da sabuwar tashar talabijin wadda zaku iya samu a wayoyin ku, ana saran fitowarta cikin mako mai zuwa. An Karrama Dr. Dahir Inuwa A Jihar Lagos SUNNAH NEWS NIGERIA DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253,08066989773, 08149332007, 08168015170 Kungiyar xaliban Jihar Gombe dake karatu a jami'ar Bayero dake Kano sun karrama Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, karramawar ta gudana ne a sakatariyar kungiyar Izala dake fadar jihar Gombe bayan tattaki da daliban sukayi Domin Karrama shehin malamin. Da yake jawabi Sheikh Muhammad Kabir Gombe ya bayyana jin dadinsa duba da yadda suka duba cancantarsa da bashi wannan lambar yabon, sannan yace lallai an bashi lambar yabo a wurare dayawa amma yafi jin dadin wannan saboda ita an bashi ne a garinsa sannan yace Kamar yadda kuke mana kyakkyawan zato Allah Ya sa har a gurin Ubangiji haka abun yake, fatanmu shine Allah ya yadda damu ya kuma yafe mana kurakuranmu. Shima Shugaban Kungiyar daliban yace sun zabi Malam kabir Gombe ne duba da gudunmawa da yake bayarwa a fannin tarbiyya da ilimi ga wannan al'umma. Shugaban kungiyar Izala ta jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe yayi jawabin godiya sannan ya ja hankalin daliban akan karatunsu da kuma taimakekeniya a tsakanin Juna. Rahoto: Musa H. Musa Darulfirk.com Takuce Domin Yada Sunnah Cibiya guda daya tilo wadda take kawo muku karatuttukan maluman Sunnah daga wurare daban-daban a kowane lokaci, aciki da wajen kasarmu Nigeria. http://facebook.com/darulfikrng SUNNAH NEWS NIGERIA – LABARAN SUNNAH A TAFIN HANNUNKU Dandalin Sunnah News Nigeria Yana Gayyatar Al’ummar Musulmai zuwa wajen daurin auren daya daga cikin malamai masu sanya ido akan wannan dandalin Mal. Abubakar Abdussalam Baban Gwale (sakataren kwamitin samina na kungiyar Izala ta kasa), wanda za’a gabatar kamar haka: Rana: Lahadi 13/04/1439, = 31/12/2017 Wuri: Masallachin Alfurqan dake No. 9A Alu Avenue Nassarawa G.R.A Kano Lokaci: Karfe 01:00 na rana, bayan sallar azahar. Sanarwa: Basheer Journalist Sharfadi

Upload: vantram

Post on 12-Apr-2018

280 views

Category:

Documents


6 download

TRANSCRIPT

Page 1: MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI · Akwai yan uwa guda 4 da suka taimaka har wannan aiki ya kammala cikinsu akwai Alh Sadiq Ayuba Sullubawa wanda ya bada tasa gudumuwar

SUNNAH NEWS NIGERIA

Labaran Sunnah A Tafin Hannun ku

MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI DATE: Friday 29, December, 2017

Kungiyar Daliban Jihar Gombe Dake Karatu A Jami’ar Bayero Ta

Karrama Sheikh Kabiru Gombe

Civilian Institute of Democratic

Administration (CIDA) tare da hadin

gwiwar kasar Ghana sun karrama daya

daga cikin maluman sunnah na

wannan kasa Sheikh Dr. Dahir Inuwa

Ibrahim, babban limamin masallacin

jumu’a na jami’ar jihar Gombe (GSU),

wanda aka gabatar ranar asabar ta

wannan makon 23/12/2017 a Birnin

ikko na jihar Lagos.

Rahoto: Abdulmalik Abuya Gombe

Sabuwar Tashar Sunnah News TV Tana Kan Hanya A yanzu dai tuni dandalin Sunnah News yayi nisa wajen samar muku da sabuwar tashar talabijin wadda zaku iya samu a wayoyin ku, ana saran fitowarta cikin mako mai zuwa.

An Karrama Dr. Dahir Inuwa A Jihar Lagos

SUNNAH NEWS NIGERIA DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253,08066989773, 08149332007, 08168015170

Kungiyar xaliban Jihar Gombe dake karatu a jami'ar Bayero dake Kano sun karrama Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, karramawar ta gudana ne a sakatariyar kungiyar Izala dake fadar jihar Gombe bayan tattaki da daliban sukayi Domin Karrama shehin malamin. Da yake jawabi Sheikh Muhammad Kabir Gombe ya bayyana jin dadinsa duba da yadda suka duba cancantarsa da bashi wannan lambar yabon, sannan yace lallai an bashi lambar yabo a wurare dayawa amma yafi jin dadin wannan saboda ita an bashi ne a garinsa sannan yace Kamar yadda kuke mana kyakkyawan zato Allah Ya sa har a gurin Ubangiji haka abun yake, fatanmu shine Allah ya yadda damu ya kuma yafe mana kurakuranmu. Shima Shugaban Kungiyar daliban yace sun zabi Malam kabir Gombe ne duba da gudunmawa da yake bayarwa a fannin tarbiyya da ilimi ga wannan al'umma. Shugaban kungiyar Izala ta jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe yayi jawabin godiya sannan ya ja hankalin daliban akan karatunsu da kuma taimakekeniya a tsakanin Juna. Rahoto: Musa H. Musa

Darulfirk.com Takuce Domin Yada Sunnah Cibiya guda daya tilo wadda take kawo muku karatuttukan maluman Sunnah daga wurare daban-daban a kowane lokaci, aciki da wajen kasarmu Nigeria. http://facebook.com/darulfikrng

SUNNAH NEWS NIGERIA – LABARAN SUNNAH A TAFIN HANNUNKU

Dandalin Sunnah News Nigeria Yana Gayyatar Al’ummar Musulmai zuwa wajen daurin auren daya daga cikin malamai masu sanya ido akan wannan dandalin Mal. Abubakar Abdussalam Baban Gwale (sakataren kwamitin samina na kungiyar Izala ta kasa), wanda za’a gabatar kamar haka: Rana: Lahadi 13/04/1439, = 31/12/2017 Wuri: Masallachin Alfurqan dake No. 9A Alu Avenue Nassarawa G.R.A Kano Lokaci: Karfe 01:00 na rana, bayan sallar azahar. Sanarwa: Basheer Journalist Sharfadi

Page 2: MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI · Akwai yan uwa guda 4 da suka taimaka har wannan aiki ya kammala cikinsu akwai Alh Sadiq Ayuba Sullubawa wanda ya bada tasa gudumuwar

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

2

Shugaban kungiyar IZALA na tsafe Alh Ishaka Abdullahi ‘yandoto (sabon gari) ya jagoranci yan majalisarsa zuwa garin Chediya da rugar Na’ali domin taya su murnar gina masallatai a yankunansu, Shugaban yana tare da rakiyar shugaban majalisar malmai Sheikh Mustapha Khalid Dumpawa, da Babbban sakataren kungiyar Malam Surajo Ibrahim Maikudi, da Malan Abubakar Muhammad yankuzo Shugaban kwamitin Da'awa, da Malan Muhammad Yahaya mataimakin shugaban kungiya Alh. Hadi Suleman Babban mai bincike a kungiyar sai Abdulhadi Salisu daga socail media.

Izala Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido A Garuruwan Chediya Da Rugar Na-Ali

Shiri ne dake kawo muku jigon sakonnin hudubobin jumu’a da aka gabatar a masallatan jumu’a daban-daban a ciki da wajen kasarnan, shiri ne da Ammar Isah Nuhu Batagarawa ke shugabanta tare da taimakawar Basheer Journalist Sharfadi, Shiri ne da yake da dimbin masu sauraro sannan zaku dinga jin halin da duniyar musulunci ke ciki a kowane mako ta cikin shirin, zaku iya samun wannan shiri da ma wadanda suka gabata a kowane lokaci a www.darulfikr.com Domin daukar nauyi ko tallata hajar ku ta cikin shirin, ko kuma aiko da taku hudubar sai a tuntubi: 08035830253, 08066989773, 08149332007, [email protected] http://facebook.com/masallatanmu.ng http://twitter.com/dagamasallatai

DAGA MASALLATAN JUMU’AR MU

Masallacin garin chediya wanda daya daga cikin wakilan jihar Zamfara a kasar Saudiya Ustaz Auwal Hamisu wanda shine ya jagoranci gina wannan masallaci mai albarka, masallacin Rugar Na’ali wanda gwamnatin jiha ta gina karkashin jagorancin dan majalisa mai wakiltar Tsafe ta gabas, a jawabin uban kasar chediya Alh. Kabiru marayen chediya ya yi godiya ga kungiyar da nuna jindadinta akan wannan muhimin aiki da aka gudanar a yankinsa sannan yayi godiya ta musamman akan namijin kokarin da Ustaz Auwal Khamis yayi domin ganin aikin ya kammala. Rahoto: Abdulhadi Salisu Tsafe

A ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, Mambobin kungiyar yan Shi’a sun kai ziyara wasu daga cikin cocinan dake jihar Kaduna da Jos domin taya Kiristoci bikin Kirsimati tare da wanzar da zaman lafiya a kasar. Kungiyar yan shi’an wanda suka ziyarci cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) Marafa Estates, sun ce addinin Musulunci addinin zaman lafiya ne sannan kuma wanzar da zaman lafiya tare da makwabci yana daya daga cikin koyarwar annabi Muhammed. Jagoran tawagar Dr. Shuaibu Musa yace: “Mun zo nan domin taya yan uwanmu Kirista murnar zagayowar ranar haihuwar wanda Annabinmu ya tabbatar da dawowarsa bayan bayyanar Imam Mahdi. Sai dai babu wani wuri da musulunci ya halatta ayi tarayya cikin bikin kirisimetin.

Rahoto: Muhammad Habib Adam

‘Yan Shi’a Da Kirista Sunyi Bikin Kirsemeti A Nigeria

A jihar Katsina an gabatar da daurori na musamman guda biyu ta mata da kuma ta bangaren maza daurar mata a masallacin makarantar secondary ta sautussunnah sai kuma bangaren maza a masallacin Kerau dake Katsina, Daurar wadda ta samu halartar ‘yan uwa da dama daga bangarori …

Malamai da dama ne a jihar ta katsina suka samu halarta, sannan daliban da suka halarta sun nuna farincikin su da ita, daurorin sun gudana cikin tsari mai matukar kayatarwa da ban sha’awa sannan al’ummar jihar na fatan a kara yin makamanciyar wannan daurar domin amfanuwar su. Rahoto: Basheer Sharfadi

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

An Gabatar Da Daura Ta Musamman A Jihar Katsina

Page 3: MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI · Akwai yan uwa guda 4 da suka taimaka har wannan aiki ya kammala cikinsu akwai Alh Sadiq Ayuba Sullubawa wanda ya bada tasa gudumuwar

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

3

Izala Ta Yiwa Dalibai Masu Yiwa Kasa Hidima Samina A Jihar

Gombe

Kungiyar Izala ta gabatar da wa’azi ranar Alhamis 28/12/2017 a jihar Bauchi, wa’azin wanda aka gabatar a masallachin Uthman bn Affan dake Bakin Kura, a jihar Bauchi, daga cikin maluman da suka samu halarta sun hada da: Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Shiekh Imam Muhammad Inuwa Dan'asabe, Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani, Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi, Imam Ibrahim Abdullahi Almadany da Hon. Isah Musa Matori da sauran malamai da kuma al’umar musulmi. Rahoto: Muhammad Nasir Abdullahi

Cikin ikon Allah an kammala ginin gidan Aisha an gina mata daki guda da kewaye da kitchen kai har ma da shago. Mun yi nazarin yanda take iya neman na kanta ta hanyar sayar da su omo magi da markade hakan yasa aka gina mata shagon. Akwai yan uwa guda 4 da suka taimaka har wannan aiki ya kammala cikinsu akwai Alh Sadiq Ayuba Sullubawa wanda ya bada tasa gudumuwar akwai kuma wanda yaki bari musan shi dukansu har da wani daga jihar Zamfara. Allah yasa ka masu da alkairi. Yahaya Muharazu ai mana godiya Sadiq. An kuma samar mta da kayan sanyi da na sa wa ita da yaranta. Rahoto: Hussain Kabir Yaradua

Akwai matasan irinsu Aminu Kaura, Uzairu dss su suka tsaye har wannan aiki ya tabbata Allah ya basu ladar wannan aikin

Izala Ta Gabatar Da Wa’azi A Garin Bauchi

SUNNAH NEWS NIGERIA DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253,08066989773, 08149332007, 08168015170

Kungiyar Izala ta jihar Gombe ta Shiryawa Musulmai masu yiwa kasa Hidima Seminar karkashin Shugaban Kungiyar ta Jiha Alhaji Salisu Muhammad Gombe. Dayake jawabi Shugaban Kungiyar yace sun Shirya Wannan taron karawa juna sani ne akan harkokin da'awa tayadda su zasucigaba da aikinsu, da yadda zasu kaucewa dukkanin al'amarin da zai zama kalubale gare su. Tare da bunkasa hanyoyin da'awa a tsakninsu da Al'ummar da suke da dama a kansu. Shugaban Kwamitin Shirya Seminar na Jihar Gombe Sheikh Dr. Rashid Abdulganiy ya bayyana cewa duba da yadda harkokin musulmai masuyiwa kasa Hidima yake gudana akwai bukatar wayar musu dakai ta fannoni da dama musamman fannin da'awa. Shugaban Musulmai masu yiwa kasa Hidima Malam Ibrahim Charanci, yayi Godiya tare da nuna farin cikinsa dangane da wannan seminar da Kungiya ta Shirya musu Lallai mun samu ilimi da zai taimakemu a rayuwa gabadaya Bama a fannin da'awa ba. Daga Karshe yayi godiya ga Shugaban tare da addu'ar Sakayyar Ubangi da falalarsa. Rahoto: Musa H. Musa

An Ginawa Matar Data Musulunta Gida A Katsina

Page 4: MUJALLAR SUNNAH DOMIN SANIN HALIN DA SUNNAH KE CIKI · Akwai yan uwa guda 4 da suka taimaka har wannan aiki ya kammala cikinsu akwai Alh Sadiq Ayuba Sullubawa wanda ya bada tasa gudumuwar

Sunnah News Nigeria –Shafi Domin Amfanuwar Musulmai

4

Wasu makiya Addinin Musulunci da ba a san ko su waye ba sun kai hari a Masallacin Juma'a na Cibiyar Yada Addinin musulunci da Al'adu ta garin Saffle da ke kudancin kasar Swidin. An farfasa gilasan Masallacin a yayin harin tare da jefa wasu abubuwan fashe wa cikin sa wanda suka lalata bangon cikin Masallacin. Shugaban Cibiyar Abdihakim Adan ya bayyana harin a matsayin abin tsoro. Adan ya ce, bayan farfasa gilasan da aka yi, abubuwan fashewar da aka jefa sun yi barna sosai, ya kara da cewa, akalla mutane 100 ne ke Sallah a Masallacin a kowacce rana. 'Yan sanda sun sanar da kammala binciken farko inda aka tsayar da zato kan cewa Masu kyamar Musulunci ne suka kai harin.

Wasu Makiya Musulunci Sun Kai hari a wani Masallacin Juma'a a

Kasar Swidin

Kotun Daukaka Kara Ta Soki Lamirin Umurnin

Shugaba Donald Trump Babbar kotun daukaka kara ta nan Amurka ta soki lamirin umurnin shugaba Trump Kotun tace umurnin hana wasu kasahen 6 wadanda yawancin su musulmai ne da shugaba Trump ya hana shigowa Amurka wannan ya wuce karfin ikon sa. Sai dai kotun tace zata dakatar da nata matsayin tukunna har sai abinda babban kotun kasa tace, wannan yana nufin umurnin zaici gaba da aiki har sai abinda babban kotu kasa ta yanke hukunci akai. A farkon wannan watan ne dai umurnin na shugaba Trump ya fara aiki. Amma tun wani lokaci can baya da yasa wa wannan umurnin

hannu a cikin watan farko na wannan shekarar mai karewa. Wannan batu ya jima yana kai komo har na kusan shekara guda, Wannan batu da gwamnatin ta Trump ta bullo dashi yayi karo da cikas tun a karon farko, wanda gwamnatin tace tayi ne da miyyar inganta tsaro.

Hukumar Kasar Saudiyya Ta Haramta Daukar Hoto A Yayin Ibada A Masallatan Madina Da Makka Hukumomin kasar Saudiyya sun fitar da sanarwa wadda ta hana masu daukar hotuna da kamara, bidiyo ko da wayoyin hannu a Masallacin Madina da Makkah. Idan har aka kama ka da saba ma wannan dokar akwai hukuncin da aka tanada. RIKO DA SUNNAH RIGAKAFIN CIWON BIDI’A SUNNAH HANTSI LEKA GIDAN KOWA

Saudia Ta Hana Daukar Hoto A Wajen Ibada

A wannan makon nan za’a daura auren biyu daga cikin maluman Sunnah da suke bada gudummuwar su wajen da’awar Sunnahr a Nigeria, Sheikh Abubakar Abdussalam (Baban Gwale) da Sheikh Dr. Jamilu Zarewa. A madadin Cibiyar Darulfikr.com da Sunnah News Nigeria muna mika sakon fatan alkhairi da neman fatan Allah ya bayar da zaman lafiya, ya kawo zuri’a ta gari Amin. @Basheer Sharfadi

SUNNAH NEWS NIGERIA –DOMIN AMFANUWAR MUSULMAI Ku biyo mu ta: http://sunnahnewsnigeria.wordpress.com http://facebook.com/sunnahnigeria.ng http://twitter.com/sunnahnigeria 09035830253, 08066989773, 08149332007, 08168015170

DAGA KASASHEN WAJE

Masallacin da aka kai harin

Sakon Taya Murna Na Musamman

Sunnah News Nigeria Zata Gabatar Da Gagarumar Bita Domin Taya Murnar Auren Mal. Abubakar Abdussalam (Baban Gwale) kayi kokari kada ka sake a baka labari.

Bitar ta hada da Kwararru a shafukan sadarwa, Lauyoyi daga bangaren shari’a, Jami’an kiwon lafiya da kuma Maluman Addini, domin karin bayani sai a kira: 09035830253, 08149332007, 08149342004

Yaki Da Cin Hanci: Saudiyya Ta Saki Mutane

23 Daga Cikin Wadanda Ta Kama

Gwamnatin Masarautar Saudiyya ta saki mutane 23 bayan cimma

wata yarjejeniya, wadanda na daga cikin manyan mutane kusan

200 da Yariman Kasar Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman

ya sa aka kama saboda zargin cin hanci da rashawa da ake musu.

Rahotanni sun ce, ana sa ran sakin sauran mutanen a kwanaki

masu zuwa.

Kafar yada labarai ta Saudiyya ce ta sanar da labarin sakin

mutanen su 23, kuma a nan gaba za a ci gaba da sakin duk

wadanda aka amince da su kan yarjejeniya da gwamnati.

Daga cikin wadanda aka kama kuma aka yi ikirarin suna shan

wahala a otel din Ritz-Carlton da ke birnin Riyadh har da Yarima

Walid bin Talal, wasu Yarimomi 11 da ministoci 4.

Jaridar Okaz ta bayyana cewa, an saki mutanen da aka kama a

watan nuwamba bayan sun amince su mika dukiyarsu da suka

mallaka ga gwamnatin Saudiyya.

An kama mıutanen ne dai sakamakon zargin cin hanci da

rashawawanda gwamnatin Saudiyya ta ce ya janyo asarar sama da

dala biliyan 100 ga kasar.